FARASHIN IZZAH

Chapter 19

by @hauwajaywrites

Firdausi kuwa ta sauka ƙasa, a compound suka haɗu.


Ibrahim yana shigowa, Firdausi ta kalle shi fuska a hade.


"Ina wuni," ta faɗa a taƙaice.


Shi kuma ya kalleta da wani irin kallon, sannan ya wuce ba tare da ya amsa ba.


Ita ma ta bi shi da irin kallon nan na rashin kunya.


Wajen unguwar nasu shiru, manyan gidaje ne, babu kowa dan kowa na gidansa. Ta fara tafiya a hankali tana  bin titin unguwar har ta kai bakin titi.


Da ƙyar ta samu abin hawa ta shiga, zuciyarta cike da tunanin Zahra da kuma halin da ta bar ta a ciki.


Ibrahim na shiga parlorn ƙasa, babu kowa.


Kai tsaye ya haura sama zuwa ɗakinsa. Ko kallon dakinta bai yi ba, ya cire kayansa sannan ya shiga toilet yayi wanka.


Yana fitowa aka kira sallar isha'i, hakan yasa yana gama saka kaya ya sauka ƙasa. Masallaci ya wuce direct.


Bayan ya dawo ne ya tsaya a kitchen na ɗan lokaci, kamar mai tunani. Sai ya ɗauki plate ya wuce dining. Buɗe warmers ɗin yayi.


Abincin da Zahra ta dafa ne a jere cikin tsari. Wani ɗan numfashi ya sauke a hankali kafin ya ja kujera ya zauna.


Ya ɗiba abincin kaɗan sannan ya fara ci a hankali. Dining ɗin gaba ɗaya shiru yayi masa


Lokaci zuwa lokaci idanunsa na ɗagawa sama kamar yana sauraron motsi daga upstairs, amma shiru kake ji .


Sai kawai ya ci gaba da cin abincin a hankali, zuciyarsa cike da wani irin tunani da shi kansa bai gama fahimta ba.


A bangaren Zahra tun kafin Ibrahim ya dawo daga masallaci, Zahra ta riga ta ji motsinsa a cikin gidan. Ko da yake tana cikin ɗakinta, amma ko da wasa bata fita ba, Duk da ta saba idan taji sawunsa tana fita..


Sai dai wannan karon... ta share.


Kwanciya tayi akan gadonta tana kallon ceiling ɗin ɗaki, zuciyarta na wani irin bugawa da bata saba ji ba. Duk shawarwarin da Firdausi ta saka mata a kai ne ke yawo a kanta.


"Ki nemo number ɗin..." Wannan maganar ta sake dawo mata


Sai kuma ta tuna yadda Ibrahim ya kwana a waje, wani rin abu taji ya tokare mata zuciya.


Da sauri ta miƙe daga gadon ta nufi toilet.


Ruwan ɗumi ta kunna sannan ta fara wanke fuskarta a hankali. Ta daɗe tana wanke idanunta musamman saboda kumburin da kuka ya saka musu.


"Ba zai gane ba..." Ta furta a hankali tana sake ɗiba ruwa.


Bayan ta fito ne ta goge fuskarta da towel mai laushi sannan ta tsaya gaban mirror tana kallon kanta.


Har yanzu idanunta sun ɗan yi ja kaɗan, amma ba kamar ɗazu ba.


Mint sweet ta jefa a bakinta sannan ta fara taunawa a hankali. "Ko muryata ba zai gane ta canza ba..."


Wani tsaki ta ja a hankali saboda yadda take ƙoƙarin acting kamar komai lafiya ne alhalin zuciyarta na cin wuta.


Wardrobe ta buɗe. Wani English wear mai matuƙar ɗaukar hankali ta zaɓa.. milk colour fitted gown mai taushi wanda ya zauna a jikinta kamar an yi shi saboda ita. Gashinta ta gyara cikin simple style sannan ta saka ɗan turare mai sanyin ƙamshi.


Da ta gama shiryawa, ta tsaya gaban mirror tana kallon kanta. Kamar a ita ba.


Kallon agogo tayi, Almost tara na dare, sai kuma gabanta ya faɗi.


"Har yanzu bai leƙo ni ba..."


Maganganun Firdausi ne suka fara dawo mata.


"Namiji idan ya ga mace tana rushewa saboda shi..." Wani numfashi ta sauke.


Ta miƙe zata fita, har ta kai bakin ƙofa sai kuma ta tsaya cak.


"Anya zan iya?" Wani soro ne ya ratsa ta.


Sai kuma last text ɗin da Firdausi ta turo mata ya faɗo mata a rai.


"Control yourself first kafin ki gano komai."


Wannan ne ya bata wani ƙarfin guiwa.


Ta dafe ƙirjinta a hankali sannan ta buɗe ƙofar ta fita, Direct ɗakin Ibrahim ta shiga.


Ta same shi zaune bakin gado, waya na hannunsa yana dannawa hankali kwance kamar babu wata damuwa a duniyarsa 


Da ya ɗaga kai suka haɗa ido, sai ya ɗan tsaya kallonta.


