NISFU DEENIY(The Yerwa family love triangle)

CHAPTER 30 (Hurricanes).

by @deejasmah

Fad'ar irin wahalar da ta sha b'ata baki ne, don tun tana kuka da k'araji har kukan ya d'auke sai cije bakin da azaba take yi tana kiran sunan Islaam da Hajjah kamar zata fasa asibitin. Suleim da ke gefenta rik'e da hannunta na hagu ne tace " Lele kiyi addua ne please, ki kira sunan Allah ".



"Toh na ji Innalillahi wa inna ilaihi rajiun, la ilaha illal lahu muhammadur-rasulullah sallallahu alaihi wa sallam !".


"Ki dinga fad'in summas-sabila yassara".


Shi ma sai ta kama ta na ta yi ba k'akk'autawa sai kuma ta ce " kai Suleim wallahi bai yi fa, wayyoni Allah ku kira min Ummuna zan mutu".



Duk yanda aka yi da Nadeefah ta k'i bada had'in kai don sai ihu kawai take yi ta kuma k'ank'ame jikinta, ba su wani dad'e sosai ba Burhaan ya iso da YaMalli da yaje ya d'auko a gida tare da kayan baby. Kusan a tare suka zo da Umma da Mommy da duk suke a rud'e sanin halin rakin Lelen, ai ko sun zo sun tarda a na daga da ita sosai. 


Burhaan ne ya shiga labor room d'in don akwai physios d'in da ake yin har theater da su saboda matsalolin haihuwa wasu kan zo samu karaya wasu kuma in akwai tsohon ciwon ƙashi sai ya tashi, da shi da Dr. Bisola da wasu nurses ne suka rufu kan ta sai dai ta fa k'i ba su had'in kai ko kad'an wanda hakan zai iya affecting babyn ko ma ya mutu ga shi Drn ba ta so ta k'ara ta da kanta gwara babyn ta bud'e ta da su suyi.



A lokacin ran Islaam d'in ya fara b'aci don gani yake da gangan take yi, nan fa ya fara mata fad'a kamar zai ari baki. Dr ce tace " sir fad'an nan fa d'aga mata hankali zai yi wlh, ka barta ta ji da d'aya please".



"In bar ta kina gani tana shirin kashe kanta da babyn?".


Shafa mata kai Suleim tayi tana cewa " Lele please ki saki k'asanki ki kuma din ga nishi wannan d'auke numfashin zai iya cutar da ke kin ji love".



"Suleim Mutuwa fa zan yi, wayyoni Allah nah ".



Mommy da duk turka-turkar da ake yi tana ji ne ta shigo cikin d'akin, Islaam da yake muzurai ta fara korawa waje a cewarta da wanne za taji da ciwon nak'uda ko da bambaminshi. Bai so fita ba amma saboda bai iyawa Mommy musu ya sa shi fita daga d'akin, in da yana fita Umma ta rufe shi da na ta masifar akan don me zai rufeta da fad'a ko an gaya masa a yanzu tana a hayyacinta ne?.



Mommy ko ruwan da tayi tofi a ciki ta kafa mata a baki, sai ko ta shanye tas ko kad'an ba ta rage ba. Jiƙaƙƙen towel ta kai goshinta ta goge mata zufa sannan ta gangara wurin K'afafunta ta bud'e su da kyau da ido tayi wa Dr su cigaba da aikinsu ita kuma ta dafe su, duk yanda ta so ta k'wace ta kasa tana jin ana sa mata hannu a k'asan wanda shi ne abinda yake sake tsorata ta ba komai ba. 




Nan ko abu ya sake tasowa gadan-gadan a k'idime tace " zan yi fitsari Mommy".


"Ki yi a wajen kar ki damu".



"Mommy poopoo nake ji".


"Ai shi muke so kiyi, yi kayan ki kar ki takura kan ki".



"Mommy ya k'i zuwa".


"Ki yi nishi da k'arfi zai zo kin ji ".




"Uhhhhhhhh Lahawla wala quwati, Ya Allah!".


"Ummunah!".


"Ya rabb! Ya latiffffff!" Ta k'arashe tana sakin nishi mai k'arfi sai ko ga kai ya fito shima da sauri ko aka rik'e kan don d'azu sai yayi kamar zai fito sai ta matse wurin. Sake wage k'afar tayi tana mai jin sabon k'arfi ya zo mata ta saki sabon nishi. Nan fa aka samu nasarar zaro k'atuwar 'yar, ba ta ko huta ba ta sake nishi sai ga uwa ta biyo baya.



Wata ajiyar zuciya ta sauke tana komawa ta kwanta, d'aura mata ita aka yi a kan k'irji ko goge 'yar da saboda wahala tun kukan farko da tayi ba ta sake ba. Lafewa tayi luf a jikinta ita ko ta sa hannayenta ta rungumeta tana mai jin wani soyayyar d'iyar mai k'arfi yana ratsa jikinta.




Excusing su Mommy suka yi inda suka fara kimtsa Lelen da babyn, fitar ta su ko suka tarda kusan duka mutanen familyn a harabar maternity ward d'in a tsaye. Don tun d'azu suka bar k'ofar labor room d'in wasu a zaune wasu a tsaye, wasu kuma na kaikawo. Haihuwar ta yi mutane kam kasancewar ta rana ce ba irin ta Suliem da Zulfaa da suka yi ta safiya, sune suka fara kai busharar haihuwar mace da Lele ta yi.


Nan fa aka rud'e da murna kowa yana hamdala a zuciya da baki, har shi uban gayyan sai da fuskar shi ta haskaka da murmushi sosai. A take kuma ya juya ya nufi masjid don an yi Asr da kusan mintina 22, kasancewar bai da natsuwa ya sanya bai tafi d'azu ba sai yanzu. Haka suma Suleim da Mommy suka tafi da sauran wainda ba su samu sallahr ba.



Nurse ce ta fito ta amshi kayan su Nadeefah da baby suka koma ciki, da taimakon nurses ta yi wanka bayan an d'inke tsaf tana ta raki kuwa. Maternity pad suka sa mata da kaya masu d'an kyau don dama ta sanya abayarta da inner wears da komai a ciki, suka shirya babyn cikin kayan jarirai na sanyi masu mugun kyau farare tas da su aka nad'eta a baby shawl shi ma fari suka fita da ita zuwa waje.



Ita kuma ta k'ofar baya suka turata zuwa amenity area inda anan akai mata allurar hutu, bayan ta sha tea mai kauri ai ko a nan take bacci ya d'auketa don ba abinda take buk'ata sai shi. 




Suna tsaka da juya yarinyar da ba abinda ta bari na uwarta ya dawo, babu ko kunya ya karb'i kayanshi daga hannun Ya Budu. Idanu ya tsura mata yana mai tasbihi ga mak'agin d'iyar shi, sosai take kama da Lele ba abinda ta bari har da tawadar dake kumatunta na hagu da na saman idonta. Babu abinda ta d'auko na shi tun a jarintar kuwa sai dai ko a gaba, amma har yanda take bacci irin na uwar ne tana yi tana tsotsan bakinta kamar wacce ke shan sweet irin dai na Nadeefah da a farko ya d'auka iyayine sai daga baya ya gane halitta ne. Yanda take tsotsar bakin ya sa dimples d'in ta da tsagen da ke hab'arta fitowa sosai. Tsagen ce kawai ta d'auko ta shi duk da yanzu gemu duk ya rufe wajen dimple d'in ne kawai ke nunawa wannan kuma kusan duka familyn suna da shi da wushirya siririya.




