29
*KUNDINA*
*NAFISATU ALIYU SASAAL*
*****
29
SALIM;
A wannan dare Salim bai runtsa ba, kwanan zaune ya yi, yana tunani yanda zai yiwa Fatima bayani, wayoyinsa ma kashesu ya yi..
★ sai bayan yayi Sallar Asuba barci mai nauyi ya ɗaukeshi..
Bayan awanni a zabure ya tashi, abinda ya fara dubawa agogon bangon ɗakinsa.. ganin ƙarfe goma har da minti arba'in da biyar ya sa ya miƙe yana maimaita;
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un"
Saboda lecture ƙarfe takwas Fatima take da shi, zuwa yanzu yasan sun fito daga lecture baya so taji labarin a bakin wasu..
Ruɗewa ya yi ya rasa ta ina zai fara, wayarsa ya ɗauko ya kunna, yatsun hannayensa suka karkarwa ya lalubo lambarta ya kira, amma ba'a ɗaga ba..
Kamar mahaukaci sabon kamu haka ya faɗa Washroom, jikinsa kawai ya ɗauraye, ya fito ya saka kaya a gurguje, ya ɗauki mukullin mota, ko wajen Hajiyarsa bai shiga ba, ya bar gidan...
FATIMA..
ban damu da rashin kiran Salim ba domin idan da sabo ya ci ace na saba. Amma na ƙudurcewa raina idan muka haɗu a makaranta zan tambayeshi ya gayamin maiyasa ya sauya, idan aure ne baya son yi ya faɗamin nasan inda na dosa...
Zuciyata cike ta tunanin maganganun da zan gayamasa idan mun haɗu barci mai nauyi ya ɗaukeni.
★washe gari tunda nayi sallar asuba ban koma barci ba, saboda lecture ƙarfe 8 da nake da shi..
Abun kari mai sauƙi na haɗa, bayan na gama na yi wanka na shirya cikin baƙar Abayar da ya haska Fuskata data rame...
Ban kammala komai ba sai wajen bakwai da kwata, a gurguje na shiga na gaishe da Baba, Direba ya fito muka tafi...
Ƙarfe takwas saura na shiga makaranta..
Group-group na samu ƴan ajinmu sun haɗa, suna ta ƙusƙus suna kwashewa da dariya..
Suna hangoni duk suka zubomin ido, suna ƙunshe dariyarsu..
Kunya da tsorone suka dirarmin lokaci ɗaya, amma na dake, na meni waje na zauna ina zaro wayata a jaka...
Cikin izgilanci wata matashiyar da ba zan iya tantace kamaninta ba ta ce;
"Girman kai da ƙin kula mutane dai ya zo ƙarshe, Sir Salim dai an shafa fatiha idan an ga dama a cigaba da kulamu, idan anga dama kuma a cigaba da ɗaga mana kai"
Tana gama faɗa gaba ɗaya wajen ya amsa da shewa da dariyarsu..
Kiran sunan Salim yasa na fahimci da ni take, dariyar da suke min har cikin kaina nake jinshi, kamar mara gaskiya haka na miƙe, ƙafafuwana suna harɗewa na fita daga cikin aji, ina jiyo shewarsu da guɗarsu..
Wajen dana saba zama naje na zauna, na fashe da kuka...
Lecture da ban shiga ba kenan, bayan kamar minti talatin naji sallamar mace a bayana..
Nasan fuskarta course mate ɗi ta ce, amma bamu taɓa magana ba...
Hawayen Fuskata na goge na amsa sallamarta..
Fuskarta ƙunshe da damuwa ta ce;
"Zan iya zama muyi magana?"
Da sauri na ɗaga mata kai, saboda gaba ɗaya a ruɗe nake, neman wanda zai yi min bayani nake yi..
Bayan ta zauna ta ce;
"Fatima kin jima kina birgeni, shiyasa na kasa jurewa na fito daga lecture na baki labari abubuwan da suke faruwa, dan naga alamar kamar baki san dalilin da yasa kowa yake yi miki dariya ba, ina so ki bani dama"
Hankalina da nutsuwata kacokam da dawo da shi kanta.. cikin ɓoye tashin hankalina na ce;
"Na gode da kulawarki, kuma na baki dama dan Allah karki ɓoyemin komai"
Zamanta ta gyara ta fara bani labarin da ban taɓa kawowa a cikin zuciyata ba;
ashe labarin wai kuskuren da na aikata a baya shiyasa Salim ya fasa aurena duk ya cika ko ina na makarantar, da auren Salim da Yasmin, kuma wai dukka waɗannan labaran sun fito ne ta hanyar Sir Lawal da ya bawa budurwarsa labari ita kuma ta bawa ƙawayenta..
