GADAR GIWA... (Toro ke buga mata ganga)
GADAR GIWA
by @auntyindo
Hamdan ya koma ya zauna tare da sauke nannauyan numfashi, sassauta murya ya yi ya ce "Daddy ku yi haƙuri don Allah!, kawai kun san rayuwa yanayin Dan Adam yana iya canjawa, kuma komai lokaci ne zai wuce in sha Allah!"
"To ai kai ne sai dai kawai a ga kana wani abu haka kamar shashasha!, ai bayani zak ka dinga yi in ma kana son ka je wani gurin ɗin ne ai sai ka gaya min ba wai in ga ka manta da sha'anina ka kama naka ba!" "A yi haƙuri zan kula in sha Allah, Ammy ku yi haƙuri ita ma Farida a ba ta haƙuri kawai ba na cikin yanayin surutun nata ne a lokacin har a yanzu ma, kuma a gaya mata ta dena yawan shishshige min ba na so!" Dukkansu ba su iya ce masa komai ba sai ido , shi Daddy ya sauka daga fushinsa Ammy kuwa takaici da mamakin abin da ya faɗa su suka sa ta saki baki tana kallonsa.
____________
"Hibba! wai kina son Hamdan ne??!" Maama ta jefo mata tambayar tana tsare ta da ido..
Dim!!! gabanta ya faɗi, ta yi saurin ɗagowa tana zaro ido, tambayar ta yi bala'in zo mata a bazata ta kuma girgiza dukka jijiyoyin jikinta.
Gaurayar da idanunsu suka yi ne ya sa ta yi saurin sauke kai ƙasa tare da girgiza shi alamar "A'a!" Maama ta ce "Ƙarya za ki yi min?, kenan ban kai matsayin ki gaya min gaskiya ba ko?" sake girgiza kai ta yi nan take dukkan rauninta ya bayyana, cikin rawar jiki ta ce "Ba haka ba ne Maa!, bana son shi ki yi haƙuri don Allah!" ta ƙarasa maganar tare da ba wa kukanta damar fitowa...
Murmushin tausayawa Maama ta saki gami da karɓe wuƙar yankan Salak ɗin nata, ta ajiye gefe sannan ta ce "Har yanzu dai ba gaskiyar kika gaya min ba!, ya zo ya same mu yana neman izini kokuma in ce ma yana neman mu ba shi Aurenki, kuma sai nake ganin kamar a gurinki ya samu ƙwarin gwiwar zuwa wajen mu don ba da ni kaɗai ya yi magana ba har da Abbanki,, kin ga kuwa yanzu faɗen gaskiyarki shi ne samuwar amsarmu !"
girgiza kai ta yi ta ce "A'a !" sai kuma ta cigaba da kuka "A'a me? wannan kukan naki ba shi ne maganin matsalar ba, ki faɗa min abin da yake a tunaninki!, ko kina da wani abokin shawara ne wanda ya wuce ni?"
girgiza kai ta yi a karo na ba adadi, ta ɗan kalli Mama kafin ta ce "Sai abin da kika ce !, idan ba kya son shi ni ma ba na son shi Maama!!! , ni ban san ta yaya ma ya shigo rayuwata ba! ba laifina ba ne fa!" ta ƙarasa maganar cikin matsanancin kuka.
Maa ta murmusa gami da cewa "Hibba kenan, ai dama duk wanda yanga laifinki to yana da ƙarancin ilimi wajen sanin girman Allah!, shi ma Hamdan ba laifi ya yi ba kuma ba shi ya zaɓi hakan ba!, yanzu dai in cewa Abba kina son...." da sauri ta katse ta da cewa "Ni zaɓin ku shi ne nawa! idan ba kya son shi fa ni ma ba zan taɓa son shi ba!!!"
"Kayya!!,,, Hibba! Hamdan fa Ɗana ne! kuma ina jin zafi da takaicin halin da yake ciki, sai aka yi sa'a ina da damar temaka masa, to tayaya kike tunanin zan ƙi shi?, shi dama can Hamdan mutum ne mai kamala da dattaku tun yana Yaro, sannan duk wani tsegumi da rigimar da ta shafi mu iyayensa ba ya shiga , ni bai taɓa ɓata min rai ba, kin ga kuwa ba shi da laifi a cikin abin da wasu daban suke yi"
"Na san ba ki da kwalo-kwalo Hibba! a maganar da muka yi na fahimci kina son Hamdan!"
cikin kuka Hibba ta ce "Ni ma ban san haka za ta faru ba"
"Oh na fahimta kuma na amince , don ta ni ba ni da matsala da Aurenku, amma ba sai na ƙara dogon bayani ba na san kin fahimta, kuma kin sani Aurar sa tunkarar ƙalubale ne,, kuma ni na yarda da Hamdan shi ma Bai-ɗaya ne kamar ke !!, idan kin shirya to ni ma a shirye nake, ba zan tauye ku ba kuma babu wani ɗan adam da ya isa ya haramta abin da Allah ya halatta!"