Kafin ya ce wani abu, Zahra ta karya muryarta cikin shagwaɓa ta ƙarasa kusa da shi.


"I missed you..."


Ta faɗa tana zaunawa kusa da shi kamar ƙaramar baby.


Ibrahim ya ɗan ɗaga gira yana kallonta.

"Tun safe?"


Ta ɗan turo baki.

"Hmmm."


Wani murmushi ya suɓuce masa.

"Amma ai kina fushi da ni ko?"


Ta ɗan girgiza kai.

"Who said?"


Sai ta kwanta jikinsa a hankali tana riƙe hannunsa.


"Please kar ka sake bace min haka."


Maganar ta bugi zuciyarsa kai tsaye.


Nan take ya saki jikinsa da ita gaba ɗaya.

"Sorry..." Ya furta a hankali yana shafa bayanta.


Zahra ta runtse idanunta.


Duk da zuciyarta ke mata zafi, ta danne komai.


A daren sosai suka sha love kamar ma babu wata matsala tsakaninsu. Ibrahim na mata hira, tana dariya tana responding yadda ya kamata, alhalin zuciyarta na wani irin aiki a ɓoye.


Wani lokaci ma sai ta tsaya tana kallonsa tana mamakin yadda yake iya zama normal haka.


Bayan wani lokaci ne suka kwanta

Zahra tayi pretending kamar bacci ya ɗauketa.


Ibrahim ya gyara mata kwanciyarta a hankali, har blanket ya ja ya rufe mata jikinta.


Ta ji yadda ya ɗauki wayarsa.


A hankali ya sauka daga kan gadon yana rage murya.


"Hello..."


Sai kuma shiru....


"Yes... I sent the 50k already."


Zuciyar Zahra ta buga da ƙarfi.

Ta ci gaba da pretending kamar bacci take.


Daga can muryar mace ta ɗan fito kaɗan daga wayar amma bata ji sosai ba.


Ibrahim yace,

"No... don't worry about it."


Shiru ya sake yi yana saurare.


Sai kuma ya ɗan yi murmushi kaɗan.

"You worry too much."


Wata magana aka sake masa. Sai yace,

"I'll see what I can do tomorrow."


Daga haka ya kashe wayar.


Zahra ta ji ƙafafunsa sun dawo kusa da gado.


Sai ya kashe light ɗin ɗakin sannan ya kwanta kusa da ita.


Ita kuwa zuciyarta har lokacin bugawa take yi kamar zata fito.


Can wajajen ƙarfe biyu na dare Zahra ta buɗe idanunta a hankali, Ibrahim na bacci.


Ta tsaya tana kallonsa na wasu seconds kafin daga ƙarshe ta miƙe a hankali. Wayarsa dake gefensa ta ɗauka.


Da hannunta na rawa ta kamo yatsansa sannan ta manna akan thumbprint ɗin. Nan take wayar ta buɗe.


Gabanta ya faɗi, da sauri ta shiga recent calls.


Last call ɗinsa...


"Pretty ❤️"


Wani irin mashi ne ya soki zuciyarta.


Da sauri ta kwafe number ɗin zuwa wayarta, hannunta har rawa yake yi saboda tashin hankali.


Bayan ta gama, ta fita daga contacts ɗin ta kashe wayar gaba ɗaya sannan ta mayar inda ta ɗauka.


Sai ta ɗauki wayarta ta turawa Firdausi number ɗin nan take.


"This is the number."


Daga haka ta kwanta a hankali, abin mamaki kuwa, nan take bacci ya ɗauke ta saboda gajiyar tunani da tashin hankali.


Da safe suka tashi tare.


Kamar kullum suka yi sallah.


Ibrahim ma babu alamar damuwa a tattare da shi. Har lokacin yana treating Zahra normal. Wannan ne ma ke ƙara rikita mata kai.


Bayan sun gama shiryawa suka sauka breakfast.


Farida ta haɗa musu tea da bread da omelette.

Ibrahim na cin breakfast ɗinsa yana ɗan duba wasu files a tablet.


Zahra kuma tana ci a hankali tana satar kallonsa lokaci zuwa lokaci.


"Yau kina da lectures da yawa?" ya tambaya.


"Hmmm." Ta ce masa


"Kar ki gaji da yawa."


Kai ta gyada masa kawai.


Bayan sun gama, suka fito tare. A compound ya tsaya yana kallonta.


"Take care."


"You too."


Sai ya ɗan matso ya sumbaci goshinta a hankali kafin ya shiga motarsa.


Zahra ta tsaya tana kallonsa har ya fita...


Tana isa makaranta kuwa, bata ma shiga department ɗinsu ba.


A wani department ta tsaya ta kira Firdausi.


Da sauri Firdausi ta ɗaga.


"Kin iso?"


"Eh." Zahra ta ce


"Ina kike?"


Zahra ta gaya mata wajen.