GADAR TSAUTSAYI 3
by @nusybee143
Page 3
A kaf cikin hotunan babu wanda aka yi a Nigeria,gaba ɗayansu daga ƙasashe ne kala-kala,wasu a Columbia,wasu a Mexico,wasu a Peru, wasu a Bolivia,wasu kuma a US
A nutse yake ƙare mata kallo cikin nutsuwa da nazari,har zuwa yanzu babu wanda ya san sunanta na gaskiya,a taƙaice ma, babu wanda ya san sunan nata, babu wanda ya san inda take, ballantana wani information game da rayuwarta
To amma kuma ai an san fuskarta,kuma tana shigowa ƙasar,to ya aka yi ta gagara kamawa?
Ko dai da gaske ne zarginsa ya tabbata akwai masu taimakonta a manyan ƙasar?
To idan hakane,a shugabanni kenan?
Kai a'a!ko da a ce a shugabanni ne dole watarana zata zo hannu,sai dai a ce bayan an kamo ta a sake ta
To me yasa ba'a taɓa kama ta ba? wayo ta fi mutane ne?ko dabararta ta fi ta mutane,ko ma dai yayane dai ƙwaƙwalwarta ai guda ɗaya ce,kuma sauran mutane ma haka, yadda take yin tunani take tserewa su ma haka za su iya yin tunani su bi ta har su ƙure mata gudu don kamo ta
Wani hotonta ya buɗe, wanda take santa da baƙaƙen kaya,ta juya baya,haruffan N.O.C.C.M. raɗau a bayanta, wannan hoton idan bai manta ba ta turo musu shi da kanta,inda ta tura musu da adireshin inda take,amma da suka je can ba su samu komai ba sai wata takarda da ta sake maimaita waɗannan haruffan,N.O.C.C.M, waɗanda har zuwa yanzu babu wanda ya san me suke nufi
Ɗan murmushi ya yi,a hankali ya ce"smart girl!
Ban taɓa ganin yarinyar da ta zubar da darajar jami'an tsaro ba sai ke,na jinjina miki,amma ina yi miki jajen lalacewar shirinki a duk lokacin da na waiwaye ki,kar ki bari na fara binki,don tabbas zan kama ki"ya mayar da computer ɗin ya rufe,ya miƙe a nutse ya fice daga ɗakin,kanshi q cushe,amma yana son ya yi tunanin ta inda zai fara cikin sauƙi
*UNKNOWN LOCATION*
Madaidaicin gida ne,flat mai 3 bedroom and parlour,sai dai haske bai wadace shi ba sosai
Fitowa ta yi daga ɗaya daga cikin ɗakunan gidan,shirye take cif cikin baƙaƙen hoodie riga da wandonta,a'a usual ta sanya scarp ɗinta, duk da cewa bai rufe dogon gashinta ba da aka gauraya shi da attachment kalar ja
Zama ta yi tana gyara takalminta samfurin sketchers,tana gamawa ta miƙe, maimakon ta nufi ƙofa sai ta daka tsalle ta kama garun gidan,babu ɓata lokaci ta haura, cikin nutsuwarta ta ƙarewa ko'ina kallo kafin ta dira,kai tsaye ta hau babur ɗinta samfurin bike,ta tayar ta bar wajen
Da wani tsananin gudu tamkar ba mace ba take tafiya,akan babur ɗin,ta yi amfani da wani handkerchief ta ɗaure rabin fuskarta
Da yan dabarunta ta kaucewa duk inda ta san da yan sanda har ta isa inda take son zuwa
Wajen ya fara shiga cikin jeji, ba tare da fargabar komai ba ta sauka a babur ɗin ta wuce cikin wajen
Ta yi ƴar doguwar tafiya kafin da ƙafa ta isa inda take fatan zuwa
Wani tsohon gida ne wanda ya fara rushewa ma, sannan ya shiga surƙuƙi da yawa,amma hakan bai dame ta ba,ta zaro wata yar ƙaramar fitila ta haska har zuwa cikin gidan
Sai dai kallo ya koma sama,a maimakon muni da zubin wahala da yake tattare da gidan ta waje,ta ciki abin ba haka yake ba,don ya yi matuƙar taruwa tamkar ba a ƙasar take ba,kau tsaye kuma ta nufi katafaren parlourn gidan
A hankali ta buɗe kofa ta shiga, mutanen da suke zaune a parlourn suka ɗago suna kallonta
Su uku ne,mace ɗaya, sai maza biyu, ƙatuwar tukunyar shisha ce a gabansu,da kwalaben giya kala-kala
Kusan dukkansu suna riƙe da glass cups, wadda suka zuba tsadaddiyar giyar,suna ganinta yanayin fara'arsu ya karu,macen ta ce
"ROXY! THE AMAZING BABY!!"
