KUNDINA

36

by @nafisatusasaal01

*KUNDINA*

*NAFISATU SASAAL*
    ***



   36


FATIMA;
Gaba ɗaya mantawa nayi da batun kayana da Aunty Amarya tace na kai mata, sai da na isa Makaranta..

Kamar dai Jiya, haka na ragewa wasu ƴan ajinmu mata hanya da zan dawo gida..

Da misalin ƙarfe ɗaya da rabi na ƙaraso gida.

 Ina shiga Sashena ko zama banyi ba, na ɗauki riga da siket ɗina na zurasu a leda mai kyau na nufi sashen Aunty Amarya..

Mai aikintace ta buɗemin, ta shaidamin tana barci, ban koma da kayan ba, na miƙa mata nace ta bata idan ta tashi...


Ina dawowa Sashena nayi wanka na ci abinci nayi Sallah, barci mai nauyi ya ɗaukeni..

Ban farka ba, sai dab da La'asar, ina nan kwance aka fara kiraye-kirayen sallah..

Jikina babu ƙarfi na miƙe na ɗoro alwala, na dawo parlo na shimfiɗa dadduma na tayar da Sallah..

Ina idarwa na kwanta akan daddumar barci ya ƙara ɗaukeni, ban farka ba sai biyar da ƴan mintina..

Gaba ɗaya ji nayi jikina babu daɗi, don haka na yanke shawarar na ɗan fita na siyo kayan motsa baki..

Kafin nayi wanka na kimtsa na kira Baba don  neman izini..

Tambayar da ya fara yi min shine a ina na samu kuɗin da zan je nayi siyayya?

Bayani nayi masa akan kuɗin da Hajiya Ni'ima ta bani ko rabi ban kashe ba..

Shiru yayi na sakanni, kamar bai gamsu ba, sai kuma can yace;

" bari ya sakamiki dubu biyar ki yi maneji"..

Godiya nayi mai, ina dariya..

Kafin ya katse ya ja min kunnen kar na yi dare, sannan muka yi sallama..

Ban motsa daga inda nake zaune ba, kuɗin Baba ya shigo.. duk da basu da yawa ba ƙaramin daɗi na ji.

Wannan yasa na tashi ina jin karsashi a jikina nima Babana ya bani kuɗin shan ice cream..

A cikin ɗikunan bikina na ɗauka riga da siket na saka. Ba ƙaramin kyau yayi min ba, a nutse na zauna nayi ɗaurin da ya kwanta a kaina, kwataccen gashin goshina ya taimaka ƙwarai wajen fidda kyan da fuskata tayi..

Mayafi matsakaicin da zai shiga da atamfar  na ɗauko na yafa..

Jaka da Takalmi su ma iri ɗaya na ɗauko da zasu shiga da atamfar.

Turare na ɗauko na fesa kaɗan, sannan na ɗauki mukullin motata na kullo sashen..

Ni kaina nasan nayi kyau.. kamar yadda naga mata masu aji suke hawa mota haka nayi, hankalina kwance na tashi motata na bar gidan..

Tsakanin gidanmu da gidansu lamiɗo babu nisa, gidan su na farko layi, mu kuma namu yana ƙarshe..

Ina zuwa daf da gidansu, motarsa tana fitowa, don ya ganni dakyau nayi kyau na yi ƙasa da gilashin motata..

Na ɗauko wayata na kara a kunne kar ya ma saka ran zan gaisheshi..

Magana nake yi, ina sakin murmushi kamar gaske..

Zan gifta bayan motarshi, yayi sauri ya ziro kai ta window motarsa da ƙarfi ya ce;

"Fatima"

Maimakon na tsaya kamar yadda na fahimci yake nufi, sai kawai na leƙo na ɗagamai hannu na ƙara gaba.. wayata na ajjiye ina ƙyaƙyala dariya raina fari fes, har wani ƙwari nake ji a jikina...

Ina hango motarsa tana bin bayan nawa, amma nayi fuska na cigaba da tuƙina hankali kwance..

Wani waje mai kyau na hango ana sayar da ice cream da ƙananun kayan ciye-ciye kana gani kasan zai yi tsada.. 

Ban tsaya dogon nazari ba, kawai nayi kwana na shiga wajen..

Yaya Lamiɗo shima kwana yayi, ya shigo harabar wajen..

Ban fito ba sai na jima tukunna.. duk Yaya Lamiɗo ya fito daga motarsa yana tsaye yana jirana..

Kamar yadda muka saba kafin mu fara soyayya haka na gaishe shi.. zai ƙarayimin magana nayi gaba na barshi a tsaye..

