KUNDINA

34

by @nafisatusasaal01

*KUNDINA*

*SASAAL*
***


34



FATIMA;
Mukullin motar na kalla na kalli Aunty Amarya, sai a lokacin na tambayi kaina to wacece ma Hajiya Ni'ima? ai ban santa ba, to amma maiyasa zata ba ni irin wannan kyautar mai girma, bayan bata sanni ba, ban santa ba???

Nutsuwa nayi na matsa kusa da Aunty Amarya, nayi mata godiya, Fuskata har lokacin ƙunshe da murmushi na ce;

"Aunty, Hajiya Ni'ima ita ma ƴar uwarki ce, maiyasa ta yimin kyautar mota irin wannan?"

Sai a lokacin Aunty Amarya ta katse videon da take yi, tana dariya ta ce;

"Mahaifiyata ce, ta baki kyautar mota ne don ki dinga zuwa Makaranta da shi ko Alhaji?"

Ta ƙarasa faɗa tana kallon Baba.. shima murmushi yayi ya ce;

"Ƙwarai dagaske, ko baki yarda ba"

Ya faɗa yana kallon yadda nayi zuru da ido ina kallonsu, kamar wacce za'a siyar..

Da ƙyar na ɗaga kaina da yayimin nauyi alamar na gamsu..

Yadda nayi da kaine yasa suka kwashe da dariya.

 Aunty Amarya tsagaita dariya tayi ta ce naje na huta, idan nayi wanka naci abinci zuwa dare nazo ta haɗani da Hajiya Ni'ima nayi mata godiya..

"To" na ce mata ina ɗamke makullin motar gam a hannuna..

Kafin na bar wajen sai da na ƙara waiwayawa na kalli dunƙulallen motar da ya tafi da nutsuwata...

A hanya ina tafe ina mamakin meyasa zata bani irin wannan kyautar? Da Baba shahararren mai kuɗi ne sai nace tayine don birgiya..

Amma Baba ba wani mai kuɗin azo a gani bane, sa'arsa ɗaya, ƙaton filin daya siya tun duniya na kwance.
kuma shi mutum ne mai ƙoƙarin gyara muhalli, domin duk girman Harabar gidanmu lallaye yake da interlock..

Motarsa ƙirar Honda ce ta zamani daidai misali, haka wanda ya siya tun duniya na kwance ya samo driver domin yin cefane da kai Yara makaranta ita ma dai ƙirar Honda ce, Hajiya Babba ce Yaya Abba ya siya mata 307 ya ɗaukar mata driver sai maigadin da ya samo domin sauƙaƙa buɗe gate... Masu aikin sashenta kuma su Aunty Ummi da Aunty Safiyya ne suke ɗaukar nauyinsu..

Farida ma sai da ta fara aiki ta siyawa kanta 206 sabo, Aunty Amarya ce kawai take jan Mota mai nauyin kuɗi, don ita duk shekara ma danginta suke canza mata Mota..

Da ire-iren saƙe-saƙen nan na iso sashena na buɗe na shiga..

A gefen drawer na ajjiye mukullin motar na fara shiga wanka..

Ina fitowa sai da na kalli gefen drawer na ga dai har lokacin makullin yana nan..

Daga lokacin da na shigo Sashena zuwa bayan Sallar Magrib na leƙa mukullin motar yafi a ƙirga..

Ban tsaya ɓata lokaci ba, ina idar da Sallar Magrib na ci abinci na zura Hijjabi nayi sashen Aunty Amarya...

Ban jima ina ƙwanƙwasawa ba, matashiyar mai aikinta ta buɗemin.. da fara'a a fuskokin mu muka gaisa, sannan na fara tafiya  a siriri coridor dake tsakanin ƙofar buɗewa da parlonta, mai yi mata hidima ta kullo ƙofar tana bina a baya..

Da sallama na taka ƙafata cikin lallausan carpet ɗin da aka ƙawata Parlonta da shi.


A zaune na sameta cikin ado kamar kullum, duk da ba ranar girkinta ba ne..

