35
*KUNDINA*
BY
*NAFISATU ALIYU SASAAL*
***
35
"Saratu! Saratu!! Saratu ki tsaya!!! ki tsaya nan nace"
Hajiya Babba banza tayi mai, bata tsaya ba, kamar ma bata jinsa, har sai da ta cimma Motar.
Da iya ƙarfinta ta ɗaga taɓarya zata rotsawa gilashin motar, Baba da yake dab da bayanta yayi hanzarin miƙa hannunsa dukka biyun ha hankaɗata gefe, taɓarya ta faɗi ƙasa..
Ba ƙaramin zafi taji ba, cikin kuka raɗaɗin da kafaɗarta yake mata da rashin samun nasarar fasa gilashin motar ta ce;
"Alhaji ni zaka kashe saboda Fatima? Da shekaruna da ƴaƴana, kenan ban isa na ɗauki mataki ba idan anyimin rashin adalci"
Cikin takaici Baba ya kalleta ya ce;
"Ban taɓa ganin mace mai irin halinki ba Saratu, baki tambayi wanene ya siyawa yarinyar nan mota ba, kawai ki yanke hukunci fasa mata gilashi.
Duk ba ma wannan ba, yanzu idan ni na siyawa Fatima mota abinda zakiyi kenan?"
A fusace ta ce;
"Wanda yafi haka ma zanyi Umaru"
Baba wani iri ya ji yanda ta ambaci sunansa kai tsaye, rabonsa da jin haka daga bakin matansa har ya manta.. bai ce mata komai ba, ya kamo hannunta da ƙarfi..
Yana tafe janye da hannunta har Sashenta, suna zuwa ya fara bubbuga ƙofar da ƙarfi...
Farida muryarta a hargitse take tambayar;
"Waye?"
Jin muryar Hajiya Babba cikin kuka tana cewa;
"Farida buɗemin, ni da Alhaji ne, so yake yi ya kasheni don nayi maganar motar da ya siyawa shashelelensa"
Da firgici biyu Farida ta buɗe ƙofar, na ɗaya kukan Hajiya Babban da ta jiyo, na biyu kuma batun siyawa shashelelensa mota..
Tana buɗewa taga Baba a tsaye damƙe da hannun Hajiya Babba..
Jikinta a sanyaye ta basu hanya..
Sai da Baba ya shiga Farida ta kullo ƙofar..
muryarsa a kausashe ya bawa Farida umarnin ta kira mai Abba..
Hajiya Babba kuka ya fasa tana cewa;
"Ni zaka haɗa faɗa da ƴaƴana, bayan baƙin cikin da ka ƙunsamin"
Baba bai tanka mata ba..
Farida ɗakinta ta koma ta ɗauko wayarta.. ba don ta so ba da dawo parlon ta kira yayanta..
Ringing ɗaya Abba ya ɗaga, mamakin jin Muryar Baba a wayan Farida bayyane a muryarsa.
Sosai Baba ya danne ɓacin ransa suka gaisa, sannan ya yi masa bayanin alherin da Hajiya Ni'ima tayiwa Fatima dalilin tausayinta da ta ji, shine ita kuma mahaifiyarsa ta ɗauki taɓarya zata fasa gilashin motar..
Ya kirashi ne, don su jawa Mahaifiyarsu kunne, kar ya yanke mata hukuncin da bazasu ji daɗi ba, banda shirme irin nata yanzu ko Hanifah idan taji labarin abinda ta aikata, ai sai mutuncinta zube, bama iya Hainfa ba har ƴan uwan da suke zuwa gaisheta..
Abba rasa abun faɗa yayi sai haƙuri da yake ta bawa Baba, har suka yi sallama Baba ya bar sashen..
Yana fita Farida ta fasa kuka, tana yi Hajiya Babba nayi aka rasa mai lallashin wani, duk kiran da Abba yake yi basu ɗaga ba...
Sun ɗauki lokaci mai tsaho suna kuka, kafin su tsagaita, Hajiya Babba ta bawa Farida labarin motar dai da suka gani da rana wai shine motar Fatima...
