NISFU DEENIY(The Yerwa family love triangle)

CHAPTER 29 (The milestone).

by @deejasmah

CHAPTER 29 (The milestone).

Ba ta tanka mata ba sai mai da kanta da tayi kan Zulfaa tana mata sharrin saura ita itama tana ramawa da saura mu dai, a nan gidan ta yini ba ta iya matsawa ko nan da can tana nan manne da yaron mai matuk'ar kama da ElSadeeq kuma kamar almara ya d'ebo haskenta don ko yaron fari ne tas irin nata. Murmushi tayi bayan idar da sallahr la'asar d'inta ta dubi Suleim taka cewa " ni dai nayi booking Afdhal wa 'yata wallahi".  





"Waye Afdhal kuma?" In ji Zulfaa dake zaune kan dadduma don tunda ta yi sallah ta kasa tashi tana daga zaune sai nishi take yi. 

"Ga shi nan babyna ai sunanshi Afdhal".



"Auuu ashe ma har an sa masa suna kenan?"


"Koma menene sunanshi ni dai Afdhal zan na kiranshi, kuma sirikana ne".



"Mai haihuwa daban mai sa suna daban, ina k'aunar shahararki".



"Ke ma ai ni zan sa miki suna yarinya, sai dai in baki haihu ba. In namiji ne Ayan mace kuma Ayanah".



"Ke zaki ga Ayyana ba ni ba, ai gwara ma namijin Ayan amma ni ban son wata Ayanah a na zaman lafiya".



Dariya Suleim da ta fito wanka tayi tana cewa "ke kuma naki me za'a saka mata ".



"Wa ma ya sani?" Ta k'arashe da gaskiyarta har cikin ranta, Zulfaa tace " Ayanahr ce zaki haifa ba komai ba''.



"Toh Allah ya rayata " ta furta tana shafa kumatun jaririn sai kuma tace "Allah yaron nan da ni yake kama, ji shi fa mai kyau sosai Allah ya taimake shi bai d'ebo wasu ba".



"Ke dai kika sani 'yar rainin sense ni ba biye miki zan yi ba". Dariya suka kwashe da shi don kowa ya san me take nufi da maganarta Farhan take tsokana, tunda kuma ba ya nan toh matarshi ce zata shigan masa ita kuma haki take fama da shi.




Sai bayan ishai Burhaan ya dawo gidan shi da su Sadeeq da Farhaan, a parlor suka zauna Farhaan ne ya shiga ciki ya nemi iso wa Sadeeq akan zai gana da Suleim. Dukansu fitowa suka yi Farhaan d'in rik'e da hannun Zulfaa don tafiyar wahala take ba ta ainun ita Nadeefah ta d'auko yaron ta kawo ma Islaam, mik'a masa yaron tayi tana zama a kujerar dake opposite ta shi.




Duban fuskar yaron yayi mai kyau da shi yana bacci wato a kiyayi rabo don tabbas rabon yaron nan ne ya hana shi furtawa Suleim yana sonta ya kuma kasa sanarwa ko shi Sadeeq d'in don da yayi haka da zai iya sadaukar da son da yake mata ya bar masa ita, murmushi ya saki again tuno shi ma akwai d'anshi lik'e a marar Nadeefah. 




Dubanshi tayi da murmushi a fuskanta tana cewa " Yaa ya ka ga yaron nan, don Allah ba dani yake kama ba?". 


"Sure wife har da yanda kike barci ma ".



"Toh Allah ya sa kar ya d'auko yawan surutun ki" in ji Farhaan yana rik'e da hannun Zulfaa da tun safe take nan dai ba wani dad'i take ji ba. Murgud'a baki tayi tace " ko kuma ya d'auko naka ba, da yaron nan ya bani wlh. Ai gwara ya d'auko nawa sau dubu da naka don kai naka sai an had'a masa da ruk'iyya ".




"Yenyenyen da shegen bakin ki mai kaifi, ai surutunki ya fi nawa......"



"Amfani ba....!" Ta k'arashe masa tana murgud'a baki, girgiza kai Burhaan yayi shi ko Farhaan k'wata yayi don ya ma rasa mai zai ce mata.



Kallonta yayi a can k'asan mak'oshi yace " Wife ai kin gama barkan na yau ko? Mu je gida ki sama min wani abu yinin yau na gaza cin komai kuma yunwa nake ji".




Cikeda kulawa tace "toh Yaa mu je gida kawai". Tana mik'ewa tsaye yaron ta d'auka ta wuce da shi ciki, a sama-sama ta yi wa Suleim sallama don ita da Sadeeq d'in are very busy. D'akin Mommy ta shiga ta mata sallama kafin ta fito sai da ta sake tsokanar su Farhaan kafin suka wuce, ba su wuce gidan ba ganin dare yayi tsayawa yayi a wani eatery suka shiga ciki ordern abinci yayi musu a wurin suka ci wanda ya d'auke su lokaci mai tsayi sosai kafin suka wuce gidan kusan k'arfe goman da ya zama kamar wani sabon lokacin komawarsu gida.




Da daren ranar aka wuce da Zulfaa asibiti don a hanyarsu ta komawa gida ruwan nak'uda ya b'alle mata, ta ko sha wuya don sai gabanin asuba ta sauka itama namiji ta haifa k'ato sosai don yafi d'an gidan Suleim sosai. Kasancewar haihuwar dare ne ya sa ba kowa ya sani ba sai asuban ne ma Burhaan ya ji bai ko koma gida ba ya wuce asibitin ba tareda ya sanar da Nadeefahn da ta kwana da zazzab'i ba itama so yayi su je asibiti da safiyan yau.




Sanda yaje har an fara shirin sallamar su taya Farhaan k'arasa cike abubuwa yayi sannan a bisa k'aida ya d'auketa zuwa gidan Mommy don zaman jego, bai dai shiga ciki ba ne ya koma gida lokacin har ta tashi tana tsaka da aikin gida.




Sanda ya shigo a parlor ya tarda ta tana kakkaɓe ƙurar wurin TV, ajiyar zuciya ya sauke yana zama a cikin kujera yana kallonta. Ajiye dustern tayi ta taho inda yake zaune zama tayi ta rik'e hannunshi a hankali tace " yau nisa kayi kenan? Welcome back" tunanin ta ko motsa jiki yaje duk da bai yi kama da wanda ya fita exercise ba.