Fuskarta ba yabo ba fallasa kamar yadda nasan ainihin Fuskarta muka gaisa..

Wayarta ta janyo, ta danna kira, ba jima ba, naji tana magana da harshen fullanci, can ta juye wani yaren da ya surka da kalmar Larabci ɗaya-ɗaya a ciki..

Abun sha da na motsa baki mai aikinta ta kawomin...

Ba don ina jin ƙishi ba, sai don na ƙara samun nustuwa na ɗauki lemo na kurɓa..

Ina can tunani na ji ta ce ;

"Fatima gashi"
Karɓa nayi kaina a ƙasa, kamar wacce take magana akan wayar tana kallona..

Gaisheta na fara yi, ta amsa murya a sake, bata bari na fara zubomata godiya ba, ya dakatar da ni da cewa;

"Yaya karatu?"

Kaina a ƙasa na ce "alhamdulillah"

Kafin na ɗora da Godiya ta ƙarar tarar numfashina da cewa;

"ina fatan kin cire komai a ranki, dama kuma shi aure lokaci ne, ga Mota nan ki dinga zuwa Makaranta, in sha Allahu next month za'ayi bikin ɗana Sarfaraz, zaku taho tare da Auntynki Hanifa, tunda tace kin ce baki gane ni ba"

Murmushi nayi kunya ya kamani, duk da haka dai ban haƙura ba na fara zubo mata godiya;

Katseni tayi ta saki dariyarta mai daɗin sauraro, cikin zolaya ta ce;

"Ohh Allah, Fatima wannan godiya haka, anya ba Company sai da motoci ma zan buɗe miki ba"


Ban san sanda na saki dariya ba, har da Aunty Amarya dake ɗan jiyo sautinta..

Tsagaita dariyarta tayi ta ce;

"Ki mayar da hankali kan karatunki kin ji, ina so naga canji a tare da ke duk ranar da zan ƙara ganinki, kuka ba naki ba ne.

Tunda muka dawo Lagos nake tunanin halin da muka baroki a ciki, Allah Ya sa ƙarshen wahalar kenan, yanzu kije ki kwanta, zan karɓi lambarki na kiraki da layina ki turamin account number na saka miki kuɗin mai, ko kuma bawa Auntynki wayar muyi magana"

Kafin na miƙawa Aunty Amarya sai da dai nayi godiyar da ya zamemin ɗabi'a..

dukkansu dariya suka saka..

Ban baro sashen ba, sai da suka gama waya, Aunty Amarya ta karɓi account ɗina...

Ina tafe bakina a washe, kamar ban taɓa shiga damuwa ba a baya..

Ina shiga Sashena inda na ajjiye mukullin motar na nufa, naga dai dagaske yana nan, dariya na saki ina riƙe haɓa..

Kafin na sauke hannuna daga kan haɓata saƙo ya shigo wayata, alert ɗin dubu ɗari biyar na gani daga asusu Ni'ima Ali Muzzafar ..

Tsabar daɗi ranƙwashin kaina nayi, ina dariya..

 Mama na kira hannuna yana rawa..

Ban tsaya mun gaisa ba, na bata labarin alherin da ƴar uwar Aunty Amarya tayi min.


 Farin cikin da na daɗe ban ji a muryarta ba naji, addu'an tsari ta shiga yimin, Sannan tace zata bari da safe ta kira Aunty Amarya tayi mata godiya..

Bayan mun gama waya, kasa jurewa nayi na nufi sashen Baba...



HAJIYA BABBA;
tunda lamura suka lalace Yaya Abba Ɗanta namiji ya kira yana ta faɗan karsu ƙara shiga duk wasu al'amuran da suka shafi Fatima..

Shi ba ya son tashin hankali.. 

Samunsa da irin gatan da yake yiwa Hajiya Babba ne yasa ta ƙudiri niyyar watsi da komai..

Farida ma kafin su Aunty Ummi su tafi, sai da suka yi mata faɗan babu ruwanta da duk wani abu da ya shafi Fatima, aure lokacine, idan itama lokacinta yayi sai ta ga itama Allah Ya bata irin mijin da take buri.. 