Ɗaya daga cikin samarin ya ce"ROXY!The shinning star!!"
Ɗayan kuwa cewa ya yi"Welcome HERMOSA!!!"
Babu wanda ta kalla a cikinsu,sai waje da ta samu ta zauna bayan ta cire ƙyallen da ta rufe rabin fuskarta, kyakykyawar fuskarta ta bayyana babu yabo babu fallasa,pipe ɗin shishar ta kama ta cika bakinta da hayaƙin shishar,a hankali ta fara fitar da shi ta hanci da baki cikin ƙwarewa, kafin ta sake jan hayaƙin shishar
Sai da ta gamsu don kanta, sannan ta ɗago tana kallonsu ɗaya bayan ɗaya, kafin ta tsayar da idanunta a kan ɗaya daga cikinsu
Kato ne,kakkaura mai ƙirar ƙarfi, baƙi ne sosai,amma hakan bai ɓoye tattoo ɗin shi da yake gefen hannunsa na hagu ba, kasancewar rigar jikinsa armless ce,sai wando da ya saka three quarter
A nutse, cikin izza ta ce"David what's up?
Nabyi kewarku fa"ta ƙarashe magana tana yin wani murmushi,tare da ƙanne ido ɗaya
Wanda ta kira da David ya yi murmushi yana kurɓar giyar da take cikin Glass cup ɗin gabansa, sannan ya sake faɗin "Roxy the amazing baby!
Wannan karon kin daɗe ba ki waiwayo mu ba,ko dai kin tsorata ne?"
Ta ɗaga kai tana kallonshi,ta ɗan yatsina fuska ta ce"da me kenan?"
Waro idanu ya yi,ya ce"da jami'an tsaron ƙasar nan mana,masu bin ki dare da rana"
Ƴar dariya Roxy ta yi, wadda ta yi kama da ta rainin hankali, sannan ta ce"ka manta kenan da Roxy kake magana?
Ashe?
Har wani jami'i yana da ƙwarin gwiwar iya farmaka ta?"
David ya ce"of course!
Don na samu majiya mai ƙarfi ta cewa an samu jami'i mai cikakken ƙwarin gwiwar da yake jin zai iya ja da ke,har ma ya kamo ki a cikin wata guda kacal!"
Da sauri ta ɗago tana kallonsa jin abin da ya ce"kafin ta kece da wata iriyar dariya,shima dariyar ya fara yi, kafin ta tsagaita ta ce"matsala ta da jama'ar ƙasata rashin kunya!
Har yanzu babu wanda ya samu wani hint na abin da ya shafe ni bayan hotunana da na tura musu,sama da shekara ɗaya kenan,na ba su damar su kama ni idan za su iya,shine don bashi da kunya yake tunanin zai iya nasara akai na?"ta miƙe tsaye tana cire hular kanta samfurin hat, wadda ta fi sakawa a yawancin lokuta, sannan ta dubi David da sauran mutum biyun da har zuwa yanzu babu wanda ya ce komai a cikinsu,sun zuba mata idanu,bata damu ba ta fara magana cikin yanayin jin ɓacin rai, saboda a ganinta an taɓa jikimarta
Cikin izza ta fara faɗin "ina son samun wani abu da ya danganci jarumin, kamar
Sunansa, ɗan wanene shi?yana da aure? yayansa nawa?ina yake yawan zuwa?me ya fi so? menene rauninsa na rayuwa?
