begging of an end
by @surayyahms
34...🦋🦋🦋
SURAYYAHMS
TALES OF THE WAZEERIS...
Book 1 FINAL PAGE ..
Thank you All for the lovely nd emotional nd funny coments. son so fanmily❤️🦋
daga nan kwata kwata basu yi minti 30 me kyau akan hanya ba dake ma ana ruwa ne kai tsaye suka wuce dashi victoria Island Extension da ake cewa VI annex. almost the same area ne dayay meeting dinsa wanda tsabar haduwar wnn anguwan a lagos state yasaka ake kirarsa da Ultramodern billionaire zone wanda ko ina ka juya iyakan Corporate nd residential luxury towers kawai zaka na gani da zallan New money power bases na real estate CEOs, oil, finance elites, anan wajen dai yawancin global billionaire city energy din yake.
Babban pent house dinsa ne kawai anan anguwan dake baida nisa da main hqtr na kamfaninsa na prime real estate group
sama kadan da wanan area ne hotel din da ushna take ciki yake, is like old and new site to ita tana cikin old main victoria island ne, shi kuma da kamfanin sa da pent house dinsa gaba daya suna can ciki cikin victoria islnd extension ne ta inda bakowani gaja ke iya shigewa nan ba sbd ire iren mutane masu dumbin dukiya da kamfanoni masu tsananin daraja da ke zama atanan.
Kwata kwata baijin shaawar komawa family house dinsun shiyasa ya zaɓi ya dawo killatacen gidan hutuwarsa sabd ya samu cikakken shiru da nitsuwa kafin gobe ya hallare office dinsa na prime real estates nigeria akaro na farko.
saida suka wuce kamfanin da kusan minti 15 kafin suka is gidan hutun nashi soft luxury marar hayaniya
an zagayeta kirif da doguwar steel gate mai dauke da facial recognition entry, bullet proof doors da drones surveillance perimeter da wasu Silent armed guards dake gadin gidan ta kowani fuska
daga waje zakaga komi na gidan simple ce amma daga cikin even his Formal dining hall is a 20 seat long table da candle lit crystal setup, akwai Private office na yin meetings, global calls, security screens akwai Indoor garden da wani babban courtyard da aka shuka olives da grapes acikin wajen, sai pools da Medical suite for emergencies nd health monitoring.
bayan private gurds dinsa mutum daya ce tall take aiki agidan ana ce mata mrs sukayal, matar ta dan girma sosai ba yarinya bace kuma bata wani tsufa sosai ba dai irin kwararun dattijan nan ne na gidan sarauta da ake trainasu sosai dan su karar da rayuwarsu wajen kulawa da dan sarki like they own son while remaining his servant forever...
miss sukayal ita take lura da duk wani abu daya shafi nan gidan kama daga kan harkan girki housekeeping da duk wani magani ko abun sha da shamsan zai saka acikinsa anan gidan. datake budurwa tay aiki ma mahaifinsa sosai dan haka babu wani abu dabata sani akan yanayinsu ba.
motocinsa suna sauka gurds ya taho da lema ya rakashi dashi har saida ya shige ciki.
sectariyarsa lara ta amshi basket din da aka saka magensa husna aciki ta damƙa ma mrs sukayal, daga nan suka juya dukansu suka koma main office dansu shirya tarban sultan acan gobe.
data bangaren ushna kuwa sosai ta jira koda ruwa zai dauke ta fito ta dan zaga anguwan amma ina ruwan lagos baimasan tanayi ba, haka ma daga family house din shamsan na banana island kowa yana jira dan daga rihanna har leelah sunyi dakon ganin dawowar sultan shamsan gidan amma sai shiru har yamma ya rufa basuga alaman sa agidan ba.
wajajen karfe 11:30pm nadare farees yaje can waje harabar gidan yagama wayarsa da budurwarsa arisha kenan ya dawo cikin gida
ahnkli ya tura kofar master suite din matarsa rihanna ya shiga jin mayen kamshin turarenta na expensive oud ya bugi hancinsa yasan batay bacci ba, a nan take ya lumshe idonsa ahnkli ya kara budewa
rihannan ce a tsaye agaban mirror tana ka kokarin gyara diamond earings dinta acikin wajen xamansu tadan tattara dogon gashinta dats black and shiny da wani katon jan ribbon tana Allah Allah tagama ta dawo kan ipad dinta domin ta gama hada files na sabbin fashion nd luxury businessess datakeyi anan.
koda taji sallaman farees ko kallonsa batayi ba jin ya taho kusa da jikinta yana kkrin shafata yasaka tadan hade rai tace what do you want farees?
farees ya sauke ajiyar zuciya yana kallonta cikin kyabe baki yace cikin ne yasaka kike min magana haka ko ya banfa fahimce ki ba...
bata amsashi ba yace
inde akan yayanki kike fushi ai nabaki hakuri. kema fa kinsan na girmesa dan kawai kuna cemasa sultan dat doesnt mean i shud bow to him....
ranta a harde tace ai maganan nan ma ya riga ya kare, uve made ur point.
matsowa kusa da ita yay yace to shikenan,.. i need a favour frm u babe
a hankali rihanna ta dago kwayar idanunta takalleshi ta mirror tce you mean money?
danshiru yayi for some seconds kafin nan yace yes...
ta juyo gaba daya ta hade hannuwanta tana kallonsa saidai kafin tay magana tagawai har ya wani rikota kasa gabanta yasaka dika gwiwowinsa akasa da yaudarreren yanayi..
