Chapter 2
by @mras
KADDARA TACE 1~2😔
LITTAFIN WATA YARINYA DA ALJANU SUKA SHIGE TA!👺☠️
LITTAFIN YANA DAUKE DA DARRUSA MASU YAWA A CIKI!
AKWAI ILMANTARWA!
DA KUMA NISHADANTARWA!!
BUGU DA KARI TANA DAUKE DA KYAYATACCEN SOYAYYA A CIKI….👇🏾👇🏾👇🏾
DAGA ALKAMIN @Mr AS…✍🏼
True life story…..👇🏾👇🏾👇🏾
PAGE 📄 2
بسم الله الرحمن الرحيم
Alaramma ne ya mike ya sake cewa qubra “ Allah uban giji ya dauke maki wanga ciwo qubra”
Har ya nufi kofa zai fita yaji qubra tace “ toh ameen dai amma ni ina ga Ai wannan ciwon KADDARA TACE rabuwa da ita saidai Kilan lahira”
Da sauri alaramma ya juyo baya yace: “ Subhanallah, Haba qubra kada ki karaya mana, Rahman Allah da yawa take a kullun takan iya shafen Bawa, kisa ma ranki a koda yaushe Kina iya rabuwa da wannan ciwo….”
“Yaushe? Alaramma sai yaushe?”
Yaji qubra ta katse shi tana mai zubar da hawaye masu cin rai.
“ Bazan ce maki ga ranar ba Amma nasan Karfin Allah yafi na Aljanu domin shine ya ara masu dama suke abinda suke so kuma a koda yaushe yana iya ansan wannan karfin da daman da ya basu”
Yadan matso kusa da ita yace:“kuma Kinga yayar ki HAMIDA ita ma Ada tana da wannan iriyar lalura Amma tunda tayi aure shikenan basu kara damun taba”
Ya kare maganar yana kallan innah dake tsaye akan su yace: “ koh innah?”
Innah tace: “ kwarai kuwa kamar ma bata taba ciwon ba” .
Qubra ta girgiza kai hawaye na kara zuba ta kumatun ta tace: “ yo innah auran ma ina alamun sa?
Sun hana ni aure
Sun hana ni karatu
Sun hana ni walwala
Sun hana ni nayi rayuwa kamar yadda ko wacce ya’macce keyi,
Duk saurayin da nayi sai ya guje ni ta dalilin wannan ciwon, yanzu ko Kabiru da muke soyayya dashi na tabbata bai San da ciwon nan ba sbd kabiru akwai shi da tsoro matuka Balle abinda ya shafi jinnu.”
Ta karashe maganar tana fashewa da kuka mai cin rai.
Daidai lokacin da zakiya ta shigo dauke da plate a hannun ta, ta ijiye a gaban qubra ta fita ko minti daya ba ayi ba ta kara shigowa da pure water 💦 guda biyu a hannun ta.
Zakiya ta zauna dab da qubra tare da jawo ta jikin ta tana rarrashin ta tace:
“Anty Dan Allah kiyi hankuri ya isa hakan kici abinci dan Allah ko so kike nima nayi kukan.?”
Qubra tayi saurin share hawayen ta tana girgiza Kai tace: “ A’a kar kiyi kuka idan ba so kike na shake ki kamar yadda na shake alaramma ba”
Ta karasa maganar cikin tsokana tana kallan alaramma da ya gwalo ido waje yace:
“ Haba qubra kenan da gan gan kika shake ni?”
Qubra tana dariya tace: “Haba alaramma Wallahi ni ban ma San meke faruwa ba, gani nai tun dazun kana ta faman rike wuya”
ta karashe maganar tana nuna wiyar shi wanda har a lokacin yana rike da ita sbd gaskiya har yanzu yana Jin zafi a wajan.
Dariyar shima alaramma yayi kana ya fice Daga dakin.
Zakiya ce ta kara maso mata da plate din tace: “ Anty kici abinci, bara naje na sawo maki Kati, Saboda dazun naga Abdul ya kira ki” ta mike kafin ta kara cewa: “ki cinye duka fa Anty”
Anty qubra ce tayi ajiyar zuciya a ranta tace “Allah sarki abdul yadda yake damuwa dani ko kabiru da muke soyayya bai damu Dani hakan ba” sai kuma tayi saurin magana a fili tace “to Ina wayar ma” Bayan ta dan zuba taliyar a bakin ta.
“Gata nan Anty sai kin cinye duka abinci tukun” zakiya ta bata amsa tana ficewa dakin da sauri.
Anty ta girgiza Kai tana murmushi “Allah ya bar minke zakiya” ta fada a ranta tana cigaba da cin taliyar.
PLZ KUYI HANKURI DA WANNAN 😂🙏🏼 MU HADU A NEXT PAGE 📄……. 🙏🏼
KUYI COMMENTS DA SHARE SBD YAN UWA SU AMFANA PLZ…..😊🤲🏽🤲🏽
Daga Alkalamin Mr AS…..✍🏼
🌟…..الحمد الله رب العلمين