37
*KUNDINA*
***
37
SADIK;
gilashin fuskarsa ya cire, da salon muryar da ya yaudare ni da shi shekarun baya ya ce;
"Ya Allah! Fatima ke ce haka? Wayyo Allah na"
Ya ƙarasa faɗa yana dafe saitin zuciyarsa..
Kallonsa kawai nake yi, a raina ina jin ko buɗe baki nayi, na yi magana yaji muryarta to baƙaramin asara nayi ba..
Mahaifiyata ta rasa aurenta saboda shi, mahaifina yayi kuka saboda shi, na rasa karatu, na rasa ƙimata a idon wasu har abada duk don saboda abinda yayi min, shine yanzu zai ƙara zuwar min da wani sabon salon yaudara, lallai Sadik ba shi da kunya..
Ganin nayi shiru ina kallonsa, yasa ya gyara zamansa, yana mairairaice idanuwansa kamar zai yi kuka sak dai waccen yanayin nasa na shekarun baya..
Murya ƙasa-ƙasa yana ɗage dukka girarsa sama ya ce;
"Fatima, shekaru biyu na yi bana gida, saboda kuskuren da na aikata miki ya bibiyi rayuwata, da taimakon Mommy na dawo hankalina na baro ƙasar da nake, kin san ina dawowa wa na fara nema? Ke na fara nema Fatima, kuma sai gashi Allah Ya haɗa da ni dake cikin sauƙi.
Wallahi na gane kuskurena don Allah ki yafemin, kin ji Baby"
Ya ƙarasa faɗan "Baby" da wani irin salo kamar zai fashe da kuka..
Ice cream ɗin hannuna naso watsamai a fuska, na fasa, ga maganganun cike fal a bakina amma na daure, saboda kar ma yaji muryata..
Kawai kallonsa na cigaba yi, kamar dutse..
Kansa ya shafo, zai ƙara yimin magana na miƙe a hankali, ina roƙon Allah Ya sa yayi tunanin kamomin riga ko mayafi..
Ai kuwa ko taku biyu ban yi ya riƙo Abayar jikina, murya ƙasa-ƙasa ya ce;
"Fatima, haba Fatimana"
Waiwayowa nayi, duƙulalliyar jakar hannuna mai ƙarfe a gefe da gefe na zaƙe ƙarfina har da cije leɓena na ƙasa, na buga mai a hannu..
"Awch" ya ce da ƙarfi ya sakar min riga..
Abokinsa da suka zo tare da gudu ya taso ya nufoshi..
Ban tsaya ba naje na biya kuɗin dana kashe na bar wajen..
Motata na shige, ina hangosu sun fito shi da abokinsa na tashi motar na bar harabar wajen..
SADIK; ba ƙaramin azaba ya ji ba, sai ya ji dama bai yi mata magana ba.
Abokinsa yake tambaya wai yaushe Fatima ta zama muguwa haka..
Shi dai Aboki nasa shiru ya yi, don bai taɓa ganin Fatima ba ma sai ranar..
Sadik yayi mamakin ganin ta shiga mota, ta tuƙa da kanta.
Da yake gwanine wajen iya shawo kan Mace, a take ya fahimci irin soyayyarsa ta shekarun baya ba zata dawo masa da Fatima ba.. yana buƙatar canza salo..
Komawa ciki suka yi, aka kawo musu abinda suke buƙata..
Suna ci, Sadik yana bawa Abokinsa labarin Fatima..
Kafin su koma gida, Abokin ya bashi shawarar kawai ya yi shahada ya je gidansu kai tsaye ayita ta ƙare..
Sam Salim bai gamsu ba, amma abokin ya bashi ƙwarin gwiwar shi zai rakashi, kawai ya saka musu rana..
A kan haka suka rabu, Sadik ya koma gida...
