KUNDINA

30

by @nafisatusasaal01

*KUNDINA*
 *SASAAL*
***


30



ALHAJI AHMAD; 
A daren ranar ya kira Baban Fatima ya shaida mai Lamiɗo ya amince..

Baba yanayin yadda ya ji farin cikin a muryar Aminin nasa yasa shima ya nuna farin cikinsa, tare da addu'ar Allah Ya sa haka ne yafi alkhairi...

A lokacin Baba yana tare da Hajiya Babba ranar girkinta.

Tsaf ta nutsu ta kasa kunne, ta kuma fahimci ina zancen nasu ya dosa, tunda ta kwana da sanin Salim ba zai auri Fatima ba...

Hassada da ƙyashi ne suka lulluɓeta, musamman da Baba ya gama waya bai yi mata bayanin komai ba..

Miƙewa tayi, da sunan zata je sashen ta dawo, don bazata iya kwanan sashen batare da tattauna lamarin da Farida ba..

Tana tafe tana zancen zucin
"Yanzu shi kenan da bata san komai ba, haka Alhaji zai binneta, sai dai kawai ta ji auren Fatima da Lamiɗo, tabɗijam da kuwa ya cuceta...

Lokacin misalin ƙarfe takwas da rabi ne na dare, Farida ba tayi barci ba...

Hajiya Babba ta jima tana ƙwanƙwasa ƙofa kafin Farida ta buɗe mata, da mamaki a saman fuskarta ta ce;

"Hajiya lafiya na ga kin dawo?"

Raɓa Farida tayi ta wuce tana cewa;

"Ina fa lafiya, ashe auren Fatima za'ayi da Lamiɗo ba mu sani ba"

Farida cikin ɗimuwar hassada ta kullo ƙofar da ƙarfi ta na cewa;

"Kai Hajiya wani Lamiɗon? ba dai Lamiɗon gidan Inna da na sani ba, wannan ne zai amince ya auri Fatima, ko dai ba ki ji da kyau ba"

Harara Hajiya Babba ta banka mata, ta ce;

"Ba na son shirme, shawarar mafita nake so ki kawo mana,  ko na kira yayyanki na ji yaya zamu yi, ko da yake ga Turai nan, naga kamar ta fini iya haɗa gadar zare"

Ita dai Farida ta kasa cewa komai saboda hassadar da ya mamaye zuciyarta.

Lamiɗo ya daɗe yana birgeta, ba don komai ba, sai don yadda ya iya kame kansa, a rayuwarta tana son Namiji mai aji, da kuɗi...

Jigum suka yi dukkansu, kowannensu zuciyarsa cike da muguwar saƙa..

Tsaki Hajiya Babba tayi ta miƙe ta ce;

"Bari na koma wajen Alhaji, da safe zan je wajen Turai, nasan a wajenta zan samo mafita"

Kai Farida ta jinjina mata saboda har lokacin ta kasa magana..

Bayan fitar Hajiya Babba Farida ta jima a zaune, tana saƙe-saƙen yadda zata dakatar da auren Fatima da Lamiɗo tun kafin lokaci ya ƙure mata, amma ba ta samu mafita ba.

Dole haka ta tashi ta kullo sashen ta tafi ɗakinta ta kwanta zuciyarta babu daɗi sam..

★washe gari Hajiya Babba ta tambayi Baba zata je gaisuwa, Allah Ya yiwa ɗaya daga cikin ƴaƴan ƙawayenta rasuwa..

Baba bai kawo komai a ransa ba, ya yi mata fatan dawowa lafiya..

Hajiya Turai ta fara kira kafin ta shirya, ta shaida mata gata nan zuwa.

A gurguje ta kimtsa, har lokacin Farida tana cikin ɗakin ba ta fito ba..



GIDANSU SALIM;

gaba ɗaya Hajiya Turai kasa gane kan Salim tayi, ya ma ƙi fitowa daga ɗakinsa, ta tambayeshi menene yake damunsa ya ce mata babu komai..

Tana cikin jimamin halin da yake ciki Hajiya Saratu ta kirata gata nan zuwa..

Abinci mai sauƙi tasa masu aiki suka shirya mata..

Tana nan zaune, Hajiya Babba ta kirata ta iso..

Masu aiki tasa suka shigo da ita..

Da sallama Hajiya Babba ta shigo parlon, tana ƙarewa ko ina kallo a fakaice, a ranta tana hamdalar  samun nasarar raba Fatima da Salim da tayi, da yanzu wannan daular Fatima zata shigo, ko ma wanda ya fi shi..

Jiki a mace Hajiya Turai ta miƙe suka rungume juna..

Ba yabo ba fallasa suka gaisa..

Sai da Hajiya Babba ta jiƙa moƙoshinta, sannan Hajiya Turai ta fara koro mata bayanin halin da Salim yake ciki..