Iska ya furzar yace " daga Yerwa nake ma, ya jikinki?". Murmushi tayi tana cewa " ya sauka ai zazzab'in me ake yi a Yerwan?". 



"Zulfaa ce ta haihu, da asuba itama namiji".



"Yiiiiiiii my Allah!!! " ta furta tana daka tsalle kamar wata yarinya, da sauri ya rik'ota yana cewa " careful, hala kina manta da abu a jikinki ne".



"Wallahi murna nake yi ne, ashe jiya duk nishin da take yi na labour ne Allah Zulfaa".


"Don kina murna sai ki min asara? Da ko kin ga k'arshen murna".



Murmushi tayi tana kwantar da kanta a kan kafad'arshi tace "I'm sorry Yaa, bari in yi wanka toh mu tafi in ga babyn ".



"Ba inda zaki fita yanzu haka jiya kika yi fa, ba zaki huta a gida ba ke ma fa ba wani lafiya kike da shi ba kuma ma yayi sassafe".



"Ni fa na warke Yaa...."


"Sai kuma ki yi " ya furta yana mai zare ta daga jikinshi ya mik'e tsaye, k'wal da idanu tayi kamar za ta yi kuka tace " please Yaa''.




"Sai anjima zaki fita Nadeefah! In kuma kika matsa min ba ma zaki fita anjimar ba in kuma kina ganin wasa ne tohm".


Yana fad'in haka yayi wucewarshi zuwa d'akinshi ya bar ta nan, da idanu ta raka shi tana murmushi 'at least ya damu' ta faɗi can ƙasan numfashi ba ta ko bi shi a baya ba ta cigaba da abinda take yi. Tana gamawa tayi wucewarta kitchen ta had'a musu breakfast milk naan da dressed chicken dessert ta had'a sai creamy latte da strawberry chocolate chip cookies.



Wucewarta tayi d'aki wanka tayi ta shirya yau ma cikin doguwar rigar atamfa, simple d'auri tayi ta baza turare. Kallon agogo tayi sai yanzu 9 tayi  b'ata fuska tayi don ta tabbatar da babu abinda zai sa su fita yanzu don ko tantama babu bacci yake yi tabbas. Tura baki tayi ta fita daga d'akin ta wuce na shi a kwance ta tarda shi kan rug babu ko riga jikinshi ya k'ure AC alamun zafi yayi masa yawa, tsura masa idanu tayi ta na mai bin k'ark'arfan jikinshi da wani d'an iskan kallon maita haka nan tana jin k'aunar kasancewa da shi.




Ajiyar zuciya ta sauke tana duk'ar da kanta k'asa ta juya da nufin komawa inda ta fito.



"Kin gama kallon ne ko in buɗe miki ki kalla da kyau ne?" ya furta wanda ya sa ta juyowa tana dubanshi, yana nan a yanda yake ko motsi bai yi ba bai kuma bud'e idon ba.



'Ni Yaa me nake kallo? Ba abinda na kalla".



"Ke ba ma ki iya k'arya ba matar nan, nan kika gama k'ureni da idanu ko k'yaftawa babu. A yunwace fa kike kallona, kamar zaki cinye ni ɗanye amma yanzu ki ce baki kalli komai ba" ya k'arashe yana bud'e idanunshi da suke nan duk sun canja kala.



"Ni ban san abinda kake magana ba".



"Ni ai na sani tunda na gani, kuma kar ki damu don ba abun kunya kika yi ba ni naki ne taho ki yi duk abinda zuciyar ki je gaya miki a kaina". Da wata kafurar murya yayi maganar wanda ya sake harba wani nuclear bomb musamman ma yanda yake lumshe idanu yana jan yaji da cizon baki kamar namijin karuwa, har wani hargitsa gashin kan shi yake yi yana miƙa mata hannun shi hakan ya sa ta kasa yin komai sai rik'e hannun da ya mik'o mata da tayi.



Luff ta shige jikinshi kamar yanda kuma ya fad'in ba ta yi k'asa a guiwa wajen aikata duk abinda zuciyar tata take raya mata a kan shi ba. Ta ɗauki lokacin ta kan duk wata gaɓa dake tsokane mata idanu bai kuma saurara ba shima ya shiga tayata.



Sun d'auki time mai matuk'ar tsayi suna faranta ran juna da raya k'auna kai kace ba za a ragewa gobe ta samu ba, sun ma manta da wata breakfast balle kuma fitan da ta sa wa k'wak'wa sai da suka tabbatar da sun yayyafawa wutar dake damunsu ruwa kafin suka sararawa juna.



Rungume juna suka yi tsam suna mai da numfashi, kitson kanta da ya sha mai ya sunsuna a hankali yana shak'ar sassanyar k'amshin hair spray d'in ta yace " Yaushe zaki kwance kitson nan, Ina missing gashin ki da colorn da kike sawa".



"Sai na koma office tukunna".



''Uhmm'' har lokacin yana sinsinarta, sai da suka samu natsuwa na kusan minti talatin kafin ya zare jikinshi ya mik'e lokacin har bacci ya fara d'aukarta. Toilet ya shiga ya d'auro wanka ya fito a zaune ya tarda ta tana lullub'e da bargo, gabanta ya matso ya zauna ya rik'e hannunta yana cewa " you okay? Ko jikin ne?".



"Ina lafiya da, bacci kawai nake ji ".



'Bacci? Hala kin fasa fitan kenan?"


Ture bargon ta shiga k'ok'arin yi ta ma manta ba tufafi a jikinta, sai da ta kusa kai k'ofar toilet ne ta lura ai ko ta k'walla k'ara tana mai shigewa toilet d'in a rikice. Dariya mai sauti ya saki yana mamakin halinta, yo me ya rage a jikinta da bai gani ba? Ai sai dai tsokar jikin ta da k'ashi amma babu wani lungu na jikinta da bai san yaya yake ba. Kai ai inda ya sani a jikinta ko ita kanta ba ta sani ba, ba kai kaɗai bane Malam ita ma ta san komai har da gyara.