FATIMA;
Ina tafe akan hanya ina mamakin ƙarfin halin Sadik, su wasu mazan sam babu tunani a cikin ƙwaƙwalwarsu, idan banda haka tayaya Sadik zai yi min irin wannan yaudarar, kuma tashi ɗaya mu haɗu a wani waje ya ce zaiyimin daɗin baki?..
Kaina na girgiza, ina jan tsaki..
Har na isa gida, na shiga Sashena na gama dukka uzurina, ban daina tuno yadda Sadik yayi ƙiba da haske ba, ni ina nan ya bar ni cikin masifa, sannan dan ya raina ni, ya ce zai ƙara dawowa cikin rayuwata..
Ringing ɗin wayata ne ya katsemin tunanin da nake yi..
Baba ne, da sallama na ɗaga, ya tambayeni nasha magani? ban yi masa ƙarya ba, na ce ban sha ba..
Faɗa ya rufeni da shi, ya ce na tashi naje nasha..
Ba don ina da maganin ba, na miƙe..
Baba bai katse wayar ba, har sai da nayi masa ƙaryar nasha tukunna..
Mama na kira tayimin addu'ar dawowa lafiya, sannan ta ja min kunnen na riƙe mutuncina ban da shishigi da rawar kai..
Mun jima muna waya har ta bawa Aunty Saliha muka gaisa sannan muka yi sallama..
Sanin tashin safe zamuyi yasa na kulle idona don na samu barci.. amma inaa barcin ƙin zuwa yayi, zazzaɓi mai zafi ya rufeni..
Sai gabannin Asuba na samu barci.. ban farka ba sai ƙarfe shida da rabi.. har lokacin jikina zafi..
Da ɗan ƙarfin da ya ragemin na tashi na ɗoro alola na tayar da Sallah.. bayan na iddar anan na kwanta na dunƙule waje ɗaya...
Sai da naga ƙarfe bakwai da rabi tayi sannan na miƙe..
Ruwa mai zafi na haɗa na shiga wanka..
Na jima ina wanka ba kamar yadda na saba yi nandanan na gama ba, saboda jikina babu kuzari..
Bayan na fito a bakin gado na zauna, na shafa mai, na ɗauko riga da siket ready made baƙaƙe na saka sannan na ɗora tracksuit mai kauri a sama..
Ban ɗaura ɗan kwali ba, sai jan mayafin da na yafa kalar tracksuit ɗina.
Mayukana da turarena na jera a cikin akwati, na shiga Washroom na kwaso sabulun wankana da soso..
A fanka na rataya soson ya bushe Sannan na sakashi a ma'adaninshi na jera su dukka a gefen kayana...
Kan gado na koma na kishingiɗa..
Ban nemi abin kari ba, saboda ba zan iya ci ba..
Har barci ya fara ɗaukata ringing ɗin wayata ya tasheni.
Aunty Amarya ce, da sallama na ɗaga na gaisheta, cikin kulawa ta amsa sannan ta ce na fito suna jirana..
Ƙarfi hali nayi naja akwatina gudun kar Baba ya fahimci halin da nake ci...
A bakin motar Baba na same su dukkansu, Farida tayi adonta cikin doguwar Abaya kalar pink sai hura hanci take yi..
Gaba ɗayansu na gaisar, Hajiya Babba itama tayi adonta cikin baƙin Abaya baƙi mai wadataccen faɗi. ba yabo ba fallasa suka amsa ita da Farida..
Baba amsamin ya yi, yana tambayata ya ya jiki?
"Da sauƙi" na ce mai ina yin ƙasa da kaina, ba don ya gamsu ba ya ce;
"Allah Ya ƙara sauƙi"
Gaba ɗaya suka amsa da Amin, suma suka yi min yaya jiki har da Farida da take ta ƙaremin kallo..
Ba yabo ba fallasa na amsa..
Farida da Hajiya Babba, motar Hajiya Babba suka shiga, driver zai kai su airport ya dawo da motar..
Ni da Aunty Amarya kuma muka shiga na Baba...
