GADAR GIWA... (Toro ke buga mata ganga)

GADAR GIWA

by @auntyindo

*🪻G
         
Maa ta É—an murmusa ta ce "Kin ji abun wani iri ko?,  to misalin haka ne, ni ma babu yadda za a yi in manta da Yayyena da Ƙanne, bare kuma Iyayena,   gidanmu gidanmu ne don haka sai naj e Taron nan ko me zai faru babu ruwan ki, sannan ke da Khalil ma sai kun je wannan Umarni ne!"  Ƙasa ta yi da kai gami da sauke wani gwauron numfashi, Khalil kuwa sai rarraba idanu yake yi. Maama ta cigaba da cewa "Rabona da zuwa Taron fa an kai Shekara Biyar tun Mahaifinmu yana Shekara É—aya da rasuwa,  yanzu ina son Æ™ara zuwa kuma zan cigaba da zuwa, ke da shi ma haka, ki ma dena faÉ—en ba za ki je ba É—in nan!"   gyaÉ—a kai kawai Hibba ta yi tana jin kamar ta fashe da kuka,  Maa-ma ta ce "Yanzu dai tunanin da na fi yi koma shi ne, abin da zan kai wa Ummina,   kawai ki yi min girki mai daÉ—i irin na Zamani sai in kai mata, ba wata burga zan yi ba,  kawai zan yi daidai Ƙarfina ne, duk wani abu na san tana da shi shi ya sa gwara a yi girkin yadda za ta yi ko lauma É—aya ne ta sa Albarka!"      "Toh za a yi in sha Allahu, Gobe za mu je ni da Khalil mu siyo duk abin da za a nema ko? tun da Abincin zamani kike so Maama"     "Eh shi nake so, Allah ya kaimu sai ku je da wuri ku dawo da wuri"  
"Amma fa ni Jibi akwai Taro da za mu yi , kuma ba a so in Æ™i zuwa da wuri bare kuma Æ™in zuwan duka"  Hibba ta faÉ—a fuskarta É—auke da damuwa     "Wannan ba matsala, za ki iya haÉ—awa biyu, ban ce dole sai kin wuni ba!"
    Ba don ranta ya so ba ta ce "To Allah ya kaimu Jibin".........

          Ranar Taro....

   Cikin sauri-sauri suka gama shiryawa sannan suka É—auki hanya a cikin Adaidaita Sahu.

  Dukkan su sun yi matuÆ™ar kyau son Kowa Æ™in ÆŠan Hassada, kuma sutturunsu masu tsada ne  a wajen mai Æ™aramin Ƙarfi, Maa-ma da Hibba Atamfa ce riga da zani suka sa amma kowacce kalar tata daban,  ba anko suka yi ba, Khalil kuma  Shadda ya saka.

  Hibba ba ta yi wata kwalliya ba kawai manleÉ“e ta shafa sai kwalli da ta saka a idanunta wanda yake matuÆ™ar Æ™ara  kusanto da Kyaun da Allah ya zuba mata, idanunta kaÉ—ai suna da matuÆ™ar kyau da ÆŠaukar hankali.
BaÆ™a ce amma ba irin wuluk É—in nan ba, za a iya saka ta a jerin masu É—an haske daga fannin baÆ™aÆ™e,   ba za a kirata Doguwa ba hallau ba za a ce mata gajera ba, kuma a dire take ta ko,ina ba aibu shap É—inta ya fita sak! gata yar dumurmur tubarkallah...... Son kowa Ƙin MaÆ™iyi.....

   Har Æ™ofar Gida ÆŠansahun ya ajiye su  suka sallame shi ya yi gaba,  Maama ta kalli Hibba da ke ta famar yin waya ta ce "Za mu shige idan kin gama kya shigo"  kai ta gyaÉ—a tare da yin baya su kuma suka shige.
  Wayar ta cigaba da yi  tana kallon gidan wanda ke É—aya daga cikin  Manyan gida mafiya girma a layin, kai tsaye ma ana iya cewa ya fi kowanne kyau da tsari domin an sabunta ginin ya Æ™ara zama na Zamani ba kamar sauran ba, hallau ba ya rabo da shan Gyara.

     Ta É—an jima nan a tsaye kafin ta katse wayar ta numfasa  gami da cewa "Dole Maama ta sha WulaÆ™anci tun da ta Auri Talaka!"  karaf! idanunta ya sauka cikin na wani bawan Allah da take ganin duhu-duhunsa tun É—azu, sai dai ba ba tsaya kallon inda yake ba ma bare ta san me yake yi, sai yanzu ta lura kawai ita yake kallo.