Ta d'an dad'e a ciki kafin ta fito sanye da bathrobe d'in shi bak'a kan ta kuma d'aure da towel. Hanyar waje ta nufa inda yake tsaye gaban mirror yana taje kan shi yana cewa " ki dawo min da robe wife don na lura in kika samu kayan mutum sai ya biyo baya'' murmushi kawai tayi ta k'arasa ficewa. 



D'akinta ta wuce tayi sabon shiri cikin Abaya bak'a free kuma plain mara design a jiki, hula ta saka ta zaro wani jersey veil fari k'al komawa parlor tayi ta d'auko handbag d'in da ta fito da shi da. Mai da shi tayi ciki hanger ta ciro k'aramar hermes fara mai kyau sosai takalmi mahad'in jakar ta ciro shi ma hermes ta zura a k'afanta. Sake gyara fuskarta tayi ta kwashi kayanta ta wuce parlor, ba ta ko jira fitowarshi ba ta fara k'ok'arin had'a abinci don yunwa ta ji tana ji a ranta kuma cewa take yi " jiya da yau suna kama da juna".



Tana tsaka da karyawa ya fito tsayawa kallonta yayi da murmushi a fuskarshi don ya tabbatar wannan cin abincin effect d'in cikinshi ne na jikinta, don in da Nadeefahr da ya sani ne ba lallai ta iya cin abinci a irin lokacin da yake mata tayin fita ba. Cira k'afa yayi ya k'araso gabanta ya ja kujera ya zauna k'ok'arin tashi ta fara yi tana so tayi serving d'in shi, hannunta ya rik'e sannan a can k'asan mak'oshi yace " kar ki i'll serve myself".




Murmushi tayi ta cigaba da cin abincinta, serving kan shi yayi ba tare da magana ba suka ci abincin duk da ta riga shi farawa sai da ya rigata gamawa. Tissue ta ja ta goge baki sauran abincin ya fitar wa securities ita kuma ta gyara wurin ta yi wanke-wanke, a gaban mirror ta tsaya ta nad'a scarf d'in ya fito da key a hannu ganin ta shirya kawai ya juya ita ma ta mara masa baya.



San da suka je gidan sun tarda ta tana ta baccin hutu don taji jiki sosai ga kuma allurar hutun da aka yi mata, d'aukar yaron ta yi ta masa addua kamar yadda ta yiwa Afdhal (ta bakinta) yana da kyau shi ma bambancin su da na Suliem kawai haske ya fishi sosai don daga Zulfaan da Farhaan ba fari a ciki. Suna dai da haske sai gayu da gyara da ya taimaki fatar ta su ga haskawa sosai, ko dan kud'in da take ci da ya ishi mai ƙaramin ƙarfi jari.




Kamar jiya bai zauna ba gidan Umma ya wuce kamar ta bi shi gidan Hajjah kuma ta fasa, suna ko zaune sai ga kiran Hajjahn tana d'agawa ta fara k'orafin wai daga yin na ta 'ya'yan har ta ajiyeta gefe ta manta da ita. 




"Ni ina na isa in manta ki Hajjahta?"


"Ki daina wani kirana Hajjahnki, ta ina na zama taki bayan kin manta da tsiron halitta ta".




"Ban isa in manta ki ba Allah, ni ma fa banda lafiya ne wlh ƙarfin hali ne".



"Duk rashin lafiyar taki ai bata hanaki zuwa gidan Yaburra ba ko?".



"Hajjah na zan zo anjima in shaa Allah, zan biyo Yaa Sadeeq in zai zo gidan Ummu ".



"Kar ma ki zo ban neme ki ba ai ".



"Ni dai nace zan zo ai ban ce ki neme ni ba, in na zo ki kore ni ".



"Zaki zo ki same ni ne ".


"Sai na zo".


Daga haka ta kashe wayar Mommy dariya tayi jin rikicin Hajjah da Lele, cewa ta yi " tsakaninku da Hajjah kam sai Allah".


"Hajjah ko rigima".


"Ba dai uwata ba sai dai ta ki".



"Laaa Mommy ba kyau fa, ke ce fa uwar tawa ".



"Allah ya shirya ki Lele ".



"Ameen ya rabbi, Mommyna".



Daga haka ta juya ta bar su nan, Suleim kuma kallonta take yi don cikin nan ba k'aramin kyau ya sa ta k'ara ba komai na ta ya fito cas da shi. Ita dai Lele ba ta ko tanka mata ba hidimarta take ta yi kan ta tsaye duk rawar kai da kararrafinta a kan wannan ciki kamar an d'auke ma ta shi. Suna zaune har Zulfaa ta tashi kasancewar parlorn da mutane ya sa ta zo nan ta zauna aka gaisheta ta amsa tana murmushi, Lele ce ta matso gefenta a kunnenta ta rad'a mata " da alamun Ya Farhan da Ya Sadeeq meeting suka yi wajen baku cikin nan".



"Ke dai yanzu kin fara zama 'yar islamiyya Allah ya shiryaki".


Dariya ta sanya kawai tana mai jingina da kujera, sai kusan azuhur da su Umma zasu wuce ne ta bi su zuwa gida suna tafe suna hira cikeda soyayya da fahimtar juna. Itama gidan Ummun ta shiga barka ta yi mata na k'aruwar da suka samu, sannan suka k'ule cikin d'aki don na su shirye-shiryen akan suna. Ganin ba ta ita suke ba ya sa tana Azuhur ta kwashi k'afafunta sai gidan Hajjah bayan ta turawa Burhaan message. 




Da sallama da muguwar d'oki ta shiga gidan bata parlor sai Yana kawai ta tarar zaune, gaisawa suka yi har da tambayar pepppersoup mai yaji sosai in suna da shi kana ta wuce ciki. A zaune kan dadduma ta tarda ta rik'e da littafin ruhul adab tana karantawa alamun idar da sallahrta kenan, zuwa tayi gefenta ta kwanta nan kan carpet d'in ta d'aura kanta a kan cinyarta.



"Hajjahnah" ta furta full of excitement, bata tanka ba sai kanta da ta dungure sai da ta kai k'arshen shafin da take ne ta harareta tana cewa " idonki kenan?".



"Allah I've missed you".


