BAƘON YANAYI

5

by @nasrullah133

“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, Astagafirullah Allah na tuba... ko wanne irin laifi ne haka na aikata? Ko wani zunubi ne ke bibiyata?” ta faɗa tana komawa ta jingina da bangon ɗakin cikin shiru.

Bacci kuwa ya ƙaurace mata gaba ɗaya, babu alamarsa sam a fuskarta. Shi kuwa Abby, tuni bacci ya yi awon gaba da shi, bai ma san halin da take ciki ba. Juyi kawai yake yi cikin bacci, har zuwa lokacin da hasken wayarta ya tada shi.

Da ya farka, matsowa yayi kusa da ita. Alhamdulillah jikinsa ya fara samun sauƙi sosai. Magungunan da yake sha da kuma abincin da yake samu sun fara aiki, jikinsa yana ƙara yin kyau Masha Allah.

Taɓa ta yayi a hankali, cikin firgici ta ɗago. Ashe tunani ne ya nutsar da ita cikin kogin rayuwar duniya da abubuwan da suke faruwa da ita kala-kala.

Ganin yadda ta firgita yasa ya tambayeta cikin damuwa,
“Ta lafiya kuwa? Am meke damunki please? Ki faɗa min gaskiya kinji. Damuwarki ita ce damuwata. Bana son ganin kina cikin baƙin ciki, kamar yadda na san ke ma baki jure ganin nawa damuwar.”

Ya ƙarasa maganar cike da damuwa a fuskarsa. Abunka da mai saurin kuka, har ƙwallah suka cika masa ido, alamar akwai tsantsar so da ƙauna mai ƙarfi a tsakaninsu.

“Eyyah sorry Abbyna, ba komai wallahi. Kawai dai abubuwa ne sai godiya ga Allah. Hakan yasa na fara tunanin gobenmu, duba da yadda rayuwar nan take ƙara rikicewa... daga wannan sai wannan.”

Tana gama faɗin haka tayi shiru. Abby kuwa, da ke zaune kusa da ita, kasa natsuwa yayi saboda yadda yake son jin cikakken abinda ke damunta.

Rungumota yayi yana lallashinta, ya cigaba da kwantar da ita a jikinsa ko hakan zai rage mata raɗaɗin da take ji a zuciyarta.

Sai da suka shafe sa’o’i a haka sannan bacci ya kwashe su duka biyun. Maimunatu kuwa a kwance take a jikinsa cikin nutsuwa.

Yanzu misalin ƙarfe huɗu da minti arba’in na asuba (4:40am), sai aka fara kiran sallar farko.

Tashi sukayi. Maimunatu ta nufi toilet ta watsa ruwa, ta tsarkake jikinta sannan tayi alwala ta fito. Shi ma Abby ya shiga yayi alwala, ya fito ya buɗe wardrobe ya ciro Jallabiya ya saka sannan ya nufi masallaci.

A lokacin da ya isa, an fara sallah.

Ana idar da sallah kenan, Abdul ma ya tashi ya cika wanda ake binsa. Bayan ya gama ya idar da sallah, sai ya nufi wani lungu mai shiru cikin masallacin inda babu hayaniya ko motsin mutane.

Nan ya zauna yana azkar da istigfari har bacci ya kwashe shi a wajen.

Maimunatu ma bayan ta idar da sallah, ta zauna kan dadduma tana yin azkar da addu’o’in da ta saba yi kullum. Hannu ɗaya tana riƙe da carbi, dayan kuma ta ɗauki wayarta domin duba saƙonnin WhatsApp ɗinta.

Sai taga wata sabuwar number ta sake turo mata saƙo. Ba tare da ta ɗauki abin da wani muhimmanci ba, sai ta shiga ta buɗe.

View once guda biyu aka turo mata. Ganin haka bai bata wani tunani ba tunda bakuwar number ce.

Da ta buɗe sakon kuwa, sai taga wani mutum zindir tsirara haihuwar uwarsa, yana aikata abin kunya da kansa.

Cikin firgici ta furta,
“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un...”

Ta cigaba da nanata istigfari kafin daga bisani tace,
“Na shiga uku... wai meke faruwa ne haka? Meyasa waɗannan mutanen banza suka kasa daina bibiyata? Sun ƙi su rabu da rayuwata ne?”

Da ta gama furucin, ta rasa meke mata daɗi. Nan take ta wurga wayar gefe guda.

Tashi tayi ta gabatar da sallah raka’a biyu tana roƙon Allah Ya kareta, Ya tsareta da imaninta daga duk wani fitina.