Farida tana jin haka ta sulale ƙasa, kamar wacce ta tayar da aljanu..
Haka suka sha fama da baƙin hassada a wannan dare, kafin ɓarawon barci ya ɗauke su...
FATIMA;
kwanan farin ciki nayi, har mafarki nayi gani ina tuƙa motata naje shan ice cream..
Tsabar daɗin barci, ban farka ba sai da aka idar da sallar Asuba...
Kafin na sauko daga kan gado sai da na fara kallon gefen drawer naga dai makullin motata yana nan lafiya ƙalau, sannan na sauko ina murmushi, na wuce Washroom..
Kamar yadda Baba yayi alƙawari, bayan na gama karyawa ya kirani a waya na fito ya kaini wajen koyan Mota..
Cikin zumuɗi na shirya, nayi kwalliya.. sai da na fara biyawa Sashen Aunty Amarya nayi mata godiyar kuɗin da Hajiya Ni'ima ta turomin tukunna na wuce wajenshi.
Da fara'a da ban saba yi ba, na gaishe shi ina matsawa kusa da motar..
Baba amsawa yayi yana murmushi yadda nake ta matsawa kusa da motar alamar dai tawa ce..
Muna haɗa ido kunya ya kamani na rufe Fuskata ina dariya..
Shima dariya ya saki.. yana tsokata da "Hajiya Fatima mai mota"
Da Bismillah Baba ya buɗe motar muka yi addu'a muka shiga..
Baba ne ya ja Motar, mu na tafe muna hirar mu gwanin sha'awa..
FARIDA;
tsabar hassadar da ta kwana da shi da zazzaɓi ta tashi, ko wajen aiki kasa zuwa tayi..
Abinci ma sai da Hajiya Babba tayi mata faɗa kamar zata daketa sannan taci, tana kukan ita kowa ya tsaneta..
Basu daɗe da gama karyawa ba, Abba ya ƙara kiran layin Farida..
Hajiya Babba ce ta ɗaga, suna gaisawa kafin yayi ƙorafin abinda Baba ya ce tayi, ta dakatar da shi, ta hanyar shirya masa ƙarya da gaskiya.
Acewarta kawai Baba ya ɗora dangin Hanifah a bakine dan kar su ga laifinshi, banda haka yaushe dangin Hanifah ma suka san Fatima, da har zasu yi mata kyautar mota..
Ba don Abba ya gamsu ba, ya yi mata nasiha cikin hikima suka yi sallama..
Ranar wuni Hajiya Babba tayi tana waya da ƴaƴanta mata.. ko abincin rana tsakurarsa suka yi, saboda damuwar da suka ɗorawa ransu..
Farida har lallaɓawa tayi ta fito harabar gidan, ko zata ga motar, amma taga wayam, hakan ba ƙaramin sosa mata rai yayi ba..
FATIMA;
Bamu jima ba muka isa Makarantar koyon motar ɗan abokin Baba..
Bayan sun gama magana, muka ɗan yi zaman lokaci aka kirani...
Sawa raina son koyon motar da wuri yasa a ranar nayi ƙoƙarin iya abubuwa da ɗan dama...
Baba tafiya ya yi, sai bayan wani lokaci ya dawo muka tafi gida..
Duk damuwar da su Hajiya Babba suke ciki babu wanda ya sani, sai Baba shima kuma bai gayawa kowa sai ni da ya jamin kunnen na kiyaye na kuma dage da addu'a...
Ni dai ko a jikina, muna dawowa gida nayi wanka naci abinci..
★Washe gari da ya kama Asabar, da driver Baba ya haɗani, muka je muka dawo..
Ranar Lahadi ma haka mukayi.
Duk motsin Fatima da zuwanta Makarantar koyon mota su Hajiya Babba suna da labari.
Adashi ta yanke shawarar shiga, idan lokacin ɗaukarta yayi dukka ƴaƴanta kowa ya kawo abinda yake da shi a haɗa a siyar da 206 ɗin Farida a siyamata ita ma mai tsada..
