33
*KUNDINA*
*SASAAL*
33
BABA;
murmushi ya yi, ya kalli Hajiya Ni'ima ya ce;
"Hajiya banƙi ta taki ba, amma ina ganin mu barwa Allah komai, da sannu mai aikawa zai shiga hannun dai-dai shi"
A jiyar zuciya Farida da Hajiya Babba suka sauke...
Hajiya Ni'ima kai ta jinjina, tana gyara zaman mayafin dake yafe a kanta, haɗe da miƙewa, suma ragowar miƙewa suka yi har da Aunty Amarya..
Da ƴar fara'a Baba ya ce;
"Ba dai tafiya ba?"
Murmushi suka yi Aunty Amarya ta ce;
"Idan basu tafi yanzu ba, zasu iya rasa jirgi"
Baba miƙewa ya yi, yana yi musu godiya..
Har da shi suka fito Harabar gidan, zuwa inda Motar Aunty Amarya yake..
Aunty Amarya na ƙoƙarin yi masa bayanin likitarta na nan zuwa duba jikin Fatima sai ga shigowar motarta..
Anan Baba ya ƙarayiwa su Hajiya Na'ima godiya suka yi sallama, tare da addu'ar, Allah Ya bawa Fatima lafiya..
Yana tsaye har motar Aunty Amarya ta bar harabar gida..
Tare da Likita suka jero zuwa Sashen Fatima, hannunta riƙe da kayan aikin da ta taho dashi, Bana yana yi mata bayanin halin da Fatima take ciki..
Kafin su iso, Hajiya Babba da tawagarta sun koma sashensu sai ƴan uwan Mama Fatima kawai..
Daga likita sai Baba ne suka shiga ɗakin da Fatima take ta dubata..
Ruwa ta saka mata, ta ajjiye wasu magungunan da ta taho da su idan tayi barci ta farka ta ci abinci a bata tasha, tunda Aunty Amarya tayi mata bayanin zazzaɓi ne tun a waya..
Bayan ta gama aikinta kuɗi mai nauyi Baba ya bayata suka yi sallama, shima ya wuce Sashensa don hutawa...
LAMIƊO;
dana sani da kunyane suka lulluɓeshi, ya rasa ta ina ma zai fara, yasan Mahaifiyarsa tana can tana jin biƙin cikin abinda ya aikata..
Daga wajen ɗaurin auren Hotel yayi niyyar wucewa, amma saboda ayi ta taƙare sai ya bi su Faisal zuwa gida..
Irin kukan da ya samu Innarsu da ƴan uwansa suna yi ne ya ɗagamai hankali...
Da ya matsa kusa da ita korarshi tayi tana faɗan ya je ya nemi wata uwar, shima Alhaji Ahmed bayan sun rabu da Baban Fatima ya dawo gida, rantsuwa yayi sai Lamiɗo ya bar masa gidansa..
Har bayan La'asar suna abu ɗaya, Alhaji Ahmed ya kafe, dole sai ya bar mai gida, yaje can ya nemi wasu iyayen...
Daƙyar da saka bakin ƴan uwa da manyan dattawan da suka zo ɗaurin aure daga rugar Innarsu aka shawo kan Alhaji Ahmed ya ƙyaleshi...
Shi da kansa da ya shiga ɗakinsa ya nutsu yayi tunani, sai da yaji wani irin kunyar kansa ya ƙara kamashi, yanzu da wani ido zai kalli Baban Fatima? Duk da a ganinsa hukuncin da ya yanke tsakaninsa da Fatima dai-dai ne, saboda ba zai iya yi mata adalci a zaman aurensu ba, ƙarshe ya ƙare a zarginta...
Yana nan kwance cikin tunanin barci mai nauyi ya ɗauke shi...
FATIMA;
sai bayan Sallah Magriba na farka, fayau na ji jikina da zuciyarta. kamar komai bai faru ba, sai dai babu ƙarfi a jikina..
Aunty Saliha na gani a gefena, da cannula a hannuna, da alama ruwan da aka sakamin ya jima da ƙarewa...
Da taimakonta, na miƙe, ta rakani bakin ƙofar Washroom nayi uzurin da zanyi, har na fito tana tsaye.
Da taimakon na koma kan gado...
Parlo ta fita ta gayawa ragowar ƴan uwa na farka..
Haka suka yi ta shigowa suna yimin sannu, abincin ma haka suka tisa ni a gaba naci, nasha magani..
Ganin yadda suke nan nan dani don na manta da komai, yasa na ɗan saki raina..
Aunty Amarya farfesu mai daɗi ta kawomin, ban taɓa sanin haka take da sauƙin kai da daɗin mu'alama ba, sai a lokacin..
Ita da Baba tisa ni suka yi a gaba da shawarwari da nasihohi masu ratsa zuciya...
Sosai nayi Namijin ƙoƙarin danne duk wata damuwata na saki jikina da ƴan uwa muna taɓa hira har da murmushi..
A daren su Hajiya Babba suka shigo dubani, bayan Baba ya kirata a waya...
Kakarmu haka ta zauna yimin nasihar na kwantar da hankalina..
Sai bayan ƙarfe goma, kowa ya nufi makwanci, ya rage daga ni sai Aunty Saliha a ɗakina..
Sai da na bari barcinta yayi nisa sannan na kira Mama..
Ashe babu wanda ya gayamata abinda yake faruwa...
Ba ƙaramin tashin hankali na jiyo a muryarta ba, bayan gama bata labarin abubuwan da suka faru..
Cikin tausayin dake tsakanin uwa da ƴa take yimin nasihar na daure na dage da addu'a, In Sha Allahu komai zai zama labari...
