FARASHIN IZZAH

Chapter 18

by @hauwajaywrites

Chapter 18


Bayan sun fito daga lecture ɗin ne aka sanar musu cewa supervisor ɗinsu yana neman duk 'yan group ɗinsu.


Zahra na tsaye tare da friends ɗinta amma ko kaɗan bata ma fahimci me aka ce ba. Firdausi ce ta matsa kusa da ita ta maimaita mata a hankali.


"Supervisor na neman 'yan group dinku Zahra"


Kai Zahra ta gyada kawai ka.


Firdausi ta riƙe jakar hannunta sannan suka fara tafiya a hankali suna bin bayan sauran 'yan group ɗin.


Bayan sun isa office ɗin, supervisor ɗin ma kallon Zahra kawai yake yi. Daga gani ba cikin normal state take ba kwata-kwata. Ko fara'ar da aka santa da ita babu.


Firdausi tayi saurin magana kafin ya tambaya.


"Sir bata jin daɗi ne, kuma zata tafi antenatal."


"Okay," ya amsa yana kallon Zahra. "You can go. Duk gyaranki zaki gani a hardcopy ɗinki."


"Nagode sir," Zahra ta amsa da ƙyar.


Daga haka suka fito tare.


Tun daga office ɗin har zuwa parking lot babu wanda yace uffan 


Sai da suka isa wajen motar Zahra suka shiga.


Zahra na saka seat belt ta juya tana kallon Firdausi.

"Ya akayi kika san I need rest har kika ƙirƙiri ƙarya wa supervisor na?"


Murmushi Firdausi tayi.

"Zahra idan ban san ki ba, ban cancanci na zama kawa a gareki ba."


Ta ɗan tsaya sannan tace,

"Zahra yanzu tada motar mu bar makarantar nan."


Ba musu Zahra ta tada motar suka fara tafiya. Na ɗan lokaci shiru ne ya mamaye motar.


Sai Firdausi ta kalleta.

"Zahra meke damunki?"


"Nothing."


Dariya Firdausi tayi tana girgiza kai.

"Zahra bamu saba haka dake ba, kar mu fara."


Shiru Zahra tayi tana kallon titi.


"Kema kin san nasan ba haka kike ba," Firdausi ta ƙara faɗa cikin tausasawa. "Na zame ki ne a school saboda bana son su Asiya su fahimci wani abu."


Sai ta ɗan rage murya "Akan ke da Ibrahim ne ko?"


Wani numfashi Zahra ta sauke. A hankali tace,

"Firdausi... zuciyata zata buga."


Firdausi ta juya da sauri tana kallonta.

"Me ya faru?"


"Ibrahim zai kashe ni..." muryarta ta ƙarshe tana rawa.


Da sauri Firdausi tace,

"Haba Zahra! Ki daina irin wannan maganar."


Hawaye suka cika idanun Zahra.

"Wallahi bana jin dadin raina... tun jiya."


Ta ɗan cije lips ɗinta tana ƙoƙarin hana kukanta fita "Na fara jin tsoron abubuwan da nake gani da wanda bana gani..."


Nan take Zahra ta fara bata labarin komai.


Tun daga yadda suka dawo daga gidan Mama cikin so da kauna, yadda Ibrahim ya nuna mata kulawa har ta tausaya masa ta manta da damuwarta na ɗan lokaci akan reaction din Mama


"Mun dawo gida lafiya..." Zahra tace tana kallon gaba. "Har naji maybe ina overthinking ne..."


Firdausi bata katseta ba, sai kallonta take yi.


"Yana toilet ni kuma na tsaya a kitchen kafin na haura sama." Ta haɗiye wani abu mai nauyi a maƙoshi. "Da na shiga ɗaki... sai naga wayarsa na ringing."


"Hmm..." kawai Firdausi ta iya cewa


Zahra ta ce "An yi saving number ɗin da... 'Lovie Dovie.'"


Firdausi ta ɗan zaro ido.

"What?"


Kai Zahra ta gyada a hankali.


"Da farko ma bansan me naji ba. Kawai zuciyata ta tsinke, har Call ɗin ya yanke sai kuma wani ya sake shigowa."