babe pls hear me out… wallah something very very urgent came up kuma banda yadda zanyi ne da wallah tallahi bazan kara tmbayrki ko asi ba ai nasan kinamun kokari kuma kinsan i can do anything for you da ace inada means irin naki. ki taimaka min just this once in sha Allah har karshen shekarar nan bazan sake tambayarki komi ba
rihanne dake kallonsa wani iri bata wani nuna alaman shan mamaki yadda ya susuce yake wani makale murya ba dan abune daya saba musmn inyana bukatar kudi kallonshi kawai ty kmar mai shirin auna gaskiyar maganarsa
can cikin kyabe baki sai tajuya kai snn ta dauki phone dinta ta ajiye a side sannan ta jingina da dresser cikin natsuwa tace..nawa ne kudin?
yace "100k$ ko ma fiye
ni ko aro kibani sbd it very urgent zan dawo miki dasu.
cikin katsesa tace i can give you what you need farees.. but there is one condition...
farees ya dago kai da sauri yace bangane ba
rihanna ta cigaba cikin daure fuska tace in har ka amince you will work under my brother’s company officially no more running around, no more free lancing toh tabbas zaka samu kudin nan kyauta ma ba bashi ba.
numfashinsa yaji ta fara masa nauyi yana wani irin jin nauyin kalaman nata kamar zasu fasa masa kirji amma yasan baida wani zabi mai sauki da zai iyabi inbe saurareta ba sbd arisha ta balain tsayawa masa a wuya he need to give her this money for the surgery inba haka ba yasan bazata kyaleshi yasha ruwa ba.
saida ya gama shanye fushinsa taciki snn ya dauke kai dan kalmar tata taba masa pride dinsa bana wasa ba waishi ne har xaiyi aiki akarkashin shamsan?
wani gulluton baqin ciki da takaici yaji ya tokare masa kirji ya dago kai da magiya ya kalleta ahankli yace kema kinsan i don’t have problem with systems i only have problem with ego driven ppl ne..meyasa ke dakanki zaki bani irin wnn condition din bayan kinsan bazamu taɓa jituwa haba riii
rihanna ta kalleshi cikin ido directly tace"ego driven ppl..you mean my brother?
shiru yay bai amsata ba cikin sauke ajiyar zuciya tace faresss you don’t even know him well enough to hate him like that..
farees ya dago ya kalleta da muryan complain yanacewa kema kinsani shine dai baiya kaunata kuma akan dan na aureki ne yasaka baya kaunata he is clearly againts me and againts our love story, inda kuma zan cutar dake ne da aurenmu bazai kai wnn shekaru masu yawan ba
rihanna ta dan yi faint smile tace or maybe you’re just intimidated bay him..yaya na fa bai tsaneka ba. nima da ai hakan nake tunani amma daga baya nazo na fahimce shi. he is just being protective of me.
cikin kufuluwa farees yaja tsaki yace Ni ma fa dan uwanku ne zan cutar dake ne?? Allah dai ya sawwake, you know i’m practical shidin ne dai yake fama da girman kai da rainin hankali ai ba akansa aka fara zama akan mulki da kazamin dukiya ba...fir'auna da karuna duk sunxo duniya kuma sun mutu sunbarshi anan
calmly tace okay fine. mr practical man, gobe zamuje wajensa nd i will him cewa you want to join the company's new projects snn idan ka kafara aiki you have to report properly no more excuses nd please no hiding behind freelance work
farees ya girgiza kai cikin rasa abunda ke masa dadi yace “fine, Allah ya kaimu goben
tana murmushi tace ameen...if eveyrything works out namaka alkwari zan tura maka kudin harda kari..
tsabar baqin ciki bai iya amsata ba ransa babu dadi ya tashi yabar mata dakin ya koma private room dinsa daga nan bata kare ganinsa ba har sai washe gari da safe.
ata fannin ushna kusan kirar sallan asubah na farko ne ya farkar da ita daga bacci cikin natsuwa tay juyi snn ta bude lumsashun idanunta bata yi saurin tashi akan gadon ba for some seconds taji kwakwalta na kkrin organizing mata duk wani tunani datayi jiya a zuciyarta.
she cant just sit here nd be receiving back to back rejection letters ga lokaci nata tafiya koma meye zai faru da ita gara dai ta dauki wani kwakwarn mataki
saida tagama raya hakan aranta snn ta mike a hankali ta nufi bathroom ta yi wanka ta gyara fuskarta da kyau snn tayi alwala ta fito ta tada sallah tay kominta a nitse yau sosai ta jima tana karatun qur'ani anan zaune inda tay sallah sabida wnnan uban tsoro da fargaban zuwa kamfanin prime real estate datakeji aranta.
har saida karfe 6.40 yay kafin ta miƙe tsaye tafara kimtsa kanta sharply duk dama tanayin kominta ne da dalili dan tanaso tayi kyau dressing inta shima ya zama dede da ajin inda zataje
jim kadan ta shirya cikin new suit inta data siya jiya, white inner buttoned shirt me aji da wata straight tailored trousers da yay ma sharp inta kyau tareda bayyana wani classy excutive look ayanayinta gashinta ta tattara shi cikin sleek low ponytail, tasaka simple accessories tay kwalliya bamai yawa ba amma me daukar hankali.
sanda takalli kanta a madubi tay murmush babu shakka ita tasan tay kyau bana kadan ba white christian labourtin heels kalar rigarta tasaka a kafarta kafin ta dauki baqin blazer shima ta saka tay rolling kanta tsaff da bakin veil inda ko sillin sumanta baya nunawa.
