KUNDINA

31

by @nafisatusasaal01

*KUNDINA*

*NAFISATU ALIYU SASAAL*
*****


31


FATIMA:
mun kusa minti goma muna waya da Yaya Lamiɗo, yana yimin tambayoyin da suka shafi karatuna.

 Har muka yi sallama  bai sakomin hirar abun da ya faru tsakanina da Sadik ba..

Yaya Lamiɗo yana barkwanci amma ba sosai ba, maganganunsa na nuna alamar son girma da sanin kansa, ba kamar Salim da muke yin wasa da dariya kamar yaro ƙarami ba..

Ban damu da son girmansa ba, domin a ganina ƙaddararta tasa na zama ɗaya daga cikin matan da basu da ƴancin zaɓar mijin auren da ya yi daidai da ra'ayinsu...

Zuciyata cike fal da tunanin ko aurena da Lamiɗo zai tabbata barci mai nauyi ya ɗaukeni...


SALIM;
Bai ɓoyewa Mariya da Yasmin batun ajjiye aikinsa da kuma dalilinsa na yin hakan ba..

Yasmin taji ciwon saboda Fatima ya ajjiye aikinsa, acewarsa don ta samu nutsuwar karatu. Ta so tayar da rigima a tsakaninsu amma daga yanayin muryar Salim ɗin ta fahimci idan tayi haka komai zai iya faruwa...

A Makaranta babu inda labarin barin aikin Sir Salim bai zaga ba a tsakankanin Ɗalibai.

Labarin barin aikin nasa yasa ɗalibai da yawa sararawa Fatima, masu tsokanarta da yi mata dariya suka daina, don sun fahimci ba wai Sir Salim baya Sonta ba ne ya yi mata haka.. ƙaddarar su ce ba ɗaya ba..

*********************************

Kwanaki sun miƙa shirye-shiryen biki ya kankama musamman a ɓangaren Salim da iyayen Yasmin..

A ɓangaren Iyayen Fatima basu shirya wani abun azo a gani ba, don ko Mama data ji labari Salim ya fasa auren Fatima, Lamiɗon Inna zata aura jikinta sanyi ya yi, bata ma gayawa kowa ba, saboda tsoro kar shima ya ce ya fasa..

Shima Baba kawai yin komai yake yi, amma babu karsashi a tattare da shi, gani yake yi, kamar shi ma Lamiɗo  zai ce ya fasa... Wasu lokutan ya kan ɗan ƙoƙarta nuna farin cikin gabatowar bikin saboda Amininsa Alhaji Ahmed da bashi da zance kullum sai akan bikin...

A ɓangaren Lamiɗo, gagarumin biki yake shiryawa shi da Abokanan aikinsa, lefe ma na gani na faɗa shi da Inna da ragowar ƴan uwansa suka haɗawa Fatima..



HAJIYA BABBA;

Hajiya Babba da Farida sun saƙa sun kwance amma sun kasa samun mafita..

Farida har ramewa tayi saboda masifar da ta sakawa ranta, ita babban baƙin cikinta kaf Samarin da take ji da su, ba su kai ajin Salim da Lamiɗo ba, ko Abokin Sadik da ya jima yana liƙemata bai kai Sadik komai ba..

Ita tafi son mijin nunawa sa'a, mijin liƙawa a goshin da ƙawayenta zasu kiyayeta, amma ace duk kwalliyarta da saka suturunta masu tsada ta kasa samun irinsu Lamiɗo..

Rashin shirye-shiryen daga ɓangaren Baba ba ƙaramin sosawa Hajiya Babba rai ya yi ba, a ganinta Baba a ɓoye yake yin komai na bakin  saboda kar ta sani.

 Ta nemi shawarar ƙawayenta bata samu mafita ba, acewarsu kawai ta kai sunansu wajen Malami a rabasu a hana ma Fatiman yin aure gaba ɗaya..

