GADAR GIWA... (Toro ke buga mata ganga)

*🪻GAƊAR GIWA...🪻*

by @auntyindo

Ba musu Isma'il ya rufa mata baya suka rankaya inda Motarsa take.

Hamdan kuwa bai san lokacin da wasu siraran hawaye suka fara bin kumatunsa ba.
yana kallo Hibba ta shige Motar wani ta bar shi tsaye, Matan wajen na ta gulmarsa.

A ɗaya ɓangaren kuwa murmushi Ismail ya saki gami  da cewa "Ƴan magana kan ce Abin da ya koro Ɓera daga rami ya faɗa wuta.(ya fi wutar zafi)"  ya ɗan murmusa sannan ya ɗora da cewa "Bayan na ɗebi lokaci ina Barar ki shiga Motata ban yi sa'a ba, sai gashi yau wani daban ya sa kin yi hakan!"
murmusawa ta yi ta ce "Shi ne har da gaya min magana saboda na shigo Motarka?" 
 "A'a Rankiyadaɗe a yi haƙuri Allah ya huci zuciyarki, kawai dai na yi mamaki ne,   ko zan iya sanin waye shi?"

 "Kenan hakan ma sai ka tambaya, ko ba  ka kalle shi ba ne?"    "Na kalle shi kuma tabbas na ga kama, cousin ɗinki ne kenan!, kuma mai yin fadanci don neman  zama Dakare ga Sarauniya Hibba ko?"
   "Ita ma dai wannan tambayar a bayyane take kuma ka san amsarta!"   Ƴar dariya ya yi kafin ya ce "Oh Sarauniya ta amsa da Eh,   amma yanzu waye Gwarzon Tsakanin ni da shi?"  

Numfasawa ta yi gami da lumshe  idanunta ta yi ɗan jim!! sannan ta buɗe, cikin nutsuwa ta ce "Tsarina mai sauƙi ne, amma yana da tsauri ga wasu, ni ban yarda  da ƙarya ba, ba na son yi kuma ba na son a yi min, ban yarda in yi wa Mutum ƙarya don ya yi farin ciki ba, don ko babu haɗuwa da Allah wataran idan Mutum ya gane gaskiyar  zai ji ciwo a lokacin fiye da gaya masa ita tun farko,  hallau ni ban yarda da Yaudara ba, kuma babu rufe-rufe a cikin lamarina!"  da sauri ya tari numfashinta da cewa "Na fahimci hakan tun ba yau ba, kuma yana daga cikin abubuwan da suke ƙara tunzura ni kan Ƙaunarki"

  "Na ji daɗi da ka fahimta!"   shiru  ne ya ratsa tsakani na wucin gadi kafin ta cigaba da cewa "Har kawo yanzu ban ji ina son kowa ba duk Duniyar nan, kuma ba zan yiwa Ƙaddarata yankan hanzari ba, zan cigaba da sauraren ta!" 
  Isma'il ya numfasa cike da ƙoƙarin danne damuwarsa ya ce "Amma kuma na hangi matuƙar Tasirin wancan Bawan Allahn a tare da ke, ban sani ba ko kin fahimci hakan?" 
"Ba zan ce a'a ba , amma ban tabbatar ba, maybe sai na nutsu zan gane gaskiyarka,   zan cigaba da saurarar zuciyata da kuma alƙaluman ƙaddarata har zuwa lokacin da zan gane abin da  suka zaɓa min,  ba wai ba na sonka ba ne! tabbas da son raina ne idan aka ba ni zaɓi tsakanin kai da kowane  namiji a Duniyar nan kai zan ɗauka, don ina da yaƙinin ko babu so zan yi farinciki a tare da kai,   ina ba ka haƙuri bisa jin wannan gaskiyar tawa, duk da tana da zafi na gwammace na faɗe ta!"

jinjina kai haɗi da  jan dogon numfashi ya yi, bai ƙara furta ko kalma ba har suka isa Unguwar su Hibba sannan ya ɗan kalle ta ya ce "Ina za mu yi?"   "Ba ka san Gidanmu ba kenan har yanzu?" ta yi tambayar tana ɗan murmushi   rausayar da kai ya yi ya ce "Eh! saboda ba ki ba da damar hakan ba, da na so zan iya bibiya, amma  na fi so   ki ba ni damar zuwa da kanki, kuma yau gashi ranar ta zo!"  Ɗan murmusawa ta yi kafin ta shiga kwatanta masa gidan.

  Suna isa ta yi masa sallama ta wuce shi ma ya san inda dare ya yi masa.
   Tunda ta gaisar da Maa-ma ta koma ta kwanta  tana saurarar wani ɗan zazzabi da yake ragargaje ta.
   "Hibba me ya faru ne?"  muryar " Maa-ma ta katse mata tunaninta,  "Ba komai!" ta faɗa a taƙaice , "Amma ba komai kika ƙi cin Abinci? kuma da an kalli fuskarki an san ba cikin nutsuwarki kike ba!"   "Da ma tun safe haka na tashi duk ba na jin daɗin Yau, gashi na gaji"      Maa-ma ta jinjina kai ta ce "To dai kar hakan ya hana ki cin Abinci, tashi ki ci ko kaɗan"   kai ta gyaɗa kafin ta miƙe ta nufi kitchen.

