GADAR GIWA... (Toro ke buga mata ganga)

GADAR GIWA

by @auntyindo



Tsakaninsa da kowa sai magana a taƙaice ita ma sai ta kama.

Abu kamar wasa sai gashi Barci mai daɗi ya ƙauracewa Ruhinsa. 
 Ko ido a rufe ko a buɗe Hibba kawai yake ji da Gani.
Tashi ya yi  ya zauna a bakin Gado  yana sauraren saƙonnin da zuciyarsa take miƙo masa,   a gefe guda yana mamakin yadda akai Hibba ta tsaya masa a rai, dama an ce ƊAN HAKIN DA KA RAINA shi ke tsokane maka ido..... Ganin abun nasa ba na ƙare ba ne yasa ya nufi toilet ya ɗauro Alwala ya fito ya fara jeranta Ibada.

    Bayan Kwana uku....
Zuwa yanzu Hamdan ya gama sanin inda ya dosa,  sai dai cike yake taf da fargaba da tunanin abin da ke shirin faruwa.
  
    Yana tsaye gaban Madubi yana ƙarewa kansa kallo bayan ya gama shiryawa cikin haɗaɗɗiyar Shadda ya murza Hula. 
  Fuskar Hibba wadda ta kasa ƙauracewa ganinsa ita ce ta fara yi masa gizo, ya saki murmushi tare da juyawa Madubin baya, "Tabbas Ƙaddarata   ta sake buɗe sabon shafi daga  cikin tsauraran Shafuka!,    na kamu da tsananin son wannan yarinyar,  kuma ina matuƙar   buƙatar ta a cikin rayuwata,     babu  tsoro ko shakka wanda za su   sa na rayu ni kaɗai  bayan tana Numfashi, rashin faruwar hakan tabbas Babban rauni ne gareni kuma dole in alaƙanta shi da Hukuncin Allah! ba wai gazawata ba !"   
cikin zuciyarsa yake zuba  surutu tare da ba wa kansa yaƙini akan abin da yake ji da kuma shawarar zuciyarsa.

  Numfashi ya ja  ya sauke kafin ya fice daga Gidan kai tsaye ya nufi gidan Hajiya Mommy.
   Ta yi murna sosai da ganinsa, nan ta saki baki ta fara zuba masa surutu, duk a tunaninta  yanzu ya fara samun lokacin zuwa gaishe ta ne  sai daga baya ta lura kawai yana  wajen ne amma tunanin da yake daban ne.
   a Ɗan ƙufule ta ce "Na zata zuwa  ka yi gaishe ni don mu yi hira? kuma ina ta magana kayi min banza?!"   "Eh to a zahiri tambayarki na zo yi, kuma gaskiya nake son ji ba kwalo-kwalo ba!"  "To na ji, ai ba tsoronka nake ji ba bare in tsaya yi  maka ɓoye-ɓoye in ma wani abun aka ce maka na yi to ni daidai nake da kowa ehe!.." 

    "Hmm!  ke komai naki rigima ne,  Yarinyar Mommu Aminatu ya sunanta? kuma ina ne Gidansu?"   "Iyye?!!... abin da za ka tambaya kenan?, to ni ban san sunanta ba, kuma ni ba zuwa gidansu nake ba tunda nima ba zuwa min suke ba don haka ba ni da amsarka!"      "Ai kuwa dole kina da ita, ko kowa ya manta sunanta ke bai kamata ki manta ba don duk matsayi ɗaya muke da ita a wurinki"
 "A'a o'o wa ya ce maka?!"       "Ai ba Allah ne ya bambanta ba, ke kika bambanta kuma illa kike yi wa Zuri'arki , ni ki bani amsa in wuce ina da abun yi" .