she look both classy corporate nd decent kana ganinta zakasan wayayya kuma musulmace me tarbiya sbda yadda tayi dressing inta mai aji da kwalliya mai balain kyau da sanyi batare da tabar ko inanta yana nunawa a fili ba.
bayan ta gama shafa turarenta mai sanyi ta dauki ladies bag dinta files dinta da komi nata naciki ta fita
sama sama tayi breakfast a kasa duk dama hanklinta ba akwance yake ba amma ko kadan bata karaya ba
she is all in for what is coming dan inhar bata samu aikin nan ba batasan ma tayaya zata koma kano ba gashi yanxu sauran mara kwanaki kadan ne oganta ya bukaci report na resumptiin daga wajenta danhaka koma mei zai faru dolene yau kawai tasan nayi.
tana gamawa ta fito waje tasamu ride tay odering kai tsaye zuwa zaikaita Victoria Island Extension.
daga pent house din shamsan kuwa tun wajajen kafin asuba shamsan yariga ya tashi yafara aiwatar da muhimman abubuwan dake gabansa.
yana dawowa daga masjid ya wuce private gym yakai 50 good min aciki yana motsa jiki kafin nan ya fito yana takawa a nitse ydda kasan duk duniya ana kallonsa kominshi cikn aji da sanyin kasaita..
yana da tsayi da wani irin fresh healthy body builder body da bai yi yawa ba kuma baiyi kadan ba shi baya iya tafiya da sauri sauri ko ahnkli kamr hawainiya his steps are powerful nd controlled da ynayin
unreadable expression dake shimfide akan kyakwkwan fuskarsa
akoyaushe kagansa he is calm nd cold like the sleeping sea, very calm frm outside ruthless nd dangeroys daga taciki, zakaga kmar duk duniyan nan babu wanda yakai shamsan sanyin nutsuwa da kwanciyar hankli amma saika taboshi snn zakagane cewa baida saukin kai ko tausayi ko kadan
dogon wando ash colour da bakin riga marar nauyi ne ajikinsa with few sweat stain daga training din dayay yanzu daga gym, kai tsaye ya shiga room dinsa yana bude kofar magensa husna ta silalo kasa daga cikin soft cradle inta ta taho straight zuwa gareshi kamar wacce tafara sabawa da kamshin turarensa.
yana ganin ta yadan tsaya harsaida ta taho sannan ya sunkuya kadan ya dauke ta da dabhannu daya ya tsaya yana kallonta for few seconds yadda ta zuba masa innocent blue eyes insa yasa ya sumbace ta a hankali a goshi..muryarsa kasa kasa yace mmm first to greet me huhhn?? ya saki wata cute smirks ya nufi couch dinsa da ita snn ya kwantar da ita akai a hankali ya dauko wata inner shirt dinsa mai kamshin sa ya lullube mata jikinta dashi tay lumuii tabi ta zuba masa ido tana mai feeling part of his presence atare da ita
ganin ta nitsu yasaka ya shiga bathroom kai tsaye bayan mintuna masu yawa ya fito jikinsa na zuba wani irin turirin ruwan zafi tareda qamshin mayun sabulan wanka masu shiga rai da sanyaya zuciya.
kafin kace wani ba yay yan shafe shafensa yafara shirya kansa tsaf cikin wani iriyar matured, intimidating executive blue suit french designer ce me double classy jacket da akesata batare da tie ba ya dauko long structured overcoat dinsa yasaka oh my god shikansa saida yaji ajikinsa cewa ya mugun haduwa.
patek philip wristwatch me daraja amma kuma very simple design marar hayaniya,duk motsinsa kusan a nitse yakeyinsa tmkr duniyarce take jiransa bashi yakeda gaggawa ba.
saida ya gama shafa turarensa snn ya dauki magensa husna da hannu daya ya sauka downstairs da an riga an tsaftace koina an zuba qamshi ga wani irin raɓar sanyi da kuxury Airmores ke fitarwa ako wani kusurwa
yazo yasamu har private chef dinsa mrs sukayal tariga ta shirya masa breakfast din sa yadda aka saba akan lkci, tana tsaye daga gefe tana kan jiransa ya fito,...ba kowani lokci bane suke da iko na masa magana dan haka ta tsaya can cak agefe kamr kungi har yazo ya wuceta
komi akan dining table din is neatly arranged perfectly with luxury precision har magensa husna ma ansaka mta nata hadin madaran a karamin bowl a gefe
shamsan yana zama ya saka husna tafara shan madara kafin nan shima yafara cin nashi abinci atsanake.
yana tsaka da ci ne hadadden wayarsa tayi vibration yaga sakone daga sisternsa rihanna tarubuta gud morning ur higness i’m coming to see you at the office.
kallo daya yay ma sakon bai taɓa wayar ba har ya kammala breakfast dinsa acikin nitsuwa kafin nan ya mike yana dan jiran husna tagama shan madararta tana kuwa gamawa ya dauketa cikin kulawa softly ya mikata ga mrs sukayal ayayinda gabaki daya qamshin turarensa ya kama jikin magen sosai..
muryansa kasa kasa yace take care of her
da girmamawa sosai tace “yes, ur highness.
tana gama amsar mgen daga hannunsa ya juya acikin takunsa mai daukar hankali ya fita.
daga waje already convoy dinsa ya riga ya shirya just 3 black armored SUVs masu tinted black windows dukansu dauke da security formations
mota ta tsakiya aka bude masa ya shiga
suka fara jansa ahnkli
zuwa prime real estate headquarters...
dagata bangaren ushna tun acikin mota ta rafka tagumi tana kallon window silently tana famar kiyasace abinda zai iya faruwa da ita tun ma kafin ya faru.
