BARRISTER SUHAIL
🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾
Mallakar
KHADIJA WRITES
YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION
(YOTA)
⸻
💖 Dedicated To My Mom 💖
⸻
kai i'm already speechles wallahi ashe haka kuke san littafin Barrister suhail naga ruwan like more Musamman my facebook peole wallahi ina alfahari daku kuma nace sai daku yan Amana
Godiya ta musamman zuwa ga
Gimbiya Rahama
mutanen hafsat hausa novel
dandalin hausa novel
docter d
basheer s basheer
ina godiya sosai
بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
🅿️----16
Cikin nutsuwa motocin suka ratsa cikin titunan Millennium city
Iman ko duk sanda ta tuna Ammi da yaya Mubarak wani sabon hawaye ya sauko mata
A hankali motocin suka parka a gaban wani katafaren gida.
aunty zaituna da baba dije suka fito da ita zuwa cikin gidan ginin flat ne wanda a ka kawata compound din da flowers masu kyau da daukar ido gidan na dauke da parking space mai cin mota biyu a haka suka karasa cikin gidan falo ne sai 3 bedroom da Kitchen ɗaya daga cikin bedroom din suka shigar da ita bakin gado ta zauna tana gyara zaman hijabin dake jikin ta baba dije ta dora tata nasihar kan wanda Malan yayi mata.
ta koma falo ya rage daga iman sai aunty zaituna cire kunya tayi ta kalli Iman ta ce"Yanzu kinga kin zama matar aure aure ibada ne kafin ya zama soyayya. Ki ji tsoron Allah a gidan mijin ki, ki kula da sallar ki duk da nasan ko a gida bakya wasa da ibadarki
“Ki kasance mai tsafta domin tsaftar mace na daga cikin abinda ke kara soyayyar ta a zuciyar mijin ta Ki kula da jikinki, kayan ki da kuma gidan ki. Kar mijinki ya dawo gida ya same ki cikin ƙazanta ko warin girki da rashin gyara duk sanda da miji keyi maki matukar baki kula da wannan bangaren zaki fita a ransa"
Abu na ukku lura da hakkin mijin ba sai lalle dole sai ya nemi ki ba kuma kar ki hana sa hakkinsa duk Lokacin da yake bukatar yin hakan na tattare da fushin Ubangiji ki zama mai riƙe sirri mijin da kuma yi masa Uzuri a duk lokacin da yayi maki abinda ba daidai ba ko wace mace zaman hakuri take a gidan ta Ki rike iyayen sa tamkar Ammi da malan ki kyautata wa yan'uwansa ko da ke basu kyautata maki ba hakkin sune a kanki"
har lokacin Iman kuka take maganganun Aunty zaituna na ratsa mata zuciya .
Aunty zaituna ko diyar ta hafsat zata aurar iya Nasihar da zata mata kenan
Aunty zaituna ta tashi ta ce"to iman sai da safe bari na turo Hafsat kuyi sallama ko"
sai lokacin ta dago fuskar ta kalli aunty zaituna ta ce"Aunty dan Allah a barta ta kwana"
murmushi tayi ta ce"a'a malan ma faɗa zai yi idan yaji ta kwana amman ki bari gobe zata dawo sai kuyi sallama dan muma jibi zamu wuce saboda monday Hafsat zata koma makaranta"
tana fita ta turo Hafsat Rungume juna sukayi suna Kuka cike da kewar junansu sai da aunty zaituna taji shiru tazo ta kirata ta iske su a haka bata raba su ba dan su kadai suka san yadda suke ji Iman da Hafsat tun suna yara basu rabuwa kwana Arba'in kacal tsakanin su haka suka tashi sun suna yara kansu a hade kafin daga baya mijin aunty zaituna ya koma Katsina.
yanzu haka idan akayi hutu hafsat zata tattaro kayan ta dawo kaduna gashi yau aure ya raba su.
aunty zaituna ta kamo hannun hafsat iman ta rike sai tayi da gaske ta fitar da Hafsat Iman ta kife kanta ta saki wani kukan mai karfi.
Zarah ce zaune Dakin Aunty Fauziya tana chanza wa junaid Pampers aunty Fauziya ta ce"Zarah bazaku je gidan Suhail din bane"
"Ban sani ba ko su Naima zasu je amman ni sa gobe junaiid nake jin jikin sa da zafi kamar zaiyi zazzaɓi"
"to shikenan Allah bashi lafiya"
tashi tayi ta koma part din mami Meerah ce kwance a palorn kan kujera cikin sati guda tayi baki ta rame Tamkar wanda aka sallamo daga gadon asibiti Zarah ta shigo kallon ta tayi ta ce"Meerah ina momyn"
"taje ta raka kawayen mami"
rikon junaid ta bata ta nufi upstair dakin mami tana zaune ita da Naima tana shayar da Ayla.