Dr. Bisola ce ta fito gaishe su tayi ta musu barka suka amsa cikin sakewa inda suma suka mata sannu da aiki, murmushi tayi ta dubi Islaam tana cewa " congratulations sir, Allah ya raya".



"Thanks, Bisola ". Ya amsa mata yana rungume da yarinyar a k'irji shi ma bayan ya gama tofeta da addua, Drn ce ta sake cewa " Sir, ya kamata yanzu a bar yarinyar don tana buk'atar hakan mun mata HP. Yanzu dai zaa kaita wurin Mamanta dake amenity room E2 itama yanzu haka bacci take yi but zaku iya ganinta".



Ok yace kawai ya kama hanyar inda aka ce take, bin shi sukayi a baya har d'akin tana ta baccinta hankali kwance har wani rama ya ga tayi masa wanda dole ne ga duk wata mai ciki tana haihuwa sai ta fad'a kamar wacce tayi ciwo. Sai dai ta k'ara haske sosai tana ta k'yalli, kwantar da yarinyar yayi a gabanta ya ja kujera ya zauna.



A haka aka dinga zuwa dubata duk da tana bacci sai dai ayi mata addua a koma. Ba ita ta farka ba sai kusan bayan Magrib da muguwar yunwa ko ta tashi da fitsari, da Zulfaa da Suleim ta fara tozali. Tasowa Zulfaa tayi tana cewa " Hajiya Nadeefah how market?" tana dariyar mugunta.



Harararta tayi tana cewa "kan ki ake ji, In law zo ki d'agani in je toilet please". Dariya suka sanya su duka ganin shak'iyanci za su mata ya sata k'ok'arin mik'ewa, da sauri Suleim ta zo ta kamata zuwa toilet d'in ba k'aramin daru sukayi ba a ciki kafin tayi tsarki da ruwan d'umi ta canja pad ta kimtsa jikinta ta fito.

Tararwa tayi har Zulfaa ta had'a mata tea mai kauri, ga peppersoup da kuma tuwon biski fari tas da shi da miyar kub'ewa, zama tayi tana cewa " shi kuma wannan mu nawa zamu ci".



"Dey play, ke d'aya zaki ci".


"Ashe ma".


"Da gaske fa sweetheart bud'e ciki zaki yi ki ci abinci, don ana kawo miki baby ta kafa baki tsotse ki tas za tayi ".


"My Allah, yanzu haka kawai mutum sai yayi ta cin abinci kamar an aiko shi?".


"Na ki wasa ne, Madam ki ci abinci ba wai ki tsaya magana ba kamar an saka ki".



Murgud'a baki tayi ta ja tuwon gabanta guda d'aya ta bud'e ta na ci, ba ta ko cinye ba ta ture gefe saboda k'amshin garlic d'in peppersoup d'in dake shigar mata hanci. Shi ta janyo gabanta har siɗe baki take yi tsabar kwad'ayi, shi ko ta sha sosai ta kora da tea sai da ta ji koina ya d'auka kafin ta yi k'aramar gyatsa ta yi hamdala. Yanzu kam da kanta ta koma toilet ta wanke hannu da baki ta fito.

Fitowar yayi dai-dai da shigowar Ya Budu dake d'auke da babyn da tun farkawarta ta ke neman abunta sai dai ba ta san abinda ya hanata magana ba. Burhaan  da Farhaan ne a bayanta suna wani magana k'arasowa suka yi ta zauna a kan gadon taa gefen Lelen. Gaisawa suka yi da Ya Budu tana tambayarta jiki amsawa tayi da Alhamdulillah, d'aura mata babyn tayi a cinya zura mata idanu tayi cike da soyayya. Sai kuma ta d'ago da mugun zumud'i tana cewa " Tana kama da niiii !!".




"Ke dai ba ki da kunya Lele, a gabanmu kike wani cewa tana kama da ni" ya furta yana harararta da kwaikwayon muryarta, rama hararar tayi harda murgud'a baki tana cewa " in rasa wa zan ji kunya sai kai?! Tab'din ai ko da na yi asara. Tunda kai ma warewa kayi ka din ga zuba rashin kunya da aka haifi Azad sai kuma in ji ta ka?".




Dariya Ya Budu dake tambayar Suleim in da ta baro Afdhal don tun zuwanta ba ta gan shi ba shi ko Azad ga shi can a waje hannun Mommy Hafsat, " a fa office na bar shi da Baraka, yanzu Daddynshi ya tafi d'auko shi". Juyawa Ya Budu tayi kan Farhaan tana cewa " kai ma da neman rigima kake Farhaan ya mace zata zage ta haihu ko gama farfad'owa ba tayi ba kazo kana mata maganar jin kunya".



"Iyayi irin na shi fa, kumani ba irin wainnan iyayen da d'in ba ne Allah yayi min kyauta in k'i gode masa saboda in birge wasu Allah sawwak'a sai kace wata ƴar daji, mutanen da ba dasu na raba azabar da naci ba tab'din ".



"Da gaskiyarki Masoyiyata Allah dai ya raya ya sa musu albarka". Da murmushi ta k'are maganar don har ga Allah tana son halin Nadeefah na rashin muna-muna, ba kuma wai kawaici ne ba ta da shi ba tana da iya nata ba dai ta iya b'oye-b'oye ba ne.



Sai lokacin Burhaan yace " da alamu dai ba wuyar kika ci ba tunda ga shi nan just hours har kina maida zance filla-filla".



"Allah Yaa da wahala, na zaci mutuwa zan yi".



"Ki mutu ki barni da wa? Ai gwara dai da baki mutun ba " Farhaan ya furta da sauri, sake harararshi tayi tana duban Islaam da ya kai zaune gefenta shi ma yana kallon fuskarta yace " ya jikin na ki ".



"Alhamdulillah Yaa" kai ya gyad'a mata yana kallon yanda ta dage wajen kallon d'iyar tata mai kama da ita ko da Farhaan ya mata ya jiki da kai kawai ta amsa don ko gezau ba tayi a kan 'yar ta kasa yarda wai wannan kyautar tata ce, bud'e idanu tayi a hankali irin bud'ewar yara ba duka ba alamun suna bak'in wuri. Cuno baki tayi sama tana motsa shi alamun neman wani abu, Ya Budu tace " ki shayar da ita Lele tunda ta fito duniya ba ta sha komai ba".



"Me ya sa haka toh, bayan a na son immediately da an haihu jariri ya sha breast milk" Islaam ya tambaya a d'an harzuk'e yana wa Lelen kallon tuhuma. Ya Budu tace " Yarinyar da tunda tazo duniya take bacci ne za a bawa nono?".


" Au ho" ya furta yana rik'e yarinyar sannan da ido yayi mata nuni da ta shayar da ita, tura baki ta yi tana kallon gefen Farhaan da ke hira da Zulfaa hankalinshi ma kusan ba a kansu yake ba. Kallonshi yayi kai tsaye yace '' Man ka fita a shayar min da 'ya".



"Au shayarwan ne ma sai na fita? Ashe ma ana jin kunyata kenan " ya tambaya bai ko motsa ba, murgud'a masa baki tayi tana kawar da kanta gefe.




Murmushi ya sake yana dubar ta wato da gasken kunyarshi take ji daurewa tayi da take masa rashin kunya, mik'ewa tsaye yayi yana cewa " babe zo ki raka ni shop d'in asibitin nan " ok tace tana bin shi a baya.



Ya budu ce ta kawo wani kwanon silver da wani ruwan magani tace mata ta wanke nonon first, nuk'u-nuk'u ta fara wurin wankewar sai da Ya Budu ta fara sababi har da cewa " uban wa kike b'oyewa nonon ni ko Islaam? Sai dai ni kam don shi kam ya riga da ya san kalarsu".



