KADDARA TACE 😔

Chapter 1

by @mras

KADDARA TACE 1~1😔


LITTAFIN WATA YARINYA DA ALJANU SUKA SHIGE TA!👺☠️


LITTAFIN YANA DAUKE DA DARRUSA MASU YAWA A CIKI!


AKWAI ILMANTARWA!

DA KUMA NISHADANTARWA!!


BUGU DA KARI TANA DAUKE DA KYAYATACCEN SOYAYYA A CIKI….👇🏾👇🏾👇🏾


DAGA ALKAMIN @Mr AS…✍🏼


❌⚠️ GARGADI⚠️ 

IDAN KIN SAN KINA DA ISKA 👺KO BAKI SON ABINDA SHAFI JINNU☠️ TO KARKI KARANTA


🗣🤲🏽KARIN BAYANI🤲🏽🗣

IDAN KUN GA NA RUBUTA ADDU’A  KADA KU SALLAKE TA KOMIN YAWAN TA SABODA NEMAN KARIYA WAJAN UBAN GIJI.  S’W’A🤲🏽🤲🏽


True life story….👇🏾👇🏾👇🏾


PAGE 📄 1

بسم الله الرحمن الرحيم 


Zakiya! zakiya!! zakiya !!!

  Wata  mata wacce akalla zata Kai shekaru 38 zuwa 40 ta fito Daga daki a gigice, kallo daya zaka mata kasan tana cikin tashin hankali sosai, saiga wata yarinya yar kimanin shekara 17 ta nufo ta da gudu tana fadin “INNAH lafiya kuwa..?”

 Da sauri innah ta katse ta da fadin “maza je ki kirawo alaramma jikin QUBRA ya Kara tashi”, 

Zakiya ta juya jikin ta ba kuzari daman tasan za’arina, sbd daga Jin yadda innah ke kwala mata kira tayi tunani ciwon qubra ne…. “Kiyi gudu mana”  Zakiya taji innah ta katse mata guntun tunanin ta. Sauran almajirai mata dake Zaune cikin tsakar gidan kuwa Wasu na koma wa dakin su yayin da Wasu kuma ke lekan dakin da qubra take kwance sai faman ihuu take tayi hade da birgima Wasu matan kuma ko aji kin su kamar basu san abinda ke faruwa ba, ba kuma don basu sanin bane A’a saidan kawai inda sabo sun saba gani Indai lalurar qubra ce.

****

Alaramma ne ya shigo dakin tare da sallama hannun sa dauke da al~qur’ani mai girma a Bayan sa kuma zakiya ce tare da wasu mazan su biyu.


QUR’ANIn ya bude ya fara karanta suratul~jinn yana yi yana Daga murya,

 Amma mai makon abin yayi sauki kawai sai gani sukai ta tashi Zirr a tsaye ta fara Wani lankwasa kamar wata macijiya tana Wani huci mai kararaji saida duka dakin ya amsa, anan mazan suka so su rike ta alaramma ya daga masu hannu alamar su kyale ta yana cigaba da karatun,

 Chan sai ta tsaya da laudin da take yi tana kallon alaramma da Idon ta wanda ya kada ya chanza launi zuwa kore kore tana Wani kalar gurnani daidai lokacin da alaramma yay mata tofi a fuskar ta Habaa aiko kamar tana jira….

 kachaff ta shake wuyan alaramma tana wani ihuu mai hade da kuka.

Ganin haka yasa matan dakin suka ruga a waje ciki ko harda innah, 

dakin ya rage maza biyun nan wanda suma Banda rawar dari ba abinda suke yi sai alaramma dake kokarin sumewa sakamakon irin kamun da qubra tayi wa wiyan sa, tun yana dukan hannun ta tare da kokarin zamewa har ya kasa yanzu ko motsin Kirki  ma bai yi..

Qubra ce ta daga alaramma sama tare dayin wata kalan ihuu cikin Wani irin katon murya wanda har saida dayan na mijin ya saki wata iriyar zawo a Wando, dayan kuma ya juya zai ruga da guda kawai ta damko shi da dayan hannun ta tana fito da halshan ta waje kamar maiya…..

 “Innalillahi wa Innalillahi raju’un innahu sulaimanu wa inna.. hu sulaim..anu laa’ilaha ilallahu laaa….“

haka dai yai ta fadin dun addu’ar da tazo bakin sa…


******

Daidai lokacin da Wani Dattijo mai kimanin shekaru 50 ya fito a dayan dakin dake manne da dakin da suke wanda Duk abinda ke faruwa yana ji Amma sai yanzu yake fitowa fuskar sa a daure tamkar bai taba dariya a rayuwar saba،


yana zuwa kofar dakin da suke ko shiga ciki bai yi ba Daga nan kofar dakin ya tsaya ya daka wa qubra tsawa yace: “kaiiii kana damun mu”


Aiko kawai sai qubra ta fadi kasa kamar wacce ta suma.. saiga alaramma kasa dimm yana numfashi sama sama! 

Wannan Dattijon ko kara bi ta kansu bai yi ba ya koma dakin sa.

Innah ce ta dawo domin dama ita ba Nisa tayi ba tana ma alaramma sannu, alaramma yadan samu da kyar dai ya zauna yana Kara dauko qur’anin sa yadan masa kadan inda qubra ke kwance ya fara karutu domin kuwa yasan har yanzu mutanan ta suna nan basu koma ba.. ya kwashe mintuna kamar ashirin yana karatu kafin ya fara Jin muryan qubra tana kuka Chan kasa kasa da muryar ta na asali yadan dakata da karatun yana kallan ta kafin ya kira sunan ta -‘’QUBRA 

  • “Na’am 
  • “Kece
  • “A’a kaine”.  ta fada tana Dan jefo masa harara tare da share kollan dake a fuskar ta kawai sai ta mike zaune tana kallon su…Alaramma yadan yi wata doguwar ajiyar Zuciya sannan yace mata “ sannu kinji” tare da sakar mata murmushi mai dauke da tausaya mata…. 


Innah ce ta kalli saurayin  dake shirin fita tace: “Kai mansur badai kashi kayi a Wando ba”


Wanda innah ta kira da mansur ne yadan Kara notse fuskar shi tare da nuna Anty qubra yace: 

     “Ba Anty qubra bace muguwar da ta haifar da kome ba”


Duka dakin dariya suka yi HARDA Anty qubran kafin tace:”dallah masa Chan masoraci kawai mutumin banza” tana mai daura dan kwalin ta.

To me nace mani mutumin banza…? Taji mansur ya jego mata tambaya.

  Innah ce tadan yi dariya kafin tace: ” Haba mansur tobashiyar kace fa”

  Mansur yace “ yo shi yasa zata sani yin kashi a Wando” yana hararan Anty qubra.


Qubra ce ta fadada fuskar ta da murmushi tace “ innah yunwa nake ji.

Innah tace “to Bari a kawo maki abinci ” 

Ta juya wajan zakiya tace mata “jeki kitchen ki zubo taliyar nan” 

Zakiya ta fita, dama tun lokacin da mutanan ta suka taso innah tasa ta dafa taliya sbd a duk lokacin da ciwon ta ya tashi to dazaran ta dawo hayyacin ta zata naimi abinci sbd da yunwa zata farka.


PLZ KUYI HANKURI DA WANNAN 😂🙏🏼 MU HADU A NEXT PAGE 📄…….🙏🏼


KUYI COMMENTS DA SHARE SBD YAN UWA SU AMFANA PLZ…..😊🤲🏽🤲🏽

Daga Alkalamin Mr AS…..✍🏼


🌟…..الحمد الله رب العلمين