Sannan su Wanene na sama da shi a wajen aiki?
Ina son sanin wadannan muhimman abubuwan a kwana uku kacal"David ya ce"done ma'am!"
Bata damu ba ta cigaba da faɗin"ina son na fara tunatar da shi wanene shi kafin ya san wacece ni?
Ina son ya fara sanin makomar manyansa da suka shiga gona ta kafin ni ya san tawa makomar!
Ba kamar yadda ya yi tsammani bane,ba shine mai juya akalar wasan ba,nice, sannan kuma zan mayar da shi abin wasa na!!
Wannan abu ma raini ne a gare ni, jami'i kamar wannan, wanda har zuwa yanzu bai gama wayewa da aikin nashi ba amma ya fara tunanin karawa da wadda ta gagari manyansa,mu je zuwa "sannan ta mayar da hankalinta kan ɗaya namijin da macen, wadanda suka kasance sun fita daban a zubin halitta da David,alamu sun nuna ba yan kasar bane
"Da harshen Spanish ta dube su tana faɗin"Sofia! Alejandro!
Barkanku da zuwa,amma da kun yi haƙuri ina nan zuwa,amma gashi kun yi gajen haƙuri kun jefo kanku cikin matsala"ta yatsina fuska tana gyara gashinta ta cigaba da magana cikin halin ko in kula "kun sani Roxy bata alƙawari ta saɓa,kayanku za su isa har Ibiza,to menene na biyo ni nan kuma?bayan kun san a yadda nake rayuwa a nan ɗin?
Kuma kun san yadda ƙasar tamu take?"ta sake jan hayaƙin shisha,ta cigaba da magana, hayaƙin yana fita ba tare da ta sake kallon sashen da suke ba
"Bana son wani ya shiga matsala saboda ni,amma idan hakan ta faru kaɗan daga aiki na ne na ƙyale ku,sai ku fitar da kanku "
A fusace Alejandro ya dube ta ya ce"za ki ce haka mana saboda kin karɓi kudinmu a hannunki,amma ki sani,wajibi ne ki biya kaya,idan ma tunaninki za ki cinye mana kuɗi ne to kin yi kuskure,ko kuɗi ko kaya,ko kuma ranki "
Dakatawa ta yi da jan hayaƙin shishar,ta dubi Sofia da ta zubo musu idanu tana kallonsu, cikin harshen Spanish ta ce"ke fa?
Me kika ce akan hakan?"
Kai tsaye Sofia ta mayar mata da amsa"ina tare da Master na!"
Miƙewa Roxy ta yi tana yin wani murmushi,ta dubi David,tana murmushi ta mayar masa da batun da suka tattauna da su Alejandro kasancewar shi baya jin Yaren Spanish,take suka fara dariya kamar taɓaɓɓu, Roxy har kusan faɗuwa ta yi tana ƙyalƙyala dariya,hakan ne ya fusata Alejandro,ya miƙe a fusace da niyyar shaƙe ta,ta yi saurin kaucewa tana aika masa da wani mugun kallo
"Cikin harshen Spanish ta dube shi tana kaɗa babban yatsanta da ɗan tsakiya a fuskar Alejandro, kafin ta fara magana a fusace"gwamnatin Spain gaba ɗaya ma kallo na take yi daga nesa, ballantana kai wani ƙaramin mara kunya wanda babu wanda ya sanka a duniyar tantirai
Kana ganin babu wanda ya taɓa yunƙurin kashe ni ne?da har kake tunanin cewa za ka gwada?
Ka tafka babban kuskure irin wanda baka taɓa yi ba!!