Ko shi sai da ya ji kunyar maganar don ajiye yarinyar yayi a wurin ya matsa can kusa da k'ofa, balle ita da ta sake duk'unk'unewa cike da kunya.



"Wai ba zaki saki jiki kiyi abu ba ne har sai hak'urin yarinyar nan ya k'are ne, kai ma almunafunfun har da wani tashi kamar k'arya nake yi ".



"Please ki daina maganar nan Ya Budu haba mana " ya furta cikeda gajiya, k'umshe dariyarta Suleim tayi tana sake maida hankali akan wayarta kamar ba ta wajen.


Gudun Ya Budu ta sake sakin wata maganar ya sanyata tsayawa ta wanke da kyau duk da tana jin sun mata nauyi sosai, towel ta ba ta ta goge kafin ta d'aura mata ita a cinya. Kamar yanda ta zargan kuwa ba ta san yadda ake shayarwan ba, nuna mata tayi tace "ki yi bismillah da ayoyin tsari in zaki ba ta, har kuma ta gama ki dinga reciting fatiha da ayatul kursiyu ba hira da labarai ba" kai ta gyad'a mata kawai tana tallafe kan ta.



Kamar ko ta san me aka bata ta bud'e baki ta zuk'o da iyaka k'arfinta, da sauri ta rintse idanu tana sakin k'ara tana zare mata daga baki ai ko ta sanya kuka itama tana lalube.


"Miye haka Nadeefah?!" Ya tambaya a harzuk'e yana tasowa, hannu ta yarfa tana cewa " zafi Yaa kamar zata cire".



"Shi ne zaki cisgeta haka kamar ta yanka ki".



"Islaam ka bita a hankali mana, dama shayarwan farko ai akwai zafi kai ko haihuwa d'ari mutum yayi sai sai yaji zafin nan idan babyn zai sha na farko. Ke kuma ba haka ake yi ba daurewa zaki yi da tayi sha zuwa uku zaki daina jin zafin".



Baki ya motsa da niyyar k'ara k'orafin ta girgiza masa kai, sannan a hankali ta sake kwantar da murya tana lallashin Lele. Haka ta daure ta sake maida yarinyar da ke kukan har lokacin kan nonon cigaba da shan ta yi a zafafen, runtse idanu Lele tayi sai ga hawaye yana tsiyaya don har ga Allah tana jin zafi amma kuma tana tausayin babyn kamar me.



Duk zura mata idanu suka yi tana shayar da ita hawayen kuma na zirara, "yau na ga salon bayar da nono da kuka, ke kuma kalar na ki salon da haka ya zo Nadeefah?".



Ba su san da shigowarta ba sai maganar ta suka ji kamar wacce aka turo, Ya Budu ce tayi k'arfin halin cewa " zafi yake mata fa kin san dama haka yake yi''.



"Yake yin mene in ba salon Nadeefah ba ke kuma da goyawa k'arya baya wai zafi, Madam share hawayen gulman nan ki ba wa yarinya nono wani ya sa ki ci waken kin san ba zaki iya jure warin tusar taki ba".



Da hawayen idanunta da komai ta dubeta tana cewa " ai Aunty Ainah warin tusa bai tab'a buyawar mai ita ba duk kuwa inda ta kai da shahara, duk ko da cewa shi ma ya san kayanshi da wari musamman ma wanda ya kwana da sanin bai isa ya yakice kayanshi ba. Shi da warin nan sai ko in ta Allah ta kasance ,,,, uhmm ina wuni Aunty Ainah ba mu gaisa ba" ta k'arashe da murmushi a fuskarta.




Dukan su kallon kin burge ni suke mata har ko da shi gogan, ita ko mandiya sai sakin dariyar yak'e tayi tana cewa " lafiya lau Lele,,,ashe kin sauka ya jikin na ki?".


"Alhamdulillah as you can see".


"Masha Allah, Allah ya k'ara sauk'i ya kuma raya ".



Ameen duka d'akin suka amsa.



Shigowar Ainah kamar aan aika goron gayyata ne wa mutanen waje don sai aka cincirindon shigowa dubata, a ranar dai asibitin ya san an samu k'aruwar jinin Yerwa a Yerwan ma Gaji ce kuma Lele ta haihu don ba wanda aka bari sai d'aid'aiku amma har su Hajjah sun zo ita da y'anuwata hakaza tun daga kan su Baba Tijjani har zuwa k'arshe Abbu ne kawai da su Daddy Prof da Daddy Senator sai kira suka yi a waya.




Bayan sallahr isha'i aka sallamesu daga hospital d'in bayan an tabbatar da lafiyarsu ita da baby da gidan Umma zaa kai ta sai dai kuma Islaam ya tubure ainun yace ba inda zata je tun tana da ciki har a gaban Umma a da su sun sha wasa ne sai dai kuma suka lura Burhaan a kafe yake da sa bakin Abba a ka bar masa matarshi tunda ma ba ita d'aya zata zauna ba ga YaMalle.



Suna komawa Mommy ta sa ta a gaba tayi mata ainihin wankan masu jego ta gasa ta sosai, ta sake ba ta abinci ta ci ita ma baby aka kimtsata suka kwantar da ita a gabanta kafin suka mata sallama suka tafi. Kwanciya tayi sai lokacin ta samu sukunin amsa waya da kuma sanarwa wasu a cikin friends d'in ta da haihuwar, kamar yadda yake a cikin policynta ba ta turawa kowa hoto ba sai ta saka emoji ta rufe kusan rabin fuska don ba abinda ta tsana kamar ayi ta sharing pic d'in yaro a social media.



Tana kwancen tana waya da Ummu  Burhaan ya shigo d'akin a zatonta duba su yazo yi ya fita sai da ta ga ya hau gadon ya kwanta da kyau ya d'auki babyn ya d'aura a k'irjinshi, gira d'aya ya d'aga mata alamun 'ya ne?' Kawar da fuska tayi tana murmushi, ta dad'e tana wayar kafin ta yi sallama da ita ta ajiye wayar lokacin har ya gyarawa yarinyar kwanciya a gefenshi ya kwanta har da kashe wuta. Kasancewar a gajiye take ya sa itama gyara kwanciyar nan ko barci ya d'auketa ba ta farka ba sai kusan 2 da yarinyar ta farka tana d'an kuka, Islaam ne ya tayata suka ba wa yarinyar nono sai da ta sha ta koma ta kwanta daga nan ko sai 9 am ta iya motsawa.



Babu kowa a gefenta sanda ta tashi sai kawai ta zarce da gyaran gado tayi don ɗakin sai an gyara shi tsaff sai ƙamshi ke tashi toilet ta shiga nan ta tarda shi a gyare sai ruwan zafi cikin bath dake ta tiriri, tale baki tayi don ta san ma'anarshi tana brush aka turo k'ofar aka shigo. D'agowa tayi da sauri suka had'a idanu da Mommyn da ba ta san yaushe tazo ba, kumbura baki tayi tana cigaba da brush d'in ta ita ma Mommyn tab'e baki tayi ta wuce gaban ruwan ta tab'a taji.



"Nda watundo Mommy" ta furta bayan ta gama wanke bakin ta jingina da mirror.


"Uhmm klewa slai, ya jikinki?".


"Alhamdulillah".


"Masha Allah, ki cire kayan baccin nan ki zo ayi wankan nan gari yayi rana ni kam ban tab'a ganin mai jego haka ba 9am ba wanka sai kin yi k'arnin nono..... ban ma tunanin kin shayar da d'iyar can nono Nadeefah ki kula fa kar ki dinga barin 'yar ki da yunwa ga shi exclusive za ku yi".