Sam bata amshi wannan shawarar ba saboda tsoro take ji, ita dai a barta da  harkar makirci da sharri, amma bazata iya zuwa wajen boka ya buƙaci abinda bazata iya ba, daga baya  ta haukace, Gara ta rufawa kanta asiri ta tara gwala-gwalanta na shiga ƙawaye da dangi da kuɗin...

Farida babu irin tunanin da bata yi, har Goggle photo ɗinta taje ta ɗauko vidiyoyin Fatima, musamman wanda Sadik yake  ce mata idan bata cire rigatar ba zai yi fushi da ita kuma ta cire... Sai dai ta rasa yanda zata sarrafa videon ya zama tarko ga Fatima tunda Lamiɗo ya jima da sanin komai..

Wani sashe na zuciyarta ya ce, to idan ya jima da sanin komai ai ba lallai ya taɓa kallo ba, kawai ki san yadda zakiyi ki samo lambarsa ki tura mai, ki jira kikaga menene zai biyo baya...

Sosai Farida tayi na'am da shawarar da zuciyarta ta bata, idan wannan bai yi aiki ba dole ta haƙura....

Sai dai inda zata samo lambar Lamiɗo ne aiki a wajenta, tunda ba wani shiri suke yi da Fatima ba.. kuma lambar WhatsApp ɗinsa ya kamata ace ta samu..

Bayan kwanaki biyu wanda yayi daidai da saura sati Uku biki.. dangin Lamiɗo suka kawo kayan lefen kerewa sa'a..

Hankalin Hajiya Babba da na Farida ba ƙaramin tashi ba, musamman Farida ta take ganin komai na shirin ƙwaceta mata, dole ta ajjiye girman kai, a dare ranar ta shirya zuwa wajen Fatima don yi mata Allah Ya sanya alkhairi daga nan ta samo lambarta...


FATIMA;
ba ni da matsalar komai ta ɓangaren kowa, muna hirarmu a waya da yaya Lamiɗo daidai misali, mu yi Chating, har hira yakan zuwa gida jefi-jefi sai dai baya jimawa yake tafiya, ya fi ganewa hirar a waya ko Chating..

Ba mutum ba ne mai yawan fara'a da son hira ba, amma ina jin daɗin soyayyarmu da babu takura sam..

Ƴar autarsu Mama Saliha da take sana'ar gyaran jiki aka Turo daga Gaya, ta  zauna da ni.

Ita take min gyaran jiki, da taimakon wasu kayan gyaran jiki na zamani a wajen Aunty Amarya...

Fes nayi kyau abuna duk inda na gifta ƙamshine kawai yake tashi..

Aunty Amarya ce tayimin siyayyan kaya masu tsada, har kyautar material blue tayi min mai tsananin kyan da tace Ɗan uwanta da ya zo kwanaki ne ya kawo Mata..

Wajen ɗinki mai tsadar da take kai kayanta, ta kaini a motarta, aka gwadani muka dawo gida..

A tsakakanin kwana biyu ɗinkunan suka kammala,  ta tura Driver ya karɓo..

Ba ƙaramin kyau dukkan kayan suka yi min ba, musamman na blue material, kamar don ni aka yi shi..

Kwana ɗaya bayan nan  dangi yaya Lamiɗo suka kawo lefen ya yi matuƙar birgeni, duk da na kasa kallon da kyau bayan an dawo da shi Sashena...

Saƙon godiya da fatan arziƙi mai albarka na tura mai... Sai kuwa gashi ya kirani.. kasa ɗagawa nayi, sai da ya kira sau uku sannan na ɗaga..

A kunyace muka gaisa ya ɗan tsokanata, sannan muka faɗa hirar shiryen-shiryen da yake ta  ɓangarensa..

Ina cikin waya da shi Farida ta shigo, ban yi mamaki ba, tsorona ɗaya menene ya shigo da ita?..

