TALES OF THE WAZEERIS

chasing dreams

by @surayyahms

33...🦋🦋🦋

SURAYYAHMS

TALES OF THE WAZEERIS...

washe gari da safe duk dama jiya shamsan yaqi ya kula kowa da ya dawo cikin banana island mansion din bai hana gidan ya kasance cikin nutsuwa ba,...

kafin karfe bakwai na safe staff suka gama shirya komai na breakfast acikin babban dining area din gidan saboda farin cikin dawowar sultan shamsan wazeeri lagos nan ma haka hajy ummu salma ta sako jikarta leelah agaba sassafe tasa ta tayi supervising din chefs har suka gama shirya komi kafin nan tawuce dakinta domin shiryawa

daga private wing dinsa kuwa tun da asuba ya idar da sallar ya shafe lokaci mai tsawone acikin private gym din dake sashen inda kwata kwata babu hayaniya komai nasa na tafiyane cikin tsarin nitsuwa da jajircewa irin wanda ya saba dashi tun yana karami.

bayan ya gama motsa jiki kai tsaye ya nufi shower yay wanka yana fitowa ya shirya kansa tsaf a cikin cambrigde grey tailored suit mai dauke da long black coat mai tsananin tsada wanda yake kara bashi wnan intimidating royal aura din nasa...

yanayin kayan dayake sakawa ajikinsan gaba daya yasha bambam dana normal yan gayu masu kudi ko kuma turawa sbd shi crown prince ne dan haka designer dinsa yake zuwa da dogoyen matured royal overcoat dan kowani irin suit zaisaka dolene kaga yakasance ahaka kodan sbd ya banbamta da kowa.

black shades dinsa masu siririn frame ne manne akan idanunsa yayin da agogon platinum dake hannunsa ke kyalli koda ya fito daga private hallway dinsa zuwa sitting room atake wajen ya dauka da wani irin qamshin turaren sa na sovereing xviii mai azaban dadi me bugarwa lokaci guda.

cikin kasaitaccen takunsa yake saukowa ahnkli kmr baxai taka kasa ba, lokcin its already past 8:00 yasan kowa da kowa yana kasa dan haka xai iya daurewa yau agaisa da kowa da kowa...

Rihanna data dau wanka taci kwalliya da babban leshi kamar ba gobe tana zaune akan chair na dinning din tare da duka family tana duba phone dinta a hankali gabaki daya hanklinta baya jikinta duk dama cikin dake jikin tan yadan kara mata ƙiba da nitsuwa sosai amma kwayar idanunta na daukene da wani irin zakuwa na son ganin dan uwan ta da ta jima bata gansa ido da ido ba.

yana shigowa sashen kasa tunbai gama karasowa ta wajensu ba rihanna ta shaƙo qamshin turarensa da wani irin sauri ta aje wayar dake hannunta akan table din ta miƙe tsaye da sauri...suna hade ido sanda tafara sakin murmushi mai sanyi ma bata sani ba da wani irin farin ciki aranta tafara tahowa tawajensa da zumudi tunbaima karaso ba taje da sauri sauri idonta cike da ruwan hawaye ta fado jikinsa ta rungumesa sosai.

da wani irin compose expression ya tsaya cak na dan sakanni yana jin yadda ta rungumesan kam kam kamar wacce tay shekara dubu bata gansa ba.

ahankali yasauke hannunsa asaman kanta da nutsuwa ita kuma ta dan janye jikinta anashi kadan tana zuba masa sanyin murmushi mai tafe da hawaye da sanyin girmamawa ayanayinta tace you are welcome back yaya.. da gefen idonsa ya kalleta na dan lokaci kafin nan ya gyada kai ahankali.

yace..kina lafiya?ta dan yi murmushi kadan tanamai share hawayen idonta tace "lafiya kalau am so glad ure back..baice komi ba kawai ya kyaleta ta riko hannunsa suka karasa saukowa tare

hajya ummu salma ce ta fara daga kai tana kallonsa da murmushi mai cike da kaunar datakewa jininta

tun kafin yay magana tamike tsaye da murna tace sannu da dawowa sultan ya dan gyada kai cikin girmamawa baice komi ba har saida suka zauna snn ya gaisheta, dan a matsayin kaka take masa, tunda dai itace agidan take bin bayan kakansa shugaba khaleefa acikin uwarjini.