ƙasa Hibba ta yi da kai tana ƙoƙarin rage wa kukanta gudu ba tare da ta bada amsa ba.
"Uhm! Allah ya tabbatar mana da alkairi , cigaba da aikinki" Maama ta faɗa tare da miƙewa don barin wurin.
Cike da mamaki Kabeer yake kallon Muhsin wanda ya rufe ido yana zubo bayani, katse shi ya yi da cewa "Muhsin! wai kai ne kake maganar kana son wannan Yarinyar daga ganinta sau ɗaya?, ni ban ga abun burgewa a jikinta ba in ba jaraba irin taka ba" Muhsin ya ce "Idan kai ba ka gani ba ni na gani, shi dama so ai haka yake ba a taruwa akan abu ɗaya, ni na fi murna ma da ba ka ga abun burgewar ba, jarababbe!"
Dariya Kabir ya yi ya ce "Ranar fa nake gaya maka gani na yi Hamdan yana bin ta da wani mugun kallon ƙurilla, Ɗan iska idan ya ga muna kula ƴan Mata ya ce ba mu da aikin yi, amma shi da ya tashi nashi yanda ka san zai mata fyaɗe da ido!" ya ƙarasa maganar yana dariya, shi kuwa Muhsin abun haushi ya ba shi saboda wani abu da ya soki zuciyarsa, cikin haɗe fuska ya ce "Kai abun yake bawa dariya ba ni ba, dama Hamdan ai kawai sai dai a yi sha'ani Shegen Mutum me tsaurin halin tsiya, ni ka rabani da maganarsa ka yi wadda ta shafe ni, ni kawai zan je wajen Yarinyar, sunanta Hibba ko?" "Muhsin ka dawo hayyacinka, wannan yarinyar fa ka wuce ajinta malam haba!, ai wallahi ko Daddynka ba zai bari ka Aure ta ba ma, duk ga Wayayyu nan Ƴaƴan Manya masu ilimi amma ka ce kana son wannan baƙar Yarinyar, kai wallahi ba ma sonta Kake ba kawai Sha'awarta kake" wani mugun kallo Muhsin ya zuba wa Kabir kafin ya ce "Amma kai Jahili ne wallahi, ni fa ba irinka ba ne !, kai ne kake yi wa kowace mace kallon Sha'awa amma ni da gaske nake kuma zan jaraba Sa'ata, tun kafin wancan Mayen ya je ya Fyaɗe ta!"
"Ai kuwa zamu raba gari a wannan sabgar, ba da ni za ai wannan abun kunyar ba, ai ni wallahi kaf ma Family ban ga wata wadda zan iya So ba, sai da soyayyar ɓata wa juna lokaci, bare ma wannan Yarinyar ai ko irin Soyayyar nan da muke da su Ikram wadda za ka samu kaya a bati ba zan iya yi da ita ba" "Ai dama ita daga ganinta ba tsararka ba ce, kuma ba kalar su Ikram ba ce, ai kamun kanta ma ya fi Ƙarfin mayen Mata irin ka" "To ya ishe ka haka Muhsin, ka saka ni gaba sai karta min maganganu kake yi akan wannan Matsiyaciyar Yarinyar mai kama da Baiwa!, to wallahi kar ma ka ƙara yi min zancenta indai kana so Abotarmu ta cigaba, shi kuwa Hamdan dama babu ni babu shi yanzu, tun da gani yake ya fi Ƙarfinmu saboda Ubansa ya fi namu Kuɗi" "Ashe ka gane gaskiya, ba dai ya ga Kuɗi suna shigo masa ta ko'ina ba, ai sai wulaƙanci kawai a ganinsa ya isa ya taka kowa, to wallahi ni bai isa ya yi min ba don duk abin da yake taƙama da shi nima na Tara!" Kabir yace "Amma fa Duk da haka akwai muguwar tazara Guy!, shi fa Ubansa ɗan Kasuwa ne Uwarsa ma haka Shi ma kansa haka, mu kuwa in banda Bin mata ba abin da muka sa a gaba!" wani dogon tsaki Muhsin ya zuƙa, har cikin ransa ya ji haushin maganar amma da ya san gaskiya ce se yayi banza da zancen.
*Aunty INDO*