"Allah Mommy ban barinta da yunwa na ma bata kusan 2 fa muka sake komawa baccin".



"Ahh toh ai hakan shi ne daidai amma ki dinga tashi da asuba ki bata ko zaki koma baccin na ga alamun ma yarinyar zata yi hak'uri in kika ci sa'a taho maza mu fara kar ruwan ya huce".



Cire rigar tayi ta tsaya nan Mommy ta shiga aikinta sai da ta tabbatar da ta gasata yanda ya dace tana fitowa ko ta shirya cikin had'ad'd'iyar atamfa mai pattern an mata stones da pattern work ta sanya d'an kunne ba yi kwalliya ba amma tayi kyau kamar amarya ( a yankin mu fa in mai jego tayi kwalliya cewa akeyi wai ta k'osa ta koma turaka😂 ).



Zama tayi kan carpet ta sha kunun gyad'an da YaMara ta dama mata da yaji madara sai bowl mai d'auke da soyayyiyar dankali da sauce a gefe kuma ga peppersoup, a bisa inspection d'in Mommy ta ci abincin sai da ta tabbatar da ta ci yanda ya kamata sannan ta d'aura mata babyn a cinya ta fita da kayan sai da ta gama kissing kayanta kafin ta shayar da ita sai da ta ga alamun k'oshi sannan ta d'aurata a kafad'a yanda YaBudu ta nuna mata sai da tayi gyatsa kafin ta fita da yarinyar.




Nan ta tarda su Suleim da sauran mutane cikeda gidan, zama tayi cikinsu ta ajiye yarinyar ta na jan Azad da Afdhal tana tambayarsu duk shiru sukayi don da alamu ba gwanayen magana ba ne.



10:15 ya fito tsaf da shirin fita gaisawa yayi da su Mommy da YaMara suma su Suleim suka gaishe shi bai ko tsaya jiran nata gaisuwar ba ya koma inda ya fito, mik'ewa tayi da Babyn a hannu ba ta ko dubi kowa ba ta bi shi a baya don ta san me yake nufi da tafiyar ta shi. A kan cushion ko ta tarda shi zaune zama tayi a gefenshi tana gaishe shi, cikin sakewar fuska kamar ba Burhaan ba amsar babyn yayi yana mai tambayarta ya suka tashi. Da murmushi ta amsa masa tana kallon yanda ya tsurawa fuskar baby idanu cike da soyayya, wayarta ta d'aga ta fara musu hotuna da videos.



A tunaninta zai yi fad'a in ya ga tana masa hoto sai kuma ga mamakinta har canja poses yake yi, juya camera tayi zuwa selfie ta yi musu suma sosai kafin ta ajiye wayar. Dubanta yayi da kyau yana cewa " akwai abinda kuke so?" girgiza kai tayi tana cewa ''no'' ok yace yana ajiye babyn a kan kujera ya na mai rik'o fuskarta a hannun shi sai ji tayi ya had'e fuskar su, zare idanu tayi da ganin abinda yake yi shi ma zare mata na shi idanun. 





Lumshe na ta tayi ta na mai taya shi abinda yake mata kamar ba jiya ta gama kuka tana neman agaji ba, sai da ya ji alamun numfashinsu yana shirin d'aukewa kafin ya zare bakinshi ya rungumeta a jikinshi yana sakin numfashi kwantar da kan ta tayi a k'irjinshi tana numfashin itama. Sun d'auki kusan 10 mins kafin ya zareta daga jikinshi, pecking kumatun ta yayi ya nufi k'ofa yana ce mata sai ya dawo ko addua ba ta iya masa ba ta samu wuri kan couch ta zauna sai da ta dawo hayyacinta kafin ta d'auki baby ta fita main parlor.




"Ai yanzu nake shirin biyoki in amshi babyn in ya so ke ki kwana a can" cewar mommy tana kallonta, tura baki tayi ta zauna sai YaMara ta cab'e tana cewa " ai da alamu yarinyar ta ku ta manta zafin haihuwar ne tunda har ta fara shirin komawa turaka".


Su Suleim ne suka saka dariya suna tuno yadda aka din ga kaffa-kaffa da su idan kuma mazajensu suka zo suka tafi ta din ga masu mita kenan kamar dai zaman jegon tsaffi, dafe kan ta tayi ta ji d'ankwalin ya zame baya nan ta gane me akewa mita sai kawai ta maze ba ta ko kallesu ba sai maida kanta da tayi kan wayarta tana jin su suna ta hirar rashin hak'urin ma'auratan yanzu.





Ba a jima ba su Sophia suka zo gidan nan suma suka din ga mata tsiya kamar yadda suka saba har da cewa wai ta wa Burhaan wayo yarinyar bata bar ta a komai ba, ganin su Mommy a wurin ya sa ba ta biye musu ba sai murmushi kawai take yi sun dad'e a gidan don sai kusan yamma suka tafi haka 'yan family ma sun zo ranar gidan kamar zai fashe.



Haka su ka cigaba da samun bak'i har da costumers d'in ta da 'yan office kai 'yan complex d'in na su, duk su na ta zuwa mata barka gidan kamar ana gagarumin taro.



Yau kwana uku da haihuwa amma kusan komai na suna ya tanada a gidan, don musamman YaBudu ta yi masa lissafin duk abubuwan buk'ata itama ta gefenta ta gama tanadin komai na taron da zata yi don ta yi alk'awarin yanda ba su yi celebrating anniversary ba ba kuma su yi gender reveal party ba toh ta na son sunan yarinyar ya zama one in town a cikin Yerwan ma. Ba ta ko jira shi ba gudun kar ya kawo k'aulin da ya saba ya hana ta fara processing lamarinta, ta biya kud'in ceremonial banner da za'a yi plain mai d'auke da suna kawai ba hoto in da aka samu cikas shi ne rashin sanin sunan don har lokacin ba su zaɓi sunan da za'a sa ba ƙika kuma shi ya tsayar bai dai gaya mata ba ne sai kuma sauran souvenirs da suma zaa yi masu suna a jiki wanda kuma aka sanar mata da ba a so a wuce yau an riga da an yi designing frame d'in suna kawai za a saka a fara printing.




Hakan ya sa yinin ranar a tsumayin shi ta yi da kuma tunanin yanda zata tunkare shi gudun a samu matsala, kamar yanda ya saba in ya fita tun safe bai dawowa sai 7 duk da ko kasancewar yau Sunday bai dawo ba sai after isha'i. Abincin da YaBudu ta had'a mai da kanta ya zauna ya ci a d'akin shi ya fito da kayan babu kowa a gidan duk an watse sai k'amshin turare da yake tashi.




Ajiye su yayi a kitchen ya nufi cikin d'akinta yana mai sallama cikin k'aramar murya amsawa tayi tana daga zaune a bakin gado, k'arasa shigowa yayi ya zauna a gefenta barka da dawowa tayi masa da tambayar ya hidima ya amsa da extra kulawan da yake bata yanzu ya na mai kallon fuskarta.



Tambayarta jikinta da baby yayi ita ma ta amsa da lafiya lau, kallonta yayi da kyau yana murmushi yace " akwai wani abu ne?".



"Yaa, ya sunan babyn?".


Dafe kai yayi alamun kamar ya mantan nan yace " Ina ta son yin zancen da ke, akwai wani sunan da kike so ne?".



"Sunan Umma Or Hajjah?".


"Ko d'aya daga ciki, mu bata sunan ta mai ma'ana unique one yanda suma suka bamu namu ba tare da yin takwara ba".