Wannan shawarar na Hajiya Babba shi ya sassauta baƙin cikin zuciyar Farida ta saki jikinta, amma duk lokacin data zo fita aiki tayi ido biyu da motar Fatima sai taji wani abu a ranta..
***********************************
Kwanci tashi a cikin sati shida na iya Mota amma ba sosai ba, dalilin yawan fashin da nake yi saboda zuwa makaranta...
"Learner(L)" Baba ya maƙalamin na fara zuwa Makaranta dashi..
Ranar ji na nayi kamar sarauniya, babu tsoro cike da nutsuwa na tuƙa kaina har Makaranta..
Burina na samu ƙwarewa naje har Gaya na ɗauki Mama muje yawo...
A makarantar duk da ba ma magana mai tsaho da ƴan ajinmu da yawa sun tayani murna, har da zan dawo na rage wasu hanya..
A ranar da Daddare bayan na dawo gida Aunty Amarya ta kirani a waya na zo tana son ganina a sashen Baba..
Gabana yana faɗuwa bayan nayi sallar Magrib na tafi a Sashen..
Ina ƙwanƙwasawa Baba ya buɗe, shi kaɗai na samu a parlon, na gaishe shi, fuskarsa a sake ya tambayeni;
"Allah Ya sa ba motarki ce ta samu matsala ba, don na san bakya yimin zuwan bayan Magrib idan ba matsala ce da ke ba"
Murmushi nayi a ladabce na ce;
"A'a Baba dama Aunty ce tace nazo tana son ganina"
Kafin ya kai ga bani amsa, muka ji an saka mukulli an buɗe sashen..
Ƙamshinta ne ya cika parlon, tayi adonta cikin material mai kyan da ya haska kyanta..
Fuskarta kamar kullum ba yabo ba fallasa ta ƙaraso, ni kam tsabar gulma hankalina yana kan Baba ina kallon yadda yake kallonta..
Ban ankara ba, sai da naji tace;
"Fatima har kin zo, na barki kina jira na tsaya uzurine"
Gaisheta na yi ina murmushi..
Ta amsamin cikin kulawa tana tambayata yaya Mota da karatu..
"Alhamdulillah" na ce ina gyara zamana..
Sai da ta zauna ta nutsu, sannan ta kalli Baba ta ce;
"Baban yara dama na kira Fatima nan ne, domin na roƙi alfarmarka tafiya da ita Yola da Lagos bikin Sarfaraz Cousin ɗina ɗan Mama Ni'ima, ƙarshe mako mai zuwa zamu tafi, sati ɗaya kawai zamu yi mu dawo"
Baba Jinjina kai ya yi yana ƙara jin sonta da ƙimarta a ranshi, amma ba zai so ace da Fatima kawai zata tafi ba, don haka ya yi gyaran murya ya ce;
"Ina jin daɗi ƙwarai yadda kika ɗauki Fatima ke da ƴan uwanki, Allah Ya saka muku da alkhairi ya raya musu zuri'arsu kema Allah Ya baki masu albarka..
Sai dai wani hanzari ba gudu, tafiya da Fatima ita kaɗai, bana jin zai haifar da zaman lafiya tsakaninki da abokiyar zamanki, duba da irin alkhairin da ƴan uwanki suke yawan yi mata, duk zuwa basa gajiya da zuwa gaisheta da yi mata hidima, ina ganin idan babu takura mai zai hana ki tuntuɓeta zuwa bikin itama idan zata je, kar ta ce kun wareta"
Aunty Amarya numfasawa tayi, domin itama tayi irin wannan tunanin, amma sanin halin Hajiya Babba na son tada fitina ba tare da la'akari da abinda zai zubar mata da mutunci ba yasa bata tuntuɓeta, amma tunda Alhaji yayi Magana zata tuntuɓeta ta ji..