Kasancewar safiya ce babu yawan ababen hawa nan da nan muka isa airport..
Bayan mun kai duk hirarrakin da suke yi, ban saka baki ba, har lokacin tafiyarmu ya yi..
Anan Baba ya roƙi Aunty Amarya idan mun isa dan Allah ta bani magani nasha..
Ina kallon Farida da Hajiya Babba suna jefomin harara ta ƙasan ido..
Kasancewar farkon hawata jirgi kenan, sai jikina ya ƙara rikicewa naji zuciyata tana tashi kamar zanyi amai..
Ɗaurewa nayi ina ta ambaton Allah, cikin ƙanƙanin lokacin da ban yi tsammani ba, mu ka isa Lagos, su Hajiya Babba sai hura hanci suke yi, musamman Farida bini-bini ta shafo hancinta..
Waya Aunty Amarya ta kira cikin ƙanƙanin lokaci sai ga Jamil ya zo ɗaukarmu, wanda na taɓa gani a sashen Hajiya Babba ya je gaisheta..
Fuskarsa tana nan da kyanta Masha Allah..
Farida tana ganinsa da kuma irin Motar da ya zo ɗaukar mu da ita, ta washe jerarrun haƙoranta da aka yiwa wanki na musamman duk dan saboda bikin, tana gaisheshi..
Shima ya amsa mata da fara'arsa..
Muna tafe Aunty Amarya da Jamil suna hira, su yi da turanci, can su juye fulatanci da wani yaren da nake kyautatan zaton na shuwan Maiduguri ne..
Ni dai ina kwance jikin seat, saboda zazzaɓin jikina daya ƙara ƙarfi...
Kamar tambayar Aunty Amarya Jamil yayi mai yake damuna, na ga ta waiwayo tana yimin sannu shima sannu yayi kin, yana cewa idan muka kai gida, muka huta zai zo kai ni Asibiti.
Farida gum tayi gashi ba damar tayi tsaki nan ba Kano ba ne...
Ba iya su Hajiya Babba ba, ni kaina sai da na ɗan ruɗe da irin kyan gidan Hajiya Ni'ima..
Da Ango muka fara cin karo zai fita, dogone sosai siriri ya tara gashin mai yawa akai, kalar farinsa gwanin sha'awa..
Yana hango Aunty Amarya ya fasa shiga mota, ya nufota da sauri kamar ƙaramin yaro, hannu ta buɗe mai tana cewa;
"Masha Allah, Sarfaraz kaga yanda kayi kyau?
Murmushi yayi ya ɗan rungumeta, sannan ya saketa suka gaisa..
Da fara'arsa ya gashe da Hajiya Babba ta amsa, kamar bakinta zai yage..
Ni da Farida haɗa bakin gaishe shi muka yi, ya amsa yana kallona..
Nuna ni yayi da yatsa ya kalli Aunty Amarya ya ce;
"Daga kyanta na gane ita ce Mama take bamu labari kullum, Fatima ko?"
Dariya Aunty Amarya ta yi, ta ce;
"Kamar ka sani"
"Amma na ga kamar bata da lafiya"
Ya faɗa hankalinsa gaba ɗaya na kaina..
Amsar "eh wallahi" Aunty Amarya ta bashi..
Bai yi jinkiri ba, ya ƙwalawa Jamil kira, don a shekaru kamar zai girmi Jamil..
Aunty Amarya bata dakatar da shi ba.. har Jamil ya ƙaraso..
Farida ƙasa tayi da kanta, Hajiya Babba kuwa bakinsu kawai take kallo..
Bayani Jamil yayi mai akan ya bari mu hutu tukunna..
Sarfaraz fasa fita yayi, ya kamo hannuna, kamar raƙumi da akala haka na bi bayansa, su Aunty Amarya suna bin mu a baya zuwa Parlon gidan✍🏻
Kuyimin afuwa uzurine ya tare ni, ku yi manage Please🙌..