leelah dake zaune daga dayan bangaren table din cikin wani elegant dark olive silk gown mai matukar kyau tasaka soft diamond pieces a kunnuwanta da wuyanta tuni tay sumewar zaune dan fiyeda komi a rayuwarta tana mutuwar son namiji mai tsananin kyau da kwarjini

tun shigowar shamsan wajen idanunta suke kansa cikin wani quiet confidence tuna cewa babu wani namiji daya kai shi class acikin generation dinsu...

saidai dake tana da aji sai bata nuna over excitement dinta a fili ba kawai ta dan gyara zamanta tana kallonsa da karamin murmushi tace welcome back to lagos sultan..

batare da yakalleta ba yadan gyada kai kadan yace thank you, sai kuma yay shiru batare da sake bawa kowa kofar cigaba da wani conversationbba..

babu irin signal din kakanta batamata dan ta tashi tay serving dinsa abinci ba amma inaa batama son ta mike tsaye bare ajega tayi disgracing kanta dan tasan bata iya komi ba

ita kanta chef ne suke zuba mata abinci idan zataci tun tana yar karama ta saba da wnn rayuwar lalaci da sangartan dadin karawa ma da akace mata sultan shamsan zata aura.

she knew he is going to be the future king duk wnn aiki wahalar ai basai ta iyasu ba...

tunda shamsan ya iso wajen farees salman ya hade ransa tamm yana zaune shiru da wata flashy ipad a hannunsa yana duba wasu charts kamar baya wajen alhalin cikin kokon zuciyarsa bala'in tafasa yakeyi da sosai ya tsane zama a inuwar shamsan arayuwarsa.

ganin baice ma shamsan din uffan ba yasaka duk yawanci akay banza dashi har chef sukazo suka fara zuba ma kowa abinci...

rihanna ta tashi ta saka ma yayanta dan sosai tasan kalar dokokin dabia dayake zagaye da rayuwarsa

baya magana sau biyu snn ba gaisuwar kowa yake iya amsawa da bakinsa ba, he can enter any room witout permision, hakama baya jira, ko daukar delays, koda a meeting ne inhar ya iso weda ure present or not zai fara aiwatar da abunsa snn ba akatseshi.

fannin abinci kuma sau daya ko sau biyu kacal yake iya cin abinci arana at the same time no variation.

baicin abinci a public space snn wani daban awaje baiya bashi abinci inba private chefs dinsa da aka riga aka kayyada ko wani jininsa ba

akowani bangare na rayuwarsa akwai tsari da aka sansa dashi dan hatta personal nd inter personal routines, da work ethics dinsa are well know to all staff, normally kowa yasan sultan shamsan mutum ne da baiya fiye son magana. amma abu mafi wahalar dauka a halinsa shine baya bada hakuri, nd he will neva ever explain himself to you komin fushin da zakayi dashi, gashi shi baya iya reacting a fili bare har ya nuna maka haushinsa a bayyane duk wani haukn tarukucen rarrashi da unnecscry shakuwa da mutane duk bai iya shi ba muddin kana tare da shi saidai yasaka ka acikin duhu amma badai ki iya karanceshi tsaf ba.

wann sanyin nitsuwar dake tattare dashi ne a shimfide ayanayinsa kusan kowani lokaci in yana cikin family gathering irin haka.

kanwarsa rihanna tun da tagama serving dinsa abinci tadawo ta zauna hankalinta gaba daya yana kansa ne tanajin farinciki aranta bana kadan ba dan ko ba komi tasan yayanta yana nan bazatanajin fargaba ko tsoron duk wani decision datake son tayankeshi akan auren ta da farees ba.

duk dama tanason mijinta kamar ranta amma kowani lokci wani case ya taso tsakaninsu bata samun wani mai bin bayanta agidan koda ta kamashi yana cin amananta ta wayane saidai kaji ummu salma ta bata hakuri amma bazata ta dora ma farees laifin komi ba.