A gefena ta zauna, suka gaisa da Aunty Saliha sama-sama.. sallama nayi wa Yaya lamiɗo, na ajjiyeta wayata a gefena..

Muna gaisawa da ita na miƙe saboda yadda zuciyata take bugawa.

" bari na ɗan kama ruwa ina zuwa"

Na ƙarasa faɗa da murmushi a saman fuskarta...

Itama Farida murmushi ta mayar min.. anan na bar wayata na shige ɗaki..

FARIDA; Allah ya taimaketa wayar Fatima bata shiga key ba, don haka tayi wuf ta ɗauka, kamar nata haka ta shiga sarrafa wayar, Saliha dake can gefe ta ɗauka wayan Faridan ne...


FATIMA; ina shiga ɗaki, na jima a tsaye sai da na tabbatar bugu zuciyata ya dawo daidai sannan na fito parlon inda na bar Farida da Saliha..

Caraf idona ya sauka kan wayata da Farida tayi saurin ajjiyewa..

Kamar ba ni ba, haka na nufeta da zafin nama, kafin ta ankara na zuba mata marin da ya kusa gigitata, a zabure ta miƙe tana ƙanƙame wayarta, ɗayan hannunta ta dafe  kuncinta da shi ta ce;

"Me nayi miki Fatima, ni zaki mara?"

Da tsananin fushi na ce;

"An mareki ɗin, me kike yimin da waya, dama abinda kika zo yi kenan?"

Zaro ido tayi zata fara zazzagamin masifar ƙarfin hali, na ƙara ɗaga hannayena dama da hagu na sauke mata mari lokaci ɗaya..

A gigice ta kawomin hannu muka kaure da dambe... Aunty Saliha ihu tasa, tana yunƙurin rabamu, ganin bazata iya ba yasa ta fita a guje..

Har Aunty Saliha ta kirawo  Baba da Aunty Amarya bamu daina kai wa juna duka ba, kafin Baba ya ƙaraso nayi nasarar kai Farida ƙasa na fara sakar mata duka a fuska da dukka hannayena tana karewa...

Tsawa Baba ya dakamin na miƙe ina sauke numfarfarshi..

"Fatima yaushe kika koma haka?"

Baba ya tambayeni muryarsa a tausashe..

Fashewa nayi da kuka ina gayamasa wayata na kama Farida ta ɗauka kuma nasan lambar Lamiɗo zata sata, haka suka yi min lokacin Salim...

Farida tana jin haka ta miƙe tana rantse-rantsen sharri nake mata..

Baba murmushi ya yi ya ce;

"Nasan ruwa baya tsami banza, sashenki ba wajen zuwan Farida bane, amma koma menene Shi Allah Ba ya sabon aiki, ƙaddarar bawa bata wuce shi, tashi ki tafi kikai saƙon da aka turoki"

Ya ƙarasa faɗa yana kallon Farida..

Rantse-rantse ta cigaba da yi, har sai da Baba ya daka mata tsawa ta ɗauki wayarta da gilashin fuskar duk ya fashe ta bar sashen...

Bayan fitarta nasiha Baba yayimin kan na duƙufa wajen kai wa Allah kukana Ya na ji kuma Yana ganin komai...

Bayan tafiyarsu nasha kuka, don ko tantama bana yi lambar Lamiɗo Farida ta ɗauka.

 Daƙyar Aunty Saliha ta lallasheni nayi shiru..
Amma gaba ɗaya ji nayi duniyar ta isheni..


FARIDA; dan dakuwa ta daku a hannun Fatima, amma ai burinta ya cika, Hajiya Babba tana ɗakinta, don haka saɗaf-saɗaf ta shige nata ɗakin..
 
Tayi Sa'a fashewar wayar bai kai cikin ba...

A daren ta turawa Lamiɗo dukka videon Fatima guda uku, da Sadik yake bata umarnin ta cire kayanta yaga jikinta...


