32
*KUNDINA*
*NAFISATU ALIYU SASAAL*
***
32
GIDANSU FATIMA;
matasan yaran maza masu ƙananun shekaru ƴaƴan ƙanwar Mamansu Fatima ne suka shigo sashen Fatima a guje..
Su na nufarfashi suka shigo Parlon da kowa yake zaune, har da Aunty Amarya da ta rakowa ƴan uwanta zasu yiwa Fatima sallama...
Saboda zumuɗin su bayar da labarin abinda da ya faru basu yi hankalin akwai mutane a parlon ba, ciki har da Fatima.
Da ƙarfi suka haɗa bakin faɗin;
"Mummy! Mummy wallahi mijin aunty Fatima ya saketa, mun ji wasu sun ce wai Video aka turamai tana cire kay...
Da sauri Mommynsu ta daka musu tsawa, sai a lokacin suka fara kallon mutanen cikin parlon..
Ba su motsa daga inda suke ba babbar Yayarsu Maman Fatima ta shigo tana salati, da kuka..
Gaba ɗaya ƴan uwan Mama miƙewa sukayi suka nufeta.. suna tambayarta "lafiya"
Cikin kuka take gayamusu abinda akace Lamiɗo ya yi..
Aunty Saliha kuka ta fashe da shi, tana basu labarin abinda ya haɗa Fatima da Farida ranar da aka kawo lefe..
Kamar yaƙi haka suka tattara dukkansu suka yi sashen Hajiya Babba.
Babbar Yayarsu Maman Fatima Hajiya Sumayya tana cewa;
"wallahi yau sai sun gane kurensu, sai Saratu tayi mana bayanin dalilin da ya sa suke yiwa Fatima dukka wannan ƙulle-ƙullen"
Aunty Amarya tari mai ƙarfi ne ya sarketa ta shiga yi babu ƙaƙƙautawa, tun taji dagaske ne Lamiɗo ya saki Fatima.
Da sauri ƴar uwarta ɗaya ta tashi ta ɗauko mata ruwa, amma ta kasa ƙarɓa.. sai da ta kamo kanta ta kafa Mata goran ruwan a baki..
Kurɓa ɗaya tayi, ta ɗago idanuwanta da suka yi jaa nan take tana kallon Fatima da tayi ƙasa da kanta cikin mayafi...
"Fatima"
Aunty Amarya ta kira sunana da wani irin rauni da ban santa da shi ba..
Ban ɗago ba, na miƙa mata hannuna da ya jiƙe sharkaf da gumi yana karkarwa...
"Ki yi kuka kin ji Fatima "
Kamar jiran furucinta nake na fashe da kukan da babu sauti...
Kai ta girgiza ta ce;
"Ki buɗe baki kiyi kuka Fatima, ki yi iya wanda zaki iya"
Mayafin kaina na yaye na karkata kaina gefe inayi mata irin kallon da ban taɓa yi mata ba.
Sai nake ganin kamar fuskar Yaya Lamiɗo a saman fuskarta.
Da sautin kukan da ya taho da hawayen da ya haɗe da majina yana saukowa ƙasar haɓata na ce;
"Meyesa sai bayan an ɗaura mana aure? Maiyasa zaka ƙaramin wani tabon akan wanda nake da shi, ina alƙawarin da ka yimin zaka kula da ni har ajali? Wannan shine sakamakon da zan samu daga gareka Yaya Lamiɗo? Ko dai ƙarya suke yi min, nasan nutsuwarka da mutuncinka ba su barka ka tozartani ba"
Na faɗa ina kamo Fuskarta da dukka hannayena..
Nata hannun ta ɗora a saman nawa tana kallon cikin idanunawa na tace;
"Babu wani taɓo da kike da shi Fatima, ke macece mai daraja, wata rana zaki ce na faɗamaki, sakin aure ba shi yake nufin rayuwarki ta ƙare ba, yanzu ne ma lokacin da zaki yi gwagwarmayar gaske don ƙara zama irin Fatimar da kowa zai yi alfahari da ita"
Ta ƙarasa faɗa tana rungume ni..
Kuka mai ƙarfin gaske na fashe da shi, ina rintse idanuwana, saboda raɗaɗin da zuciyata take min.. ji nake yi inama da zan mutu na huta, ina ma ban san Yaya Lamiɗo ba..
Ƴan uwanta da su kaɗai suka rage Parlon suma kasa riƙe hawayensu suka yi, babbar cikinsu Hajiya Ni'ima da yanayin kamewarta ke nuna izzarta, da zafin kanta cikin fushi ta ce;
" yanzu Hanifah haka zaku barshi ba zaku ɗauki matakin komai a kanshi ba? ƴaƴa mata nawane suka yi abinda yafi nata muni kuma aka aure su? Wannan ai cin zarafi ne, gaskiya idan Alhaji zai yarda mu da kanmu zamu ɗauki tsatsauran mataki akansa, mu nuna masa ikonmu da gatan ita kanta yarinya da ya ci wa zarafi, ina laifin ma ya bari sai ta tare ya yi sakin asirinsu a rufe"
Aunty Amarya kai ta girgiza mata, saboda tasan halinta kaf danginsu babu masu zafin kan ƴan ɗakinsu, kira ɗaya zata yi, Lamiɗo ya shiga masifa, tasan kuma Alhaji ba zai ji daɗi ba, Amintarsu da Alhaji Ahmad zai ɓaci..