Sai da barci ya fara ɗaukata sannan mukayi sallama, tana katsewa kiran Baba na shigowa..
Shima dai nasiha ya ƙara yimin tare da umartata nayi addu'a na kwanta...
★washe gari shawara ƴan uwan Mama sukayi, kowacce ta turamin kuɗi masu nauyi daidai gwargwadon samunta a cikin account ɗima, duk don naji sanyi a raina..
Na yi godiya, har Mama da Baba na faɗawa a waya, suma sukayi godiya musamman Baba har sashen shigo ya nuna farin cikinsa ƙwarai..
Bayan kwanaki biyu, ƴan uwa Mama suka tafi, har da ƴaƴan Hajiya Babba, sai ya rage daga ni sai Aunty Saliha..
Itama bayan kwanaki uku ta shirya tafiya washe gari, tare da yimin alƙawarin zata dinga zuwa akai akai tana yimin kwana biyu...
Ranar da Aunty Saliha ta tafi shiru na wuni, cikin tunanin rayuwata, na kwana cikin kaɗaici, ko ringing wayata tayi sai gabana ya faɗi na fara leƙawa ko baƙuwar lamba ce Yaya Lamiɗo ya kirani da ita zai ce ya mayar aurenmu, amma sai naga ba shi ba ne..
Mama kullum sai ta kirani ita da ƴan uwanta..
Aunty Amarya da Baba har da Hajiya Babba kullum sai sun shigo dubani...
Kwana biyu da tafiyar Aunty Saliha nayi wanka, na tsaya a gaban mudubi ina kallon kaina..
A hankali na furta;
"Ba sai wasu sun so ni zan rayu ba, nima na ishi kaina, ba dole sai na rataya farin cikina a wuyan wasu ba, nima zan iya bawa kaina, me zan yarda shi na samu farin cikin da ƙwarin gwiwa mai ɗorewa a rayuwata?..."
Na tambayi kaina..
Murmushi mai tafe da ƙwalla nayi na bawa kaina amsar;
"Yarda da cewar duk abinda yake nawa ba zai taɓa wuce ni ba, ko da ya tafi ko ya gushe wata rana zai dawo gareni"
Kuka na fashe da shi, nayi iya wanda zan iya, har sai da naji ƙwarin gwiwa na shiga duk wasu ƙofofin gashin jikina..
*KUNDINA* na ɗauko, a gaban labarin Salim, na fara rubuta gwagwarmayar dana ƙarasha akan Yaya Lamiɗo zuwa sakina da yayi, kalmar karshen da na rubuta shi ya sani rintse ido "yanzu ni Bazawara ce"..
Na jima rungume da KUNDINA a ƙirjina, ina ƙarfafar kaina ba dole sai da wasu a cikin rayuwata zanyi farin ciki ba.
Wayata na waiwayo na kalla, nayi murmushi, da daa ne da yanzu Yaya Lamiɗo ya kirani ya ji yaya nake... Hannuna na miƙa na ɗauko wayar na goge duk wani abu daya shafi Yaya Lamiɗo kamar yadda nayiwa Sadik da Salim...
Daga wannan rana na ƙudirin niyyar canza rayuwata, zuwa abinda nake muradi daidai gwargwadon yadda addinina ya yarjemin, ba wai nayi rayuwa don wasu suji tausayina ko na birgesu ba...
Innarsu Lamiɗo da ƴan uwansa, har gida suka zo suka duba ni, tare da bani haƙuri..
Innarsa ta ce ita har yanzu kallon ƴa takemin, kar na bari abinda Lamiɗo ya aikata ya shiga tsakaninmu...
Mun jima tare, har tayimin kyautar sarƙa fashion mai kyau.. basu tafi ba sai da Baba ya dawo suka gaisa kamar komai bai faru ba, ta shiga ɓangaren Hajiya Babba da Aunty Amarya suka gaisa..
Har bakin gate na rakosu, muna hira da ƙannensa..
Bayan watanni uku lamura suka shuɗe, kamar babu abinda ya faru...
Lamiɗo ya koma bakin aikinsa, a ɓangaren Salim suna zaune lafiya shi da iyalinsa sai dai ƴar matsalar da ba'a rasa ba..
FATIMA;
A ɓangarena naƙara samun gogewar rayuwa, abubuwan da suka faru da ni, sun zamarmin kamar wani tsanin da ya taimaka wajen gogewata da ƙaramin sanin ƙimar kaina..
Ɗabi'una na makaranta basu sauya ba, bana kula kowa, bana zama a inda mutane suke...
Samun tabbacin dagaske Salim ya bar aiki saboda ni, ba ƙaramin ƙara masa ƙima yayi a idona ba, har nake ganin Gara shi da Yaya Lamiɗo da Sadiq da suka gujeni a lokacin da nake tsananin buƙatarsu..
Ƙwarin gwiwarta ba ƙaramin birge Baba ya ya yi ba....
Ranar babu zato babu tsammani na dawo daga Makaranta Aunty Amarya ta bani mukullin Mota wai inji Hajiya Ni'ima..
Ban ƙara ruɗewa ba, sai da naga motar da ko Baba bashi da irinta..
Dariya su kayi ta yi min ita da Baba, Aunty Amarya tana yimin video..
Mukullin motar na kalla na kalli Aunty Amarya sai kuma a lokacin nake tambayar kaina to wacece ma HAJIYA NI'IMA ai ban santa ba, maiyasa zata yimin kyauta mai girma irin wannan, bayan ban santa ba, ba ta Sanni ba????? ✍🏻
Please kuyi manage, masu comments da like🙏🏻