LAMIƊO; wayarsa tana hannunsa lokacin da Farida ta turamai saƙo, amma saboda sabawa da yayi da marasa tarbiyyan ƴammata masu samo lambarsa su tura masa shirme da shiririta musamman ma da ya kusa auren nan yasa bai buɗe ba....


Bayan kwanaki shirye-shiryen bikin ya ƙara kankama, Farida kullum sai ta turawa Lamiɗo videon Fatima baya buɗewa, ganin abinda nata da gaske ne, sai ya yi blocking ɗinta..

A ɓangaren su Salim tun saura kwana uku ɗaurin auren Fatima suka fara shagulgulansu..

A gidansu Fatima ma baƙi na nesa duk sun zo har da manyan ƴaƴan Hajiya Babba, ƴan uwan Mama duk sun zo, Aunty Amarya ma danginta mutum uku mata sun yi  mata kara sun zo, zasu yi kwana biyu su koma...


FATIMA; gaba ɗaya kawai yin komai nake yi, amma hankalina da nutsuwata sam basa jikina, ga dai shi muna waya da Yaya Lamiɗo lafiya ƙalau, amma na kasa samun nutsuwa...


Ana saura kwana ɗaya ɗaurin aure muka yi shirin zuwa Dinner da Lamiɗo ya shirya..

Kaf gidanmu babu wanda bai je ba, sai Baba da Kakarmu ta wajen uba, amma har da yayyen Mama da suka zo, duk sun je..

Kwalliyata tayi kyau ba kaɗan ba. 


HAJIYA BABBA;
hassada kamar ya kashe da tawagar ƴaƴanta..


FARIDA;
A wajen Dinner  ta haɗu da Aminin Lamiɗo da suke komai tare, ba don yayi mata ba saboda rangwamen kyansa, sai don cikar muradinta suka yi musayar lamba.. 

A ɓangaren su Salim daren ranar da su Fatima suka yi Dinner, Yasmin ta tare a gidanshi sai dai fatan Allah Ya basu zaman lafiya...


FARIDA;
Ko wajen Dinner bata bari ba, ta turawa abokin lamiɗo videon Fatima, tare da roƙonsa ya nunawa Lamiɗo bata so yayi zaɓen tumun dare.. 

Abokin Lamiɗo Faisal bai san alaƙar Farida da Fatima ba, Video ɗaya ya buɗe yaji ransa yayi mugun ɓaci mutuncin Fatima ya zube a idonsa ya turawa Lamiɗo..

Ganin har dare ya yi sosai Lamiɗo bai buɗe saƙonsa ba, gashi ɗakinsu ba ɗaya ba yasa ya kirashi a waya ya ce ya duba ya turomai saƙo...

Lamiɗo video ɗaya ya kalla yaji ranshi ya ɓaci, ba wai don Fatima ta bayyana dukka tsiraicinta ba, iya ƙirjintane kawai amma yadda namijin yake bata umarni tana bi, da kuma abokinsa da ya gani ne yasa yaji komai ya tsaya mai cak...

A take zazzaɓi mai zafi ya rufeshi, kishi kamar ya halakashi..

★har zuwa washe gari babu wanda yasan halin da yake ciki, sai Faisal, kuma yaƙi buɗe mai ƙofa balle yaga halin dayake ciki, sun dai yi waya yace mai yana ɗan jin zazzaɓi...

A daddafe Lamiɗo ya shirya don dakatar da komai.

Domin idan ya auri Fatima a yanzu bai zai iya yi mata adalci ba, Gara kawai a tsaida komai, idan zuciyar tayi sanyi sai a ɗaura...

ALHAJI AHMAD;
Bai bi takan rashin zuwan Lamiɗo ba, tunda Faisal ya zo, suka fara haramar barin gida don ƙarfe goma da rabi za'a ɗaura gashi har goma ta gifta...

Suna fitowa harabar gidan motar Salim na shigowa, alama Alhaji Ahmed yayi masa ya samesu a can..