she know this is a huge stupid risk amma she dont care gara dai taje tagwada sa'arta da hausawa sukace na zaune ne baiga gari ba.
after series of security checks sai wajajen karfe 7:20am na safe kfi nan ride inta ya tsaya a street na kamfanin prime real estate headquarters.
ginin wajen gabaki daya a tsaye yake gashi da girma da wani irin stylish glass walls masu cold reflection da ke nuna cewa wnan ba wurin wasa yaran bane waje ne da manyan kwari
tun daga nesa ta tsaya takarewa wajen kallo sai tafarajin gabanta na mugun faduwa kamar zai fetto waje, cos frm the looks of security layers tun daga gate zuwa entrance din tasan ana aiki ne awajen cikin kwarewa barin ma yau da akasan cewa mai kamfakin gabaki daya zaizo.
gani tay kamar kowa a nan yana rayuwa ne under a strick system rules nd regulations babu wani alaman too much freedom ko space na ganganci
ushna ta tsaya daga gefen gate dinta idanunta suna bin building din daga sama har kasa sai can snn takara matsawa gaba
ko kusa da gate din batay ba wani security man ya dakatar da ita almost immediately
yana mai gaya mata cewa ba a tsaya musu a bakin gate.
karasowa tayi gabansa tafara attempting bayyana kanta amma baiko tsaya jin mema zatace masan cikin hade rai ya dakatar da ita.
madam fine face you can’t go in to this premises without a proper appointment abeg shift.
yanayin yadda yay mata maganan da lagos ruggednes yasa taji tsoro ta koma can gefe ta makale kamar yar kyanwa dan kwata kwata batasaba ganin irin haka ba
tun karfe 7:20 din nan tana tsaye arakube acan gefe ba ta tafi ba tanata observing
movement din guards da entry pattern da yadda staff suke shigowa aiki daya bayan daya with flashy cars tafarajin kamar duk staff na wajen hala babu wani tlaka dan har ynxu bataga wani ma'aikaci daya wuceta ba acikin wata kyaffefn mota me tsada sosai ba
tana cikin dube dube sai can taga janitor access point ta baya kadan inda masu shara aikin gardening da sauran tarkacen suke wucewa.
hanklinta ta maida wajen sosai har saida idanunta suka sauka akan side corridor dake nuni da back service entrance
cikin mintuna kadan wani bright idea yazo mata tay sanda sadaf sadaf ta nufi wajen tay sauri ta shiga ta baya ba tare da drama ba
tana samun shigewa janitor section tay maza maza ta dauki uniform dinsu,omo blue colour ne, yanayinsa kamar overall ta zarge zip din kasa sharply ta saka uniform din a saman suit dinta ta rufe blazer dinta tsaf tabi tacusa takalmi da jakarta acikin dirt pusher ta gyara posture dinta tayi sauri ta shiga rububin wanda zasu shige ciki, batama gama lura cewa da badge ajikin rigar ba harsaida tazo zata wuce wani gardener yafara kirar sunanta da tsokana...
ahhh ahhh iyaaa karimo mai jego wato kinji oga pata pata zaizo kinyi maza maza kinxo aiki da sassafe ko..
tsokananta ya dingayi kanta na kallon kasa taki tace komi wasu securities sunata musu dariya ushna tabi tasauya yanayinta da yanayin tafiyarta zuwa wanda banata ba
gabanta ya dinga wani bugawa kawai ta daga masa hannu shikuma yanata dariya yana cewa zakizo kisameni.
dakyar da ikon Allah ta samu shiga building din tasha mamaki ganin an searching din kowa ita ba adubata ba, badon komi ba saida sabida badge inta ashe kayan wata mata me bala'in barkwanon masifa ta saka kusan kowa yasan ta awajen aikin ta haihune kwama biyu sai yakasance bata zuwa akai akai.
normally masu searching basu fiye dubata ba sabd tsabar iya zage zage da zafin rikicinta ahaka har kuwa ushna ta wuce albarkacin uniform din wnn matar batare da an dubata sosai ba.
tunda suka samu suka shiga cikin building sai taga kamar ba kowane ma yake lura da ita sosai ba, suna dan haurawa ta sama tay sauri ta wuce gaba direct inda aka rubuta restroom na first floor ta danna kofar ya budu ta shiga kirjnta na bugawa tahau cire janitor unifom din a hankali ta ninkeshi neatly snn ta gyara zaman suit dinta da blazer inta ta saka takalmi ta ciro jakarta tasake tabbatar da cewa kominta ya dawo daidai.
kara gyara fuskarta tay da powder sama sama sabd tsabar tsoro duk sanyin dake wajen bai hanata zufa ba, bayan tay tsaff ta kalli kanta a mirrorn bayin na seconds sannan ta rataya jakarta ta cikin dannne tsoro tabi bayan wasu staff ta jira har saida suka shiga elevator sukayi sama snn itama ta shiga
silent ride up yakaita 14th floor kowane mintina da irin level na tension din datakeji elevator na tsaya saiga wata mata zata wuce kai tsaye ushna tace excuse me...HRs receptionist floor?
matar tamata kallo sama da kasa amma ganin kalar confidence din dake cikin kwayar idanun ushna yasa tace "yeah, go left.