"Ga zahiri nan ai saboda tsabar missing har k'iba kika k'ara, ke Lele me Burhaan yake baki ne kika bud'e haka?".



"Hajjah ni nayi k'iba? Innalillahi!" Ta k'arashe da sauri tana mik'ewa mirror ta nufa tana kallon kan ta don a duniya in da abun da ta tsana toh k'iba yana d'aya daga ciki shiyasa ma take aikin motsa jiki.



Tashi daga dadduma Hajjahr tayi tana cewa " toh miye in kika yi k'iba".



"Muni zanyi ga kuma matsalolin lafiya, ina ba zai yiwu ba dole in fara exercise gobe".




"Da k'aramin cikin ne zaki fara motsa jiki salon ki je ki b'arar da shi a banza a hanya saboda ke hankali ba wani isan ki yayi ba ko?".



"Hajjah wa ya gaya miki ina da ciki?"



"Sai an gaya min zan san kina da ciki Lele?".



"Kai Hajjah!! ke komai kin sani ne wai?".



" Ba a sani ba, in kuma ji maganar zuwa motsa jiki again ki gani".



"Don Allah Hajjah da gaske na yi k'iba?".



"Ba kiyi ba ramewa kika yi , kar ki dame ni ".



"Toh Alhamdulillah, amma ana zaman lafiya in yi wani k'iba?".



"Ke dai sakara ce miye a k'ibar, ko mu mun mutu ne"


"Ai ba a shekaru na kika yi k'iba ba sai da kika sha miya, mutum ko amarci bai gama ci ba ya fara kayan kitse".



"Don Allah in k'ibar ya zo in kin isa ki hana shi Lele kiyita zama kamar one in damuwar wani ne, k'ila an gaya miki k'aramar mace tana k'iba ne? ".



"Theoryn masu k'iba ba ni an dad'e ba a kalleni k'aramar mace ba in dai har sai nayi k'iba tukunna".



Dariya Hajjah ta sanya ganin da gaskiyarta take maganar ba ta son k'iba, har da k'yaccinta da shan aradu sai ga Yana da bowl d'in peppersoup nan fa Hajjahn ta sake sakata a gaba sai wacce ba ta son k'iba ne bata da aiki kullum sai cin ƙwalama da kayan kitse. Ita dai ba ta biye mata ba don gudun kar ta sa peppersoup d'in ya fitan mata a rai, shan abinta tayi ta gyatse ta haye gadon tayi kwanciyarta fita Hajjahn tayi ta bar ta nan tana baccin da ba ita ta iya tashi ba sai da aka tasheta.



Sai da tayi sallahn ne suka zauna zaman hira da Hajjah wanda rabinshi a kan rainon ciki ne, tips d'in su na tsofaffin 'yan gayu take ta bata ita ko tsaf take aikin haddace su ta kuma d'ora da duk wani kayan k'walama na masu ciki da ta ji tana son ci she shouldn't hesitate in telling her so ita kuma in shaa Allah za ta had'a mata da kanta.



Ba ita ta bar gidan ba sai gab da Magrib lokacin har Umma ta wuce, a kitchen ta tadda Ummun tana aikin abincin dare ita da maid d'inta. Rungumeta tayi da sauri tana mai cewa " Ummuna".



"Habibtie".


"Ummuna guess what.....?"


"What sweetheart?".


"I'm pregnant,,,,Ummu zan zama uwa nima". Ta k'arashe da ihun murna, kasak'e Ummun tayi tana kallonta. 


Dukda cewa ta sake da  Nadeefah amma ba ta tab'a zaton zata iya gaya mata tana da ciki ba sai ga shi ta share mata tantama don ta faɗa mata tana da ciki ba tareda ta kuma ji komai ba.



"Masha Allah sweetheart, congratulations". Ta furta da iyakar gaskiyar ta.



"Me ya fari Ummu? Na ga jikinki yayi sanyi ne me ya faru?".



"Nothing sweetheart, ina taya ki murna ne. Allah ya muku albarka ke da abinda zaki haifa".



"Ameen sweet Ummu nah , yanzu sai ki fara shiri".



"Wata nawa ne?".



"Ummu ba mu sani ba fa, mun dai yi PT Yaa yace zamu je asibiti a gwada".



"Shine kike tafe kina faman yad'awa? Ke Nadeefah".



"Ban gayawa kowa ba Ummu, ke na fara gaya mawa shi ma saboda ina farin cikin na kusa zama uwa" ta maimaita karo na barkatai.



"Zama uwa ba wai iya a baki ba ne sweetheart, soyayya ce da sadaukarwa. Kina kallon gudan jikin ki abinda kika fi so yana girma daga cikin ki har ya zo hannun ki, dole ki ba shi kulawa da lokaci ke komai naki ma zaki ba shi don dama shi ne ke da duk abinda kika mallaka".




Ajiyar zuciya ta sauke tana kallonta don kalamanta sun tab'a ta ainun haka nan take jin ta shirya zama duk wani abu da zai tallafi yaranta zata ba su duk wata kulawa da soyayya ta zame musu uwa da zasu yi alfahari da ita a duniya da lahira.



"Zan zama uwa ta gari In Shaa Allah Ummulkhair, kamar ke".



"Allah ya baki iko sweetheart, Allah ya albarkaci duk zuriyar da zaki haifa nan gaba ya sa su zama silar shigar ki aljanna".


Sake rungumeta tayi tana jin wani sanyi a gab'banta tabbas zama uwa ba wasa ba ne, amma zata tsaya tsayin daka wurin adduar Allah ya bata ikon zama abinda ta kud'ira a rai da ruhinta. Murmushi tayi ta rungumeta itama tana mai jin wani nishad'i a ranta kafar jiya ne ta fito daga labour room tana riƙe da ElSadeeq da itama Nadeefahn sai ga shi a jiya ta rungume d'an Sadeeq anan gaba kuma ta riƙe na Lele tabbas wata kyautar sai ubangiji.




Tare suka yi aikin had'a abincin daren in da Ummu ba wani sake mata komai tayi ba, tana kuma yi tana tambayar ta ko akwai abunda yake damunta ita kuma tana bata amsa da tana lafiya ba kuma abinda yake damunta.