Ganin kamar da kokwanto a cikin zuciyata yasa ta zaro wayarta ta nunamin hoton Salim da Yasmin, wai Sir Lawal ne ya turawa Budurwarsa ita kuma ta turawa ƙawayenta..
Bayan ta gama nunamin hoton ta ɗoramin da nasihar na kwantar da hankalina, Bawa baya wucewa ƙaddararsa..
Na kasa kuka, murmushi kawai nayi na ce mata na gode...
Sallama tayi min ya rage sauran ni kaɗai a zaune..
Ban san iya adadin lokacin da na ɗiba a zaune ba. Jikina nake ji kamar ba nawa ba, tunani ya tsaya cak...
Hayaniyar mutane ne, ya ɗan dawo da ni hayyacina, hannuna da ya yi min nauyi na ɗaga na ciro wayata a jaka na kira Baba..
Da sallama ya ɗaga, sai dai yadda ya ji nace; "Baabaa" yasa hankalinsa ya tashi..
"Kina ina Fatima? "
Ya tambaya a ruɗe..
A fizge na ce;
"Makaranta"
"To ki zauna a inda kike ganin zuwa kin ji"
Ya ƙarasa faɗa haɗe da katse wayar..
Ina ajjiye wayar Salim yana ƙarasowa inda nake.
Tsakiyar idonsa nake kallo sai nake ganinsa kamar ba waccen Salim ɗin ba..
Daga yanayina yasan na riga na ji komai, cikin kame-kame da ƙanƙan da murya ya ce;
"Fatima dan Allah ki saurareni, karki kashe rayuwarki, ki salwantar da karatunki da farin ciki, ina so ki fahimceni wallahi ƙaddara ce"
Murmushi nayi idanuwana cike taf da ƙwalla na miƙe ina Kallon tsakiyar idonsa na ce;
"Don me zan kashe rayuwata? Don me zan kashe karatuna da farin cikina? wai dukka don saboda kai? Saboda ka ƙi aurena?"
Dakatawa nayi na ɗanyi murmushi na ɗora da;
"Ban so rabuwarmu ta kasance a haka ba Salim, me nayi maka da zafi haka da zaka barni ni da Iyayena cikin shiri da jiran tsammanin ranar da ba zata zo ba?
Idan har zaka iya yimin haka kuma ka cigaba da zuwa wajen aikinka don cigaba da gina rayuwarka, to don me ni zan kashe nawa karatun? So ba yaƙi ba ne, balle nace ka ci yaƙi zan ajjiye makamaina, yanzu na fara gwagwarmaya gina rayuwata kuma In Sha Allahu wata rana zan yi dariya kamar kowa, Allah zai bani wanda zai tsayamin ya duba nadamar da nayi ba kuskuren dana aikata ba.."
Daga haka na saɓa jakata na bar shi a ƙame..
Tafiyata ta fara nisa, na ji takunsa a bayana yana kiran sunana, ban juyo ba, cikin ikon Allah na hango motar Baba ya faka..
Daga nesa da ya hangoni shi da Alhaji Ahmed da suka taho tare suka fito lokaci ɗaya..
Baba da hanzarinsa ya ƙaraso gareni, ƙasa zan durƙushe ya ɗagoni, ya rungume ni yana shafa bayana...
A hankali cikin kukan daya tahomin na ce;
"Baba ashe Salim ya yi aure, ya bar ni"
Da wani irin karaya a muryarsa ya ce;
"Idan ya barki Allah Ya na tare da ke, muma muna tare dake kin ji,"
Kai na ɗaga mai, Alhaji Ahmed bai ji maganganun ba, don haka ya matsa kusa da Salim da ya ƙaraso wajenmu amma bai matso kusa ba..
Ko da Alhaji Ahmed ya tambayi Salim, cikin kame-kame ya fara yi masa bayani...
Alhaji Ahmed bai gama saurarsa ba, ya dakatar da shi.. ya bar shi a tsaye..
Kamar daga sama muka ji Muryar Alhaji Ahmed, ya ce;
"Idan har ka amincemin ina nemawa ɗana Muhammad Salim Lamiɗo auren Fatima, ayi shi kamar yadda aka tsara tun farko"
Shiru muka yi, Baba ya sake ni, ya kalli Alhaji Ahmed ya ce;
"Karka damu Alhaji, shima Lamiɗo ba lallai ya yi na'am ba, ka taho mu tafi gida zamu yi maganar daga baya"
Baba ya ƙarasa faɗa yana jan hannuna zuwa cikin mota, ko inda Salim yake tsaye bai kalla ba.