..kafin ta kara mata tambaya taga ushna har ta kara da gaba
karamin tsaki taja da tunanin ko ushna ma irin yaran masu kudi din nan ne masu shegen jiji dakansu in sunzo booking appointmnt
anitse ushna tabi left tana tafiya fuskarta da yanayinta cike da kwarjini amma har cikin hanjin cikinta kadawa yake kar kar da masifar tsoro da fargaba.
da taurin kai ta wuce kai tsaye ta nufi front desk din reception wajen ya hadu iya haduwa bata taba tsmmnin akwai irin wayann wajajen a africa ba.
tana tsayawa agaban wata budurwa dake reception din taga ko dago ido sama ta kalleta batayi ba
acikin gyaran murya tace good morning.
matar tana danne danne a system dake gabanta tace "yes, good morning how can i help you.
ushna tadanyi shiru sai can tace i’m here for internship enquiry.
cak taga receptionist din ta dago kai ta kalleta sama da kasa da wani kalar raini then back to her screen da silent dismissiveness dake nuna cewa bayau tafara ganin wawayen yan mata yan naci da cusa kai irinsu ushna ba.
dan kowa yasan basu daukar interns ko wani fresh applicant infact inkaga ka samu aikin yi anan wajen to wani babban matsayin karatun ki da tarin baiwarki ne kawai ya kawoki nan.
ganin ushna zata kara mata magana da wani irin attitude tace am sorry maam but we don’t take interns. please leave.
ushna ta tsaya cak snn tace i understand, but i need to speak with ur HR. ta bude jakarta tana kkrin fitowa da file inta tace i’m a final year student from LSE london, and this program is part of a royal golf real estate programme dat is connected to
tun bata kai karshe ba receptionist din ta daga mata hannu without even looking up properly tace hey
miss, i said we don’t take interns. you can leave now or i wll call security.
idanun ushna take suka kada sukay jaaa tarasa mema zatace next adan matse tace please maam, i’m not here for general application. i just need a verification from your HR. five minutes.
matar dake kan danne dannenta tace madam ders is no access ithout appointment here. kije ki hada appoitnment dashi saiki dawo.
ushna tay shiruuu bata ce komi ba sai tafara maida file inta acikin jakarta jin kanta ya cirke tarasa uban miye zatayi yanxu
caraf sukaji motsi daga bayansu mayen qamshin turaren mr yusuf mutumin da kowa yake balain jin tsoronsa a building gaba daya cos he is the head of HRs and public relations, cikin sauri ya sauko daga elevator with visible prideful nd arrogant energy dayake ji dashi,
yana tare ne da wasu junior staff da ke bin bayansa dan kamar duk abin da ke faruwa da kananan maaikata anan sashen yana daga karkashin iko da umarninsa ne
baida mutunci ko na minti daya, he is harsh, insultive, gashi ya iya zagewa yaci mutuncin mutum dake kasa dashi komin girmansa
msmn ma irin masu musu shara da goge goge innan.
already karfe takwas da minti 30 yay dan haka ya fito ne da ya tarban dan uwansa mr jafar wanda ake ta tsammanin zuwansa cikin building din yau sbid ganawarsa da interviewers.
dan uwansa shine mutumin da aka yima sultan bayaninsa jiya
gayen yana da wani irin baiwar zane ne na msmn dayasaka ake rububinshi shiyasa suke da wani irin jiji da kai a familynsu.
suna bullowa ta wajen su ushna kusan kafin yakaiga elavator xuwa kasa a walakance yay dismissing din junior staff din dake binsa abaya suna matsawa
deidai yana shirin danna button din elevator kenan kwayr idanunsa suka sauka akan ushna dake nan
tsaye looking confuse nd bit nervous a wajen receptionist counter,
mr yusuf ya tsaya kamr me aljanu yana ta evaluating inta wanda tun kafin ma ya fahimce meya kawo ta yaji ya tsaneta sbda yadda yaganta so calm gata kyakkwa sosai.
da zafinshi ya taho kansu yace..who is this? kafin receptionist ta amsa ya daka ma ushna tsawa "keeeee malama meya kawoki
jin muryarsa ta fito da wta zzfar unnecessary harshness yasaka jikin ushna yafara rawa rawa receptionist din tay sauri tace am sorry sir, she is just about to leave.
wani irin mugun kallo yama receptionist din cikin katseta da hannu.
idanunsa suka koma kan ushna da tsawa yace
"young lady...talk... what bring you here
da matukar tsoron yanayinsa ushna ta gyara tsayuwarta snn tafara masa bayani muryanta na rawa rawa nan da nan tasake bayyana masa kanta, ta fada masa qualifications dinta da duka dalilin zuwanta,
amma da mamaki sai taga ashe ba ma jinta yakeyi ba kawai dai kallonta yake da wani kalar tsana da raini.
tana rufe baki yaja wata kalar tsaki snn yace young lady kalleni nan i don’t care about ur explanations, we don’t take interns so leave the premises.
ushna ta tsaya still tana mamakin kalar zafin ransa saidai tun bataja numfashi ba taji ya daka mata ihu akai
i said leave..did you not hear me? ya kike wani abu ne kmar wanda kwai ya fashe miki aciki
tsabar ta razana da muryansa atake taji idonta yaciko da ruwan hawaye masu shegen zafi ta budi baki zata amsa shi kenan sai ruwan hawaye suka kwace mata.
mr yusuf yana ganin haka yaji kmr kunna shi tayi, ta inda yake shiga bata nan yake fita ba yafara zaginta yanata cemata wai makaryaciya doluwa yasan ba ta taba zuwa london bama bare dubai kawai tazone ta dame mutane
receptionist din sosai taji tausayin ushna
jikin ushna na rawa sosai tana hawaye bata kara kula ihun dayake mata ba tayi sauri ta doshi elevator tanaji kamar zuciyarta zai fashe dan zafi,
kana ganinta kasan she is frustrated nd silently regreting why she even came here.