San da Abbu ya dawo da ba don Ummu ta nunassheta ba da sai ta gaya mi shi, sai da ta mata alk'awarin gaya masa da kan ta kafin ta hak'ura. Saɓanin jiya da suka yi dare yau ana ishai Burhaan ya zo ya kinkimi kayanshi zuwa gida inda ta tafi da tsarabar girkin Ummu, haka ya sa yau ma ba ta yi girkin ba sai abincin Ummun da suka ci Burhaan kuma ya fanshe a jikinta don dama abinda ya sa shi d'aukanta da wurin kenan.




Tun da aka yi haihuwar kullum tana hanyar Yerwa ko gajiya ba ta yi wani lokacin su je da Islaam in ya ji zuwa wani lokacin kuma ta tafi ita d'aya a motar ta. Kasancewar an had'a sunan rana d'aya wato randa Zulfaa ta haihu aka k'ara kwana guda kan na Nadeefah ya sanya ana gobe ta d'auko y'an saloon d'in ta suka musu lalle aka yi mata gyaran gashi su kuma aka yi musu kitso banda facials da halawa da aka musu tun ko kafin washegari amaren jegon sun fito tsaf sun kuma haska.




A ranar sai kusan 11:30 suka wuce gida don da ita kwana ta so yi sai da Burhaan ya zo ya d'aure fuska ne ta shiga motar tana kumbura baki, bai ko tanka ta ba sai da suka isa gidan ta kwanta da niyyar hutawa ne ya tara mata gajiya ainun kafin ta koma gefe tana haki.



Gajiyar da ya tara matan ne ya sa ko da safen ba ta samu energyn zuwa gidan ba sai kusan 10am, abinka da gidan sunan 'yan gayu ko shirin sunan ba ayi ba don in ka cire su Najwah da Insiyaa da ta zo daga Kano tun sallah ba ta koma ba. Kasancewar ita zata musu makeup ya sa ko hutawa ba tayi ba ta fara aikinta, simple makeup tayi musu su duka wanda ya fito da fuskarsu sosai ta ɗaura musu ɗankwaki. Tun a lokacin wireless_shot ya fara aikinshi na d'aukansu hoto su da su Sadeeq da Farhaan, ita ma Nadeefah yana gefe da wayarta tana aikin ɗaukan su wani tana streaks wasu kuma status take yi.



Kusan 2 ta kammala shiryawa cikin lace b'aki mai adon gold da cream da aka yiwa d'inkin A-straight kaftan da ya samu jikinta ya rungume tsam, ya kuma fito da hasken da tayi sosai ba ta ko yi kwalliya mai tsayi ba kawai sai nude lips da kuma cat eyes da ta zana wanda ya k'awata kyawun idanunta ainun. Simple d'aurin d'an kwali tayi ta baza turare golden costumes tayi using har a hujin hancinta, da takalmi sai d'an siririn chantily veil d'in ta d'an yafa a kai ta fito.



Nan hankalin kowa ya dawo kanta don dama Nadeefah ta k'ware in dai wajen siye wankan mutane ne, duk had'uwarka tana fitowa sai ta doke ka. Kowa fiddo waya yayi ya fara mata video haka shima wireless shot d'in ita ko sai bata style da take yi tana maimaita musu kowa ya tura mata hotunanta, duk abinda aka yi idon Ainah k'yar a kanta don da tazo sa shirin yada mata magana a gidan sunan sai kuma ta ga kamar ba zai yiwu ba tunda alamu ya nuna tana da ciki hakan ya sa duk taji ba dad'i don yau ba wanda za taci kasuwa a kanshi.



Ita dai aikin gabanta take yi musamman don tabbatar da sunan Yusuf Sadeeq Yerwa da ta lak'abawa Afdhal a tun ranar haihuwarshi tunda Sadeeq yace sunan Abbu zai saka da Mohammed Farhaan Yerwa da shi ma bisa zab'in suna irin nata ta sawa Azad. A nan garden d'in gidan Mommy akayi taron sunan yaran gata wanda aka ci aka sha aka chase duk babu Islaam sai bayan Magrib yazo gidan da tashi kayan sunan mai matuk'ar aji banda wanda Nadeefah da tayi mc a wurin sunan ta lafto da sai da Mommy tayi mata fad'an su don sun yi yawa ita dai ko a jikinta don bata yi abunda take son yi ko rabi ba, ba kuma tayi don kowa ba ne face don zumunci da soyayyar dake tsakaninta da iyayensu ba kuma ta nuna bambanci ba duk kai d'aya tayi musu. Tabbas yara sun yi goshi don su Ummu ma sunyi bajinta wajen kayan barka, ita Umma suka kawo kayan ana tsaka da taron sunan kuma mafi burgewa shi ne ko shela ba ayi ba don ba duniya ko fariya suka yi wa ba illa nauyin al'ada da suka sauke.



Sanda Islaam yazo ta na kwance kan gadon su Suleim tana juyi sakamakon ciwon kan da sark'afeta ko ta kan su Ainah dake aikin d'aga kayan suna ba ta bi ba. 




Mommy ce ta lek'o tana cewa " Lele ki tashi ki had'a kayanki tunda Islaam ya zo sai ya tafi da ke ai an gama sunan".


"Mommy ni fa sai anjima zan wuce".


"Saboda ina wasa dake ko? Zaki tashi ko sai na zo na faffale ki da mari anjima wa zai mai da ke gidan ko ke zaki yi driving kina fama da kai?".



"Toh mommy ba sai in kwana ba?".


"Ki jira in sake dawowa in tarda ki a d'akin nan ki gani, ki bar ganin ba ki da lafiya". Daga haka ta juya ta fita daga d'akin, tana ganin fitarta ko ta koma ta sake kwanciya don shi kawai take buk'ata a lokacin.



"Wai ba dake aka gama magana yanzu ba? Kina ta wani abu kina hura hanci kamar a kanki aka fara ciki?".