   Yaro ne haÉ—aÉ—É—e kuma tsadadde, daga ganinsa bai wuce shekaru Ashirin da uku zuwa da huÉ—u ba, amma fa zabgege ne mai Ƙirar Sadaukai.
Kawar da kai gefe Hibba ta yi kamar bata san da Mutum ba ta sa kai zuwa cikin Gidan.
Wayarta ce ta sake yin Æ™ara ta yi saurin É—auka ta kara a kunnenta tana faÉ—in ''Zan zo fa,  kin san muna da Taro ne yau na Dangi abin ya haÉ—e min!"    
Duk hankalinta na kan wayar da take yi duk ba ta lura da Rukuni Uku da ke a tafkekiyar Harabar ba.

  A gefe ÆŠaya Maza ne su Uku Matasa majiya Ƙarfi kuma masu ji da kansu...
ÆŠayan gefen kuwa sun kai su Bakwai har da Mata guda Biyu sun sha wata Shiga ta banza mai bayyana surorin jikinsu, kuma sun yi dumu-dumu kafaÉ—a da kafaÉ—a da Maza suna hira suna tafawa har sai da suka ankara da  Hibba sannan Wutarsu ta É—auke suka dawo kallonta.
  ÆŠayan gefen ma Maza ne zasu kai huÉ—u,   su ma Æ´an saffa-saffa masu  tsadar Gaske, abin mamaki kaf kallonta suke yi kamar  sabon watan Ramadan.

  Takaici  da kuma bugawar da zuciyarta ta fara yi da sauri ya sa ta yi saurin tsinke wayar ta cigaba da  tafiya.....

 "Ke!!" ta ji an kira ta cikin tsawa,  da sauri ta juya tana kallon inda  ta ji muryar,  daga cikin rukunin da suka fi yawa ne,  "Zo nan!"  wanda ya kiratan ya Æ™ara faÉ—e.
   Ba musu ta Æ™arasa inda suke tana Æ™aÆ™alo murmushi ta ce "Sannun ku!"       "Wace ce ke? daga ina?" 
    "Daga Gidanmu, sunana Hibba!"  É—aya daga cikin Æ´an matan wanda suke bin ta da kallo mai cike da Tsana ta ce "Na ganki wata Ƴar Matsiyata da ke!, me ye haÉ—in ki da gidan nan!"  
Ta É—an murmusa ta ce "Oh! ashe ba ku gane ni ba, ai matsayina É—aya da ku ni ma Jika ce"   a Tsawace Budurwar ta ce "Ke!??   wa ya ce miki Matsiyaci da mai ArziÆ™i É—aya ne?, Wane Shegen ne Ubanki a cikin Mazan gidan nan da har kike wannan gadarar??"    

 "Ya ilahi!" Hibba ta faÉ—a gami da É—an dafe goshi, cigaba ta yi da cewa "Wai kina nufin duk ƳaÆ´a Maza da Kakarmu ta  haifa Shegu ne?? ki ce gwara da Allah ya sa Mace ce ta haife ni a cikin su  ba Namiji!" 
     Ashar budurwar ta luntsuma gami da É—ago hannu a zafafe ta kaiwa Hibba Mari......
Da sauri É—aya daga cikin Æ´an Samarin ya riÆ™e hannunta gami da hankaÉ—a ta Baya  wani a ciki ya rungumo ta yana faÉ—in "Sorry Sister!" .

  Shi kuwa wanda ya harbo ta baya MiÆ™awa Hibba hannu ya yi don su yi musabaha tare da cewa "Sunana Sabran!"  Ta É—an murmusa ta ce "Sannu"  a É—an kunyace ya janye hannunsa sai kuma ya ce "Am...  Ikram ta É—an yi maganganu masu tsauri, amma ke kuma taki tanfi zafi, ita banta fayyace ba duk da maganar  ta yi kama da hakan,, ke kuma duk sai kika zage mana Iyaye!"  
Ƙare musu  kallo ta yi É—aya bayan É—aya ta ga dai kallon ta kawai suke yi  wasu dai da alama sun ji haushinta wasu kuwa da gani kallon  neman wurin shiga ne kamar dai  shi Sabran É—in....  a tausashe ta ce "Ku yi haÆ™uri fa!, kawai kun san zuciya wani lokacin da wuri take fusata!" 
   Cikin zafin rai Ikram ta fizge daga hannun Hafiz da yake ta famar shafa ta   ta juyo  kan Hibba tana faÉ—in "An gaya miki ke kaÉ—ai ce mai Zuciya? to wallahi za ki ga abin da zai biyo baya, Za ki gani banza Ƴar Matsiyata!"  banza Hibba ta yi mata sai ma kallon Sabran da ta yi ta ce "Ku yi haÆ™uri fa!, ni zan shige ciki!"  ba ta jira amsa ba ta juya gami da watsa idanunta  don tana sane da sauran da ta gani a Harabar wanda tana da tabbacin duk sun girmi WaÉ—annan Fitinannun Yaran, mamakin ta É—aya ya akai aka rasa mai tsawatarwa???  duk da suna wani gefen amma alamar faÉ—a ko kurma zai gane ta, bare har an kai ga kawo duka.