Ga mamakin Hajiya Turai ture zancen Hajiya Babba tayi, ta sako mata zancen Fatima fa har ta ƙara samun mijin aure..

Fuska Hajiya Turai ta yamutsa alamar bata fahimci ina Hajiya Babba ta dosa ba, a tunaninta  sun rufe babin Fatima, kenan idan ta fahimci Hajiya Saratu ba wai tarbiyyace Fatiman bata da shi hassada ne kawai?

Don ta ƙara tabbatar da zarginta ta ce;

"To yanzu yaya kike so ayi Saratu?"

Zama Hajiya Babba ta gyara ta ce;

"So nake yi shima wannan auren a fasa shi, amma na rasa ta ina zan fara, saboda shi  wannan ɗin da zata aura shi da iyayensa, sun san gaskiyar komai, ba ni da wata hanya da zan ɓullo musu a fasa auren, shine na zo ki samarmin mafita"

Baki hanci da ido Hajiya Turai ta saki tana kallon Hajiya Babba, da yake ita Macece kaifi ɗaya bata iya ɓoye-ɓoye ba, kai tsaye ta ce;

"Saratu!! Wallahi kin ji kunya kuma kin yi asara, Allah Ya sakawa Salim, me ƴar kishiyarki ta tare miki ki ke binta da irin wannan sharrin? amma ke ba ƙaramar wahalalliya ba ce ba wallahi, duk akan yarinya ƙarama kike wannan abun? Duk ni'imomin da Ubangiji ya yi miki, sannu an gaisheki Saratu, wallahi duk a tunani yarinyar nan ƙarya takewa Salim, don ta yaudareshi, dama can ta saba, shi kuma so ya rufe masa ido ya kasa ganewa..

Bari ki ji na gayamiki ni duk abuna bana zalunci bana bin boka, don haka tashi ki bar min gida"

Zuru Hajiya Babba tayi da ido, zata iya cewa tun take a rayuwata bata taɓa jin irin kunyar da ta tsinci kanta a ciki ba..

Ba tada zaɓi, dole haka ta saɓi jakarta gwiwarta a sanyaye ta bar gidan..


Hajiya Turai ta fi minti talatin a zaune bayan tafiyar Hajiya Babba ta kasa tashi saboda mamaki.. a haka Salim ya fito ya sameta..

A gefenta ya zauna, idanuwansa duk sun faɗa, murya ƙasa-ƙasa ya ce;

"Hajiya zan ajjiye aikina, kawai na riƙe kasuwanci na zai fi min sauƙi"

Kamar daga sama yaji muryarta a raunane ta ce;

"Saboda Fatima ko?"

Murmushi ya yi ya jinjina mata, alamar "eh"

Kasa shiru tayi ta bashi labarin abinda ya faru tsakaninta da Hajiya Babba.. sannan ta ɗora da;

"Da Fatima zata amince da mun naimi afuwarsu ka aureta a ta biyu, ba ni lambarta" 

ta faɗa tana ɗaukar wayarta ta miƙa mai..

Salim hannunsa yana karkawa ya karɓa ya saka mata lambar Fatima..


FATIMA;

★washe gari tunda nayi Sallar asuba ban koma barci ba, ina zaune cikin tunanin kala-kala, gaba ɗaya na manta da batun Lamiɗo sai da Baba ya kirani..

Nasiha ya ƙara yimin kamar yadda ya saba, Sannan ya sako min batun yadda suka yi da Alhaji Ahmed akan maganar aurena da Lamiɗo har an bashi lambar wayata..

Shiru nayi ban ce komai ba, a ganina ya kamata ace su Baba su bani sarari na warke daga rashin Salim tukunna, amma ba yanda na iya..

Baba bai nemi jin ta bakina ba, ya ƙara yimin nasiha tare da gargaɗin na ci abinci sannan ya katse wayarsa...

Zugum nayi a zaune, ban san halin Lamiɗo ba, amma namiji ne da kowacce mace zata yi fatan samu, saboda kowa yasan kamun kansa da nutsuwarsa..

Tunani na fara yi, ko  da wani salo Lamiɗo zai zo min? 

A nan na zauna har gari ya yi haske, sannan na koma kan gado, barci mai nauyi ya ɗauke ni...

Ina cikin barci ringing ɗin wayata ya tashe ni..

Ban lura da lambar ba na ɗaga, muryar Namiji na ji, mai tsananin sanyi da zaƙi kamar na Mata anyi sallama..

Zaro wayar nayi daga kunnena, don na ga waye, sai naga baƙuwar lamba ce..

Mayar da wayar nayi kunnena na amsa sallamar ina jiran na ji waye, don sam ban ɗauki murya ba..