da sallama ta cika Mami ta ce"har kin dawo daga ɗakin uwar daki"
Kallon Naima tayi ko ba'a faɗa mata ba tasan ita ce ta fadawa mami tana part din aunty Fauziya
Zarah ta ce"haba mami laifi ne dan naje dakin aunty Fauziya matar Abba ce fa kuma tun safe ita ke fama da Amatullah yanzu ma zuwa nayi naga ko tayi bacci na dauko ta kuma ta ce na bar ta kwana achan"
Naima ta ce"ba wani nan ko kayan ki ma ai chan kika kaisu Allah ya sauwake ka wai dan lalacewa ka fifita kishiyar uwarka akan mahaifiyarka ko dan waya sani ma ko asiri ce ku tayi nidai wallahi nafi karfin duk wani tsafin ta"
Zarah tayo kanta zata bigeta Mami ta tare ta ce"ni ya kamata ki buga tunda ni na fara magana ai"
cike da bacin rai Zarah ta ce"mami duk Abinda Naima take cikin gidan nan ke ke goya mata baya ta raina kowa a gidan nan kuma kar ki manta shekaru sama da Bakwai na baki kafin ke ma akwai Suhail
tsaki Naima taja tana hararar ta ta cire Ayla daga jikin ta goya ta ta fice daga dakin.
Zarah a ranta ta ce"Allah ya ganar da mami"
Suhail ke shigo wa gidan bayan tabbatar da babu kowa a compound ta Kofar baya yabi ya shiga dakin sa kayan jikin ta cire ya shiga bathroom wanka yayi ya shirya cikin wani light brown din yadi marar nauyi wayar shi fara Ringing ganin Abba ya sa shi saurin ɗaga wa.
"ka same ni a part dina" Abba ya ce ya katse wayar.
bai ma san Abba yaga shigowar sa ba.
a palorn sa ya same shi ya sami waje kan carpet ya zauna ya gaishe da Abba tare da masa ban gajiya.
gyaran murya Abba yayi ya ce"Congratulation Suhail Allah ya sanya albarka a auranku abinda nake so na fada maka Yarinyar Amana ce akan mu gaba ɗaya Kamar yadda muka rabo ta daga gaban iyayenta inaso ka riƙe ta amana Allah ya baka ikon sauke nauyin da Allah ya dora maka"
"Amin Abba"
cigaba yayi da zama Abba ya ce"ka tashi ka tafi dare nayi"
dakin sa ya koma ya haɗa kayan sa da duk yasa zaiyi amfani dasu ya saka a booth din motar sa ya tafi.
Iman ce kwance akan gado har yanzu kukan take yi tayi kanta yayi mata nauyi da kyar take bude idanun ta jin ta kamar zazzaɓi nasan zubo mata ta tashi da kyar.
kayan jikin ta ta fara ragewa ta dauko towel din dake cikin kayan ta ta daura ta shiga bathroom bata wani sha wahalar amfani da kayan dake cikin toilet ba dan akwai su a gidan aunty zaituna.
da kyar ta iya sakar wa jikin ta ruwa ta fito daure da towel wata pink din sleeping gown ta saka mai karamin hannu ta tsaya mata iya gwiwa ta hau gado tayi kwanciyar ta.
motarsa ya faka a hankali cikin compound ɗin.
a hankali ya fara kwashen sa yana shiga dasu dakin sa bayan ya gama ya kwashe kayan ya kashe fitilun palon ya wuce dakin sa sai da ya gama jera kayan shi a closet ya chanza kayan jikin sa zuwa jallabiya
ya fito zuwa dakin Iman kwance take kan gado duk ta takure jikin ta kare mata kallo yayi cikin rigar baccin kirjin nan sun cika kamar sun fasa riga su fito a tsaye gyam karo na Farko da ya taba ganin mace a haka ya jima a haka kafin ya rage mata hasken dakin ya ja kofar ya koma Dakin sa.
bacci mai nauyi yayi awan gaba dashi bashi bya farka sai da aka fara kiran sallar Asubar farko.
alwala yayi ya fito zuwa Masallaci wanda duk akan kunnen iman dan tun cikin dare ta tashi , ta kasa komawa bacci hakan yasa ta dauro alwala ta fara jero sallar dare tana zaune har aka kira sallah Asuba.
sai lokacin ta tuna da tabar fitulun Dakin jiya a kunne amman da mamaki ta tashi ta gansu a kashe kunya ta kamata dan tasan sarai shine ya kashe su to da yar rigar nan ya shigo ya iske ta gashi ita bama tasan a wani yanayin ya iske ta ba jin haushin kanta tayi ta tashi ta tayi sallar Asubah sai da ta gama azkhar din ta kaf ta tashi ta linke Prayer mat din ta leka window kenan Suhail na dawo daga masallaci ya juyar da fuskar sa hakan yasa bata samu ganin fuskar saba.
TO ALHAMDULLILAH ANAN ZAMU TSAYA SAI ALLAH YA KAIMU BAYAN SALLAH ALLAH KARBI IBADUN MU YASA MUYI SALLAH LAFIYA MU GAMA LAFIYA
Like
share
comment