  Dayan gefen suna nan, Manyan ciki ne dai saura É—aya a cikin uku, biyun duk sun watse, yana jingine a jikin wata Farar Mota hannunsa harÉ—e a Ƙirjinsa, ga mamakinta shi É—in ma fa ita yake kallo kamar dai sauran.
   Duk ta tafi tunani ba ta san ma tana kallonsa ba sai da ta ga sun yi ido huÉ—u ,,,, ba ta san ma sanda ta ja Tsaki ba, ta yi saurin canja akalar tafiyarta zuwa cikin gidan, zuciyarta cike fal da takaicin  su manyan banza da ba za su iya tsawatar wa na Æ™asa da su ba.

    Cikin wani taku me kama da sanÉ—a ya rufa mata baya,  Wasu daga cikin abokan rigimar ma suka biyo bayansa.
Cikin wanda suke su huÉ—u ma Mutum biyu ka sa jira suka yi sai da suka  bi Sawu.

  Ikram kuwa fizgar hannun abokiyar cin mushenta ta yi wato Inayah, suka zagaya baya suna mita da bala'i, cikin hirar tasu za ka gane ba wai Maganar Hibba ce ta Æ™ona musu rai ba kawai ganin Yadda   duk hankalin samarin nasu  har ma da na gefe ya koma kanta daga shigowarta ne ya tsaya musu a rai, musamman jin yadda Ƴan Samarin suka fara santi suna yaba mata,  jin hakan kuwa ya sa suke ganin kamar za ta Ƙwace musu Kambunsu ,  wanda suke ganin sun fi kowace Ƴa farin jini a Family É—in, duba da yadda suke juya Æ™waÆ™walen Samari suke KarÉ“e ƳaÆ´an Banki,  gashi gani suke sun fi kowacce kyau da Ƙira da iya kwalliya da shiga ta alfarma kawai don suna shiga irin ta jan Ra,ayin maza da kuma tonawa kai Asiri.
   TaÉ—i suka cigaba da yi akan abin da zabsu yi  su Æ™untatawa Hibba sai dai sun rasa yaya za su yi don ba a cikinsu take ba bare su wulaÆ™anta ta, Æ™arshen abun kenan a nuna mata bambanci tsakanin Talaka da mai KuÉ—i.

      Duk wannan abun da suke yi ,  su ma ƳaÆ´a ne na É“angaren Mata a gidan,  Ikram Æ´ar Ƙanwar Maa-ma ce , amma ita Babanta yana da É—an KuÉ—insa hakan ya sa ita ma Ummanta Hajiya Nafisa ba raini tana murza kuÉ—i, sai dai ba kamar ƳaÆ´a Maza na gidan  ba.  Inayah kuwa Ƴar Yayar  Maa-ma É—in ce, ita Kuwa  za a iya kiransu Talakawa akan sauran,  Da, suna da É—an kuÉ—in daidai gwargwado daga baya Lamura suka koma baya, hakan ya sa ita ma Hajiya Karima ta zama Ƴar bayan Ƙeya a cikin gidan, sai dai ba kamar Maa-ma ba don duk da haka Hajiya Karima tana da É—an nata ita,    da ma Maa-ma Talaka ta aura tun farko, kuma yanzu ma Talakan take Aure, ita kuwa Inayah duk da su ba komai ba ne akan sauran ita É—aukar kanta take ta fi kowa,,, don tana matuÆ™ar wankar  kuÉ—in Samari a cikin Family  da waje, halinsu ya zo ÆŠaya da Ikram, shi ya sa Abotarsu take tsawon rai kuma ake zama lafiya, aikinsu kenan yaudarar Maza da ci musu kuÉ—i kuma babu yadda suka iya suna ji suna gani, gashi kafin Namiji ya yi zuciya da su aiki ne, Allah ya yi musu baiwar Abun, ba dai su kafa Æ™waÆ™wa akan Namiji kuma ya tsira ba, shi ya sa ita Inayah ba ta san wata Æ™amfa ko lallaÉ“a rayuwa ba, kawai rashin Mutunci take zubawa son ranta.