they always tell her dat men are polygamous in nature saidai tayita masa addua..atleast now dat her big bro is back tasan shide bazai gaya mata irin haka ba duk dama tasan baiso aurenta da farees ba kwata kwata

she is not even suprise dataga basuce ma junan su uffan ba, gani take kmar farees normally yasaka aransa ne cewa sultan baya kaunarsa sbda case da akayi na aurensu, she have no idea cewa akwai wasu dalilai na daban da fareesh din yake boyewa.

calmly kowa yake cin abincinsa in a classy royal style ummu salman tanadan jan shamsan acikin hirar business sama sama shikuma yana amsata da kalma daya.

suna cikin maganan wayarta yay ringing ganin mijinta ne ya saka tay excusing dinsu ta haura sama cikin sauri

ficewar ummu salma daga falon bada jimawa caraf leelah ta dago idanunta da suka sha kwalliya ta kalle shamsan dasu ahnkli tace...ur highness tun bayan wacan lkcin da mukayi waya shikenan then you disappeared for months

jin bai amsata ba kunyar idonsu rihanna da farees yasaka tadau coffe tay sipping, ta dago kai kenan kafinta kara budan baki cikin katseta ahnkli yace..

"i was busy....

dan shiru ne ya ratsa wajen kafin nan leelah ta jingina bayanta da kujera cikin kakaro makanta steeze tace anyways,.. i was thinking of hosting a private welcome dinner for you this evening, close circles only...

shamsan ya aje glass cup din ruwan dayasha ahankli muryansa kasa kasa yace

“cancel it....

leelah ta daga girarta sama dasauri tareda rolling masa eyes ayangace tace haba ur highness you haven’t even heard the plan.

yana aje food napkin dinsa ya miƙe tsaye almost in a whisper yace excuse me, i have meetings.

...acikin nitsuwa yafara gyara agogon hannunsa leaving them speechles

farees yafaraji kmar ya tashi ya shakeshi cos he hated his guts bana kadan ba, irin kadinga jin aranka waime yaron nan yakeji dashi ne sbd tsakaninsu baifi shekra daya zuwa biyu ba gani yake ma kamr ya girme shamsan din dan yanxu farees is going to 34yrs yasan kuma shmsan bazai wuce 32-33yrs ba so akwai wann turirin hasada da rainin knwing shamsan is far far ahead of him in everything in this life kuma yasan idan yana nan bazai ci kudin rihanna anyhow kamr yadda yasaba ci ba

daidai nan ummu salma ta karaso falon da waya a hannunta ta dan kalleshi da sauri ganin ya mike tsaye tace ahhh ahh ranka shi dade sultan... ina zakaje kuma tun baka huta ba?

bai ce komi ba kawai ya juya ya fita daga dining area din with this silent authority da yasaka wajen sake yin shiru.

leelah bata iya dauke ido akansa ba har ya bace ma ganinta kafin can ta sauke ajiyar zuciya suna hade ido da kakarta ganin tana mata wani irin kallo tace oh gosh grand ma he has meetings okay..

da masifa tace mata toh meyasa ke bazaki hanzarta kibishi ya saukeki anaki office din ba..ahaka ne zaki iya rike namiji???

cikin sauri leelah ta mike tanamai gyaran expensive silk gown dinta yayin da high heels dinta ke kwas kwas akan marble floor din mansion din cikin hanzari tace good idea grand ma..i will see u when i am back.

tana fadin hakan ta dauki designer hermes bag inta ta fice tana tafiya ahnkli cikin wata kalar yanga da uban jiji dakai dan tajima tanaji ajikinta ita matar sultan ce nd with the way she carry herself so high tun batakai haka ba gashi abun har ya bi jikinta sosai, tana fitowa tasamu har cars dinsa sun kara da gaba..

rau rau tay da idonta in disbelive tace wait.. har ya fice already? ta fada tana kallon daya daga cikin staff dake tsaye cikin tsananin jin tsoronta yace...“Yes ma’am. da wani irin kallon raini tace masa "where???

yace..Eko Atlantic maa.

