Chapter 20
Zahra ta haɗiye wani abu a maƙoshi.
Firdausi tace,
"How long?"
"Almost two months."
Firdausi ta ɗan kalli Zahra kafin ta sake maida kallonta kan yarinyar.
"Kin san yana da aure?"
Nan take yarinyar ta haɗe gira.
"A'a."
Firdausi ta nuna Zahra dake zaune shiru kamar mutum-mutumi.
"Wannan matarsa ce. Kuma yanzu ne ma suka yi wata da aure."
Ba ƙaramin mamaki yarinyar tayi ba.
"What?!"
Sai ta sake kallon Zahra sosai.
"Amma taya zan yarda?"
Firdausi bata ce komai ba sai ta shiga Instagram page ɗin Ibrahim a wayarta sannan ta miƙa mata.
Da sauri yarinyar ta karɓa.
Nan take idanunta suka sauka kan hotunan wedding ɗin Ibrahim da Zahra.
Pictures masu kyau, videos, posting ɗinsa yana celebrating matarsa.
Baki ta taɓe cikin mamaki.
"Wallahi ni bansani ba..." tace kana gani kasan tayi mamaki. "Bai taɓa gaya min yana da aure ba."
Zahra dai tana zaune shiru tana kallonta.
"Ni ma dama ba aurensa zanyi ba." Yarinyar ta ƙarasa cikin rashin damuwa. "Kawai cin kuɗinsa nake yi."
Firdausi ta dafe kanta kaɗan.
"Toh dan Allah ki fita daga harkarsa. Kinga matar sa tana nan, kuma ace da dare yana fita wajen wata lokacin da yakamata yana gida?”
Yarinyar ta ɗan gyara zamanta.
"Wallahi ma zan yi blocking ɗinsa. Amma sai ya turomin kuɗin da zai bani."
Zahra da tun farko bata ce uffan bane ta ce
"Nawa ne?"
Yarinyar ta kalleta.
"20k."
"Account number ɗinki?" Cewar Zahra
Firdausi ta juya da sauri tana kallon Zahra.
Ita ma yarinyar mamaki ya kamata, sai kawai ta faɗi account number ɗinta.
Nan take Zahra ta ɗauki wayarta tayi mata transfer na 500k.
Kusan seconds kaɗan alert ya shiga wayar yarinyar.
Da sauri ta zaro ido.
"Jesus!" Zaro idanu tayi tana kallon screen ɗin wayarta.
"Half million?!"
Ta miƙe tsaye tana dariya harda sallen murna.
"Wallahi nagode Anty!"
Sai ta juya da sauri tana buɗe WhatsApp dinta
"Yanzu ma zanyi blocking ɗinsa."
Nan take ta block number Ibrahim a gabansu.
"Anty ko zan iya samun number ɗinki muna gaisawa?"
Zahra ta miƙe tsaye a hankali.
"Mungode."
Sai ta juya tana kallon Firdausi.
"Let's go."
Firdausi ta miƙe itama tana bin bayanta, zuciyarta cike da mamaki da kuma tausayi ga Zahra wacce duk da ciwon da take ji... har yanzu tana cikin nutsuwa da class.
Da suka shiga mota, Firdausi ta daɗe tana kallon Zahra kafin daga ƙarshe ta girgiza kai.
“Wallahi kuɗin yayi yawa Zahra”
Zahra na driving bata ko juyo ta kalleta ba ta ce
“Ba komai.”
“Haba Zahra, 500k saboda kawai ta rabu da shi?”
Sai Zahra ta sauke numfashi a hankali.
“Ai kinji ta da kanki… yarinyar nada son kuɗi. Haka ne kawai zai sa ta rabu da shi gaba ɗaya.”
Firdausi ta ɗan taɓe baki.
“Toh amma half million fa…”
“Firdausi,” Zahra ta katseta a hankali. “Idan wannan ne zai sa ta fita daga rayuwata da ta Ibrahim, wallahi ba yawa bane.”
Shiru ya ɗan ratsa motar, kowa da tunanin da yake yi
Can kuma Zahra ta sake magana cikin wani irin ciwon rai da ta daɗe tana dannewa.
“Please…” ta faɗa tana kallon titi. “Mai Ibrahim ya gani a jikin wannan da zai dinga binta?”
Firdausi ta kalleta.
Zahra ta girgiza kai da murmushi mai ciwo.