    wannan kenan

A cikin gida.......
   Maa-ma tana falon Farko a tsakure kan Carpet  kanta a Æ™asa lokacin Hibba ta shigo, Tsugunnawa ta yi har Æ™asa tana gaishe da Hajiya Mommy sai da ta maimaita sau uku sannan ta amsa da "Lafiya" ta cigaba  da cewa  "Ke Rabi! Rabi!!  zo ki je   ki kai  Abincin nan a bayar ga mabuÆ™ata kar ma ya ruÉ“e, ai ganganci kika yi Amina ai kin san ba ni da yunwa babu abin da Abincinki zai yi min , ni a Ƙoshe nake su ma Yaran babu mai ci duk sun wuce ajinsa"
    Cikin wani mugun baÆ™in ciki da takaici Hibba ta  zuba wa Maa-ma ido tana jin tamkar zuciyarta za ta yi tsawa.
      
Hamdan ya Æ™araso wajen yana cewa "Rabi!  Ki ajiye min Plate É—aya  kafin ki Bayar!"   
   daga haka ya wuce gaba yana jin Hajiya Mommy na cewa "Ba ka ci Abincin banne ko an ce maka babu ne?? , ga Abinci can mai rai da lafiya ka ci ka bayar sai ka ce...." ganin ba saurarenta yake ba ya sa t aja tsaki ta yi shiru.
 
   Wanda suka biyo Hibba a Baya wasu dariya suke wasu Mutum biyu daga ciki kuwa sun yi kicin-kicin da fuska.  MiÆ™ewa Hajiya Mommy ta yi tana cewa "Ke Amina tashi ki kai ƳaÆ´anki su gaida iyayensu sai ki dawo, ni ma yanzu wucewa zan yi can Mmu sha hira!"      "to" Maa-ma ta ce gami da tashi tana gayyatar su Hibba...


   Jiki a sanyaye suka rufawa Hajiya Mommy baya har suka isa wani Æ™aton Falo kuma Ƙawatacce,  duk iyaye Mata suna nan ana zaman jin kai, zaman Na isa,  ke ba ki isa ba,  ado da kwalliya kuwa kowacce tana wane wata!. 

   A gefe guda akwai Tsirarin Æ´an mata, da Yara.
     Sallama Maa-ma ke ta rafkawa amma an rasa mai amsawa , sai da Hajiya Mommy ta ce ga fa Amina nan ku gaisa.

   sai lokacin suka kalle ta ita da tawagarta wato Hibba da Khalil,  wata Farar Mata  haÉ—aÉ—É—iyar Hajiya ta ce "To fa!  yau kuma a taron namu har da Gajiyayyu da marasa Ƙarfi?"      Maa-ma ta yi murmushi mai ciwo ta ce "Har da mu!, ina wuninku "   "Lafiya!" wasu a ciki suka amsa.
   Hajiya Nafisa ta murmusa ta ce "Hajiya Madina tawa!, Gajiyayyu ma ko su gayyar SoÉ—i!"
    "Ai duk ÆŠaya!" wata Matar ta faÉ—a tana dariya.

  Hajja Mommy ta taÉ“e baki ta ce "Hmm!  ta kawo Abinci ma, amma na ce a kaiwa MabuÆ™ata don babu buÆ™atarsa anan, shi ne na ce bari in gaya miki don an ce gwara a dinga faÉ—en alkairi ko?"
wasu dariya abun ya ba su , wasu kuwa kallon sheƙeƙe sukai wa Maa-ma suka taɓe baki.

  "Ku Yaran nan ba a koya muku Gaisuwa da girmama manya ba ne?"
FaÉ—ar Hajiya Nafisa  tana bin su Hibba da kallon Æ™asÆ™anci.
  Hajiya Madina ta ce "Wannan ita ce wannan Agolar ko?"   "Ita ce mana, kin ga ta girma ko?"   Hajja Mommy ta faÉ—a cikin kauÉ—i da zaÆ™in murya irin nata.
    "Ah!,  ta fa girma, shi ya sa ta tsaya mana a tsaye" FaÉ—ar Hajiya Madina.