"Like Yusairah?!".


"Meaning?".

"Arziki , wadata, yalwa".

"Masha Allah, Allah ya raya Yusairah".


"Yaa" ta furta tana zare idanunta da su ma yanzu ya gama lura irinsu Yusairahn ta kwasu, kallonta yayi yana mik'ewa daga zaunen yace "sai kayan souvenirs baki tura min kud'in da suka ce ba nawa ne?".


Gaya masa tayi yace "okay, ki tura min account numbern su so i'll transfer ki kuma barin saka miki kawai sai ki tura musu".


"Ok Yaa Allah ya k'ara bud'i" 

"Ameen".


"Uhmmm......".

"Akwai wani abun ne kuma?".


"No, thanks Allah ya raya Yusairah ya shirya mana ita bisa sunnah".


'Ameen ya rabbi' ya fad'i shi ma yana hawa gadon, d'aukarta yayi tana ta wutsil-wutsil ta tsurawa popn saman idanu kamar me neman abu yace " ke baki yi bacci ba?".

Kamar ta gane shi ta kuma san me ya fad'i ta fara murmushin k'uda tana kallonshi, shi ma murmushin yayi kamar an fisge shi yace " yarinyar mugun wayo zata yi just like you".



"Komai dai irin nawan ta d'auka kenan".


"Sure" ya amsa mata kan shi tsaye, gyara zama yayi ya d'auketa kamar yadda Manzon Allah ( S.A.W) ya koyar yayi mata khud'bah ya d'ora da " wainniy sammaituha Yusairah, wa inna uizuha bika wa zurriyatuha minas shaitanir rajeem, Ya Yusairah-qnuti rabbiki was judi war ka'iy ma'ar raki'in" Ameen ta furta loudly ya k'ara cewa " Allah ya shirya ki, ya raya ki ya sa ki zamo sanyin idanu garemu ya sa ki samu abun alfahari gare mu a nan duniya da lahira ya ba mu ikon tarbiyartan dake ya tsare ki da sharrin shaidan na mutane da na aljanu  ya bamu ikon nuna miki hanyar gaskiya ya sa kiyi rik'o da bezar ma'aiki".



"Sallalahu alaihi wa sallam, ya sa kuma mu zama iyaye na gari wanda manzon Allah zai yi alfahari da mu ranar k'arshe" shi ma Ameen ya furta yana sake rungumeta tsam a jikinshi yana mai jin sonta a jininshi.



Ba su wani jima ba bacci suka kwanta bacci kamar kullum yau ma ta tashi sai dai kukan bai yi nisa ba aka kawo mata d'auki tayi luf tana sha abinta tana gamawa ta samu tayi gyatsa ta kwantar da ita ta koma ta kwanta, kusan 4 ma sai da ta sake tashi daga nan kuma ba ta kuma ba sai safiya.



A ranar ne aka yi k'auri ta bakin hausawa, ba kan sa aka dafa ba su kaji ne aka yi peppered d'insu duk wanda ya zo ya ci da kuma kunun gyad'a mai jego ma saboda k'aunar ta da kifi an kawo mata manya sosai aka yi mata pepper soup ta kuwa ci sosai da sosai gefe guda kuma ta na sake shirye shiryenta don tun jiya ta tura musu da sunan babyn. Da dare su Ummu suka zo da Abbu da su twins ai ko ta samu wuri ta dinga baza shagwab'a suna mata dariya Ummu cewa tayi ''kin fa zama Mommy yanzu ya kamata a ce kin daina shagwab'a".


Tura baki tayi sama tace "ni babu wata mommy da zan zama in daina muku shagwab'a ai ni ce autar ku ko?".


Abbu yace " leave her kin ji qurratu ainiy ke ƴar autar mu ce".



"Wlh shiyasa yarinyar nan take iskanci son ranta ashe Abbu ne ya ke sakata" cewar Tayyib dariya suka sanya su duka jin yadda ya fad'i maganar har da rantsuwa. 


Juya idanu tayi tace " nan gani nan bari kuma ba".


"Ya kamata dai ki girma yarinya, yarinta ba inda zai kai ki".



"Ka zo ka girmar da ni tohm".



Shi dai Dalhat bai ce uffan ba sai da ya gama kallon yarinyar yace " gaskiya Lele yarinyar nan tana da kyau".


Komawa kusa da shi tayi tace " kamar ni ko?".


"Ai kin fita kyau sosai da kina jaririya, ask Ummu ki ji ".


Washe baki tayi tace " amma ai itama zata yi kyau ko?".


"Sosai ma zata yi baki ga ita akwai wasu kamanni na daddynta ba". 


Sai lokacin Burhaan yayi murmushi tunda ya shigo parlorn, nan fa Dalhat ya duk'ufa bata labarin jarintarta da yanda kakansu Aji Garwa yake kiranta da wasira ( balarabiya) ko larusa (amarya) ita kuma Hajjah ta fara kiranta da Gagi/Gaji (auta) sai dai bai dad'e ba tana girma tace bata so sai Lele tun a na ce mata da tsokana har ya bi bakin mutanen familyn kowa ya kamata.



Sun dade a gidan sosai ta kuma ji dad'in zuwansu don tun da ta haihu take jin kewan gida sosai, amma zuwansu ya sa duk taji ya tafi kamar ma ba a yi ba.


5 days da haihuwa mai lallenta ta office tazo gida tayi mata bak'i da ja wanda ya samu hannunta ya zauna a cikinshi tsaf don tabbas @Fahteez_henna ta iya lalle sosai. Washe gari ko around 8 ta tashi shi ma har gida aka zo aka gyara mata kai aka mata kitso k'anana two steps, ya ko yi kyau sosai da sosai tun kuma a lokacin amaryar jego ta fara had'ewa kamar ka saceta.




Ranar suna a can main mosque aka sa sunan Yusairah Burhaan Yerwa, inda wurin 7 iyaye suka yi ta su walimar a nan masallacin su da abokan arziki. Gidan suna ko bai fara d'aukar harama ba sai kusan 12 aka fara cika lokacin msi jego ta ci gayu cikin tsadadden lace black mai touches na red ba ta yi kwalliya ba amma tayi kyau ainun ana ta hotuna da videos. Azuhur event planners d'in da ta kira suka iso har da bannern sunan da aka yi tun a gate suka ajiye welcoming banner mai d'auke da sunan Yusairah Burhaan Yerwa.



A harabar gidan da ke da girma sosai don ko wani gini aka tada zai iya yin parlor madaidaici da 2 bedrooms har da kitchen da toilets sai dai ba irin shahararren mai girman nan ba, du ka motocin kuma aka shigar da su can cikin garage. Sun yi decorating wurin da komai pink and white ga balloons da ribbons aka jera chairs da tables dama da djn su da MC suka taho, sai ga caterers daga Yerwa cuisine suma wurin su daban.


To 3 aka mata simple make up wanda ya hau da fuskarta da skin tone d'in ta da kyau, nude aka mata komai har ido da lips d'inta kuwa aka mata simple d'auri a kanta bayan ta shirya cikin wata atamfa aura da ta ji embroidery work d'inkin modern Senegalese da ya samu jikinta ya zauna ta yi ado da gold tun daga kunne, wuya, hannaye da yatsu hancinta ma barimar gold ne mai lilo sai yatsar kafanta da anklets suma haka. D'aukar baby Yusairah da ta sha baby dress pink color da white an nad'e ta a shawl white kar da shi sai k'amshi yake tashi.