Ainah ta furta kanta tsaye cikeda tsegumi, da sauri ta d'ago kai daga kwancen da take ta kafa mata idanu yayinda su kuma 'yan d'akin na su idon yake yawo daga kan fuskar d'aya zuwa d'aya kamar masu neman wani abu. Muskutawa tayi cikin son k'ularwa ta sake yatsina fuska irinta masu ciki tace " Toh ya za'a yi Aunty Ainah abu ne fa ya had'u da wainda suka dad'e suna nema, ga shi kin san su juya basu iya samun wurin ba da sun ci wake sai sun yi tusar da sai ya addabi kowa da wari".



Nan kallo ya koma sama don kuwa maganar da ta fad'i ta zo musu ne a bazata, don babu wanda ya zaci Lele zata iya fad'in wannan maganar ko kusa kuwa ma. Balle ita kanta Ainahr da ta saki baki da hanci tana kallonta kamar ta ga bak'uwa, Ya Budu ne tace " wlh fa Allah ya sa wasu suna da hancin shak'arta, in ba haka ba haki zasu fara tabbas " itama da yare ta fad'i kamar yacce Lelen tayi don ba ta iya jure doguwar hausa ko kad'an.



Insiyaa da bata san dawar garin bane tace " wai Lele ba zaki tashi ko fita bane sai Mommy ta dawo?".



Suleim da shigowarsu kenan ita da Zulfaa daga yi masa godiya tace " k'ila Yaa Islaam d'in take jira yazo ya d'auketa" maganar tata ya sa kowa kwashewa da dariya banda Lelen da ta rik'e kai tana hararar Suleim d'in, Ya Budu tace " k'yale su Lele ki tashi kafin Mommyn ta dawo ko dan ke ki samu kiyi bacci kin ji ko?".



Kai ta gyad'a ta tashi kayanta da ta sako cikin wata babbar leda ta d'auka da handbag d'inta da sai da ta tabbatar da kasantuwar wayoyinta a ciki kafin ta yi musu sallama ta fita, ta bar Ainah tana juyayin maganar da ta fad'in mata ta kuma rasa takamaiman kalamanda zata iya had'awa wajen ba ta amsa ga su kuma 'yan d'akin kowa ya cigaba da harkar gabanshi ba tareda ya bi ta kanta ba.




A zaune a parlor ta tarda shi da Mommy wanda alamu ya gwada magana suke yi mai muhimmanci ko dan yanda ya natsu yana sauraronta, tana kuma shigowa ya d'ago idanu yana kallonta k'yarr hakan ya sata jin wani iri. Mommyn ce tace " har yanzu kan ne Lele ?" Gyad'a mata kai tayi ta d'an rab'e a kujera one sitter tana gaishe shi da kulawa ya amsa har da tambayar ta abinda ke damunta a hankali tace kai sorry ya furta cike da kulawa kai kawai ta gyad'a ba tareda ta iya bud'e baki ta amsa ba.



Mik'ewa yayi da sauri yana cewa " Mommy bari mu zo mu tafi".


"Ok Islaam Allah ya tsare, Lele sai da safe Allah ya k'ara sauk'i".


Ameen suka amsa a tare suka fita daga gidan, su na fita ko da sauri ya rik'ota ganin tana had'a hanya har mota sai da ya tabbatar da zamanta a cikin motar kafin ya rufe k'ofar ya zagaya d'ayan side d'in. Wristwatch d'in hannunshi ya duba ganin dare bai wani yi sosai ba ya sa ya karya kan motar zuwa BAY's clinic, kafin kuma su isa har ya kira Dr. Bisola dake general medicine department a kan yana da patient.



Da suka isa clinic d'in ma shi ya sake rik'ota cikin jikinshi har zuwa ciki, office d'in Drn suka shiga inda ta shiga aikinta. Ba ta mata tambayoyi masu yawa ba don ba wani iya amsawa tayi ba, sai shi ne da ya jaddada cikinta ya kuma buk'aci a binciketa a san wata nawa ne cikin da kuma magungunan da suka kamace ta. Nan ko ta k'ara k'aimi ga sanin abinda yake damunta, wanda a take ta tuno stress ne ba komai ba don Nadeefahr tayi overworking kan ta sosai. Allurai ta had'a mata wanda da taimakon Islaam aka samu aka yi su amma ba salin-alin ba duk da haka taci kukam shagwab'a maishi, sannan ta had'o magunguna ta basu sai gwajin cikin da sakamako ya nuna d'an satittika 11 ne.



Cikeda murmushi ya sake rungumeta yana mai jin shauk'in duk abinda yake cikin, lokacin har baccinta ya fara nisa. Tana kammala binciketa ya d'auketa a hannunshi zuwa mota, kwantar da ita ya yi a kan kujera ya kwantar da seat d'in yanda zata ji ta comfortable ya warware mata gyale da d'ankwali kana ya zagaya zuwa side d'in shi. Motar ya ja irin d'azu cikin natsuwa zuwa gidansu a nan ma sake d'aukarta yayi zuwa ciki, a kan gadon shi ya kwantar da ita bayan ya rage mata kayan jikinta kafin ya sallaci ishai da ta riske su a hanya ya ci abincin da ya siyo ya zauna kallo. 



Har 10 da ya tafi ya kwanta bata ko motsa ba idanu ya tsura mata yana mai jin wani sukuni a tare da shi, murmushi yayi ya musu addua ya tofe su musamman cikin kafin ya rufe idanu a haka bacci ya d'auke shi. Ba ita ta farka ba sai kusan 12am wanka tayi tai sallah ta samu oversized shirt d'in shi har da boxers ta zura kafin ta fita zuwa kitchen don tana jin yunwa, indomie ta dafa ta had'a tea ta sha saannan ta koma d'akin, brush tayi ta koma ta kwanta.




Tun daga ranar kuma kamar an gayyato mata ciwo haka laulayi ya sark'eta, sosai take ciwon jiki da zazzab'i in da Allah ya taimaketa ba ta amai ko kad'an. Ciwo ne take sosai wanda sai da ya kaita da kwanciya a asibiti kusan sau uku, hakan ne ya sa har wainda basu san tana da cikin ba suka sani don ko haka aka din ga tururuwar zuwa dubata. 



Hajjah har so tayi a bar mata ita tayi jinyar a nan gidanta sai dai iyayen mulkin yayi tsalle ya dire yace bai san wannan batun ba, sai dai ita Hajjahn ta zo ta zauna da ita ganin yadda ya tubure ne ya sa Hajjahn samo mata wata YaMalle daga can Yerwa ta zauna da ita single room dake parlorn gidan aka bata ta zauna.