     Hamdan!
gefen Titi ya samu ya tsaya  don ba ya son komawa Gidan a dame shi da tambayoyi.
  Lumshe idanunsa ya yi tamkar mai bacci,  tunane-tunane yake barkatai har da wanda bai san asalin su ba,  yana hangen gaba yana hangen baya.
Kafin ka ce me! ciwon kai ya rufe shi, jikinsa ya ɗau zafi rau!.
A gefe guda wata zuciyar na gaya masa ya rabu  da Hibba  wata kuma tana gargaɗinsa da aikata hakan, wani sashin kuma na tambayar sa Idan da gaske Hibba tana son Ismail fa?..........

    Ya ɓata lokaci mai tsayi kafin ya samu ya ja jiki ya koma Gida.
   Waɗanda ya samu a Gidan daga maza har Mata duk ido suka bi shi da shi. 

Ba baƙon abu ba ne haɗe rai a wurinsa sai dai yanayin na yau yana da bambance-bambance tsakanin kullum,  gashi shi kuma irin Mutanen nan  ne masu wuyar Fassara saƙon kan fuskarsu.
   Yana gaida su Ammy ya wuce ɗakinsa ba tare da ya tsaya ba ta amsarta ba......

Isma'il
    Tun da suka rabu da Hibba sunan Allah yake maimaitawa yana tasbihi da istigfari.
  Sosai yake jin ƙuna  a Zuciyarsa, ga kuma hasashe da zuciyar ke yi masa wanda sun fi komai ɗaga masa hankali, don haka ya mayar da hankalinsa ga Ubangijinsa , ta haka ne kawai zai samu sauƙin Fargaba da tsoro Gami da Ƙuncin da suke damunsa.

  
  .......Kwana Biyu kenan Hibba ba ta ƙara komawa wajen aiki ba, sai yau hakan ma don Aunty Rahma ta dame ta  ne.

   Hamdan kuwa a Kwana biyun ba ranar da bai je neman ta ba sai a ce masa ba ta zo ba.

Ismail kam yakan kira ta  su ɗan gaisa ya ji lafiyarta.

      Kowannensu yana karɓar yanayi daidai nasa, babu wanda bai rame ba a cikin su ukun. Sai dai Hamdan duk ya fi su shiga Matsi.

Hibba kuwa yawan tunani shi ya sa duk ta fita daga hayyacinta.

A ɓangaren Isma'il  akwai tunani sai kuma Takaici da wani irin Ƙunci da bai san dalilin su ba,   duk irin shariyar da Hibba take yi masa a baya ta ƙi karɓar soyayyarsa bai taɓa shiga tashin hankali da ƙunci irin na yanzu da Hamdan ya kutso kai cikin rayuwarta ba................

     *BAYA........*

 Yau ta kasance ranar Biyar ga Sallah Ƙarama............

 Da daddare...........
 Hibba, Khalil, Maa-ma  suna zaune suna hira  Khalil da Hibba suna ba wa Maa-ma labarin Fitar da suka yi ganin gari suna ta Dariyar yadda suka gamu da Mutane iri daban-daban a Gidan Zoo, Garden's, Shop's, guraren Cin Abinci su shan Ice-cream......

     Lokaci guda Maa-ma ta yi musu shiru tare da buga tagumi, ga dukkan alamu ta tafi wata Duniyar.

 "Maa-ma! lafiya kuwa?"      Hibba ta tambaya,       ɗan murmushi ta yi ta ce "Kalli yadda Khalil yake ta rawar kai kamar bai taɓa zuwa ba!"   Hibba ta ɗan murmusa ta ce "To ai zuwan Sallah ya fi daɗi don a nan za ka ga Mutane  iri-iri wasu ma tsoro za su ba ka, wasu kuwa garin Dariya har sai ka yi tuntuɓe!"   ta ƙarasa maganar tana dariya.  Maa-ma ta ce "Shi ma Khalil ɗin ai duk sammakal, don zuwan nasa irin wannan yawon ai ba yawa, don ke ce mai kai shi kuma ba ki da lokaci!"   da sauri Khalil yace "Ai yanzu na girma sosai Maa-ma don dai ba kya son in je da kaina, amma wallahi zan iya zuwa kawai kuɗi Yaya za ta ba ni, Shekara ta Goma sha-shida fa!" 
   "To na Mazugal, Shabiyar dai!, ko ni ban fi Sha-shidan ba!"   Hibba ta faɗa tana doka masa harara,    "To ai na wuce Shabiyar tunda na ƙara watanni!"   "Watanni ko wata?,    bai fi wata ɗaya ko biyu ba ka ƙara akan shabiyar ɗin, kawai ka bari a shabiyar Malam,   gyambo uban son Ggirma!, ki ji fa Maa-ma!"  ta faɗa tana maida kallonta kan Maa-ma, ganin ta ƙara komawa tunanin ya sa Hibba ta ɓata rai ta ce "Wai me kike tunani Maa?"     ɗan nisawa ta yi ta ce "Ranar Bakwai ga Sallah za a yi taron Family na gidanmu, to sh......"  da sauri Hibba ta katse ta da cewa "Meye na tunanin su tun da ba zuwa za ki yi ba Maa? ki manta da su kawai"

   "Wannan magana ce da hankali ba zai ɗauka ba;,     ke ma ki manta da Khalil kin ji?   bar ta ni da nake raye,    ki Manta da Mahaifinki da ya rasu kin ji?"   Hibba ta yi Sororo tana kallon Maa'ma,   ta ma kasa gane ina maganar ta dosa, shin Gori ne ake yi mata  ko cin Fuska??...........


*Aunty INDO*