FARASHIN IZZAH

Chapter 17

by @hauwajaywrites

Kitchen ɗin gaba ɗaya ya ɗauki ƙamshin girkinta mai daɗi. Farida na tsaye tana miyan kayan lambu yayin da Zahra ke haɗa spicy jollof rice ɗin da ta dafa da chicken mai dadi, Gefe kuma akwai fried meat da salad da suka haɗa cheffing dish


“Wallahi Hajiya kin iya girki,” Farida tace tana murmushi.


Zahra ta ɗan yi dariya.

“Da gaske?”


“Eh mana, tun da na fara jin ƙamshin shikenan na fara ji yunwa.”


“Ke dai bari kawai,” Zahra tace tana ɗan motsa cokalin hannunta. “Maman Oga tana son abinci mai ɗan haɗi ne shiyasa nace bari muyi abin kirki.”


“Toh ai zata ji daɗi sosai.”


Bayan sun gama komai, suka fara zubawa a warmers masu kyau. Zahra na gyara yadda komai zai yi neat cikin basket ɗin.


“Wannan salad ɗin ki saka a gefe.” Cewar Zarah


“Toh Hajiya.”


“Kar chicken ɗin ya zube fa.”


Dariya Farida tayi.

“Toh.”


Bayan sun gama jera komai cikin basket mai kyau, Zahra ta sauke numfashi tana kallon abincin.


“Alhamdulillah.”


Farida tace,

“Hajiya ki tafi ki shirya yanzu, ni zan gyara kitchen.”


“Kin gaji fah” inji Zahra


“A’a wallahi.”


Murmushi Zahra tayi sannan ta juya ta fita, haurawa sama tayi 


Tana shiga ɗakinta ta samu Ibrahim zaune bakin gado yana duba wayarsa. Ya ɗaga kai suka haɗa ido, kallonta kawai ya tsaya yi.


“Me?” Zahra tace tana murmushi kaɗan.


“Kin ƙara kyau ne ko ido nane”


Dariya tayi tana cire hijab ɗinta.

“Ka bari Noory.”


Ya miƙe ya ƙaraso kusa da ita.

“An gama girkin?”


“Eh.”


“Hmm… Zahra matar aure.”


Ta tura shi kaɗan tana dariya.

“Please bari nayi wanka.”


“Toh madam.”


Toilet ta shiga. Ruwa mai ɗumi ta kunna tana jin gajiyar jikinta na sauka a hankali. Bayan ta gama ta fito jikinta na ƙamshin gel tare da kamshin turaren wanka


Wani dogon gown mai matuƙar kyau ta saka, colour ɗin wine mai ɗan haske, hannayensa cike da stones masu kyalli. Veil ɗinta kuwa ya yi matching da kayan. Ta tsaya gaban mirror tana ɗan gyara lips ɗinta.

 

A baya Ibrahim ya tsaya yana kallonta ta mirror.


“Zahra…”


“Hmm?”


“Kin sani ko? Duk lokacin da kika shirya haka bana son fita da ke saboda kowa sai ya tsaya kallon matata.”


Ta ɗan cije lips ɗinta tana murmushi.

“Drama king.”


Shi ma ya shirya cikin wata black native mai matuƙar kyau. Agogon hannunsa da turarensa suka ƙara fito da ƙyansa sosai.


Bayan sun gama, suka fito tare.


A parlorn ƙasa Ibrahim ne ya ɗauki basket ɗin warmers ɗin. Zahra ta kalleshi tace,


“Bari na ɗauka mana.”


“Karki damu.”


Suka fito tare har zuwa wajen motar, suka shiga, Ibrahim ya kunna wata soft love song mai sanyin gaske.


A hankali motar ke tafiya yayin da song ɗin ke tashi.


Zahra ta jingina kanta jikin seat tana kallon waje, Ibrahim kuma lokaci zuwa lokaci yana kallonta yana murmushi.


“Me kuma?” tace bayan ta kamashi yana kallo.


“Nothing… ina kallon matata ne kawai.”


Ta ɗan kau da kai tana murmushi.


Haka suka isa gidan Mama.


A compound Ibrahim yayi parking. Ya fito ya zagaya ya buɗe mata ƙofa. Ita kuma ta sauko a hankali yayin da shi ya ɗauki basket ɗin warmers ɗin.


Tare suka shiga ciki.


Suna shiga kuwa suka haɗu da Mama, shigowarta kenan daga backyard . Tsayawa tayi tana kallonsu, musamman basket ɗin dake hannun Ibrahim.


“To oo…” tace tana ɗan ɗaga gira. “Yanzu Ibrahim kai ne da ɗaukar basket? Ko dai dama da gaske ne abinda naji?”


Nan take Zahra taji wani iri a ranta, ta ɗan sunkuyar da kai.


Ibrahim ma wani iri yaji, amma sai yayi saurin cewa,

“Haba Mama ai kinsan Zahra ba lafiya take da shi ba”


Sai Mama tayi murmushi irin na manya.