Tsayawa tayi a jikin console d'in parlorn aka shiga d'aukarsu hotuna, sai ga Burhaan shi ma sanye da shadda carton color ya had'a da bak'i shi ma ya fito. Sun yi kyau ainun nan fa camera man ya cigaba da aikinshi, sun yi pics sosai da yawa kafin d'aid'aikun wainda ke parlorn suka shisshiga aka yi da su har da Su ElSadeeq da suka fito daga part d'in shi wani hoto suka yi su suka shidan shi da ita a tsakiya babynsu a hannunsu, Suleim da ElSadeeq a gefen dama su ma sun rik'e Fadhal Farhaan da Zulfaa a hagu da Azad a hannayensu. Sannan aka kwantar da yarinyar ita ma aka d'auketa da different style ita ma ta zauna aka masu da ita shi ma Burhaan d'in ya zauna aka d'aukesu da babyn kafin mai cameran ya fita wajen taron mutane suka bi shi a baya dubanta yayi a hankali yace " kun yi kyau wife".



Juya mai idanu tayi tace " kai ma kayi kyau PaaPaa". 

Murmushi yayi yace "uhmm,,,,,Su Adnan sun iso fa ki d'auko mayafi ku zo ku gaisa bari in kai Yusairah first". Okay ta furta ta nemo mayafi champagne color ta yafa ta bi bayan shi,su na da d'an yawa babu laifi har da su Sadeeq da Farhaan da tun da su ka kawo matansu suke gidan barka suka mata suka gaisa cikin barkwanci sannan suka had'o wani k'aton pack wai ga kayan barka godiya ta musu sosai kafin ta fita bayan ta tabbatar da an kawo musu abincinsu Burhaan ya rakota da Yusairah a hannu a parlor suka rabu ya bata ita ya koma su na ta masa tsiya musamman Adnan da shi da biyu yake yi bai ko tanka musu ba tunda shi ba gwanin magana ba ne ElSadeeq ne ma kan kare masa a wasu lokutan.




A waje ko gagarumi k'ayataccen taron mata zallah a ka gabatar wanda tabbas ya kafa tarihi a Yerwa an ci an sha an yi hotuna an bada gifts kamar babu gobe an kuma yi rawa aka watse taron daidai Magrib kowa ya wuce gidanshi da tsarabar souvenirs daga iyayen baby. Maids ne suka gyara ciki suka koma gyara wajen tsaf kamar ba a yi wani taro ba, ranar ko tayi baccin gajiya sosai don ko shigowar Burhaan ba ta san da shi ba sai da tsakar dare ta gan shi.




A haka suka cigaba da rainon Yusairah cikin kulawa da soyayya, ga kuma iyaye da kakanni ta kowani fanni su na basu gudunmawar da ta dace da su ba su yin kwana biyu ba su lek'o su ba. Da jinin haihuwa ya d'auke ko k'in nunawa Burhaan ta yi don ta gama karantar so yake ta koma turaka kafin arba'in.



A hankali kwanaki su na tafiya su ka yi arba'in saboda son ya bar ta tace masa bai tafi ba, ya ko ji haushi don ya gama saka rai hakan ne ya sa ya k'yaleta bayan ta gama zagayen dangi a Kaduna ta wuce Abuja satinta d'aya a can har office d'in ta sai da ta lellek'a ta had'a reports na yanda abubuwa ke tafiya aka kuma tsumata yanda ya kamata. Daga can Lagos wurin su Suleim da tun gama suna da kwanaki ta bi mijinta ta wuce shi ma ta shak'ata yanda ya kamata, ta yi booking jirgin Kano su ma ta kai musu ziyara kwananta uku ta komo gida.



Ai ko yanda Burhaan ya shak'a sai da ya fanshe a ranar da ta dawo babu ko d'aga k'afa sai da ta yaba wa aya zak'i da kanta ta yi nadamar tafiyar tata ta kwana 18 a dare d'aya kacal, sannan ya koma gefe ya bar ta da tsamin jiki ta fara bacci babu dad'ewa Yusairah ta farka. Ji tayi kamar ta daki yarinyar haka ta d'auketa ta shayar da ita Allah ya taimaketa bata dad'e ba bacci ya d'auketa ta koma ta sake kwanciya duk Burhaan yana jin ta amma ko motsi bai yi ba don ba wani hucewa yayi ba.



A tafiyarta har wani maraya ya zama na k'arfi da yaji bai tab'a sanin haka ya shak'u da ita ba sai da bata nan a lokacin ya tabbatar da ko ba sonta a ran shi to ta lashe kaso mafi tsoka na zuciya da rayuwarshi. 




Hutun 1 week ya d'auka yana hutawarshi babu kama hannun yaro, duk da yana mata mugunta ne amma har ga Allah tana jin daɗin abinda yake faruwa. Sai aiki ne da ya so mata yawa don YaMara tun da akayi arbain ta koma inda ta fito da sha tara ta arziki daga su da iyayensu, ta musu sosai musamman da aka bata driver sukutum ya d'auketa da kayanta zuwa Maiduguri.




One week da dawowarta ita da shi suka koma bakin aikin su, da Yusairah take tafiya in tana aiki ta saka ta a d'an crib d'in su na jarirai wani lokacin kuma ma'aikaitan wurin ba sa wani barin ta da ita tana hannunsu don ba ta k'uiya ko rigima don ma bata fara cin abinci ba exclusive suke yi.



A wannan lokacin zata iya cewa bata tab'a rayuwar da ta kai wacce take yi ba dad'i don sosai Burhaan duk da yawan kulwar da baby yake yi amma tana jin dad'in hakan ainun don ko ba komai Yusairahn jininta ne. Duk da dai bai hira da ita bai kuma cika zama da ita ko a gida ba balle a kai ga maganar shawara wasu abubuwan ma sai dai ta ji a bakin Ya Budu ko Safwaan da ya d'an janye jiki da zuwa gidan.



Ta san shi ba gwanin hira ba ne amma abun ya fara isanta a ganinta lokaci yayi da su zama abu d'aya tunda sun shak'u kuma zamansu ya kamata a ce ta d'auki saiti ko yaya ne, d'an Adam da nuna gajiyawa sai ta ji ta k'osa har ta kasa jurewa ranar tana hanyar zuwa office ta kira Suleim sai dai bata d'auka ba sai da ta gama parking har sai ga kiranta d'agawa tayi ta fita daga motan suna gama gaisawa ta fara gayawa Suleim halin da take ciki yanzu a lokacin tana kan staircase karo tayi da wata ba ta ko duba wacece ba don magana take yi hannu kawai ta d'aga mata alamun sorry sai da ta kai kan matakalar k'arshe ne ta juyo jin idanun wacce ta bigen a kanta suna had'a idanu waccan d'in ta juya da sauri ta sauka k'asa tab'e baki tayi itama ta shige floor d'in na su. 


Zama tayi inda a nan Suliem ta din ga ba ta shawarwari masu muhimmanci da nuna mata lokaci yayi da zata fara kama kanta kar ta sake zurmawa da yawa, maybe hakan zai janyo hankalinshi kanta duk da sun kusa yin lattin aikata hakan amma ta gwada ta gani ko za a dace. Godiya tayi mata ainun inda a d'an kwanakin ta fara practicing abinda aka gaya mata ai ko sai ya fara shige mata kamar ba shi ba, in tayi shiru ya dinga nan nan da ita kenan a take ta fahimci cewa maganar nata ne bai cika so da yawa ba ta kuma gane yana son kamewa da aji ko yaya ne.