Hajiya Ni'ima na yunƙurin ƙara yin magana Baba ya shigo, fuskarsa duk ta faɗa, ya yi baƙi kamar ba shi ba, kamar ma kuka yayi kafin ya shigo..
Muryarsa a raunane yake tambayar;
"Ina Fatima? Hanifah ina Fatima take?"
Babu wanda bai ji tausayinsa ba a cikinsu, sai a lokacin Aunty Amarya ta lura da sakin jikin da Fatima tayi a jikinta, salati ta saka, ƴan uwanta suna tayata..
Baba hankalinsa tashe, ya ƙaraso ya kwantar da Fatima a jikinsa yana shafa mata ruwan gorar da Aunty Amarya tasha ta rage...
Dogon numshi Fatima taja daidai lokacin Yara suka shigo suna ihun wai Baba ya zo ana dambe a shashen Hajiya Babba...
Dole haka Baba ya ƙara miƙewa hankalinsa a tashe ya nufi sashen.....
SASHEN HAJIYA BABBA;
kaf ƴan uwan Fatima yaransu da manyansu sashen suka yiwa tsinke, kowacce ranta a ɓace da bayanin da Aunty Saliha tayi musu..
Kakarsu Fatima tana sashen da dukkan ƴaƴan Hajiya Babba da jikokinta suna hira...
Sumayya ce tayi sallama ragowar suma suka danni zuciyarsu suka shiga parlon da sallama a bakinsu...
Bayan sun gaisa babu yabo babu fallasa Kakarsu Fatima ta ce;
"Lafiya na ganku haka zuga guda"
Cikin isa da jin haushin tambayar Hajiya Sumayya ta ce;
" ina fa lafiya, zuwa mukayi mu ji abinda ɗiyarmu ta tarewa Saratu take korar mata Mazajen aure"
Babbar ƴar Hajiya Babba Aunty Ummi tana jin haka ta miƙe cikin izgili ta ce;
"To menene kuma ya faru iyayen son rigim.."
Bata ƙarasa ba Babbar ƴar Hajiya Sumayya, Lubabatu ta tashi a zafafe ta sakar mata naushi a baki...
Ihu Aunty Ummi ta kurma tana zaro ido..
Kakarsu Fatima ido itama ta zaro tana cewa;
"Wai menene haka ɗiyarki tayi Sumayya? Dukka fitannan wai ta mecece bayan an riga an ɗaurawa Fatima aure"
Hajiya Sumayya cikin fushi ta juye mata abinda Aunty Saliha ta faɗa musu, da kuma sakin da Lamiɗo ya yi wa Fatima..
Ruɗewa tayi tana salati..
Hajiya Babba wani irin daɗine ya lulluɓeta lallai Farida ta gama biyanta..
Farida shiru tayi tana danna wayarta, kamar ma bata san da mutane a wajen ba...
Aunty Saliha kallon Farida tayi haushi ya kamata, da zafin nama ta fizge wayar, da wurgashi ya daki bango.
Farida ta miƙe zata yi mata masifa, Aunty Saliha da dama jiranta takeyi, a take ta kwashe mata ƙafafu ta haye saman jikinta tana dukanta ta ko ina...
Hajiya Babba da ƴarta ta biyu Aunty Safiyya , har da surukurta matar Abba, miƙewa suka yi suka nufi Aunty Saliha, sai dai basu kai ga ƙarasa ba, suka ji duka ta ko ina..
Hajiya Sumayya ta na cewa;
"Tunda halin ƙaranta ne daku, bari muma mu nuna muku namu kalar halin ƙarantar, mu ba irin Maryam ba ne(Mamansu Fatima) da kuka raina, mu idan aka yi mana ba daidai ba jikin mutum ne zai gayamasa.
kuma ba zamu tafi ba, sai kun yi mana bayanin menene dalilin yasa kuke haɗa makircin da baka son Fatima tayi aure"
Ita dai Kakarsu Fatima lallaɓa kanta tayi ta shige ɗaki, gudun kar su faɗo mata su haɗata da wahala..
Bayan ta shiga ɗaki ne ta kira Baba bai ɗaga ba, dole ta kira ƙaninsa ya turo a nemoshi, gasu Saratu da Sumayya suna dambe...
Kafin su Baba su zo, Farida ta suma saboda azaba, ita kuwa Hajiya Babba cewa takeyi su ƙyaleta wallahi bazata ƙara ba..
Babu wani abun ƙyale-ƙyalen parlon da ba'a lalata ba, har Tv sai da suka fasa mata..
Aunty ummi tunda taji naushin farko ta wayance ta shige ɗaki bata ƙara fitowa ba..
Matar Usman da Aunty Safiyya tun suna mayar da dukkan har suka gaji suka fauwalawa Allah...