  "Wai  ba ku ji abin da aka ce ba ne?" Maa-ma ta faÉ—a cikin tsawatarwa, durÆ™usawa suka yi suka gaishe su amma sai mutum biyu ne suka amsa.
   Hajiya Mommy ta ce "To ai kun gaisa ko?   ku koma Ƙasan ai za su Fito"
   kafin ta rufe baki Hibba ta juya ta nufi hanyar fita,  caraf suka sake haÉ—a ido da Maridin Ƙaton da yake  neman addabar rayuwarta da kallo (a cewarta),  ba shi kaÉ—ai ke kallon ta ba amma za ta iya cewa duk ya fi su Ƙwarewa wajen sa ido don kuwa kallon nasa matuÆ™ar kaifi yake mata.....
   Fatali ta yi da lamarinsa ta yi waje, sai da ta je Falon ta zauna sannan su Maa-ma suka iso.

Shiru ne ya ratsa tsakani kafin Maama ta ce ''Ni fa sai daga baya nake tuna labarin da kuka ba ni ranar da kuka fita Garden sai abun yake ba ni dariya"  Hibba ta kalli Maama ta kawar da kai saboda ganin irin murmushin da take yi wanda ya fi kuka ciwo,   wai kuma a hakan Æ™oÆ™ari take ta kawar musu da damuwa, "Maama zan tafi, na samu kiran waya ya fi a Æ™irga saboda jirana da ake yi"  Hibba ta  faÉ—a tare da tashi tana gyara riÆ™on Æ´ar jakarta.

  "Kar ki tafi yanzu gaskiya , ki bari sai É—an anjima"    "Me zan yi a nan Maa?!    kawai mu zauna kamar korarrun karnuka É—in shi ne  kar in tafi?"      "Eh ni na faÉ—a, duk da can ya zama dole to nan ma  ya kama ki ne"  "Ni fa ba ni da wata alaÆ™a da gidan nan, kuma in sha Allahu ba zan Æ™ara zuwa ba"
  "Ba na son rashin hankali Hibba!, gidan Iyayena ne fa kike yiwa wannan furcin!"  "Maama ba haka ba ne, gidan wasu dai da suka gina gidan suka ba wa Iyayen,  nan bai yi kama da gidan iyaye ba, inda za ka zo ana cewa ka zo gayyar soÉ—i, inda ake  korarka wai shi ne gidan Iyaye??!"  "Zan faska  miki mari fa!, na gaji da jin surutan banzan nan naki, ko ki so, ko ki  Æ™i gidan iyayena ne, hasali ma Mahaifiyata a Gidan nan take rayuwa, haka Mahaifina ya rayu a Gidan nan  kafin Allah ya karÉ“i ransa,  kuma na ce miki dole ki zauna!"  
ÆŠora hannu ta yi a ka  tana zagaye wajen cikin sauri ta kai minti biyu tana kai mari ta kai gwauro sannan ta tsaya ta ce "Maa-ma ki taimaka ki yafe min ki bar ni na tafi don Allah!  ba don na gaji ba kawai don ana buÆ™atar ganina a wani wurin,     Maa duk a yau za mu gabatar da Sabon Project na aikinmu fa!".
 
   "Gaggawar me kike haka?, ki yi haÆ™uri   ki bi abin da Maa-ma take so ! "   wata baÆ™uwar murya ta ji a cikin kunnenta, ta juyo da sauri don ganin kowaye, Shugaban Æ´an sa ido ta gani tsaye  a bayanta  ya Æ™ureta da idanunsa da suke matuÆ™ar yi mata Barazanar da babu dalili,   "Please!"  ya Æ™ara faÉ—e yana sake wararo mata idanu, Æ™asa ta yi da kai  ciki disashshiyar murya ta ce "Okay".

Ya ɗan murmusa kafin ya koma gefe ya zauna ya harɗe ƙafa ya zaro Waya ya fara danne-danne.
     Hibba kuwa zagayen ta cigaba da yi tana yi tana duba Agogo.

   Maa-ma ta É—an kalli Hamdan ta ce "Na daÉ—e ban ganka ba Hamdan!, ina ga ko Zuwana na  Æ™arshe taron nan ban ganka ba saboda....."  kasa Æ™arasa maganar ta yi saboda tuno yadda ta koma gida cikin Mawuyacin hali saboda cin mutunci da tozarcin da ta fuskanta a ranar.
   
