BARRISTER SUHAIL

BARRISTER SUHAIL

by @officialkhadeey

🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾

Mallakar

KHADIJA WRITES

YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION
(YOTA)


💖 Dedicated To My Mom 💖


بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

🅿️----15

Aunty zaituna ta kalli Ammi cikin tausayi ko a faɗa tasan tana tunanin akan abinda Naima tayi ne

“yaya lafiya kuwa?”

ɗago jajayen idanunta Ammi tayi ta sauke ajiyar zuciya tana kallon aunty zaituna

“Wallahi zuciyata babu daɗi zaituna…”

Gefenta aunty zaituna ta zauna.
“Saboda yarinyar nan ko ?"

Kai Ammi ta jinjina.

“Tun shigowar su nake kallon yadda take kallon wajen nan tamkar ta raina mu…wallahi tsoro nake ji kada Iman ta shiga gidan da za’a riƙa wulaƙanta ta kiga abinda wannan Yarinyar tayi mana"

Aunty zaituna ta dafa hannunta.
“Haba yaya kar ki saka wa ranki tunani ai ba ita zata zauna da Iman ba kuma ai da sauran zakiyi la'akari yadda suka nuna mana girmamawa"

Ammi ta share hawayen da suka cika idanunta.
“kinsan halin Iman sarai yarinya ce mai sanyin hali da haƙuri ina tsoro kada mutanen nan  suyi anfani da hakan su takura mata"

Murmushi aunty zaituna tayi ta ce"idan har mijin ta na santa bazai bada kofar da za'a wulakanta masa mata ba"

tashi tayi ta ce"bari na shigo da kayan ciki wai ina iman suka shiga da hafsat ne"

Ammi ta ce"Sun fita da Mubarak kasuwa"

Yau ta kama jumma'ah a yaune za a daura Auren Suhail hidima ake babu kama hannun yaro gidan Alhaji munnir ya cika tab da baƙin nesa da kuma na kusa ciki harda kannesa bahijja dake aure a kano tare da iyalan ta kaf sun sauka a garin kaduna.

Tukwanen abincin kawai ake saukewa ana dorawa wanda duk aunty Fauziya ce tsaye komai mami tayi kwance a daki duk wanda yayi mata magana sai ta ce ai bata da lafiya duk A'isha ke kula da nata ɓangaren da Zarah

gidan malan ma tun da safe ya dauki harama ya cika da mutanen arziki sai hada hada ake tun safe iman ke kwance a ɗakin Ammi taƙi fitowa har wajen karfe sha biyu sai bacci take.

hafsat ce ta shigo gidan ta dawo daga amso musu dinki ita da Aunty zaituna a kofar daki ta ga Ammi ta ce"ina Iman"

Ammi ta ce"tana ciki"

Iman ce kwance aka gadon Ammi sai baccin take kwasa hankali kwance ayi mata kanannun kitso wanda jelar gashin ya sauko har gadon bayan ta an zane mata hannun nan tas da ja da bakin lalle.

Hafsat ta ce"wai bazaki tashi ki shirya ba mai kwalliyar fa tana hanya"

turo baƙi tayo ta ce"ke nifa babu wanda zaiyi min wata kwalliya"

ran hafsat ya baci ganin yadda take kwance kamar ba Ranar bikin ta ba tashi tayi ta ce"bari naje na fadawa maman"

wajen aunty zaituna ta koma ta faɗa mata abinda ke faruwa tare suka dawo dakin.

Aunty zaituna ta ce"iman miye haka tun dazu fa na tashe ki ki yi wanka mai make up tana hanya kinsan sarai basu san bata lokaci"

hade rai tayi ta ce"Aunty yanzu fa zan tashi"

sauka tayi daga kan gadon ta daura towel ta shiga bathroom din Ammi dake cikin dakin ba wani lokaci mai yawa dauka ba ta fito ta fara shafa kenan Hafsat ta shigo tare da mai make up ba bata lokaci aka fara mata.

Ya salam!! shine abinda hafsat ta ce ganin yadda kwaliya ta zauna a fuskar iman tayi matuƙar yi mata kyau ta fito sak a amarya ita kanta mai kwaliyar ta yaɓa kyan da iman tayi dan ta jima batayi kwalliyar data birge ta haka ba cikin zolaya take fadawa iman"gaskiya angon nan sai ya karamin min kudi"

Hafsat ta ce"gaskiya kam irin wannan kyaun haka"

kayan da aunty zaituna ta ajiye ta dauka wani golden Ash din lace ne anyi mata dinkin staright gown daidai jikin ta da mayafin har kasa ta saka komi yayi mata dass a jikin ta.

Karfe biyu rana dubbanin Al'ummar suka shaida daurin auren Suhail munnir Mahmud tare da Amarya khadija iman Abdallah a masallacin Sultan bello dake garin kaduna bayan sallar juma'a.


Mayan mutane da malamai suka hallarci daurin auren bayan samun gayyata daga malan da kuma Alhaji munnir.

Suhail ne sanye da farar babar gida shida Sameer a gefe guda tare da abokan su Abban kuma na bakin masallacin yana gaisawa da mutane tare da amsa fatan alheri da kowa keyi masa

fuskar Suhail ba yabo ba fallasa ko magana ba ya iyayi Sameer ke ji da mutanen kallo ɗaya zaka mishi ka tabbatar baya cikin walwala

sai da kowa ya watse suka kama hanyar gida hostel Suhail ya kama ya  kwanta da baya ma san komawa gidan  su .

ko wani bangare aci an sha karfe 8 na dare Motocin daukar amarya suka faka kofar gidan Malan Iman na zaune a dakin ta tare da ƙawayen aunty zaituna ta kamo hannunta zuwan dakin ammi.

ganin da gaske tafiya zatayi ta bar Ammin ta faɗa jikin ta riƙe gam ta cusa fuskar cikin jikin Ammi ta fashe da kuka a wannan karin Ammi ta ƙasa daure ganin ita ta fashe da kukan aka rasa wanda zai ba wani haƙuri ɗaya daga cikin yan uwan malan  ta raba Iman daga jikin Ammi ta ce "haba Maryama nasiha zakiyi mata ba kuka"

Ammi ta girgiza kai cikin kuka ta ce"Iman babu abinda zan ce maki nasan kina da hakuri amman ki kara kan wanda nasan ki dashi Allah yayi miki albarka ya zaunar dake lafiya a gidan ki"

Yayar malan da aunty zaituna suka fito da ita zuwa Dakin malan Nasiha yayi mata mai ratsa jiki wanda ko wani mahaifi ya kamata yayi wa diyar sa ranar auren ta haka malan yayi iman tare da bata wasu addu'a da ya kamata ta rinƙa domin kawar da shaidan a zamantakewar aure"

nan aka fito da ita zuwa cikin motar da dangin anguna suka kawo Mutane yan kadan aka diba kamar yadda aunty zaituna ta bada umarni.

aka kama Hanyar gidan Suhail dake melenium city daya daga cikin gidanjen abba ne ya mallaka masa kafin ya kara sa nashi.

IDAN NA SAMU 200 LIKES ZAN RINKA SAKAR MUKU 2 PAGES KULLLIN