Nan ko ta fara morar aurenta da kyau sai dai bai yi tsayi ba ya fara b'ullo da wata d'abiar kuma, wato rashin zama a gida musamman da dare don in ya tashi fita sallahr Magrib da mota yake fita in kuma ya fitan sai ya kai 9:30 wasu lokutan kuma 10 pm kafin ya dawo yana dawowa kuma ya rungumi waya kenan shi da ba gwanin waya ba ne amma yanzu sai ya kai 11 a kanta yana ajiye wayar kuma zai addabeta, tun abun bai damunta har ya fara damunta da tayi magana a karon farko a rayuwar ta da shi ta fuskanci yayi k'arya don cewa yayi " wai wani lectures ne yake attending" amma abin mamakin shi ne mutum irin Burhaan ne zai yi online lectures a waya me yaci system da ba zai yi da shi ba? Kai abun sai dai in gyaran taku ne.




Zura masa idanu tayi tana kallon ikon Allah bayan kamar 3 months sai ya canja pattern don daga office ya koma dawowa 5 pm a d'an lokacin yake kallon news su d'an yi hirar da da ba sa yi yayi wasa da Yusairah da a lokacin take rarrafe ba inda ba ta zuwa an kuma fara bata abinci a gidan Hajjah ma take barinta wata rana taje office, a d'aid'aikun lokuta ne take zuwa da ita. D'an sauyawar da ya yi ya sa ta yarda da abinda ya fad'a mata na lectures don lokacin ya gaya mata yana son ya sake komawa sports therapy da addua ta taya shi kawai don ba ta san komai kan course d'in ba sai wanda ya gaya mata.

Some weeks later.

A gurguje ta fito daga wankan da ta shiga sakamakon jiyo sautin mutsu-mutsun Yusairah na tashi daga bacci, don ma ba ta da hayaniya 'yar lab'ub'uwar baiwar Allah. A zaune ta isketa tana k'ananun gwarancinta na alamun yaro mai magana, murmushi tayi ta na mai cewa " sweetheart kin tashi?" ta k'arashe tana duk'awa gaban gadon cikeda soyayya inda Yusairahn take ta mik'o hannu alamun tana son zuwa wurin uwarta, cewa tayi "sorry my love bari in saka kaya in zo please, just two minutes".



Wucewa tayi zuwa mirror ta zauna tana hangen d'iyar dake cigaba da zuba gwarancinta tana kallon Maman, mai ta fara shafawa tana mai hira da ita cike da lallashi gudun kar tayi mata kuka kafin ta gama. Cikin ikon Allah ko taci sa'a don har ta gama ko uhm bata ce ba sai ma komawa da tayi ta kwanta tana wulla y'an k'afafunta sama, closet ta nufa ta ciro wani cargo pants khaki green da wata crop top mai mannewa a jiki cream color. 



Komawa gaban mirror tayi ta taje gashinta da tayi spraying d'in shi da hair spray mai dad'in k'amshi na rosemary,cloves, hulba mai hana karyewar gashi, d'aure shi tayi bata shafa wax ba ta bar gaban a haka ga sajenta da suka kwanta a kan skin d'in ta da ya k'ara fitar da kamala da sirrin kyan nata sosai.


Turare ta k'ara fesawa kafin ta nufo wurin yarinyar tata, d'aukarta tayi ta na mai cewa " mu je in ma baby shirin bacci". Toilet ta wuce da ita bayan ta cire mata kaya diapern jikinta ta zare ta saka a waste bin, ta fara mata tsarki kafin ta sanyata a ruwan da ta had'a mai madaidaicin zafi. Nad'o ta tayi a towel ta fito, ta na tsaka da shiryata kira ya shigo wayarta da sauri ta tashi tana cewa "papan princess is back " wayar ta janyo ta kara a kunnenta kafin ta kai ga magana ya tare ta da maganar dake yawan hargitsa mata kai da tuno mata da wani lamari most esp jin muryarshi babu walwala ko karsashi wato "ki zo ɗaki na yanzu" ya kashe wayar gabad'aya kafin ma ta kai ga amsawa.



Ajiyar zuciya ta sauke ta k'arasa shirya yarinyar da sai mik'a hannu take yi a k'irjinta alamun ta na jin yunwa, bodysuit ta sanya mata ta sa mata turaren yara kafin ta tashi da ita a kafad'a tana lallashi. A parlor ta same shi yana ta kai komo ganinta ne ya sa shi sakin bayyananniyar ajiyar zuciya yana mai nuna mata wurin zama, zama tayi a hankali ta d'aura yarinyar a cinya ta fara k'ok'arin shayar da ita gudun k'arewar hak'urin yarinyar.



A zafafe ko ta k'arba har sai da taji zafin yanda ta ja nonon kamar za ta tsinke shi, zama yayi a gefenta yana cewa " ita wannan ya akayi take yi kamar ta yini bata ci ba?". Cewa tayi " wanka muka yi daga tashinta, ina shirin feeding d'in ta ka kirani".



"Ayya, sorry sweetheart " ya k'arashe yana rik'e K'afafunta da take shillawa alamun tana jin daɗin nonon har kwanyarta ma, ita ko Nadeefahr tana shayar da ita ne amma rabin hankalinta yana kan shi jira take ya mata maganar da ya sa shi kiranta. Don taga alamun bakinshi da magana tun a shigowar ta d'akin kai in ma ba k'arya tayi ba sai tace ya kai 1 month a wannan halin sai dai kamar bai san ta ina zai fara maganar ba don gabad'aya ya rasa a suitable word that'll be perfect for him, d'an gyaran murya yayi da ya sa ta dube shi da kyau tana cewa " Yaa a kawo abinci ne?".



Kai ya girgiza mata yana cewa " sai anjima yanzu dai ina son yin magana da ke ne wife".



Tattara hankalinta tayi kan shi don son jin abinda yake tafe da shi wanda take hango tarin girman da yake da shi a cikin idanuwanshi da fuskarshi, kallonta ya kuma yi wanda ya kashe masa k'warin guiwarshi gabad'aya wanda sai yanzu ya yarda mata suna wa mazajensu kwarjini musamman a irin maganar da ya d'auko.



Sake gyaran murya yayi yana mai cewa "Nadeefah!!".


"Naam Yaa Islaam".



"Ina son in fara da gode miki akan kyawawan halayen ki wanda suke da wuyar samu a wurin mata duk da ana cewa nobody is perfect amma ke kin tara komai. Soyayy, kyautatawa da kyautayi duk suna cikin sunan ki. A rayuwata ban tab'a jin labarin mace irinki ba mai matuk'ar kyau, hankali da nagarta, wanda ko na yi rantsuwa ba zanyi kaffara ba ke d'in ce irin matan da manzon rahama ya suffanta da mace ta gari don duk motsinki a gidan nan faranta min rai kike yi, ba ki tab'a d'aga muryarki saman nawa ba, baki tab'a judging d'ina akan duk irin abinda nake miki ba kina shanye duk wata musgunawa da nake miki wanda by Allah na sani hakan ne kuma ya sanya min wani kab'akin ganin girma da kwarjininki a idanuwana ainun".




Shiru yayi ya nisa yana sake dubanta da itama dubanshi take yi cikeda damuwa don bata san dalilinshi na wannan dogon maganar ba ya cigaba  da cewa " don haka duk abinda zai faru kar ki sake kiyi tunanin wai zarafinki zan ci ko kuma wai ban sonki, wlh ko d'aya don duk yawan matan da zan yi a duniya da lahira ke ce sarauniya a tsakaninsu. Kuma kece sirrina marufar asirina ta har abada so wannan abun da zai faru ki sa a ranki k'addara ce wacce ta riga fata, kin san yanda ƙaddara take aiki......in ta zo babu makawa sai ta faru ba zan yi shi don musguna miki ba ne but......" 