Lumshe ido Hamdan ya yi   ya nisa kafin ya buÉ—e su akan Hibba yana cewa "Maa-ma ni É—in ne Ja'iri ne, ba na son zumunci, na fi mayar da hankali kan Kasuwanci, shi ne ya fi burgeni fiye da Komai, shi ya sa Taron ma ban fiya zuwa ba,  yau É—in ma ina ga rabon katari ne, don kuwa ni ma dai kamar ita! ina da meeting yau!"  ya Æ™arasa maganar yana nuni da Hibba tare da  Æ™ara zuba mata na Mujiya, ya rasa me yasa ya kasa gajiya da kallonta , a zahiri ba É—abi'arsa ba ce yawan kallon Mutum amma yau a karon farko ya kasa janye idanunsa daga kan Hibba.

   Maa ce ta katse masa tunanin da cewa "Ah lallai kam Ja,iri ne!, to Allah ya taimaka ya bada sa'a, ai dama kyaun ÆŠa ya Gaji Mahaifi, indai kuwa ka gaji Abbanka ai ba za kai sanya wajen Kasuwanci ba!"   Ya jinjina kai gami da cewa "Haka ne Mommu Amina!   ina da jajircewa sosai akai da yake ra'ayina ne, sauran abubuwan da ba ra'ayina ba kuma fa ina da wuyar sha'ani a kai, kin ga ni ba na son HaÉ—a Kasuwanci da Daddy, amma Daddy da Ammy sun fi son haka, kuma gaskiya  ina da É—an wuyar sha'ani akan hakan!"     "Ai sun san zaka tsaya tsayin daka akai shi ya sa suke ta zawarcenka, don haka ka dage ka yi abin da zai faranta musu ka ji?,  in ka haÉ—a biyu ai duk za ka iya tun da kana da Æ™wazo da jajircewa!"   "Haka ne! ina yin Æ™oÆ™ari sosai, kuma zan Æ™ara ninka Æ™oÆ™arin in sha Allah" .

    Hajiya Karima ce ta Æ™araso wajen fuskarta ba yabo ba fallasa ta ce "Hamdan kana nan kana hira da Mamanka? ina ga rabon da ta ganka tun ba ka iya É—aura Zariyar wando  ba ko?!"   Dariya suka yi duk amma banda Khalil da Hibba.

    Hajiya Karima ta ce "Ki yi haÆ™uri fa Amina!, komai lokaci ne kin ji?, koda a haka Allah ya tsarawa bawa rayuwarsa to fa dole wataran komai zai canja tun da ba Duniya ce madawwama ba, ki yi haÆ™uri kin ji!, duk da na san da bakya haÆ™uri da yanzu idan aka ce ina danginki ma ba za ki nuna mu ba,  Yaran dai su ne abun rarrashi yanzu!"        Maa-ma ta murmusa  ta ce "Ba komai fa, dama haka ne ai,  duk ba mu yi fushi ba ma!"    Kafin Hajiya Karima ta ce wani abu Hibba ta katse su da cewa "Ni fa na tafi Maa, yanzu ma kin ga Ismail ne yake kirana!"      Kafin ta rufe baki Hamdan ya tashi ya samfe daga wajen, Maa-ma ta bita da  addu,a, Khalil ma tashi ya yi zai bi bayanta Maa-ma ta hana.

    Tana fitowa daga falon ta yi tozali da Hamdan,  "Ko in raka ki ne?" ya jefo mata tambaya, ganin mukullin Mota a hannunsa ya sa ta ce "A É—ansahu na zo kuma a shi zan koma, a shi  nake zuwa duk inda zan je!"   ya saki baki yana kallonta.

  Kafin yayi wani motsi ta fice....
   A wajen Get ta gamu da wanda ta fara gani tun kafin ta shigo, yanzu ma kallonta kawai yake yi ko Æ™ifta ido ba ya yi tamkar wani saÆ™ago...
Hibba ta zumÉ“uri baki ta yi gaba da sauri don kuwa ya fi mata kama da  Mashayin Giya ga kallon da yake mata irin na Æ™walama,,, kar ta je yana jin haushinta ya sauke gajiyarsa akan ta.

        Maa-ma ba wani daÉ—ewa ta Æ™ara yi ba ta tashi ta koma gidanta dan kuwa har yara ƳaÆ´anta idan sun zo wucewa kallon matsiyaciya suke mata su wuce, wasu ma har da aje mata magana don kuwa sun ga iyayensu suna yi...

       Hamdan.... har ya gama zamansa ya bar musu Gidan  bai nutsu da kowa ba don Hibba ta gama ficewa  da hankalinsa.......


Aunty Indo