BAKON YANAYI
Mafarkin Ban Mamaki

Gari ya waye sosai. Yanzu misalin ƙarfe goma na safe kenan. Bayan Maimunatu ta gama haɗa musu breakfast, shi kuwa Abby tun dawowarsa daga masallaci ya samu wuri ya kwanta, bacci kuwa ya sake ɗaukarsa.

Cikin baccin ne ya tsinci kansa a wata sabuwar rayuwa tamkar ba shi ba.

Sai gani yayi ya yi sabon aure da wata kyakkyawar mace mai tsananin kyau.
Yana cigaba da kallonta cikin mamaki sai daga can yanayin wurin ya sauya gaba ɗaya. Duhu ya mamaye komai, iska mai sanyi tana kaɗawa cikin firgici, zuciyarsa kuma ta fara bugawa da ƙarfi.
Can sai yaji wata murya mai ban tsoro tana amsa kuwwa kamar daga cikin wani rami mai zurfi. Muryar tana fita a hankali amma cike da razanarwa,
“Ya kai wannan bawan Allah...”
Nan take jikinsa ya mutu murus. Ya tsaya cak yana sauraron muryar cikin tsoro da ruɗani.
Muryar ta sake cewa cikin wata irin dariya mai firgitarwa,
“Ka sani cewa zan baka wata sharaɗi wanda idan ka cikashi zaka samu dukiya mai tarin yawa...”
Sai muryar tayi ɗan shiru kafin ta sake magana cikin ƙara zurfafa da tsoratarwa,
“Ka san cewa matarka na mutuwar sonka... kamar yadda kai ma kake sonta. Saboda tsananin ƙaunarka gareta zaka rufe idanunka, baka gani baka ji, zata fita tana wahalar neman abinci domin ku rufawa junanku asiri. Har wasu kayan ɗakinta zata siyar saboda kai...”
Abby a mafarkin ya tsaya tamkar an dasa shi a ƙasa. Gumi ya fara keto masa yayin da zuciyarsa ke bugawa da ƙarfi.
Sai muryar ta sake cewa,
“Abinda zaka yi shine... da kuɗin nan da zata tara, ka nemi auren yarinyar da ka gani tare da ita ɗazu. Idan kayi haka zaka samu duk abin da kake so... hahahahaha!”
Wata irin dariya mai razanarwa ce ta cika wajen, tana amsa kuwwa ta ko’ina.
Nan take Abby ya farka daga baccin a gigice yana haki da sauri. Gaba ɗaya jikinsa ya ji sanyi.
“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un...” ya faɗa cikin tsananin firgici.
Ya dafe ƙirjinsa yana sauke numfashi a hankali kafin ya fara magana shi kaɗai cikin zancen zuciya,
“Wannan kuma wane irin mafarki ne haka?... Na shiga uku. Mummunan mafarki ne ko kuwa wani gargaɗi?”


___________________________

 *MMA Flight Station* 
 _Abuja, Nigeria_ 

Cool da Esha misalin ƙarfe takwas na safe suka iso Abuja.

Suna sauka daga jirgi kuwa, sai ga motar da zata ɗauke su kamar an haɗa baki, domin lokaci guda suka iso ita ma ta iso ɗaukar su.

Driver ɗin ya gyara parking suka shiga motar, sannan ya saka musu kayansu a boot ɗin motar.

Daga nan suka tafi kai tsaye zuwa location ɗin da Hajiya ta bashi address.

Da suka isa, ya sauke su tare da kayansu ya basu key ɗin gidan. Har ya taimaka musu da shigar da kayan ciki kafin daga bisani ya sake fita domin siyan kayan abinci kamar yadda aka umarce shi.

Cool da Esha duk sun gaji matuƙa. Babu wani ƙwari a jikinsu.

Da ƙyar suka samu suka shiga bathroom suka watsa ruwa, sannan suka ji jikinsu ya ɗan saki.

Fitowa sukayi suka sake kwanciya tamkar kayan wanki, saboda gajiyar tafiya.

Bayan wasu sa’o’i, sai suka ji ana knocking a ƙofa.

Cool ta daure ta tashi a hankali tana cewa,
“Waye?”

Daga wajen ƙofar aka amsa da cewa,
“Driver ne. Saƙon Mommy nazo kawo muku.”

Sai da ta numfasa sannan ta ƙarasa bakin ƙofar ta buɗe masa.

Shigowa yayi da shopping na foodstuff da ya siyo musu. Tun kafin su iso ma, Hajiya ta riga ta san abubuwan da zasu buƙata. Yanzu abinda ya rage kawai shine su fita shopping tare da driver ɗin idan sun huta.

Misalin ƙarfe ɗaya na rana (1pm) driver ya sake dawowa kamar yadda suka tsara tun farko. Su kuma dama sun gama shirye-shiryensu, jiran zuwansa kawai suke domin su fita.