zata danna button na elevator kenan taji an rigata budewa da sauri ta daga idonta sama
mr jafar ne atsaye da wani mutum agefensa kamar manager dinsa ne.
mr jafar din ne agaba cikin takun jiji dakai wanda kana ganinsa ka san yana da alaqar jini da mr yusuf sbd suna kama da juna sosai, yana wani irin fitowar takama daga elavator in kamar shugaban kasa da wani irin arrogant confidence da mugun jiji dakai da girman kai
kallo daya zaka mai kasan cewa shi irin mutanen nan ne da aka saba zuzutasu ana musu fadanci, he is all about this celebrity life yanajin kansa manyn kamfanoni ne kawai suke rububinsa har a kasashen waje.
yasaka wata sharp fancy suit me tsada mr yusuf yana ganinsa atake ya wani irin sauya fuskarsa nan take ushna taji an wani tureta gefe da karfi har saura kiris ta fadi kasa
ya matso da sauri kamar bashi yagama mata ihu yana zaginta ba, suka rungume juna da dan uwansa cikin wata brief but formal embrace na brothers
welcome back, big bro
mr yusuf din ya fada ma mr jafar ayayinda suke zuba murmushi ma juna
mr jafar din yadan fishi jiki da shekaru shi kuma duk damuwarsa ba komi bane face ganin ushna dayay ta tsaya can gefensu a dan tsorace kuma da hawaye bajabaja akan fuskarta.
jafar ya kalleta daga sama har kasa yace ma mr yusuf and who is this spoilt lost sheep da alama baka cin uban yaran nan fa.
mr yusuf ya juya kai kamr baisan da ita a wajen suna hade ido yace...ohhh she is a nobody just someone trying to force her way in
jin haka yasaka mr jafar ya matso kusa da ita kadan da wani irin arrogant insultive look in disguised yace ikon Allah no wonder she looks like she knows exactly how to get attention from men.
take taji hawayen dake saukowa a idonta sun tsaya cakk jin ranta ya fara baciii wani tsaki ya kwace mata tafara kkrin barin wajen a fusace dan tasan bazata iya daukar cin fuska ba kuma
har zatabi gefensu ta wuce da mamaki taga mr jafar din yawani sha gabanta yana mata dariya
kanta taji yana juyawa dan bayan ya hanata wucewa kuma sai ya fara gaya ma mr yusuf cewa ai yasha haduwa da yara marasa kamun kai ire iren su ushna
....you think your beauty is going to earn you a spot in this big building? this is prime real estate babygirl not some place for lost ashawo wandering lagos girls
ushna ta ja baya jin
numfashinta ya fara canzawa hannunta ya fara rawa tanaji kamar zata zabga masa mari afuskansa inyaso saidai aje a kulleta
saidai ganin kmar habit dinsu ne kuma sun girmeta nesa ba kusa gasu maza yasa ta hadiye fushinta ta sake yin attempting yimasa magana koda zai bata hanya ta fice
ahnkli tace excuse me sir...ure on the way.
ya shareta bai saurare ta ba, hawayenta ya kara sauka ta juya a zuciye zatabi stairs sai taji an fixgota baya
you trespassed into a secured facility and now you’re acting angry? ke waye ehhh
..who is ur father in this country...ina miki magana kina harara na
ihun da mr yusuf ya mata yasaka sauran staff dake aiki ata wajen duk suka fara fitowa daya bayan daya suna kallonta.
ganin attention din mutane ya dawo kanta
jikinta ya fara rawa sosai hawayenta suka sake tuluwa a idanunta suna zuba ba tare da ta yi niyyar hakan ba
the whole situationn starts to turn into a masive humiliation sai taji yanayinsun yafara cracking in composure dinta tafara panicking taciki tafarajin gara kawai ta basu hakuri dan subarta ta tafi
dan datasan zatazo nan a walakanta da ko kadan bazata kawo kanta nan wajen ba
mr yusuf dake mata ihu yace...tunda kina da zuciya toh bazaki tafi ba wait for security to have you escorted out like a criminal you stupid ashawo girl....
ana cikin wnn zazzfar drama in aciki daga waje kuma motocin sultan shamsan suka fara shigowa
lokacin ana neman karfe tara na safe da wajen saura minti goma yacika
ana bude masa mota ya fito calmly ba tare da ya kalle kowa ba sabida yadda presence dinsa ya sa dukkanin surrounding din ya yi shiru automatically kowa ya tsaya agefe guda ana miko masa gaisuwa da fadanci acikin girmamawa...
bai amsa kowa ba yana kan tafiyarsa a nitse agefensa kuma sectaryiyarsa ce lara charles tana tahowa da sauri tana rike da brief case sai gurds dinsa....
kusan daf zasu shige main entrance kenan saiga nan yar uwarsa rihanna da mijinta farees sun iso.
da murmushi tazo ta gaishesa bai amsa ba ya gyada kai as usual basuce ma junansu uffan da farees daya wani hade rai cikin wata fancy suit dinsa data masa muni ba
koda rihanna taje kurkusa da shamsan suna tafiya shi baya baya yayi dasu ya jero dasu sectaryiyarsa yana tahowa cikin shan qamshi
duk tarukucen gurds dinsa da sectary da su rihanna atare suka bi ta normal elevator..
shamsan kuma yabi private elavator nashi na musammn shikadai
its very fast amma kusan lokaci guda suka hadu within few min suka iso 14th floor
lokacin mr yusuf da dan uwansa sun gama saka ushna kuka suna kkrin kira mata securty dan fitar da ita waje awalaknce karshe ma shiru tay ta sunkuyar dakanta kasa ta dena kallonsu dan batasan laifin meye tay suke zaginta ba.