YaMalle dattijuwa ce ba tsohuwa tukuf ba akwai karsashi da son aiki ba tada k'yuwa ko son jiki ko kad'an ga tsafta, ko kadan ba ta amfani da tarin kayan wutan  da aka girkewa Lele sai a wuraren da suke buk'atan haka. Lele ba ta aikin komai a gidan sai rainon ciki da kula da rigimar mai cikin da bata k'arewa don ma yana d'aga mata k'afa musamman a wajen girki da gyaran d'aki da shi yake kayanshi abinci ko na YaMalle yake ci in kuma suka ji kwad'ayinsu ya kwashe su su fita su je su ciwo kayansu a yiwa Yamalle takeout. Suna dawowa kuma ya b'arje guminshi ba ko kawaici don ta nan kam bai tausayinta ko kad'an ga kuma cikin shi ma abinda yake so kenan don sosai ya sa ta zama wata jarababbiya na musamman, sai an gama ne ta koma gefe tana numfarfashi shi ko zazzab'i ya tashi abunshi hakan kuma ba shi yake hana da ya dawo ta sake rungumarshi ta biye masa.



Ba ita ta samu sauk'i ba sai da cikin ya shiga wata hud'u a na biyar lokacin har babban sallah tayi baya da kusan sati gida time d'in zazzab'in ya d'auke d'if da kasala, jiri ciwon kai da sauransu ya bar ta da zafin jiki kawai. Sai kyau da ta k'ara sosai ta bud'e kuwa shape d'in da a da bata da shi duk ya bi ya fito saboda cika, ga kuma hasken d'anyen ciki da ta yi wanda ya kusan ninka na ta na da a shek'i da d'aukar ido. Ba kuma irin hasken nan ba ne na rashin lafiya Aa wannan ko makaho ya shafata ya san akwai lafiya tattare da ita kuma tana samun kulawa yanda ya kamata daga ko wani ɓangare hatta shi Burhaan bai gajiya da kallonta kuma yana alfahari da samunta a matsayin matarshi na aure ko da ko bai fad'i ko ya nuna ba.



Tana samun sauk'i ta fara fita office d'in da rabonta da shi tun kafin su tafi Umrah, ta kuma koma aikin ya na gyaran gida musamman side d'in Islaam da girki da sauran buk'atu wanda wani lokacin sai YaMalle ta tsawata don gani take tana wahal da kan ta ita da ba lafiya ba. Tare sukan je awo da Islaam a wasu lokutan kuma taje ita d'aya don ba kullum yake cikin mood d'in fitan na su tare ba.



Tana dawowa ko zai tasa ta a gaba su shiga gym d'in shi na gidan wai sai tayi exercise d'in masu ciki wai kar tayi nauyi da yawa, ai ko tana amsa a jika wanda tun tana haki in tayi duk da ba wanda zata gajiyar da kanta ba ne amma kuma kun san lamarin ciki da takura k'irji har ta saba in ma ba tayi ba ba ta jin dad'in jikinta. Ita dai YaMalle tana kallonsu suna gid'iminsu in dare yayi ya sake d'aukarta su fita strolling da sun dawo ya zage yayi mata massage musamman a k'afafu gudun kar su kumbura wanda inda Allah ya taimake ta ma ba ma su tab'a kumburar ba, gefe guda kuma tana yawan muamala da fruits sosai fiyeda komai don a gidan daga mocktails da take yawan yi zuwa drinks da smoothies sai salad da suma duk abinci sai an had'a da su. Tun kuma cikin na k'arami ta k'auracewa sugar shi ko wanda ƙoƙarin  YaMalle da Islaam ne, haka nan ta rungumi ba zuma a duk wani abun sha in dai na ta ne.



Kwance take ta kammala shirin bacci tana ta jujjuya maganar da ke bakinta sai dai bata san yanda zata fara masa maganar ba, k'arasowa gabanta yayi yana mai nazartar ta don ya ga alamun akwai magana a bakinta. Zama yayi a bedside d'in gefen da take yace " ya aka yi?".




Zama ta gyara tana cewa " nothing me ka gani?".



"Ke kullum in aka tambayeki abinda yake damunki sai ki ce ba komai, bayan fuskar ki duk ya nuna kina da magana mai k'arfi wai yaushe zaki gane cewa Ni ɗan kai tsaye da ban son corner-corner ba ne huh?". Ya tambaya a d'an hasale.



Ajiyar zuciya ta sauke kana tace "I'm sorry Yaa...."



"Ki ajiye haƙurin ki, ki gaya min abinda ya faru tohm ?".



"Yaa dama maganar gender reveal party d'in mu ne naji shiru ba ma shiri shi ne nace......".



"Gender reveal party?!". 


"Yes Yaa".



"Dama na ce miki zan yi wani gender reveal party ne da kike tambayata a kai?''.



''No dama.......''



"Dama me Nadeefah?! Dama what? Na miki kama da shashasha ne mara sirri da zai yarda da wani shirme gender reveal party or what ?".



"Yaaa....!"



"Dama kallon d'an iska da bai san darajar kan shi ba kike mun ko? Haka nan sai in yarda da wata gender reveal saboda in nuna ma duniya na wa matata ciki ko?".




"Yaa ba fa ko d'aya daga abinda ka fad'i ba ne ba, abu ne na rana guda d'aya da za mu yi inviting 'yanuwan mu su yaya mu farin ciki. Ba wai iskanci ko makamancin shi ba".



"Nadeefah!! Ina gargad'inki da ki san irin abunda zaki din ga kawo min gabana, wai kinji shiru ? In ba ma kin raina ni ba har zaki kawo min wannan maganar gabana uwar ita gender reveal d'in, idan kika kuma min maganar ta kuma sai ran ki ya ɓaci!!".