Kasa k'arasawa yayi ya d'ago ya tsura mata idanu, wanda ita ma da wani irin kallon take bin shi yayinda zuciyarta take wani irin tsinkewa da bugawa kamar zata b'urma k'irjinta ta fito a rik'e mata shi a hannu. Had'iye abunda take ji tayi tana mai cewa " Yaaa, me yake faruwa ne haka? Kana tsorata ni don bai yi kama da kai ba. Mijina da na sani is a straight forward person bai tsoron komai kullum yana faɗin abinda yake ran shi bai shakkar abinda wani zai ce, meyasa yanzu kake kewaye ne? Ko kana tunanin ba zan iya d'aukar ko me kake tafe da shi ba ne?" Ta k'arashe da wani irin numfashi na hakin bugawar zuciya.



Muk'ut ya had'iye wani yawu ya girgiza kai yana cewa " ko d'aya Wife, kawai I'm very sorry ".


"Why are you sorry? Ka gaya min don Allah Baby".


"Aure zan yi.....''

D'aukewar numfashi na wucin gadi ne ya kamata, k'yarr ta tsayar da kyawawan idanunta a kanshi ta kasa motsi sai kuma kamar an dawo da ita daga duniyar ta fisgi numfashi da k'yar tace "Aure...??!"


"Yeah, but ki fahimce ni wlh ba wai zan yi aure don ci miki mutunci ba ne....."




"Zaka auri wacce kake so ko?" Ta katse shi.


Girgiza kai yayi yana mai cewa " ba fa zan yi auren nan don ban sonki ba ne....."


"Kana son d'and'ana dad'in auren soyayya right? Ka yi iya ƙoƙarin ka don ganin ka so ni but ka kasa ko? Well, na fahimta" ta sake katse shi tana mai jin wani d'aci yana tasowa daga k'irjinta zuwa mak'wogaranta har kan harshenta.


"Ko d'aya ba haka ba ne maganar so duk ki ajiyeta a gefe".


"Ba zaka iya so na ba huh?".


"Ina son ki mana, ke da jini na ce kuma uwar ɗiya ta mom mutum na farko da ta tab'a bani farinciki a siffar Yusairah in ban so ki don komai ba ai na so ki don nagarta da kyawawan halayenki so please ki daina cewa ban sonki". Ya k'arashe yana mai kamo hannunta guda d'aya.



"Ban da matsayin da ya wuce uwar ɗiyar ka ko?".


''Nadeefah!!!".


Hannunta ta zare daga na shi tana mik'ewa gabad'aya ta manta da wata Yusairah a jikinta, ko da ta farga ba ta bi ta kanta ba cisgeta tayi daga nonon ta dire ta kan kujera kallonshi tayi mai cike da wasu mabanbantan yayi a idonta shi ma kallontan yake yi cewa tayi.


"Allah ya sanya alkhairi ya baku zaman lafiya" ta juya da mugun sauri don jin wani hawaye na taso mata ficewa tayi a d'akin zuwa na ta yacce ka san an biyota da gudu, kafin ya tashi sai k'arar buga k'ofar ya jiyo shigewa tayi cikin d'akinta ta fad'a kan gado bayan ta datse k'ofar da key ta bar shi a jiki.




Wani irin kuka take yi mai tsuma rai da zuciya, yi take yi kamar ran ta zai fita ba kuma wai na auren ba ne zallah don shi wannan na shi daban ne yanzu wanda take yi na yanda ta zama sakarya kuma sokuwa a kanshi ne. Ba ta tab'a jinta a mara daraja kamar yau ba, wato ashe ba abunda ya kai k'ask'anci zafi, k'ank'ancin ma na kai don ba shi ya k'ask'anta ta ba itace ta zubar da kanta. Wato duk effort d'inta a kan shi na neman soyayyarshi ta zama a banza kenan? Shi bai tab'a mata kallon wata aba mai daraja ba sai baby mama.



''Ni sakarya ce!!" Take ta nanatawa cikin kuka tana mai jin duniyar ta fita ran ta sai dai kamar jaraba mugun son shin nan yana nan a yanda yake ba abinda ya ragu in ma ba k'arya tayi ba sai tace k'aruwa yayi akan na da wanda shi ne yake sake tunzurata ga yin kukan. Biyota yayi ya zo bakin k'ofar yana knocking da kiran sunanta tana jin shi amma ko motsi ba tayi ba, da yake k'ofar sound proof ce na waje bai jin na ciki but na ciki na jin na waje ya sanya bai jin kukan nata sai yayi tunanin ko ba room d'in take ba.



Bud'e sauran k'ofofin yayi har na artroom duk bata ciki, dawowa nan yayi ya cigaba da bugawa yana kiran sunanta sai dai ko motsi ba tayi ba balle ya sa ran bud'ewarta. Juyawa yayi zuwa part d'in shi neman spare keys nan ya tarar da Yusairah tayi kuka har ta shid'e thank god kujerar shi ba irin k'ananun nan ba ne akwai fad'i sosai, da sai ta fad'o k'asa d'aukarta yayi yana jijjigawa amma sai laluban k'irjinshi take yi alamun neman nono jin babu ya sanya ta sake tsandara ihu.



Wayarshi ya d'auka ya fara kiran Nadeefahn sai dai duk tulin kiran da yake mata ta k'i picking bai bi ta kan neman spare keys ba ya sake komawa k'ofar d'akin nata, knocking ya cigaba da yi yana cewa "Nadeefah!! Ki buɗe ƙofar nan". Tsaki tayi tana cigaba da kukanta sai kuma ta tsinkayo kukan Yusairah kamar ta k'yale shi da kayanshi sai kuma zuciyarta ta k'wabeta, don kuma ya mata laifi ai bai shafi 'yarta ba.



Goge hawayen idonta tayi ta nufi k'ofar tana bud'ewa yarinyar ta zaburo zuwa uwarta cikeda zak'uwa, karb'arta tayi ba tareda tace masa komai ba ta koma d'akin da niyyar ta sake kullewa ya turo k'ofar ya shigo cikin d'akin. Wani mugun kallo ta jefe shi da shi ta koma bakin gadon, jijjiga yarinyar ta yi ta bata ruwa ta sha ba ta ba ta nono ba don ba yunwa take ji ba in ma kuma ba ta k'oshi da nonon ba to sai dai ta bata cerelac kam ba wai nono ba. 



A kan kafad'a ta sanyata ta na ta ajiyar zuciya ita kuma har lokacin ba ta daina kukan ta ba, sosai take cigaba da kukan dake sake kassara k'warin guiwar Burhaan tabbas in da yana da yanda zai yi da ya fasa auren nan ko dan yanda ya hangi tashin hankali da damuwa a idanunta amma kuma bai jin zai iya hak'ura da Fareesah don haka nan ya k'wallafa rai a kanta bai taɓa jin son wani abu kamar ta ba in kuma ya sake ya rabu da ita to yana jin zai iya shiga mafificin tashin hankalin da ita take ciki.




 A halin yanzu hankalinshi ya rabu biyu d'aya shi ne damuwar da Nadeefah take ciki wanda a da bai zaci hakan ba, ɗayan kuma shi ne yanda zai tunkari su Abba da maganar auren har ma su goya masa baya wannan abu ne da yake ganin yiwuwarshi ba lallai ba amma ko kusa ya fi damuwa da halinda Nadeefah take ciki fiyeda wanda zai tarar gabansu Abba.............




Ji wata lukutar masifa wai aure!! Like what?! Why please? Like why exactly jama'a mai maza suke nema ne🥺?
Deejasmah ✍🏼