Ba don suna so ba, suka tattara lamarin Fatima suka watsar..

Ranar da driver Hajiya Ni'ima ya tuƙo motan Fatima zuwa gidan, Hajiya Babba bata nan taje Unguwa, haka ma Farida tana wajen aiki, kuma ko da suka dawo basu kowa tunanin na Fatima bane.

Tun da zuwa da tsalatsalan motoci gidan daga dangin Aunty Amarya ba sabon abun ba ne a wajensu..

Ko da dare yayi Hajiya Babba ta zo shashen Baba, bai yi mata maganar an bawa Fatima kyautar mota ba, saboda yasan halinta na baƙin kishi..

Suna ƴar hirarsu sama-sama Fatima ta ƙwanƙwasa ƙofa, dukkansu wajenta tunaninsu yaje, domin ita kaɗai ce mai yi masa irin wannan zuwan idan tana da uzuri..

Hajiya Babba dannar zuciyarta tayi ta tashi ta buɗe mata ƙofa...

FATIMA
Ban lura da yanayin fuskar Hajiya Babba ba, saboda farin cikin da nake ciki,  gaisheta nayi haɗe da kullo ƙofar na wuce inda Baba yake zaune..

Daƙyar na nutsu na gaisheshi hannuna yana rawa na nuna masa wayata...

Baba dariya nishaɗi ya saki, ya ce;

"Masha Allah, Allah Ya haɗa jininku da Hajiya Ni'ima, Allah Ya ƙara mata buɗi"

Bakina a washe nace;

 "Amin"

Baba dariya ya ƙarayi yana kallon irin farin cikin da nake ciki ya ce;

"Anya yau zaki iya barci kuwa Fatima?"

Kunya ce ta kamani na ɓoye Fuskata ina dariya.

Shima dariya ya yi yace;

"Tashi kije ki kwanta, gobe da kaina zan kaiki inda zaki fara koyan Mota, Kinga kin huta da hawa tsohuwar mota"

Dariya na saki na miƙe ina yi masa godiya.

 Sai da safe nayi musu amma Hajiya Babba bata amsa ba..

Ko kallon gefenta banyi ba na bar sashen...


HAJIYA BABBA; Fatima tana fita ta huro matsakaicin hancinta ta ce;

"Alhaji me nake ji haka? Mota ka siyamata baka siyawa Farida ba"

Kasaƙe Baba yayi yana kallonta, bai taɓa ganin mace mara hikima da rashin iya magana ba irinta..

Bai bata amsa ba, ai kuwa ta fusata tana faɗin;

"Wallahi bazan yarda da irin wannan rashin adalcin ba, ai ba wani ne ya saka Fatima fitar da tsaraicinta ba, da har kake shirin yin rashin adalci a tsakaninta da Farida, kuma idan motar ce ma, ai Farida da ta riƙe mutuncinta ya kamata a siyawa ba Fatima ba"

Kamar dutse haka Baba ya shiru, kamar ma ba da shi take ba...

Baƙin cikine ya isheta ta fasa kuka, haɗe da ɗaukar wayarta ta nufi ƙofar fita..

Baba bai yi niyyar kulata ba, amma gudun kar ta je tayi ɓarna yasa ya bi bayanta..

Hajiya Babba kamar zata tashi sama haka ta nufi kitchen ɗin Sashenta, ɗunkulallen taɓaryar daka ta ɗauko.. a kan hanyarta na zuwa Harabar ajjiye motocin gidan suka haɗu Baba..

Fuskarsa a ɗaure ya ce;

"Saratu ina zaki je?"

Banza tayi mai ta cigaba da tafiya yana bin bayanta..

Tana isa wajen idonta ya sauka kan motar da ta gani da rana, kenan shine motar Fatima, Fatiman dai data sani..

A guje kamar sabuwar kamu ta nufi Motar.

 Baba shima yabi bayanta a guje yana ihun kiran;

"Saratu! Saratu!! Saratu!!! Ki tsaya, ki tsaya anan nace"✍🏻