Har ya fara bina kome ya tuna, sai kuma naga ya juya.. daga nan ban ƙara ganinshi ba..

Waje na samu na zauna kamar wacce dama can ta saba zuwa...

Abinda nake so, na saka aka kawomin..

Ina nan zaune har shida tayi, sai da na bari shida da kwata sannan na miƙe... Ana kiraye-kirayen sallah Magriba na isa gida..


Ko zama ban yi ba, na kira Baba na faɗa masa na dawo gida..

Ban tuna haɗuwarmu da Yaya Lamiɗo ba sai da na zo kwanciya, tsaki mai ƙarfi naja, ina tambayar kaina ko me zai gayamin oho..

Hankalina kwance nayi barci...



LAMIƊO;
tunda ya hango Fatima a cikin mota, ya ji daya sanin da bai ji ba tun bayan sakinta da yayi. Wannan dalilin yasa ya yanke shawarar binta a baya.. ya na ganin kamar lokaci yayi da zasu sasanta tsakaninsu...

Bai yi tsammanin Fatima ta samu gogewar da zata shareshi ba, shiyasa ya yi tunanin ko ya koma gida kar ta wulaƙantashi a gaban jama'a..

Fasa zuwa inda yayi niyya, ya dawo gida wajen Innarsu..

A Parlo ya sameta, da mamaki a saman Fuskarta ta ce; 

"Lafiya ka dawo gida?"


Ƙeyarsa ya sosa ya ce;

"Dama yanzu naga Fatima, nayi mata magana bata tsaya ba, kuma na bi bayanta bata saurareni ba, shi nace na zo mu yi magana dake, ki taimaka ki yiwa Baba magana"

Kasaƙe tayi kamar wacce bata fahimtar abinda ya ke cewa, can ta nisa tace;

"Ita wacece Fatiman? A ina kuma ka santa? Kaga rabani da wannan shirmen zancen naka, miƙomin wayata na kira ƴar uwarka, ɗazun ta kira ni ba na kusa"

Ya na miƙo mata wayar ta karɓa ta haye sama, ta barshi da sakakken baki..

Bashi da zaɓi dole haka ya ƙara barin gidan, yana saƙe-saƙen yadda zai ɓullowa lamarin..


FATIMA;
★washe gari, da yake ba ni lecture ban nemi abin kari da wuri ba.. da misalin ƙarfe 11 Aunty Amarya ta kirani a waya, bayan na gaisheta ta amsa, ta shaidamin  na shirya zan rakata wani waje..

Tana katse wayar, na shiga kitchen na ɗora indomie a gurguje, kafin ya dahu na shiga wanka..

Shima ban ɓata lokaci ba na fito, Indomie na fara zuwa na sauke na zuje a plate..

Kafin ya huce nayi sauri na shirya cikin Abaya ruwan ƙasa..

Sai da na gama komai sannan na ɗauko lemo mai sanyi a fridge, na zauna naci da Indomie na ina santin daɗin da yayimin..

Bayan na gama na gyara bakina, na zura takalmi, ba ɗauki jaka ba, a hannu na riƙe wayata..

Ina zuwa Sashenta itama tana fitowa..

Bata gayamin inda zamu je ba, tayi gaba ina bin ta a baya, muka shiga mota..

Wajen gyaran jiki mai kyau da tsada muka je..

Kamar yadda aka yiwa Aunty Amarya gyaran jiki, nima haka akayimin, anan ta nemi me zuwa gida kullum da yamma tana yi mana, saboda ina zuwa makaranta ita kuma bazata juri zuwa kullum ba..

Kuɗi mai yawa suka gayamata, ta biya nan take, muka fito daga wajen jikinmu fes sai ƙamshi muke yi..

A wajena sabon abune don ko lokacin bikina Aunty Saliha ce ta yimin, ban samu gatan zuwa wuri irin wannan ba..

Bamu dawo gida kai tsaye ba, sai da ta biya damu wajen siyyaya ta siyamin mayukan shafawa da shower gel masu kyau da tsada..

Bata siyawa kanta komai ba, sai apple da ta ɗiba da yawa..

Tun muna hanya nake mata godiya tana dariya, acewarta yawan godiyata dariya yake bata..

Muna zuwa gida na hango motar Baba, ban tafi Sashena ba, na nufi sashen Baba da gudu.. Aunty Amarya ta bini da kallo tana dariya.

Na yi sa'a a buɗe sashen yake, shi da Hajiya Babba suna zaune ita tana waya shi yana cin abinci..

Da tsananin farin ciki na gaisheshi, ina miƙa masa ledar hannuna..

Abinci da yake ci ya matsar gefe, ya karɓi ledan yana murmushi..