Ya k'arashe Yana jin ɗaci a kan harshen shi, shi fa har ga Allah ya tsani terere a rayuwar shi. Bayan nan kuma bai son yayi mata wani abu da zai sa a ranta wai ya fara sonta, balle ta samu abun yin tink'aho da iyayi da shi. Ita ko kallonshi take yi cikeda mamakin tutsunshi kamar wani mutumin da, don Allah miye a gender reveal party na tada hankali. In bai so ba zai iya cewa bai so ba har sai ya sa ta ji kamar bata kai na ba? Miye aibun maganarta a mahangar muamala miye kuma laifin kalmar No da ba zai iya fad'i kai tsaye ba.


Danne hawayenta tayi a hankali tace " ka yi hak'uri ban san ba ka so ba ne, zan kuma kiyaye in shaa Allah ba zan sake ma ka maganar da baka so ba".


Ta k'arashe tana komawa ta kwanta tana mai jan bargo ta lullub'e jikinta, kallonta ya tsaya yi yana son nazartar reaction d'inta amma  ya kasa don ya shanye shi ta kuma runtse idanu gudun yin kuka. Hasbunallahu ta dinga maimaitawa a k'asan ranta har ta samu abinda take ji ya lafa, daga haka ma bacci ya d'auketa ta bar shi a nan zagado sai da ya ga tayi bacci kafin ya koma ya kwanta shi ma ya na ta tunani.




Daga nan ba ta sake tada maganar ba shima kuma ya rantse ba zai yi ba suka cigaba da rainon cikinsu, ba ma a dad'e ba suka yi scanning gendern babyn wanda ya nuna mace ce sosai suka yi murna suka cigaba da siyayyan kayan baby da suke tayi d'ayan d'akinta mai shabby chic aka gyara da yake akwai girma sosai aka yi side d'in yara.



Komai na mace suka zuba a ciki tundaga kan crib da wardrobe d'in yara zuwa kayan sawa da stickers a bango da wallpaper na baby girl, haka toys da sauran kayan wasa na mata. Zagewa tayi tai arts na jarirai da su aesthetics da suka yi daidai da shekarunsu aka lillik'a an dai shirya komai da sunan Daddy's princess komai na 'yan gayu dai.




A lokacin babu wani abu da suke jira sai na haihuwar d'iyar inda both side suka d'aukantu da haihuwar as if basu tab'a rik'e ba, kowa shiri na musamman yake yi ba kama hannun yaro.





Kwance take a sofar office d'in ta da tunda tazo take wajen, sakamakon matsananciyar ciwon bayan da ya sark'eta tun asuba ba kuma ta d'auke shi wani abu can ba saboda tun farkon shigar cikin wata 7 take fama da shi da mara sai yanzu ne take jin kamar ya zarce wainda tayi a baya. Don yau ko magana ba ta iyawa saboda yanda yake rik'e mata kamar an d'aura mata wani abu a kan mara, gaba'daya ta rasa inda zata tsoma ranta taji dad'i don duka marar da bayan suna buk'atar taimako.




Tana a haka aka kira Azuhur lallab'awa tayi ta mik'e da dafa bango ta isa toilet d'in tana zuwa fitsari ne ta lura da wani ruwa fari dake bin ta a jiki wanda a da bata gan shi ba sai yanzu, ruwan d'umi ta tara ta yi tsarki ta goge jikinta. Panty liner ta saka a sabon pant da take ajiya a office wai ko in period ya risketa ta b'ata na jikinta, sawa tayi taji ya mugun matsanta don normal size d'in ta ne yanzu kuwa ta k'ara sosai. 




Tsaki tayi ta cire ta zare linern ta mai dashi inda ta d'auko a haka ta fito tana dafa bango, praying areanta ta nufa ta tada sallah da yanzu take yi a zaune. Sai dai tana idarwa ta gaza tashi baya yace bai san zancen ba, a lokaci guda kuma ruwan da yake bin jikinta ta ji ya k'ara gudu sosai har ya jik'a hijabinta. Ai sai ta sa kuka tana yarfa hannu don gani take mutuwarta ce tazo ga shi ta kasa tashi balle ta d'auki wayarta tai kira, cikin lud'ufin Allah aka turo k'ofar aka shigo ganinta kan dadduma ta kuma ba wa k'ofa baya ya sata cewa " ashe sallah kike yi".



Da sauri ta waigo da hawaye shab'e-shab'e tana kallon Suleim da jin shirun nata yayi yawa ne ya sa ta zo taga ko lafiya musamman da PA tace mata yau gabaɗaya a kwance take, da sauri ta k'arasa shigowa tana cewa " me ya faru Nadeefah?". Kamata ta shiga k'ok'arin yi ta gaza nan hankalinta ya sake tashi tace " Lele me yake faruwa da ke ne haka, Innalillahi".



"Wani ruwa ne yake zuba Suleim, bayana k'afata, marata! Mutuwa zan yi wayyo Allah ".


"Mun shiga uku, ko dai haihuwar ce. Akwai wani a nan wurin? Don Allah a taimake ni" maaikata ne suka shigo office d'in a firgice su PA da Fatee, ganin yanda Suleim ta rikice ne ya sa suma suka rud'e sai da ta musu tsawa ne su Fateen suka tayata kama Lelen. Hauwah kuma ta d'auko jaka da wayar Lele da Suleim d'in tace a d'auko, motar Lele dake parke ta bud'e suka saka ta a back seat Fatee ta shiga bayan PA Kuma ta koma gudun a bar ciki ba kowa. Suleim ta shiga gaba passenger's seat Hauwah ta ja motar zuwa BAY clinic da bai da wani nisa da wurin duk bisa kwantancen Suleim ita kuma ta shiga neman layin Islaam ta wayar Nadeefahr.



Ringing biyu yayi picking a gajiye yace "wife".



"Ba ita bace Suleim ce yanzu muna BAY's clinic ".



"Me ya same ta ?" Ya tambaya a d'an tsawace, cewa tayi " naƙuda ta fara a nan office ".



"What??!" Ya sake tambaya da mamaki don bai zaci zata iya haihuwa a tsukin ba tunda a k'aidar EDDn ta saura kusan 3 weeks ko fi ma. Suleim ba ta bi ta kan shi ba katse wayar tana kallon hanya, after like 7 minutes suka iso clinic d'in babu wata-wata aka amsheta alamun an san da zuwansu don suna gama waya Islaam ya kira Dr. Bisola akan suna tafe da patient................

Deejasmah ✍🏼