shikuma mr yusuf so yake ya walakanta ta sosai har sai ta rasa meke mata dadi sbd kar wata rana tasake jin shaawar dawowa nan kamfanin neman aiki a tunaninsa kawai itama irin yara yara karuwen lagos din ne masu tsabar karya da tsaurin ido.
suna tsaka da rikici haka kawai ushna tafarajin zuciyarta na bugawa da karfin tsiya kamar zai haukatata
within minute sukaji private elavator yay kara dake sound dnsa daban kusan kowa yasan wayene zai shigo da wani irin watsewar zabbi taga kananan staff sun koma post dinsu yadda kasan mala'ikal mutuwa ne yake kkrin fasowa.
hatta mr yusuf dataga yana playing mr evil van helsing God jikin sa yafara rawa kawai taga yafara ihu ihu ma staff yana ce ma kowa ya gyara kansa tsaf ya tsaya a post dinsa
kafin ma tagane meke shirin faruwa taga yazo ya wani cakumo hannunta da karfi zai turata kan makala a mugun walakance ita kanta batasan daga ina karfin hali tazo mata ba ta fauce hannunta anashi da karfi tace dont you dare touch me.
kamar wani zaki yana huci yataho da sauri ko zai shakureta ne ko zai jawota ne oho ganin haka yasaka ta mugun razana tana ja da baya sai ding elevator din ya budu.
wani irin sauyawa iskan wajen yay gabaki daya wajen ya dauki wani irin dead silent
ushna tana daga idonta sama amugun tsorace wani caraf suka hade kwayar idanunsu waje guda da sultan shamsan for some min basu iya motsi ba wani yarr na bin jikinsu alokci guda
kai tsaye ya ganeta tsaff sbd sosai ya kalleta ranan acikin ruwan saman daya mata duka ranan nan data fadi a cikin datti saidai dayaganta agabansa yanxu kuma sai yafarajin kamar ma mafarki kawai yake yi
kirjin ushna kamar zai faso waje tafara jin kanta na juyawa she tot ko dan walaknci datasha anan ne yasa tarude tafara ganin fake hallucinations na fuskar crush inta na can dubai
zuciyarta atake ya fara bugawa abnormally jikin ta ya sake wani luiiiiii tay kamar zata fadi kasa da sauri taji an riketa tana daga ido lkcin hawayenta na zuba kamr ruwan teku nan taga wata mata fara kyakkwan gaske ta rikota da tausayi...
da damuwa ayanayinta tace "hey,...are u okay?
ushna bata amsa ba ta tsaya kusa da matan taga kamar tana debi da sultan, amma sbid kara bugawa da kanta yayi dataga mr abdul abayan shamsan ya saka ta kasa motsi.
rihanna dataga alamar ushna is in shock nd trauma sai tay sauri ta janyeta suka wuce cikin wani office ata can shashen inda VIP office din shamsan din yake.
suna barin wajen mr yusuf yafara bare baren baki in kagansa kamar bashi ba
har kamar zai fadi kasa tsabar respect wajen fara gaishe da sultan shamsan kenan sectariyarsa lara ta katsesu da tambayoyi aka yanayin da sukazo suka samu ushna
dan tun bayau ba ake yawan kawo korafi da karar mr yusuf na yadda yake bala'in walaknta staff, da cleaners da mutane kuma tun last week aka dinga warning dinsa akan kar ya sake yabari yayi wani abu da zai jawo hankalin sultan yau sai gashi kuwa an memeta.
she was so dispointed ayayinda datake kan questioning dinsa gashi arogant bro dinsa sai tsoma musu baki yakeyi yana dada fallasa kalar walakncin da sukayi ma ushna.
shi a tunaninsa ai akan gaskiya suke, dama bai kamata ana barin yara yan iska masu neman cusa kai dan sunga suna da kyau suna shigowa wajejen da yafi karfinsu ba...
mr yusuf sai ido yake masa akan yayi shiruu kodan sbd idon sultan shamsan amma ina jin kansa yake kmar wani celebrity atunaninsa komiye ya furta yasan baza'a iya koransa awaje ba.
barema gani yake ai abunda sukama ushna shine daidai.
mr yusuf yarasa me zaiyi sai zufa yake keto masa daga kai har fuskansa
and the receptionist was not even helping matters dan da aka tambayeta meye faru tsabar taji tausayin ushna she politely explain truthfully cewa ai ushna fa bata musu komi ba kawai tazo making enguiry ne kuma har ma sun gama magana shine kawai yazo ya tsareta.
mr jafar yana kkrin daka ma receptionist din tsawa tare da accusing dinta da cewa halama itace ta kawo ushna wajen
amugun dake sultan yace "you...
da sauri ya daga kai da fargaba jin muryan shamsan yasaka atke wajen yay shiruuuuu
shamsan yace who are you again??
gani irin kallo me darsa fargaba da sultan din ya masa yasakashi nitsuwa cikin gyaran murya ya fara bayanin kansa confidently har yana fadin masa duka achivemnt dinsa with pride irin gashi shi shegen nan yazaga duniya anyi dashi
yana gama rufe baki shamsan yabishi da wani kalar kaskantaccen kallo yana tuna abunda yaita cewa akan ushna ransa yaji ya balaen baci haka kawai
...saidai dake baya iya nuna emotions a fili sai bazaka taba zaton hakan ba
da kamar ma bazai masa magana ba sai can muryansa ya fito kasa kasa yace..get out...