  Zazzare ido ta shiga yi tana tunanin abun, lallai ba zata so abin da take zargi   ya faru ba,  domin ta fi so idan Jikokinta za su yi Aure komai ya zamo na gani na faɗa kuma na kece raini"     "Wallahi zan nuna fushina Hajiya Mommy!,   inda abin da ban tambaya ba ne da tuni kin gaya min ai!"  "Banza masifaffe, sunanta Hibba ne ko wace ce?  kuma ni ban san a inda suke rayuwa ba!"   
  "Hibbah!"  ya furta  gami da sauke wani zazzafan numfashi ɗan jim! ya yi kafin ya ce "Ai kina da phone Number ɗin Mommu Amina ki ba ni ita"        "Wai kai me za ka yi ne da ita?"     "Ni da uwata don na nemi number ta har sai kin tsare ni da tambaya?  wai wannan wace irin rayuwa ce Hajja Mommy? me yake damun ku ne?"     "Oho!   nema kake ka ɗaureni da jijiyar jikina!,   to ni uban me na yi anan da ka zo kana tuhuma ta?, wannan Ɗa da kai ka haife mu   ba mu muka haife ka ba da mun shiga Tara!"    "Ku shiga Tara sau Casa'in ma,   ni ki ba ni jira nake "  a ɗan fusace ta miƙo masa wayar tana cewa "Gashi nan ka ɗauka, kuma wallahi kar in ji kar in gani!"   wani kallo ya zuba mata cike da rashin sanin martanin da zai  mayar mata,, "Lallai ma matar nan!" ya faɗa a ransa kafin ya mayar da hankali kan wayar.

          Tunda Hamdan ya Karɓi lambar Maama Sai bayan Ƴan kwanaki sannan ya samu ƙwarin Gwiwar kiranta domin jin inda zai samu ganin Hibba...


      GABA.....    (CI GABAN LABARI...)


    "Aunty Hibba wai ki zo !" Budurwar da ta leƙo Class ɗin ta faɗa cikin ɗaga murya.

    Ajiye almakashin da ke hannunta ta yi gami da maida kallonta kan me kiran,  "Wa yake kirana?"    "Wani ne sunansa Hamdan yana waje yana jira, kuma  Aunty Rahma ce ta ce ki je"     murmushi ne ya suɓuce mata ba ta dere da ta shirya ba, ta ɗan gyaɗa kai kafin ta kalli Matan da take koyarwa ta ce "Ina zuwa"  ba ta jira amsa ba ta fice.

   Yana tsaye a jikin Mota kansa a ƙasa  sai tufka da warwara yake yi, jin motsi a kusa da shi ya sa shi saurin ɗagowa,     zuba mata ido ya yi kamar yadda ta zuba masa  , ta yi saurin kawar da kai ta ce "Me yasa ka kuma zuwa inda nake?"  da sauri ya ce "Kiyi haƙuri, na kasa jurewa ne!"    "Ka fi so ai ta maimaita magana ɗaya kenan?, kar ka takurawa rayuwata do Allah "    ƙasa ya yi da kai cikin rashin sanin abun cewa.

    "Ba na so ka ƙara nema na, ka dena don Allah"  tana faɗen haka ta juya da nufin barin wajen  "Hibbah!  me yasa ba za ki so ni ba?, mene ne nakasu a tare da ni?, ko kuma ni na cancanci ɗaukar nauyin laifin da ba ni na aikata ba ?"  sai da ya kai ƙarshe sannan  ta sauke idanunta daga kan fuskarsa, jikinta ya yi wani bala'in sanyi  tabbas tana matuƙar tausayin sa ,  ɗan nisawa ta yi ta ce "Kai ma me ya sa ka shigo rayuwata?, ai ganganci ka yi ka san babu haɗi tsakanin Biri da gada!, me ya sa ma duk Ƴaƴan masu kuɗin duniyar nan ka rasa wadda za ka so a cikin su     sai da ka hauro kaina?, saboda ni ce zan fi daɗin wulaƙantawa ko??"
   lumshe idanunsa da suka ciko da ƙwalla ya yi gami da haɗiye wani ƙullutu da ya tsaye a maƙoshinsa.

  Cikin  nutsuwa ya tako zuwa daf da ita sannan ya ware mata  idanunsa da ke bayyanar da tsantsan ƙaunarta  "Ban san dalilin da yasa nake sonki ba Hibbah!, kawai..... kawai ina sonki  kuma ina son ki zamo Matata!"

   "Ban san wace rantsuwa ce zanyi ki yarda da ni ba!  na riga na taka sawun ɓarawo!,  amma Hibba!,,,  Tabbas farincikina yana a tare da ke,   kin fi dacewa da ni fiye da kowace Mace!'"......    .

   "Hibbah!   na rasa  duk wani nazari da tunanina, ba na iya komai gabakiɗaya ba ni da nutsuwa na riga na burkice , na rasa jina da gani har ma da hankalina,   Kuɗi!, Dukiya!, Lafiya!, ƙasaita!, duk na manta mene ne daɗinsu,    ke kawai nake hange! ke nake son mallaka a matsayin Matata , maybe sai bayan hakan ne zan dawo hayyacina!  amma ban sani ba ko haka zan cigaba da rayuwa  a burkice cikin mawuyacin hali!".........




Aunty Indo