"Kin ɗaga?" Firdausi ta tambaya


"A'a... na kasa." Ta amsa


Ta share hawayen da suka zubo mata.


"Yana fitowa daga toilet ya sake ganin call ɗin. Wallahi Firdausi yadda ya tashi da sauri ya ɗauki wayar... sai ya mayar silent ya saka a aljihu."


Firdausi ta haɗe gira.

"Then?"


"Ya fita daga ɗakin, shine abun daya bani mamaki"


"Ya dawo?"


Kai Zahra ta girgiza mata.


"Har ƙarfe goma sha ɗaya ban ganshi ba. Daga baya ma bacci ya ɗauke ni. Da asuba na tashi... har lokacin baya ɗakin."


"Subhanallah..." cewar firdausi 


"Tun da muka shirya bayan dawowata gida, Ibrahim bai taɓa barina ni kaɗai a dare ba. Sai jiya..."


Muryarta ta fara rawa.

"Da safe ma babu explanation. Babu inda ya ce ya je. Kawai ya shigo ɗaki kamar babu abin da ya faru."


Firdausi tayi shiru tana sauraronta.


"Bayan wani lokaci ma ya fita. Ni kuma na shirya zuwa school..." ta sauke numfashi. "Kawai naji ƙarar gate."


"Shi ne?"


"Eh. Na buɗe curtain naga yana fita da mota." Hawaye suka sake cikowa idanunta. "Wallahi Firdausi kamar an dasa ni a wajen. Ko sallama bai min ba fah, just imagine...."


Firdausi ta ɗan dafe kanta.

"Ya Salam..."


"Shiyasa nace miki zuciyata zata buga." Zahra ta ƙara faɗa cikin kuka. "Bana son yadda nake jin kaina yanzu. Bana son tunanin da nake yi."


Firdausi ta kama hannunta.

"Shhh... calm down."


"Ki gaya min idan ba wani abu bane me yasa zai fita haka? Me yasa zai ɓoye min wayansa? Me yasa zai kwana a waje?"


Shiru Firdausi tayi na wasu seconds kafin tace,

"Kin tabbatar ba wata business issue bace?"


"Da ace haka ne ai zai gaya min." Zahra tace da sauri. "Ibrahim ba irin mutanen da suke waya da mace suna saving number da 'Lovie Dovie' saboda business ba."


Wani shiru ya cika motar.


Sai Zahra ta runtse idanunta tana kuka a hankali.

"Firdausi bana jin zan iya ɗaukar wani ciwon zuciya daga Ibrahim..."


Firdausi tayi shiru na ɗan lokaci tana tunani, sannan ta juya tana kallon Zahra sosai.


"Pls kiyi kokari ki nemo number ɗin."


Zahra ta ɗan haɗe gira.

"Number ɗin wa?"


"Wancan 'Lovie Dovie' ɗin."


Gabanta ya faɗi ta ce

"Firdausi kar dai kiranta zaki yi?"


Firdausi ta ce da sauri. "No!!! Just find her number ki turomin immediately. Kuma kar ki bari Ibrahim ya sani."


Zahra ta gyada kai a hankali.

"Amma me zakiyi da number ɗin?" ta tambaya cikin damuwa.


"Ke dai ki samo min ita." Firdausi ta bata amsa a takaice


Kai ta sake gyadawa.


Sai kuma ta sauke numfashi tace,

"Firdausi ina zan kaiki yanzu?"


"Ki kai ni gida kawai."


"Toh."


Zahra ta juya steering tana canza hanya.


Dukansu suka yi shiru na ɗan lokaci, amma wannan karon shiru ne wanda dukkansu fadawa duniyar tunani suka shi 


Firdausi na kallon Zahra lokaci zuwa lokaci. Yadda hannunta ke rawa saman steering ya tabbatar mata cewa kawarta tana cikin wani irin hali.


Firdausi ta ce "Zahra..."


"Hmm?" Cewar Zahra


"Kar ki fara conclusions yanzu."


Sai Zahra tayi murmushi mai ciwo.

"Yaya ba zan yi ba?"


Firdausi ta sauke numfashi.

"Saboda baki da complete answer tukuna. Kuma idan kika bari tunani ya rinjaye ki yanzu, zaki cutar da kanki ne."