Daga yanayin saka kayan Lamiɗo zaka san an samu matsala saboda burin da ya ɗora akan bikin...

Duk yanda Lamiɗo ya kai ga son su keɓance da mahaifinsa bai samu dama ba har aka ɗaura..

Ransa ne ya kara ɓaci, zuciyarsa tayi zafi matuƙa, shaiɗan ya dinga ingizashi, ji yake yi kamar idan ya bar wajen da igiyar auren Fatima a wuyanta  mutuwa zai yi.

Inda Mahaifinsa yake tsaye da su Baban Fatima suna gaisawa da Abokanansu ya nufa..

Muryarsa ras mutanen wajen suna jinshi ya ce;

"Baba tun ɗazun nake binka, ka saurareni kaƙi bani dama"

Da sauri Alhaji Ahmed ya waiwayo kansa haƙoransa dukka a waje saboda farin ciki ya ce;

"Ai yanzu zamu koma gida, sai mu tattauna ka  j..."

Bai ƙarasa ba furucin Lamiɗo ya sashi tsuke bakinsa nan take;

"Baba ba zan iya zama da Fatima ba, ka gafarceni na saketa saki ɗaya"

Baban Fatima, kansa ya sukunyar ƙasa, bai ji  kunya sosai ba, tunda ya saba da jin makamancinsa, sai dai na yau yazo masa a bazata..

Alhaji Ahmed mari mai gigita lissafi ya saukewa lamiɗo, ya riƙo kwalar rigarsa, ya ce;

"Maimaita abinda kace Lamiɗo, dan Allah Karka yimin haka kaji, ka tausayamin karka kunyatani a idon duniya"

Lamiɗo maimaita furucin sakin Fatima da yayi ya ƙara yi, wanda yasa Baba Fatima rintse idonsa da ƙarfi...

Sakin kwalar rigarsa Alhaji Ahmed ya yi ya ce;

"Ka mayar da ita ko na tsinemaka"

Da sauri Baba ya janyoshi ya ce;

"Haba Ahmad, da girmanka zaka yi haka, karka ga laifin Lamiɗo dole yana da dalilinsa, kuma ko da ya mayar da Fatima, ni a matsayina na Mahaifinta zan yi ƙararsa, don ba zan lamunci zamanta a inda za a rusa ragowar farin cikinta ba.. Fatima Macece mai daraja, tana buƙatar wanda zai fahimci ƙaddara ya yi aiki da nadamarta ba kuskurenta ba, idan Namiji yana son Mace da gaske abinda Fatima tayi bai kai hujjar da zau rabu da ita ba, tunda Namiji yana iya ɗauko mace daga bariki idan tayi nadama ya aureta su zauna lafiya balle Fatima"

Babu wanda maganar Baba bai ratsa ba, har Lamiɗo sai da kunya ya kamashi..

Alhaji Ahmed zai yi magana Baba yaƙara cewa;

"Babu abinda zai raba amintarmu Ahmad ko yau Lamiɗo ya samu matar aure zan zame masa waliyyi, Allah Ya sa hakane ya fi alkhairi, mu bar maganar haka, muna cikin Jama'a"

Babu wanda bai tausayawa Baban Fatima ba, saboda yanayin fitar kalamansa na bayyana ciwo mai raɗaɗin dayake ƙoƙarin dannewa..

Kafin kowa ya watse batun rabuwar auren ya bazu ko ina, waɗanda basu san abinda Fatima tayi ba a ranar sai da suka sani, wasu su bawa Lamiɗo laifi wasu kuma su bawa Fatima...

Gidansu Lamiɗo labari ya fara zuwa, Innarsu da ƴan uwansa suka ruɗe da koke-koken Lamiɗo ya zubarwa da Babansu da gidansu mutunci...

Kafin Babansu Fatima ya isa gida labari yaje musu...✍🏻