Chapter 3
by @mras
KADDARA TACE 1~3😔
LITTAFIN WATA YARINYA DA ALJANU SUKA SHIGE TA!👺☠️
LITTAFIN YANA DAUKE DA DARRUSA MASU YAWA A CIKI!
AKWAI ILMANTARWA!
DA KUMA NISHADANTARWA!!
BUGU DA KARI TANA DAUKE DA KYAYATACCEN SOYAYYA A CIKI….👇🏾👇🏾👇🏾
DAGA ALKAMIN @Mr AS…✍🏼
True life story….👇🏾👇🏾👇🏾
PAGE 📄 3
بسم الله الرحمن الرحيم
Wacece QUBRA ..?
Qubra ‘ya ce ga malam Mudai wanda asalin mutumin dosso ne a chan kasar Niger 🇳🇪
Iyayen Malam Mudai wato kakannin qubra, asalin su zabarmawa ne,
wato Alfa Musa da matar sa Khadija wacce ake ce mata Ainha .
Alfa Musa ‘ya ‘yan sa biyar mata hudu na miji daya wato
Rabi,bandado,zainabu,cisai sai autar su muhammadu wanda ake kira Mudai.
Sakamakon azamanin ilimi bai yalwan ta a Niger 🇳🇪 ba.
Alfa musa ya dauki Mudai da Kansa a lokacin Mudai yana da shekaru 6 ya Kawo shi anan kasarmu Nigeria 🇳🇬
Inda ya kawo shi wajan Babban malamin nan kuma shehi wato sheick Yusuf Ibn Abdulsalam wanda ake kira da shehu jauga anan birnin kebbi wato jagar kebbi state kenan.
lokacin da Alfa musa ya kawo Mudai wajan shehu jauga sai ya shaida wa shehu jauga akan ga dansa nan ya bar masa akan yana son ya sami ilimi mai yawan gaske kuma masu albarqa wanda kaf duniya zata yi alfahari dashi.
Sannan ya nanata wa Mudai akan ko shi ya mutu bai yarda Mudai yazo jana’izar sa ko ta’azziya ba idan bada yardan shehu jauga ba.
Atakaice dai ya bada Mudai.
Haka ko aka yi tun zuwan Mudai makarantar ko nace zawiyyan shehu jauga ki manin shekaru ashirin bai taba barin da sunan zuwa ganin gida ba.
Kuma sun saba zuwa fatawa har cikin kasar Niger 🇳🇪 din Saboda shima yanzu ya zama babban malami kuma na gaban goshin shehu jauga.
Sbd idan shehu jauga baya gari ko baya jin dadi to Mudai ke wakiltan sa.
Bayan Shekaru talatin da zuwan mudai Nigeria abubuwa da dama sun faru.
A ciki ko harda rasuwar mahaifin sa da kuma rasuwar malamin sa (shehu jauga) Sannan yabar zawiyan shehu jauga sakamakon daidaito da sabani da kiyayya karara da yaita fuskanta daga sauran almajiran shehu jauga,
dama Wasu Daga cikin ‘ya’yan shehu jauga, musamman mazan.
yayi aure wanda shehu jauga ne ya aura masa yarsa Wacce yafi so akaf ‘ya’yan sa mai suna Halima Amma kowa yana kiran ta INNAH.
Alhdulillah rayuwa tayi albarqa malam Mudai wanda yanzu ake kira BABA DATTIJO.
Ya gina nasa makarantar wacce tafi ta shehu jauga girma da yawan mutane domin shi harda matan aure ,
wadanda suke karatu a wajan matar sa innah yar shehu jauga anan cikin gidan sa,
Shima Dattijo gidan sa yana nan dai cikin birnin kebbi.
Amma kuma dudda haka bai daina zuwa zawiyar shehu jauga ba sbd hatta sallar Jumma’a a Chan yake yi.
Baba Dattijo Yayi fice ya shahara akaf fadin Africa asan shi, ban garan ilimi musamman wajan warkar da Mara sa lafiya kamar masu iska, ko kamun mayu, Kai harda mahaukata Dattijo yana warkar dasu cikin ikon ALLAHU.
Baba Dattijo yana da ‘ya’ya hudu 4
1~Yusuf mai sunan malamin sa wanda ake kira shaiku mai shekaru 30 wanda yanzu haka yayi aure shima har yana da 1 wato barhamu wanda har yanzu ke shan nono ,
2~Hamida wacce yanzu tana chan Abuja zaman aure.
3~Musa waton takwaran mahaifin sa, shekarun sa 23 wanda tun sanda aka yaye shi da wata daya ainha ta dauke shi yanzu suna Chan dosson ana kiran sa baba hanno,
4~Autar su mai shekaru 20 wacce ita kuma aka sa mata sunan ainha wato khadeejat, wannan ne yasa Kowa na gidan yara da manya suke kiran ta da Anty QUBRA.
Nasan da yawan ku zasu yi tambayar ita zakiya fa..?
Zakiya ba Yar Dattijo bace, asali ma ita ba bazabarma bace, iya yan ta nupawa ne suna zaune a garin bidda, Niger state.
Karatu ne iya yan ta suka kawo ta anan gidan Dattijo tun tana Yar shekara 6 har kawo yanzu da take da shekaru 17.
Saboda yadda suka shaku da anty qubra tun suna kanana har yanzu shi yasa koda ta sauke al’qurani mai girma innah ta nemi alfarma wajan iya yan ta su kyale mata ita domin ta dinga taimakawa anty qubra, ta dinga kuma raka ta aduk inda zata je saboda laluran ta.
Idan ba ka rayu a gidan Dattijo bane baza ka banbance‘ya’yan saba Saboda irin kyawkyawan alaka dake sakanin iyalan sa da almajiran sa.
Aunty Qubra ta taso da hazaka ga son karatu da ibada kusan itace Yar lelen baba Dattijo, wacce tun tana Yar shekara 8 take fama da lalurar iskah wato jinnu. 💀 kuma har yau abin yaki cinyewa saidai kullum yaita karuwa, Saboda yanzu data shiga bacin rai za su tashi.
Abinda yake daurewa Kowa Kai shine yadda aka San baba Dattijo wajan cire wa mutane iskah ko na shekara nawa ne!
Mutum ne wanda idan yana ruqi’a, to ko bai karanta aya sai Aljanu sun sauka…
Wani wajan ma daga yazo ko baiyi magana ba zaki ji sun lafa a dole sbd su karan kansu aljanun sun San shi suna kuma shakkan sa…..
Sai gashi ace wai Aljani ke wahalar da Yar lelen shi yadda yake so😏
Ya hana ta aure sbd a kabilan zabarmawa macce mai shekaru har ashirin ba aure gaskiya abin cecekuce ne akai……😔🤔
PLZ KUYI HANKURI DA WANNAN 😂🙏🏼 MU HADU A NEXT PAGE 📄……. 🙏🏼
KUYI COMMENTS DA SHARE SBD YAN UWA SU AMFANA PLZ…..😊🤲🏽🤲🏽
Daga Alkalamin Mr AS…..✍🏼
🌟…..الحمد الله رب العلمين