GADAR GIWA... (Toro ke buga mata ganga)
GADAR GIWA
by @auntyindo
Shiru ne ya ratsa tsakaninsu kafin ya cigaba da cewa "Ina son in rayu da ke Hibba! ina sonki da dukkan gaskiyata, ni a gurina kina da Martaba da Kima, kuma na riga na zaɓe ki na shirya rabuwa da abubuwa da yawa akan ki idan har buƙatar hakan ta taso!"
"Uhm! sai surutu nake yi kuma ba lallai ki yarda da ni ba , ki je ki cigaba da aikinki, dama!... dama kawai ina son ganinki ne , ki yi haƙuri bisa takura miki da na yi ,,,,, zan yi kwana Bakwai ba tare da na takura miki ba!" ya ƙarasa maganar yana sakin
wani maraitaccen murmushi....
Banda ido ba abin da ta iya bin sa da shi, ta ji me ya ce a ƙarshe sai dai ta rasa ƙwarin gwiwar ɗaga ƙafarta ta bar shi a gurin.
Cigaba tayi da ƙwalalo masa idanu zuciyarta cike taf da tunane-tunane ta rasa gane me yake shirin faruwa da ita , ko shakka babu ta yi bala'in damuwa da damuwarsa haka kawai take jin ina ma za ta iya zamowa maganin matsalarsa?!,,, "Hibbah! kar ki damu da abin da ya dame ni fa!, saboda.....!"" shiru ya yi saboda kukan da yake shirin kufce masa... da sauri ya juya ga motarsa ya shige ya fara ƙoƙarin barin wajen......
Sakin baki ta yi tana kallon motar cike da mamakin abin da take gani tamkar a mafarki.
Har sai da ya ɓacewa ganinta sannan ta koma cikin sanyin jiki, tun da ta zauna ta buga tagumi ko ido ba ta ƙara ɗagowa ta kalli kowa ba.
"Na zaɓi Ismail,,, gashi Damuwar wani daban ta dame ni, tabbas idan na sake na kama son Hamdan na ɗaukar wa kaina Dala ba Gammo, kuma na cuci kaina domin na san ba zan yi farinciki da Aurensa ba koda kuwa da gaske ne abin da yake faɗa min!"
kaɗan daga cikin zantukan da take yi ita da Zuciyarta kenan.
..... ....... Duk yadda ta so dakatar da kanta da faɗawa Rintsin Son Hamdan ta kasa, gabakiɗaya hankalinta ya koma kansa, a koda yaushe tsammanin ganinsa take yi, sai dai shiru gashi har kwana biyar sun shuɗe, ta yi zaton ganinsa ko a Gida ko a wajen Aiki amma abun ya ci tura.
Duk jikinta ya yi sanyi ƙalau , zuciyarta ta yi rauni!, tsananin tausayin kanta ya gama kama ta, yanzu ta tabbatarwa kanta tana son shi kamar dai yadda zuciyarta take gaya mata tun ranar da ya bayyana mata soyayyarsa.
Tana zaune kan Kujera ta kifa kai akan Keken ɗinki tamkar wadda take bacci, sai dai ba baccin take ba ido biyu ne mai kama da mafarki.
Raihana ce ta ƙaraso wajen tana cewa "Madam Hibba! kin zama wata muguwar raguwa fa yanzu, ba kya aiki sai gyangyaɗi Ɗalibanki suna ta ba ni Maja wallahi!" idanunta da suka ƙanƙance ta ɗago ta zuba wa Raihana kafin ta ce "Ayya ku yi haƙuri don Allah, in sha Allah zan dawo daidai, kawai ƴar damuwa ce kaɗan!" Raihana ta murmusa gami da cewa "Damuwar ma Ƴa ce kike ganin? damuwar Soyayya kuwa ba ƙaramar damuwa ba ce don na ga alama ke ma kin fara bin Sawun Saurayin naki shugaban Natattu!" "Kamar ya kenan ? waye natacce kuma?" Hibba ta faɗa cikin alamun mamaki.