Ganin tayi shiru kamar mai tunani yasa Baba ya ƙara cewa;
"Ba ina takura miki ba ne, idan kina ganin akwai matsala kawai ku yi tafiyarku"
Aunty Amarya kai ta girgiza ta ce;
"In sha Allahu gobe zan tuntuɓeta naji mai zata ce"
Murmushin jin daɗi Baba yayi ya ce;
"Na ji daɗi Maman Yara, Allah Ya ƙara arziƙi"
Murmushi tayi ta amsa da "Amin"
Ina saurarar dukka hirarrakinsu kaina a sunkuye, daɗi duk ya isheni zanje Lagos da Yola biki...
Baba cewa yayi na je na kwanta, Aunty Amarya dakatar da ni, tayimin bayanin gobe na kawo mata size ɗin kayana, za'a kai min ɗinkin anko..
Godiya nayi mata ina dariyar jin daɗi, shima Baba ya ƙara yi mata godiya da addu'ar buɗi mai albarka..
Sai da safe nayi musu, na bar sashen..
Ina tafe ina hasaso kaina a cikin dangin Aunty Amarya..
"Anya zanyi kyan fasali kuwa" na tambayi kaina, ba wai don ina da muni ba, kyakkyawace ni, sai dai su nasu kyan, kyau ne da ya haɗe da dumbin dukiyar da yasa wasun su suka yi siffa da ruwa biyu..
Har na shiga Sashena na yi kimtse-kimtsen da zanyi na kwanta, bai daina hango kaina a cikin danginsu Aunty Amarya ba...
HAJIYA BABBA;
★washe gari da safe tana zaune, Farida ta tafi wajen aiki, Aunty Amarya ta zo sashenta..
Mamakine ya kama Hajiya Babba, a ranta tana addu'ar Allah Ya sa lafiya, don rabon Hanifah da sashenta tunda ta rako ƴan uwanta suka gaisheta Lokacin bikin Fatima..
Ba yabo ba fallasa suka gaisa, Hajiya Babba da kanta, ta je kitchen ta kawo mata lemo da ruwa da kayan motsa baki...
Ruwan gorar kawai Aunty Amarya ta ɓalle ta tsiyaya a kofi ta ɗan kurɓa, bayan shi bata taɓa komai ba..
Sai da ta nutsu kamar yadda ɗabi'arta yake a yawanci lokuta sannan ta yiwa Hajiya Babba bayanin bikin Sarfaraz da ya kawota..
Baki Hajiya Babba ta washe tace;
"Haba Hanifah, idan ban je bikin nan ba, ai ban kyauta ba, alkhairin ƴan uwanki kaɗai ai abun dubawa ne..
Ina sha Allahu ni da Farida zamu yi shirya, Allah Ya kaimu lokaci"
Aunty Amarya murmushi tayi, ta ce;
"Amin"
Daga haka suka yi sallama..
Tana fita Hajiya Babba ta miƙe ta kasa zama, ji tayi kamar zata je wata duniyar da zata yi arziƙin da ita da talauci har abada...
Kasa jurewa tayi ta ɗauki wayarta ta kira Farida ta nemi izini a wajen aiki, ta dawo gida..
Farida ta ɗauka wani mugun abin ne ya samu Hajiya Babba, don haka tayi ƙaryar mahaifiyarta Babu lafiya ta kamo hanyar gida...
A tsaye ta samu Hajiya Babba tana zarya..
Hankalinta a tashe ta iso gareta tana tambayarta;
"Hajiya lafiya? Menene ya sameki? Baba yayi miki wani abun ne?"
Hajiya Babba kai ta girgiza ta kamo hannunta suka zauna..
Albishir ɗin gayyatar da suka samu daga Aunty Amarya tayi mata..
Zabura Farida tayi ta miƙe, ta kama siririn hancinka ta shiga rangaɗa guɗa, tana taka rawa..
Hajiya Babba dariya ta shiga ƙyaƙyalawa har tumbin cikinta na motsawa....
Yaya kuke ganin wannan tafiyar anya za'a kwashe ta daɗi kuwa, me kuke hasashen zai faru???✍🏻