"Masha Allah, nasan wannan aikin Hanifah"

Baba ya faɗa yana kallona..

"Baba har gyaran jiki ta kaini"

Na ƙarafa faɗa ina nuna masa gefen Fuskata..

Dariya nishaɗi Baba ya kwashe da shi, yana jin daɗin yadda Fatiman take sakin jiki da shi tun bayan fasa bikinta da lamiɗo..

Fuskarta ya kalla ya ga da gaske tayi kyau, sai dai kafin ya tofa Hajiya Babba da gama wayar ba jimawa ta cika tayi fam ta ce;

"Ke wai baki da kunyane, kin shigo sakaka ko gaisheni baki yi ba, banda lalacewa mahaifinki kike cewa ya kalli fuskarki, ikon Allah"

Ta ƙarasa faɗa kamar zata taune harshenta..

Ƙasa nayi da kaina na gaisheta, ta amsa a daƙile...

Baba bai tofa ba, ya miƙomin ledata ya ce naje na huta, zai je har sashen Hanifah yayi mata godiya..

Da sauri Hajiya Babba ta ce;

"Ba dai yau da yake ranar girkina ba, wallahi Alhaji na rasa yaushe zaka fahimci Hanifah son raba kan ƴaƴan nan take yi, idan ban da haka tayaya zata tafi da Fatima gyaran jiki ta ware Farida"

Murmushi Baba ya yi ya ce;

"To ke da kike son haɗa kan nasu, gobe sai ki shirya ki kaisu tare a yi musu, ki samu lada, ko kuma bari na kira Hanifah a gabanki ki tambayeta dalilin dayasa take son raba mun kan Yara, Kinga sai na ɗauki mataki"

Tana jin yace haka, sai ta saki Fuskarta ta ce;

"Ni fa ba haka nake nufi ba, karka canzamin magana"

Baba ƙunshe dariyarsa yayi ya cigaba da cin abincinsa..

HAJIYA BABBA; A daren ta kwashe dukka kuɗin asusunta, ta turawa asusun Farida itama washe gari ta fara zuwa ayi mata gyaran jiki...


FATIMA; bata damu da abinda Hajiya Babba tayi mata ba, tana zuwa Sashenta tayi wanka da sabon shower gel ɗin da Aunty Amarya ta siya mata, bayan ta fito ta mulke jikinta da sabon lotion..

Abinci ta ɗora..

Kafin ya dahu mai aikin Aunty Amarya ta kawo mata apple guda biyar, wai inji Aunty Amarya.. 

Mai aikin tana miƙa mata ta juya..

A fridge ta ƙarba  zuba huɗu, ɗayan kuma ta zauna ta cinye..

Sai da ta zo kwanciya, suka yi waya da Mama, bayan sun gama ta kira Aunty Saliha suka sha hirar.. cikin barkwanci Aunty Saliha take mata addu'ar Allah Ya sa ta samo miji a Yola su zo su sha biki.. dariya Fatima tayi, da ire-iren waɗannan hirarrakin suka yi sallama...



HAJIYA BABBA;
★washe gari ƴaƴanta mata ta kira a waya, ta hura musu wutar, su tura mata  kuɗi, zata siyi kayan sawar zuwa Biki..

Shi kuma Abba tace ya tanadin kuɗin da zai bata, ta bayar gudunmawa kuma bata son ƙananun kuɗi, masu kauri take so.

Ba su da yadda suka iya da ita, haka suka amsa mata da to...

FATIMA;
A tsakanin kwanakin biyun da suka biyo baya kullum sai an yi mana gyara jiki ni da Aunty Amarya  a Sashenta..

Fatarmu tayi wani irin kyau, musamman ni da ban saba ba, ga mayukan da nake amfani da su da sabulun wanka..


A daren ranar da ya rage saura kwana biyu mu tafi Lagos, mai aikin Aunty Amarya ta kawomin ɗinkunana har Sashena...

Atamfar mai kalar coffee ba ƙaramin haskamin fata yayi ba, ɗinki riga da siket ɗin ya zauna a jikina sosai, sai lesuna guda biyu suma duk sun yi min kyau.. 

Ɗaya daga cikin a kwatunan lefena na sauko da shi, na juye kayan ciki, na jera wanda Aunty Amarya ta kawomin, na ƙara da wani blue material da ta ɗinkamin lokacin bikina da yaya lamiɗo, tuna tace ɗan uwanta ya siya mata kayan yasa na cire shi gudun kar mu haɗu da wanda ya siya mata kayan ya gane ni ta bawa..