Da alamu kana jin cewa kana da karfin da za ka iya ƙwatar wani abu mallakinka a hannun Roxy,to wannan shine kuskuren ka mafi girma
Tunda ka nuna cewa za ka iya ƙwatar haƙƙinka mu je zuwa,zan gani ko za ka iya!"ta ja baya tana kallonsa da alamun cikakken shiri
A fusace ya kai mata naushi,amma sai ta goce,hakan bai bawa Kowa mamaki ba, musamman ga wadanda suka san wacece Roxy,dambe da gwada ƙwanji ba baƙonta bane,cikin wata iriyar dabara ta sa ƙafa ta taɗiye shi,ya zube a gabanta
Yana daga kwance yake bin ta da kallo yana ɗan murmushi, cikin kwanciyar hankali ta wuce inda tukunyar shishar nan take,ta cika bakinta da hayaƙi,sai da ta zo daidai saitinsa,ta tsugunna a gabansa tana kallonsa, kafin ta hura masa hayaƙin,ta yi ƙasa da murya tana faɗin"ROXY the shinning star!
No one can harm Roxy"ta juya yare zuwa Spanish ta ce" ka ci Sa'a bana sata,don haka zan dawo maka da kuɗinka,da ace ina cinye haƙƙin wani,da ba za ka sake jin ɗuriyar kuɗaɗenka ba, ballantana ka yi tunanin samun kaya,na gama magana,sai haɗuwa ta gaba"ta miƙe tsaye tana kallon David ta ce"ku bar nan wajen nan da ƙasa da mintuna biyar, sannan kar ka manta aikin da na ba ka akan wannan tsageran jami'in,yana bukatar ya san wacece Roxy!
Na ga har yanzu akwai iyayin sababbin jami'ai a tattare da shi, zuciyarsa ta rufe, ƙwaƙwalwarsa ta rufe ya kasa tuna cewa manyansa sun ja da Roxy sun kasa, ballantana shi ƙaramin alhaki"tana kai wa nan ta fice daga parlourn ba tare da ta sake kallon kowa a wajen ba
Da wani murmushi Alejandro ya bi ta da kallo, kafin ya mayar da kallonsa ga David, cikin harshen turanci yana murmushi ya ce"kyakykyawa ce,kuma tana da kaifin basira,bata da tsoro,jaruma ce, tabbas tana burge ni,ko a haka ma na san na ci ribar kasuwanci da ita"David ya miƙe yana faɗin
"Ko ma dai yaya ne!
Ka tashi mu fita daga gidan nan,don tunda ka ji ta yi magana da gargaɗi akwai ƙaton dalili "babu musu Alejandro ya miƙe, David ya wuce,suka bi shi a baya don ficewa daga gidan ta ɓarauniyar hanya kamar yadda suka shigo, saboda ɓad da sawu
*MALIYA ESTATE, KANO STATE, NIGERIA*
"Kai jama'a!ikon Allah!!
Aunty Arfa kin ji wannan matar!
Tabɗijam!!!"
Aunty Arfa, wadda ta kasance mata ce ga babban ɗan Hajiya Sa'adatu,wato Muyassar,kuma ƙanwa ce a wajen Hajiya Ruƙayya,ta ɗago kai ta tana kallon Iman da take wannan maganar a fusace,a hankali ta ce"to fa!ke dai ba iya gajiya da daru!!
Menene yake faruwa ne?"
Surayya ta kalli aunty Arfa ta ce"maganar gaskiya aunty!
Kawai don abu ya samu mutum sai ya zama kowa ma sai ya same shi?
Ki ji Ummeey da wata magana da,wai menene da menene,kar a kai mu karatu this and that,tarbiyyarmu zata lalace bla bla bla, imagine fa!
Wallahi ya kamata wannan matar ta kama girmanta,don wallahi idan ta cigaba da yi mana irin wannan halin Allah da gaske zan iya yi mata duk abin da na ga dama,sai dai abba ya dandaƙa ni, daɗin ma su Mommy sun mayar mata da amsa"
#Nusy_bee