Baba da ragowar ƴan uwansa da ƙyar suka ƙwaci Hajiya Babba, har lokacin Hajiya Sumayya faɗi take;
"Sai nayi ƙararki muguwa jikar talakawan fitik, inda arziƙi na bada ƴanci to wallahi Fatima ta gama Shan wahala a hannunku munakai kawai"
Daƙyar Baba ya tausheta tayi shiru, suka tsatsaya kowacce ta na sauke numfashi...
Farida aka fara taimakawa ta dawo hayyacin, ta kasa buɗe idonta ɗaya da ya kumbura..
Baba wani irin sanyi ya ji a ransa, ko ba komai yanzu Saratu zata ɗan dawo cikin nutsuwarta, ta rage wasu abubuwan akan Fatima, amma a zahiri bai nunaba ya danne..
Sai da ya tabbatar komai ya lafa sannan ya buƙaci duk su biyosa sashen Fatima...
Daƙyar su Hajiya Babba suka ja jiki.
Kakarsu Fatima, da Aunty Ummi da suka ɓuya a daƙi suka firfito zuwa sashen Fatima...
SHAHEN FATIMA;
Bayan fitar Baba, ɗaki su Aunty Amarya suka mayar da Fatima, suka kwantar...
Aunty Amarya ta kira likita Macen da take zuwa dubata har gida, ta zo ta duba Fatima saboda zazzaɓin daya fara kama jikinta...
Parlon suka dawo, suka zazzauna cikin alhini, kowacce ta kasa cewa komai, a haka su Baba suka samesu..
BABA bai damu da zaman ƴan uwan Aunty Amarya a Parlon ba, bayan kowa ya gama shigowa an zazzauna, aka kori yara masu ƙananunu Shekaru..
Gyaran murya Baba yayi, cikin ƙarfin hali yayi sallama, ya ɗora da addu'o'i sannan ya fara bayani kamar haka;
"Ban ji daɗin abubuwan da suke faruwa ba, nayi tunanin ƙaddarar Fatima zata zama darasi da zai sa mu nutsu mu ƙara riƙe ƴaƴanmu da kula da tarbiyyarsu, ba muyi ta faɗa da juna ba.
Ni ban yi imanin da akwai wanda ya isa ya hana Fatima aure idan lokacinta yayi ba.
Waɗanda suke tunanin suna da dabarar hanawa ta hanyar amfani da kuskuren da ta yi abaya, su sani lokacin aurenta be bai yi ba, shiyasa Allah Yake basu dama domin ya gwada imanin Fatima..
Ina roƙon kowa da yayi haƙuri, mu sawa zuƙatanmu dangana, muyi wa Fatima addu'ar Allah Ya kawo mata sauƙin halin da take ciki..
Kuma inaso Kowa anan ya zama shaida (ya faɗa yana kallon Mahaifiyarsa) duk ranar da Saratu ta ƙara tsoma baki a sha'anin auren Fatima to ta sani babu ni babu ita har abada, kuma babu wanda zai bani haƙuri ta ƙara dawomin cikin rayuwar Iyali, saboda naja mata kunne ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba, ba irin barazanar da banyi mata, amma taƙi ta tsaya a matsayita, don haka ku zama shaida..
A ƙarshe ina mai ƙara bawa Kowa haƙuri, da kuma godiya mai tarin yawa, Allah Ya maida kowa gidansa lafiya, ina kuma roƙon ku, kuyiwa Fatima addu'a Allah Ya sanya mata dangana"
Baba ya ƙarasa faɗa yana muryarsa tana rawa..
Hajiya Ni'ima cikin isa da takaicin data kasa dannewa ta gyara zamanta tana shafo dogon siririn farin hancinta ta ce;
"Amma Alhaji haka zaku bar maganar nan, baza a binciki mijin aji wanene ya tura masa Videon ba, bai kamata abar maganar ya tafi haka ba, a binciko asalin videon daga wajen wa yake, a ɗauki matakin Shari'a akansa"
Kowa na wajen kallonta yake yi, yana wassafa dukiyar da aka zuba wajen siyan tattausan leshin jikinta zuwa kan gwagwalen da tayi ado dasu, har zuwa kan fari tas ɗin kafar data yiwa ado da sarƙa gwal, sanye cikin tattausan Takalmi, ko ba su tambaya ba, sun san jinin su Hanifah ce..
Babu wanda bai san aikin Farida ba ne a wajen, amma gudun halin da Baba zai shiga yasa kowa yayi shiru yana jiran abinda zai ce..
Farida ƙanararren idonta da yasha bugu ta buɗe da ƙyar tana kallon Hajiya Ni'ima da bata taɓa ganinta ba sai ranar, don tunda suka zo bikin Hajiya Ni'ima bata fito ba, ragowan dai sun shiga sun gaishe da Hajiya Babba amma banda ita.. ji tayi zuciyarta na bugawa kamar zai fasa ƙirjinta ya fito, tana addu'ar Allah Ya sa Baba ya rufa mata asiri..
Kowa poster yayi yana jiran furucin Baba..✍🏻