atake fuskar leelah ta sauya da rashin jin dadin jin hakan taja wata miskillalen tsaki ayangace ta rataya hermes bag dinta ta dan cije lips ahankli tana jin haushin yadda shamsan ke cigaba da treating dinta kamar baisan da cewa ita zai aura anan gaba ba

she notices how he treat everyone with same cold distance duk da kusancinsu na family

can ta daga kanta cikin isa tace ma staff din hey u big for nothing ugly fool just bring my car around....

within few minutes ya bar wajen saiga nan wata luxury black range rover ta parker agabanta nan ta shiga ahankli tanamai gyara designer shades dinta kafin nan motar ta fice daga banana island mansion din cikin nutsuwa aka kaita nata office dinta dake cikin lekki dan yanxu ita take handling abubuwa dayawa na kakanta anan nigeria da kuma kasashen waje dake sune suke riqe da harkan mechanise agro investment na ahalinsu na waxeeris gabaki daya...

dagata fannin ushna kuwa da asubahin fari ta farka daga bacci da adduar tashi daga baccin abakinta kafin nan ta tattare gashinta daya barbaje wajen bacci ta sake maidashi cikin hula kfin ta sauko kasa taje tay alwala.

after few minutes ta fito ta kama sallah, tay normal routine inta na azhakar da karatun qur'ani tana idarwa bata koma bacci ba ta jawo laptop inta ta duba email da sauri ganin sabon sako ya saka ta bude taga instant rejection letter ne da aka dawo mata dashi..

memakon taji haushi sai ko ajikinta, sake dalewa kan gadonta tayi ta sake rubuto wani application din me zafi ta hada harda attachemnts na qualifications dinta ta sake turawa aranta tana cewa zakuga maita kuwa

bayan ta rufe laptop din ne ta bude wani leda cikin kayan da mahaifyarta ta bata ta dauko dry mint ta kunna tea maker data gani awajen ta tafasa mint in bayan ya dan sha taje tay sieving a sink ta dawo ta zuba natural honey ta shanye abunta tasss after like 10 mints saita koma bacci.

ba ita da farkawa ba sai wajajen karfe goma na safe jin yunwa na cin hanjin cikinta yasaka ta jawo wayar dake wajen ta kira kasa tay oder na abinda zataci tana gama saka oder ta fada wanka bata jima ba ta fito, tafara shiri ganin kayanta kwata kwata basufi guda biyar anan ba yasa tafara tunanin sake sayan wasu koda kdan ne kafin nan Allah yasaka a karbeta a wancan kamfnin

irin dressing in data sabay a london tay multi colour stylish oversized shirt da denim skirt saita daura vintage scarf kalar rigar ya mata kyau sosai musmn ma data rataya side bag inta tasaka highheel mai aji ta sauko.

duk dama bata fiye son kwalliya mai yawa ba amma bakaramin ido ne yake bibiyarta ba, kana ganinta kasan ba yar talaka bace, most ppl assume she is not even nigerian amma dake anriga anga yanayin musulunci atattre da iya yasaka gayun basu tun karota kai tsaye ba.

atsakane ta zauna akan table aka kawo mata oder inta ta zauna tacinye abincinta tsaf, tana ci sai addarta arisha ta fado mata arai..she wonders why arisha bata kirata ba kodan ihun data mata ne oho...koma miyene dai ita yanxu bata wani lkci babbn damuwarta baifi taga an karbeta awann kamfanin ba

bayan tagama cin abincinta dake batasan garin lagos ba sai tafara jin tsoron ficewa waje mai nisa yin siyayya karta je ta ɓata ta kasa dawowa nan gashi batasan kowa a nigeria ba sai iyayenta da yan gidan su.