“Toh ku shigo mana, kun tsaya a bakin ƙofa.”


“Ai Mama ke kika tsayar da mu,” Ibrahim ya amsa.


Shiga suka yi.


Zahra ta zauna a parlorn tana jin kanta not comfortable kwata-kwata. Ita kanta batasan dalilin da yasa maganar ta tsaya mata a rai haka ba.


Ibrahim kuwa dining ya wuce ya ajiye basket ɗin.


Yana juyowa zuciyarsa ta ɗan cunkushe. Haka kawai yaji bai so abin da Mama tayi ba. Musamman ganin yadda fuskar Zahra ta canza a take.


A parlorn suka zauna tare da Mama suna hira lokaci zuwa lokaci. Mama ta tambayi Zahra ya jikinta, ya makaranta, ita kuma tana amsawa cikin ladabi duk da zuciyarta bata gama sakin jiki ba.


Ibrahim kuwa ya lura da canjin Zahra tun bayan maganar basket ɗin, yasan pretending take yi wajen faking murmushi, shiyasa lokaci zuwa lokaci yana kallonta idan Mama bata kula ba.


Har aka kira sallar magrib suna gidan. Ibrahim ya tashi ya tafi masallaci, bayan ya dawo sannan suka dawo parlorn suka ci abincin da Zahra ta kawo. Mama ma ta yaba sosai da girkin.


“Zahra kin iya girki sosai,” Mama tace tana ɗan ɗiba miyan.


Murmushi kawai Zahra tayi.

“Nagode Mama.”


A haka suka gama dinner. Bayan sun ɗan zauna kuma, suka yi wa Mama sallama.


“Allah ya kai ku lafiya,” Mama tace.


“Ameen,” suka amsa tare.


A cikin mota kuwa daga Zahra har Ibrahim babu wanda yace komai. Song ɗin da aka kunna ma a hankali yake tashi amma dukansu suna cikin nasu tunanin.


Ibrahim ya ɗan kalleta sau biyu amma bata ɗago ba.


Sai kawai ya juya steering ya tsaya a wani eatery mai kyau.


Ta ɗan kalleshi.

“Me kuma?”


“Mu ci abinci.”


“Ai mun ci a gidan Mama.”


“Still…”


Bata ƙara magana ba suka shiga ciki.


Wajen ya yi sanyi da haske mai kyau. Suka zauna a wani corner mai nutsuwa sannan suka yi order.


Zahra ta ɗauki noodles da chicken, shi kuma ya ɗauki burger da drink.


Duk da suna cin abinci ne, akwai wani irin shiru tsakanin su.


A ƙarshe Ibrahim ya sauke spoon ɗinsa yace,

“Zahra…”


Ta ɗago tana kallonsa.


“I’m sorry.”


Shiru tayi.


“Ban so yadda Mama tayi magana ɗazun ba.”


“Ai babu komai,” ta amsa a hankali.


“Da gaske?”


Kai ta gyada masa.

“Please kar ka damu.”


Yadda tayi maganar yasa ya ɗan sake.


A hankali ya kamo hannunta saman table ɗin.

“Thank you.”


Ta ɗan murmusa masa.

“Ka daina wannan worried face ɗin.”


Daga haka ya ɗan saki jiki suka fara hira kaɗan-kaɗan. Har dariya Zahra tayi lokacin da Ibrahim ya fara bata labarin wani abu da ya faru a office.


Da suka fito daga eatery ɗin, yanayin dake tsakaninsu ya ɗan lafa.


A mota ma Ibrahim ya riƙe hannunta yana driving da hannu ɗaya. Ita kuma duk da zuciyarta bata gama warkewa ba, tayi ƙoƙarin nuna masa komai lafiya ne saboda taga ya damu sosai.


Da suka isa gida, Ibrahim ya wuce toilet domin yayi wanka. Ita kuma Zahra kitchen ta tsaya tana duba wasu abubuwa kafin daga baya ta haura sama.


Tana shiga ɗakin, idanunta suka sauka kan wayarsa dake gefe tana ringing.


Sunan da aka yi saving ɗin number ɗin yasa gabanta ya faɗi.


“Lovie Dovie…”


Wani irin abu taji ya tsinka mata zuciya.


Wayar ta daina ringing.


Sai kuma wani call ɗin ya sake shigowa.


Kafafuwanta kamar sun manne a wajen.


Har ta matsa zata ɗauki wayar… sai kuma ta fasa.


Wani irin zafi taji a zuciyarta.


Jin motsin Ibrahim zai fito yasa ta bar wajen da sauri. Gaba ɗaya mood ɗinta ya canza.


Kai tsaye toilet ta shiga itama dan tayi wanka ba tare data sake kallon inda wayar take ba.


Bayan ta fito tana saka kaya, Ibrahim kuma yana gyara sleeve ɗin kayansa a mirror.


Sai kuma wayar ta sake ringing.


A wannan karon Zahra ta sace kallon wajen.


Shi ma Ibrahim ɗin ya ɗaga kai ya kalli wayar.