"Wannan wanda kika sharawa marin mana, kullum sai ya zo Masana'antar nan fa, amma can baya yake tsayawa ni ina ganinsa ke kuma ba ki taɓa lura ba don ba kya ta kowa yanzu, ban san me ye dalilinsa na zuwa yana laɓewa ba kuma wataran da zarar kin tafi shi ma yake tafiya, ni dai yadda na fahimta kawai zuwa yake don ya gan ki!" "Uhm! daɗina da ke akwai iya tsara Tatsuniya, kin ga muje ki raka ni in ɗau hutu kwana biyu ba zan zo ba!" ta faɗa tare da tashi tana haɗa ƴan komatsenta.
Raihana ta ce "Ke kuma matsalarki rashin yarda, na gaya miki ni ba na ƙarya kawai yawan faɗi ba a tambaye ka ba shi yake damu na, kuma ki je ki duba yanzu za ki gan shi tun da lokacin tafiyarki ya kusa" "Wai kina nufin an kai kwana biyar kina ganinsa anan kuma?, ta ya zan yarda da hakan? haba dai ni ki ƙyaleni don Allah"
A fusace Raihana ta ce "Ni wallahi na tsani in faɗa wa Mutum gaskiya ya ƙi yarda, me ye haɗina da shi da zan zo ina miki ƙaryar ganinsa?, aikin banza!, ki je ki tambayi Aunty Rahma ma za ta ba ki tabbaci, kuma sai ki fita ki duba don gane wa idonki!" ta ƙarasa maganar tana ƙoƙarin barin wajen,,, da sauri Hibba ta riƙo ta tana cewa "Ai na yarda yi haƙuri, mu je ki raka ni in gan shi don Allah" "Wallahi banda kin haɗa ni da Allah da ba zan je ba!" Raihana ta faɗa tare da zumɓurar baki ta yi gaba.
Cikin sauri Hibba ta bi bayanta tana cewa "Amma dai daga nesa za ki nuna min ba zan je inda yake ba" "Oho miki!" Raihana ta faɗa ba tare da ta juyo ba.
Sai da suka je wajen motar Sannan Raihana ta ce "To ga motar nan, ni dai Mota kala biyu na ga yana zuwa da ita, da wannan da wata Fara" kamar za ta fashe da kuka ta ce "To kuma sai ki kawo ni gurin? a nesa fa na ce miki!, kuma wannan Motar ma me baƙin Glass ta yaya zan ga wanda yake ciki?"
Jin Raihana ba ta ce komai ba yasa ta yi saurin juyowa tana faɗin "Wai me!...." shiru ta yi saboda jin ta gabje wani daban ba Raihanan ba , ta yi baya da sauri tana zazzaro ido zuciyarta na dukan sittin saba'in....
"Hamdan!" ta faɗa cikin rawar baki, "Na'am ! yau da wuri za ki tafi ne?" ya faɗa yana murmushi da sauri ta girgiza kai tare da mayar da kallonta ga Raihana wadda ta yi gefe tana Dariya,,, murguɗa mata baki ta yi ta ce "Me ye amfanin laɓewa daga nesan to?, kai ma Yallaɓai sai wani Bi bango kake yi , ni fa na fi so in ga ana kashe love !" Hamdan ya yi murmushi gami da cewa "Ƙawar nan taki akwai ta da Barkwanci!" "To ina ruwanka?!" Hibba ta faɗa a hasale, ƙasa ya yi da kai yana ɗan sosa ƙeya.
"Za ki fara kenan!, ni kin ga tafiyata!" Raihana ta faɗa tare da yin gaba.
"Wai me ya sa kake wahalar da kanka ne?!" "Ke ma me ya sa ba za ki so ni ba?" "Malam shi fa so ba haka yake ba!, wai ma me yasa kake zuwa kana ƙare min kallo ba tare da sani na ba?" "Saboda na miki alƙawarin ba zan takura miki ba har Sati ɗaya
*Aunty INDO*