amamakance mr jafar yace ...sir?.am sory what..
witout looking at him yace "you are disqulified. leave this premises immidetly.
atake jikin mr jafar din ya fara rawa rawa yanaji kamr karye ne kunnensa ne baiji da kyau ba, bashi din aka kora akan wannan babban contract din daya gama saka raiba..
ganin dagaske sultan yay maganan atake sai yaji rikice bazata yay loosing contril ya tunkaro shamsan din kamr wanda zai iya kama dambe dashi jikinsa na rawa rawa gurds suna rikesa ya kara zaucewa yafara ihu yana cewa no no sir you cant do this to me....sirr sirrr pls si
ganin ya rikice sosai yana fixge fizge yana kkrin matsowa da gigin borin haukansa kusa da sultan shamsan sectariyarsa da bata sauraran nonsense maza ta riga gurds dinsa ciro bindiga cikin tsaresa da tsawa tace
"step back or i will shoot ..securitty...
kafin security suxo har gurd din shamsan sun rirrikesa kamar barawo anyi baya dashi yanata huci, tuna asarar daya tafka yanxu akan yar yarinyar nan sai kawai ya fashe da kuka yana cewa sir sir please sirrr sir pls we can talk abt this, sai roko yake kamr bashi ya shigo da gingimen girman kai ba dan sunsan waye shamsan din sarai
he has d money nd leverage to buy off their entire generation
mr yusuf yaji kamar zai narke kasa dan tsananin baqin ciki tsoro da mamaki sanin cewa tsabar kwarewr dan uwansan nan ba'a taba rejecting dinsa a koina ba
kuma wnn harka yasan bakaramin kazamin kudi zasu samo ba.
akan wann yarinyar shine har sultan zai kore dan uwansa akan babban contract ji yayi inama da kashe ushna kawai yay ya huta ma ransa.
tuni ya zube giwarsa akasa kamr bashi ba yafara rokon shamsan shima yana kuka wee wee haryana cewa wai dukansu zasu bawa ushna hakuri..
shamsan yay kamar bada shi sukeyi ba
kananan staff kuwa sai lekowa suke suna jin dadi wasu kuma suna shan mamakin yadda sultan ya dauki tsattsauraan hukunci akan wata stranger.
fareess sai ɓari yakeyi taciki cos he knos who mr jafar is mutum ne mai daraja this is a huge shock nd lost for him yasan har duniya ta nade bazai manta cewa asara da rejection dinsa na farko akan wata strange yarinya aka koresa akan babban contract ba
duk dama shima din kansa har yanzu a mugun kulle yake yanata tunanin ta inda akayi har ushna tazo lagos nigeria har tasan wann kamfanin..
mamaki yakeji aransa kamar zai kashesa gashi ya yaga matarsa rihanna tajata cikin office tana rarrashinta duk sai ya rasa ta ina zaije yaji sanyi...
shamsan yana tsaye shikansa yarasa meyasa ma ya tsayar dashi anan din cos deep within his heart yasani inbadan wai ushna yagani ana ciwa mutunci ba da bazai taɓa iya tsayawa anan ana surutu meyawa haka agabansa ba.
sectariyarsa tagama sawa akan a fitar da mr jafar kenan ta juya sai taga shamsan ya koma cikin elavator din quietly da alaman zai haura sama can can karshe inda bababan conference room dinsu yake.
Da barin jiki mr yusuf ya tashi akasa da hawaye sharbe sharbe yafara cewa sir sirr please ..sirrr..give me a chance sirr pls sirrr
baiko kallesa ba ya kalle sectarynsan adake yace "Suspend this moron till further notice... nd schedule my next meeting now.
da sauri tace yess sir.
tana juyowa taga mr yusuf ya fadi kasa a rikice gwaraf kamr buhun masara yanata karkarwa yabi ya dora hannunsa a kirji yana nishi me karfi kamar mei heart attack jin wai anyi suspending dinsa till further notice..
akabar farees yana tsaye a kangare yanata jin tsananin mamakin yadda shamsan ya rufe idonsa ya kore top experts within minutes kuma duk wai akan laifin da akama ushna
......
ALHAMDULLAHI
ANAN NAKAWO KARSHEN BOOK 1 ABUNDA MUKA FADA DAIDAI ALLAH YA BAMU LADA WANDA BAMU FADA BA ALLAH YA MANA AFUWAM.
*KARKU MANTA WANNAN GABAR KAMAR SHARAR* *FAGE NE,TALES OF THE WAXERIS LABARI NE ME* CIKE DA ABABEN NISHADI SOYAYYA ME KAMA ZUCIYA DA KUMA KAYAN AL'AJABI ME CIKE DA DARUSA NA RAYUWA..
TALES OF WAZEERIS BOOK 2🦋🦋🦋
ZAI FITO NE BAYAN SALLAH DA SATI DAYA.
DAGA ZARAR NA FARA BAZAMU JIRA WANI BA
KUDIN KARATUNSA
WHATSAP: 700: AMMA ZAKI IYA BIYAN 500 daga daren yau har zuwa ranar wednesday wato SALLAH day KACAL
THIS IS MY BIRTHDAY GIFT TO FANS❤️❤️❤️
VIP TELEGRAM; 2K
VIA ***
MOHD SURAYYA SULE
OPAY
TURO SHAIDAR BIYA
TA ***
MASU MANHAJAR AREWA PEN ZAKU SAMESA A KUDI ME RAHUSA ACT DIN
@ SURAYYAHMS
show your love to writer...
saimun hadu bayan sallah
thanks for all ur unwavering
love nd support
SURAYYAHMS
20226