“Na fita da komai fa…” Wannan maganar tata ta fito ne daga zuciyar kana ji kasan taji zafi
“Kinga ni mana… na fita da kyau, ilimi, kudi, komai…” ta haɗiye wani abu a maƙoshi. “Then me yasa?”
Firdausi ta sauke numfashi.
“Ai maza kenan…” tace a hankali. “Allah kyauta.”
Sai ta ɗan matsa kusa da Zahra.
“Kuma ki daina comparing kanki da wata mace saboda namiji. Wallahi babu inda yarinyar nan ta kai ki.”
Zahra tayi shiru kawai tana driving. Sai dai zuciyarta bata daina mata zafi ba.
A haka ta kai Firdausi gida. Kafin ta sauka, Firdausi ta riƙe hannunta.
“Please ki kwantar da hankalinki yanzu. At least kin ga ita ɗin ba wani serious abu bace.”
Kai Zahra ta gyada mata.
“Text me idan kin isa gida.” Cewar firdausi
“Toh.” Ta amsa
Firdausi ta sauka ta shiga gida.
Zahra kuwa ta juya motarta ta nufi gida, zuciyarta cike da abubuwa mabambanta… ciwo, haushi, da kuma wani irin son Ibrahim da bata iya cirewa daga ranta duk da abun daya ke mata
Da Zahra ta isa gida, parking tayi a hankali kafin ta kashe motar.
Na ɗan lokaci bata fito ba.
Hannunta na kan steering, idanunta kuma a lumshe.
Yanzu kam komai ya canza.
Ba kamar kwanakin baya ba da take kuka kawai tana jin tsoro. Yanzu tana da tabbaci. Tabbacin da ya zauna mata a zuciya kamar dutse.
Ibrahim yana fita wajen wata mace.
Wani numfashi ta sauke kafin daga ƙarshe ta buɗe motar ta fito.
A hankali ta shiga ciki.
Farida ce a kitchen tana gyaran kayan girki. Jin motsinta yasa ta leƙo.
"Sannu da zuwa Hajiya."
Zahra ta amsa da murmushi kaɗan.
"Yawwa Farida."
"Tea zan haɗa miki?"
"A'a."
Daga haka ta wuce sama.
Yau bata ji buƙatar kuka ba kamar kullum. Sai dai zuciyarta ta yi wani irin sakayau
Direct ɗakin Ibrahim ta shiga.
Komai nasa tsaf kamar yadda ya bari da safe. Turarensa har yanzu na tashi a ɗakin. Ta ƙarasa slowly ta zauna bakin gadon.
Idanunta suka sauka kan pillow ɗinsa.
Sai ta tuna yadda yake kallonta da soyayya... yadda yake rungumeta... yadda yake saka ta jin kamar ita kaɗai ce a duniyarsa. Sai kuma ga gaskiyar nan.
Murmushi tayi.
Wani irin murmushi mai ciwo.
"Amazing..." Ta furta a hankali.
Wayarta ta ɗauka ta shiga gallery ɗinsu. Pictures ɗin da suka ɗauka ranar dinner ɗinsu suka bayyana.
A ɗaya daga ciki Ibrahim ya rungumeta yana kallonta kamar babu wata mace a duniya sai ita.
Zahra ta daɗe tana kallon picture ɗin kafin daga ƙarshe ta kashe screen ɗin.
"Ai actor ne..." Ta miƙe a hankali ta nufi wardrobe ɗinsa.
Ta buɗe.
Shirts ɗinsa neatly arranged. Watches. Perfumes.
A hankali ta ɗauki wata shirt tasa ta matso kusa da hancinta.
Ƙamshinsa.
Zuciyarta ta sake bugawa.
Duk da komai...
har yanzu tana sonsa.
Wannan ne abinda ya fi bata tsoro, sai ta mayar da shirt ɗin ta rufe wardrobe.
A dai-dai lokacin ta ji ƙarar gate, ta tsaya cak.
"Ibrahim..."
Da sauri ta fito daga ɗakin ta wuce nata.
Kafin ya shigo sama, ta riga ta zauna kan bed tana duba wani handout kamar mai karatu.
Bayan wasu seconds ta ji motsinsa a parlorn sama.
Sai muryarsa.
"Zahra?"
Ta ɗaga kai kamar yanzu ta lura da dawowarsa.
"You're back?"