Sai da muka gaisa ya ce;

"Lamiɗo ne" 

Kunya ce ta kamani, daga ɓangarensa murmushi ya yi, cikin kamewa ya ce;

"ki ajjiye lambata anjima zamu yi waya"

Cikin kunya na amsa da;

"To"

Barcin da ban koma ba kenan, na miƙe ina tunanin ta yadda zamu fara soyyayya da mutum irin Lamiɗo.. lambar nayi saving da Yaya Lamiɗo..

Ban tashi daga kan gado ba, sai da yunwa a fara cin ƙarfinta, sannan na tashi na shiga kitchen na dafa shayi da soyayyan kwai..

Ina nan zaune a inda na karya, wayata ta fara ringing, baƙuwar lamba ce, a tunanina Lamiɗo ne don haka na ɗaga da sallama, murya mace na ji...

A mutunce muka gaisa, ina shirin tambayar da wa nake magana na ji ta ce;

"Hajiyarsu Salim ce"

Ƙara gaisheta nayi muryata a sake cikin ladabi, ga mamakina yafiyata ta fara nema, ta shaidamin wallahi Hajiya Babba ce duk ta ƙara hargitsa mata lissafi, amma tana neman alfarma a wajena na yarda azo a bawa Baba haƙuri Salim ya yi ta biyu da ni...

Ban yi nauyin baki ba, na shaida mata Baba ya riga ya yanke hukunci, yayimin mijin aure, ba zan iya watsa masa ƙasa a ido ba..

Murmushi tayi, muryarta a sanyaye tayi min fatan alkhairi... Muka yi sallama..

Ban bari tunanin wayar mu da Hajiyarsu Salim ya dameni ba, batun Hajiya Babba kuwa, nasan zata aikata abinda ya fi haka, amma Allah Ya fi ta..

Tashi nayi, na yi wanka na kira Mama a waya muka sha hira, ban nuna mata komai ba..


SALIM;
Hajiyarsu tana katse wayar, ya kasa jurewa ya rungumeta zuciyarsa na yi masa raɗaɗi..

Daga ranar ya yi shawarar yanke duk wata alaƙarsa da Lawal... Ya kuma sawa ransa gina kansa da gaske ba ya dogaro da dukiyar Iyayensa ba, domin da ya gina kansa tun farko da bai samu Matsalar da ya samu akan auren Fatima ba, ko da zan samu kaɗan ne...


HAJIYA BABBA;

kasa kiran Driver ta yi yazo ya mayar da ita, ita da kanta take jin kanta a matsayin munafuka mai haɗa masifa, amma indai akan Fatima ne, wallahi sai inda ƙarfinta ya ƙare...

Tana zuwa gida ta kira manyan ƴaƴanta, tana  neman shawararsu..

 amma abun takaici ba ta samu wani cikakken mafita daga garesu ba, dole ta yanke shawarar fara shigewa Baba don samun mafita...



FATIMA;
Bayan mun gama waya da Mama na shiga gyaran sashen duk don kar nayi zaman tunani.. ina yi ina ƴan waƙe-waƙe na...

Sai daf da La'asar na kammala, na ƙarayin wanka, na shirya bayan nayi sallah na tashi don zuwa gaishe da Baba..

Na jima a sashen yana yi min nasihar na kwantar da hankalina..

 Har na baro sashen ban bashi labarin abinda Hajiyarsu Salim tace Hajiya Babba tayi ba, na barta Allah har zuwa ranar da Zai tona mata asiri..

Bayan sallar Isha'i ina zaune ina ƴan karance karancena kiran Yaya Lamiɗo ya shigomin, har ga Allah muryarsa birgeni take yi..

A nutse na ɗaga, na gaisheshi cikin girmamawa.

 Da alama ya ji daɗin girman da na bashi daga yanayin amsawarsa..

Muryarsa ya ƙara yin ƙasa da shi ya ce;

"Allah Ya sa ban takura miki ba, tunda ban nemi izinin gimbiyar mata ba"

Daɗi da kunyane suka  kamani lokaci ɗaya, a raina nace;

 "amma Fatima ke sokuwa ce, daga ce miki gimbiyar mata shikenan sai kiji daɗi, kin manta daɗin hirarku da Salim, kuma daga ƙarshe ya auri wata ba ke ba"

A zahiri murmushi nayi ban ce komai ba...

Da wani irin salo kamar ba Lamiɗon da na sani ba ya ce;

"Ina son mace mai kunya Fatima, kuma tunda Baba da Inna suka yi min maganarki naji kin kwantamin ina fatan kema haka?"

Kamar mara gaskiya a hankali na ce;

"Eh"

"Eh me? Fatiman Lamiɗo, ohh my bad Amaryar Lamiɗo ya kamata na ce" ya ƙarasa faɗa yana ƴar dariyar nishaɗi..

Nima murmushi nayi ina ɓoye Fuskata kamar yana ganina..✍🏻

Barkanmu da Jumuah 🙌😄