GADAR GIWA... (Toro ke buga mata ganga)
GADAR GIWA
by @auntyindo
"To ai kamata ya yi ka fita daga rayuwata ba wai ka dinga laɓewa kana kallo na ba!"
murmushi mai ciwo ya yi "Hibbah Don Allah ki Aure ni!" ya faɗa yana zuba mata narkakkun idanunsa da suka cika taf! da ƙwalla.
Da sauri ta juya masa baya tana cewa "A'ah!" cikin rawar murya.
"Don Allah ki temake ni Hibba ! ni kaina ban san a wane hali nake ba a yanzu ji na nake tamkar wani zautacce!, don Allah ki Aure ni koda ba zaki Kyautata min ba, ko da ba za ki taɓa sanya ni farinciki ba, zan rayu da ke a haka!"
Dogon numfashi Hibba ta ja tare da ƙoƙarin hana kukanta fitowa. Goge ƙwalla ta yi kafin ta juyo tana fuskantar sa, "Me yasa wai dole sai ni?, me yasa ba ka zaɓi kowace Mace a Danginku ba sai da ka zo kan Marainiya wadda ba ta da gata sai Allah?!" "Ƙaddara ce Hibba!, duk ba ni da amsar da zan ba ki, amma za ta iya yuwuwa Sakayya ce!"
"To idan na amince zan Aure ka,,, kai da izinin wa za ka Aureni?"
"Yardar Allah kawai nake nema sai taki!, ba zan gaza ba muddin kin Amince min!"
shiru ne ya ratsa wajen na ɗan lokaci kafin Hibba ta ce "Na yarda Ƙaddara ce Hamdan!, amma ni A
amincewar Abbana da Umma shi ne amincewata, sai kuma Ismail;, kamar yadda za ka nemi Yardar Ummana da Abbana haka za ka nemi Yardar sa, idan har ya sakar maka to na shirya wa Tarar wannan Tsatstsauran Ƙalubalen!" zirr!!! hawaye suka fara gudu akan kumatunsa, cikin shashshekar kuka yace "Amma Hibba idan Maama ta karɓe ni shi ma Abba na san zai Amince domin ta, amma shi Ismail ta yaya zai yarda ya bar min ke idan ba ke kika zaɓi hakan ba? Hibba babu wani Namiji da yake son ki kuma ya yarda ya bar wa wani ya Aure ki!, don Allah ki canja min wannn Jarrabawar, ta yi min tsauri da yawa please Hibbana!" ya ƙarasa maganar yana ƙara rushewa da kuka tamkar ƙaramim Yaro....
Sauke numfashi ta yi tare da juyawa ta ce "Idan ka shirya sai ka tunkare shi, ni yanzu na gama magana, ko kowa ya amince dole sai Ismail ya amince sannan za ka samu dama ta, saboda ya cancanta!"
"Ya salam! Hibba don Allah ki fahimce ni mana!" banza ta yi masa ta cigaba da tafiya, ya rakata da ido har ta ɓace wa ganinsa, sannan ya koma mota cikin sauri,,,, "Wai wannan wace irin Masifa ce na faɗa! , yanzu ya zan yi?!" ya jefa wa kansa tambayar tare da rungume kansa da duk hannayensa.
"Ya zama dole kabyi abin da ta ce indai har da gaske kake!" wani sashi na zuciyarsa ya ba shi wannan shawarar wadda ta yi nasarar zama daram a tunaninsa.
A waje ya gama wuninsa da gallafiri duk ya rasa inda zai sa kansa, sai da ƙyar ya iya danne halin da yake ciki sannan ya tunkari Gida....
Ammy da Mamy da Arman ne kaɗai suka tambayi lafiyarsa, don kuwa duk yadda ya kai ga iya danne labarin zuciyarsa dolensa fuska ta bayya, sauran Ƙannensa kuwa wasu ba su lura da sauyawarsa ba, wasu kuma sun san ba amsa don haka ba su tambayi lafiyarsa ba.
Ammarah, Hairanah, Arman, Fauzan, Hamdan, Hairan, Sabran, suna zaune a Babban Falo suna Hira,.... su Arman ne ƙarfin Hirar Hamdan da Hairan kuwa Ƴan shiru-shiru ne, kowa ya cukune fuska yana tunanin abin da ya dame shi.
Daddy ne ya bayyana a Falon yana Ƙwallawa Hamdan kira , Mamy da Ammy na biye da shi...
Sai da ya haɗiyi wani ƙullutun yawu kafin ya miƙe yana cewa "Ga ni anan fa Dad!"
A masife Daddy ya ce "Ina kake zuwa ne kwanan nan?! wai me yake damun ka ne???" Girgiza kai ya yi ya ce "Ba komai!" "Ƙarya kake Dan Ubanka!!"" Daddy ya faɗa a fusace kamar zai hau kansa da duka,,, cigaba ya yi da cewa "Na lura yanzu hankalinka ba akan aikinka yake ba, ga yawo da ka sa a ranka!!!,,, ka san Allah kar ka yarda ka jawo min Asara!, wallahi in ka yi haka sai na saɓa maka, wai ma ina kake zuwa ne?? me ya dame ka duk ka yi wannan burkicewar kamar wanda ya fara Shaye-shaye???!!" ya ƙarasa magana cikin tsawa.
Ammy ta ce "Ato! kai ma sai ka jarraba ni dai na yi juyin Duniya na kasa gane abin da yake damunsa, amma fa dan canjawa ya canja, Farida Ƴar Hajja Sumayya da ta zo yaron nan sai ya nuna bai ma san ta ba, ƙarshe ma sai ya hauta da faɗa kamar zai kai mata naushi, kuma Da ba haka suke ba hira yake da ita sosai dan har soyayya ma suke!"
Sosai jawabin Ammy ya ƙara hasala zuciyar Daddy, ya ƙara ware masa idanunsa wanda suka cika taf da tsananin Ɓacin rai, cikin tsawa ya ce "Ba magana ake maka ba?!! ko
ka fara Shan Giya ne ??!"
Cike da Ɓacin rai da takaici Hamdan ya ce "Na ce ba abin da yake damu na! kawai yanayi ne, kuma zan dawo daidai, don Allah ku bar takura min da tambaya mana!" " Okay! Umarni kake ba mu ko shawartar mu kake?! Kai Mace mai ciki ne da yanayi zai sa ka dinga wannan Abun?!!! " "Ya Allah!! Daddy don Allah ka fahimce ni mana!, ni ba ni da wata damuwa!, inda nake zuwa kuma kawai na ware wa Rayuwata lokaci ne don ina buƙatar in dinga sararawa kamar kowane Mutum mai Ƴanci! , ina buƙatar in yi yawo a gari don Ƙara wa kaina ilima ba wai in ƙare wajen saitawa da lissafin shiga da fitar Kuɗi ko Kaya ba!!, don Allah a yi min wannan uzurin! ! ! !"
"Wallahil azim ina ƙara gaya maka kar ka bari ka jawo min asara!, ka san dai kana da taka Dukiyar, don haka ka san da sani ba zan raga maka ba tun da wauta ce ta jawo ba tsautsayi ba!"
"In sha Allahu babu abin da zai faru, ka yi hasashen alkairi ba irin wannan ba don Allah!"
wata shegiyar Harara Daddy ya zuba masa cike da rashin sanin abun cewa, sai kuma ya yi ƙwafa gami da jinjina kai.
*Aunty INDO*