A nan Baba ya tashi mota muka bar Salim a tsaye...
Tun muna hanya Baba da Alhaji Ahmed suke ta tafka muhawara akan batun Lamiɗo, Baba ya ce shi baya son a takurawa kowa, Alhaji Ahmed ya bari idan yaje gida su yi shawara da iyalinsa.
A kan haka suka bar maganar, Baba ya sauke Alhaji Ahmed a gida, dama daga wajen taro suke...
Har muka zo gida Baba nasiha yake min, da kanshi ya rakani har Sashena, ya kuma ja min kunnen kar na faɗawa kowa na daure, Allah zai kawo min mafita..
SALIM;.
ya daɗe a tsaye bayan tafiyarsu Fatima, waɗanda abin ya faru akan idonsu, tuni sun fara kwaza labarin ga Sir Salim can da Fatima sun yi faɗa...
Salim kasa zaman makarantar ya yi, ya koma gida, kunya da danasani duk suka dabaibayeshi..
Ya kira wayar Fatima ya fi a ƙirga amma bata ɗauka..
Ya kira Lawal yana masifar meyasa zai je makaranta yana bayyana sirrinsa, Lawal bai tsaya gama saurarar ba yayi tsaki ya kashe wayarsa..
Cigaba yayi da kiran Fatima daga ƙarshe ya ji tayi blocking ɗinsa..
Dole haka ya haƙura..
FATIMA;
Ban yada nasihar Baba ba, sosai na sawa zuciyata jarumta, sai dai na yi kuka, irin wanda ban san lokacin dana ɗauka ina yi ba..
Matakin farko dana fara ɗauka shine blocking ɗin Salim, na biyu kuma na ɗauko *KUNDINA* na rubuta labarin soyayyarmu, domin ya riga ya zama tarihi a gare ni..
Rubuta duka labarin soyayyata da Salim a cikin *KUNDINA* ya taimakamin waje gane Salim ba namijin da zan ɓata lokacina da tunani a kansa bane, sai dai salon soyayyarsa zai yi wahalar mancewa a gareni...
Kafin nayi barci sai da Baba ya ƙara kirana a waya, yayi min nasiha ya ce nayi addu'a na kwanta,, Allah Ya na sane da komai.
Daren wannan rana, ya shiga ɗaya daga cikin darare mafiya ƙunci a cikin rayuwata..
GIDAN ALHAJI AHMAD;
Daga yanayin damuwar da ya shigo da shi, Iyalansa suka san ba lafiya ba..
Matarsa baffulatanar ruga ce, kyakkyawar gaske mai siriri jiki da tasho, haka ƴaƴanta ma suke, kamar Alhaji Ahmed ne mahaifinsu ba, saboda shi baƙine mai kaurin jiki...
Muhammad Salim Lamiɗo shine ɗan su na fari, sai ƙannensa mata huɗu, ɗaya tayi aure da ƴaƴanta biyu. Bai baro mahaifiyarsa a komai ba, sai hali..
Lamiɗo dogo ne sosai kyakkyawa siriri kamar ka ɓallashi biyu, ga alfahari da izza kai ka ce yafi haka idan baka sanshi ba, babban ma'aikacin Banki ne, yana da shekararu Talatin da biyar a duniya..
Mahaifiyarsu Inna babu ruwanta, duk amintakar da ke tsakanin mijinta da Baban su Fatima bata shiga sabgar matanshi musamman Hajiya Babba, ita ko maƙota ma bata shiga..
Tashin farko ta nuna farin cikinta, bayan gama saurarar bayanin Mijinta akan batun Fatima...
Shima Lamiɗo da dare ya yi, ya dawo daga wajen aiki ya huta suka kirashi suka yi mai bayani..
Ya san fuskar Fatima sosai, sai dai ban da gaisuwa babu abinda yake haɗashi da ita.
Shi babbar matsalar da yake rabasa da mata, shine son girma, yafi son idan ya ce mace tayi to tayi nan take ko da ita bata so, baya son musu ko jinkiri, shiyasa baya yin wata ɗaya da budurwa sun rabu..
Bai musa ba, ya ce ya amince Allah Ya sa hakane yafi alkhairi...
Ya ya kuke ganin wannan haɗin????✍🏻 Ina jiran sharhinku