Zuciyata ta ce min, a ina masu kuɗi zake gane wani kaya, kawai ki tafi da abunki tunda yana yi miki kyau.. ba tare da dogon nazari ba, na ɗauko kayan na mayar cikin akwatin..

Sababbun Abaya kala biyu na ɗauko a cikin na lefena, baƙi da kalar ruwa madara na ƙara a cikin akwatin, na zaɓi takalma da jakan da zasu shiga da kayan duk a cikin na lefena na jerasu a ciki, sai kayan barci gudu uku dana ɗiba tunda tace sati zamu yi.. sai da zuba komai har undies sannan na kulle akwatin na jingine a gefe...


A ɓangaren su Hajiya Babba suma ɗikunansu ya kammala, Farida har sashen Aunty taje ta tambayeta kwana nawa za'ayi ana biki, tace mata sati ɗaya...

Don haka suka sake shiri da Surutu na alfarma..

 Baba shi ya ɗauki nauyin siyan tikitin zuwansu Lagos  gaba ɗaya har Aunty Amarya.

Duk da Aunty Amarya ta so biya, ya ce ta bari ta biya ta dawowa..


FATIMA;
★washe garin da ya kama saura kwana ɗaya mu tafi Lagos, tunda a can zasu fara biki, daga baya su tafi Yola ayi ɗaurin aure a can, na haɗu da Farida, tana ƙoƙarin buɗe motarta..

Kallo ɗaya nayi mata, naga fatarta ya ɗashe alamar ta mayar da hankali wajen shafa mayuka ƙara haske..

Ban tsawaita kallonta ba, na ce mata "sannu" na nufi mota ta, ba tare da jiran amsawarta ba.

Har na buɗe mota na shiga tana tsaye a jikin motarta tana bina da kallo, nunawa nayi kamar ban ganta ba, na shige motata na bar gidan...

FARIDA; Fatima tana shigewa motarta ta rintse ido tana shafo fatar Fuskarta, bata taɓa sanin haka Fatima ta ƙara kyau ba, wallahi banda tana kwaɗayin haɗuwa da masu kuɗi, da kuma faɗan Hajiya Babba da ba zata je bikin nan ba..

Tunda mai gayyatar tasu bata maraba da zuwansu, banda haka ta yaya Aunty Amarya zata dinga fifita Fatima a kanta..

A sarari ta ce;

"Ji wani baƙin Abaya da ta saka, ko da yake laifin Lamiɗo ne, da ya bar mata lefensa, bai zo ya ƙwace kayansa, aikin banza kawai"

Ta ƙarasa faɗa tana buɗe ƙofar motarta da ƙarfi ta shiga... Da wani irin speed ta bar gidan...



FATIMA; har muka gama lecture muka fito muka ƙara shiga  wani na kasa cin komai.. jikina babu ƙarfi, haka nake fama a kwanakin nan, sai nake jin kamar zazzaɓi yana son kamani..

Da muka tashi yanke shawarar zuwa wajen da naje waccen satin nayi, akwai wani tsire da ice cream ɗinsu da na sha mai daɗi..

Sai da na nemi izinin Baba tukunna.

Kamar waccen satin bai gaji ba, ya ƙara turamin dubu biyar, tare da umarta ta na tabbatar na siyo magani nasha...

Alfarmar waɗanda nake  ragewa hanya na nema, akan zanyi tafiyar sati ɗaya su taimakan min da duk abinda za'ayi idan ba na nan.. basu nuna damuwar komai ba, su ka yi min fatan dawowa lafiya..

Duk da bana jin daɗi sai na kai su inda na saba ajiyesu, sannan na wuce inda nake son zuwa..

Na kuwa yi sa'a samun tsirensu, ina ci ina lumshe ido saboda daɗi..

Maza biyu ne, suka zauna a teburin kujerun gefena, sai dai ban ga fuskokinsu ba..

Bayan na gama cin tsire, ina cikin shan Ice cream... Na ji ance

"FATIMA!"

Ban waiwayo ba, tunda ba ni kaɗai ba ce mai suna Fatima ba, sai da yanayin muryar wanda ya ambaci sunan "Fatima" yayimin kama da na Sadik... wannan dalilin yasa na dakata da shan Ice cream, ina jiran naji ko zai maimata...

Tasowa yayin ya dawo saitin fuskata, muna kallon juna..

Dagaske shine, ya buɗe yayi ƙiba, ya ƙara kyau  da haske...

Gilashin fuskarsa ya cire, da salon Muryar da ya yaudare ni da shi shekarun baya ya ce;

"Ya Allah! Fatima ke ce haka? Wayyo Allahna"

Ya faɗa yana dafe saitin zuciyarsa..😂✍🏻