wayarta ta dauka tana kan exploring hotel din sai taga ashe ma suna da mini shoping mart aciki she find her way using google map sabida yadda ake kallonta fresh nepo baby da wani irin ido yasaka kwata kwata bataji shaawar tambayr kowa ba can sama ta haura tukun ta fado acikin wani waje da ake saida shoes, dresses da tarkace saidai gaba daya irin na lagos baddies dinnan ne short skirts, slit gowns...da kyar ta samu wasu suite dede size inta daya baki daya kalar kasa kawai sai ta saya guda biyu da wani black gucci blazer ta biyasu kudinsu ta sauko kasa

koda takoma dakinta still wani rejection letter din ta sake gani an dawo mata dashi kamar ma automated message ne da alaman sakon baya isa xuwa ga kamfanin kawai daga ka turo inde application ne system dinsu zai detecting snn yatura maka automatic rejection letter.

saida ta tura sau uku taga abu dayane ake dawo mata dashi kafin taji hanklinta yadan fara tashi atake tafara tunanin next abunda ya kamata tayi..

tagama jera sabbin kayanta a trolly inta kenan da niyyar zata fito waje tunda the same area suke da kamfanin zata booking ride yakaita ko survey taje tay ta dawo...

tana gama ayanna wann tunanin bata ma samun daman booking ride inba kawai aka fara ruwan sama...

********

ata bangaren sultan shamsan agaban wata hadaddiyar hotel dake eko atlantic motocinsa suka sauka nan da nan luxury black convoy dinsa na RR ya tsaya a private entrance.

tun daga reception floor akay clearing tarukucen jamaa har saida ya shige inda zai gana da da dukakn african partners dinsa daga bangarori daban daban akwai boards of representatives dinsu daga morocco, south africa, kasar egpyt duk dai sun hallara suna zaune.

dake sultan din ne jagorar project din yana isowa wajen babu bata lokaci aka fara gabatar da komi atsanke wanda akalla meeting din ya dauki kusan 2 good hours suna discussing multi billion dollar projects, smart cities, luxury coastal expansions da mining agreements...

daga gefensa wata siriyar mata ce ana ce mata mrs Ameeenah maude, zaune take a cikin neat corporate dress tana famar organizing masa every financial detail without mistake.

daga gefenta akwai younger front desk sectary insa me suna omolara charles ana ce mata lara kwrriyace sosai dan itama kasar waje tay karatu kuma ta girma laran ce asalin sectary da zatana zama killum tare dashi a office tana running official errands da files, meeting nd visit schedules. tare da su akwai wani mutum ana ce masa mr sani bello abolarin wanda yakansnce shine CEO na prime real estate group na nigeria tun kafin sultan ya karaso.

iyasu ne kawai suka rakosa meeting din dan baison tarukuce

bayan kusan an shafe awanni snn aka cimma babbam matsaya akan komi with respectful handshakes.

sultan yana ficewa ayarinsa suka rufa masa baya, mrs amina tana gefesan with quiet professionalism tana masa bayanai ayayin da suke tafiya private hallway din executive floor na hotel din har suka fito

snn ta mika mata wani karamin file sectaryrsa tay maza ta karba ta bude snn ta mika masa.

mrs amina maude tace sir dama akwai update ne daga recruitment department na cewa an samu wani young structural designer da ake rade raden cewa he is the best, sunansa jafar. he is extremely gifted according to his portfolio snn several real estate firms have been trying to recruit him for months amma dake younger brother dinsa mr yusuf is crrently working with us har ya amince xai yi aiki da mu.

ganin irin kallon daya mata yasaka mr sani bello abolarin yace she mean mr yusuf sir, the head of HRs and public relations sir. shine wai yake da alaqa da yaron

ahankali ya janye idanunsa kansu with calm indifference yace

"people get praised everyday,..i’ve seen architects better than whatever internet hype follows him, ya rufe file din baiko duba ba yace schedule him for the interview tomorrow nd if he dint pass 100% send him out akwai wanda suka fishi iya aiki dayawa..

da sauri cikin girmawa tace..yes sir.

batare daya kalle sectariyarsa lara ba yace i need my pent house ready..

ta dago kai kadan tace “sir?..ganin baiko juya ya kalleta ba yasaka ta ja baya ta lalumo wayarta agaggauce ta kira domestic staff ta fara basu instruction na cewa sultan yana tahowa pent house dinsa dake victoria island yanxu maza su tabbata komi yana kimtse...

SURAYYAHMS

***

COMENTS

SHARE