KUNDINA

38

by @nafisatusasaal01

*KUNDINA*



38

Sarfaraz fasa fita yayi, ya kamo hannuna, kamar raƙumin a akala haka na bi bayansa, su Aunty Amarya da Hajiya suna bin mu a baya zuwa parlon gidan..


Kamar wajen sai da kayan alatu haka aka ƙawata ƙaton gidan parlon, haske ta ko ina..

Manyan mata da matasa maza da mata masu irin shekarunmu ne a zazzauune, kowanne da wayarsa yana dannawa su na taɓa ƴar hirar, a tsakanin su, har da waɗan da shekarunsu  ja ba'a barsu a baya ba, kowacce da wayarta a hannun...

Mai tsananin kama da Sarfaraz ce ta fara hangomu, ba zan ce ƙanwarsa ba, sai dai na ce yayarsa, saboda shekarun da suka bayyana a saman Fuskarta..

"Aunty Hanifah" ta faɗa da sautin da yasa hankalin mutane da yawa ya dawo kanmu..

Kamar sun ga wani abun kambabawa haka duk suka miƙe, kowa na kiran sunan Aunty Amarya.. 

Hajiya Babba da Farida da ni kaina sai muka zama ƴan kallo..

Sarfaraz ne ya ja hannuna zuwa ciki, su Hajiya Babba kuma dole suka nemi waje suka zauna..

Muna tafe ina tambayar kaina;

"Maiyasa ƴan uwan Aunty Amarya suke ji da ita haka? Baba ba attajiri ba ne, ita ma kuma ma ba wata shararriya ƴar kasuwa ba ce, asalima ko Sa'a bata yi"

Shigowarmu wani parlon, daban ne ya katsemin zancen zucin da nake...

Wasu mata masu kama da Sarfaraz ne a zaune, suma dai wayar suke dannawa ɗaya tana nunawa ɗaya abu a waya, sai Babbar Mace ɗaya a cikinsu, itama hankalinta na kan waya, ban kawo itace Hajiya Ni'ima ba..

Sai da Sarfaraz ya ce;

"Mama ga kyauta na kawo miki"

Kanta ta ɗago tana ganina ta saki dariya tana buɗemin hannu.. a kunyace na ƙarasa kusa da ita..

A kan cinyarta ta zaunar da ni tana dariya haɗe da tambayata;

"Yanzu kin gane ni?"

Murmushi nayi na ɗaga kai alamar eh.. "to yaya sunana"

Da na rasa me zance, kawai sai na ce; 

"Mama Hajiya Ni'ima"

Gaba ɗayansu dariya suka saka.. a raina na ce ohh rayuwar masu wadata akwai daɗi...

A gefenta ta zaunar dani muka gaisa, na gaishe da ragowar suka amsamin murya a sake..

Sarfaraz bayani yayi mata bani da lafiya, da fuskar tausayi ta ce;

"Haba naji hannunta zafi, ina su Hanifah suke, ya kamata a kaita Asibiti"

"Suna Parlo ita da abokiyar zamanta" Sarfaraz ya bata amsa yana ƙoƙarin fita daga Parlon.

Da sauri waɗancan matan su biyu suka miƙe, da alama wajen Aunty Amarya zasu je.

Hajiya Ni'ima miƙewa tayi ta kama hannuna muka bi bayansu..

HAJIYA BABBA DA FARIDA;

kamar an manta  dasu haka ƴan uwan Aunty Amarya suka cigaba da taraiyayar ta,  itama kuma daɗin ganin dangi yasa ta manta dasu..

Gaba ɗaya ji suka yi dama basu zo ba, musamman Farida da take jin kamar an wulaƙatasu an mutunta Fatima...

Tunda su Fatima suka fito idon Hajiya Babba yake kan hannun Hajiya Ni'ima data riƙe Fatima da shi..

Hajiya Ni'ima maimakon ta nufi wajen Aunty Amarya wajensu Hajiya Babba ta ƙarasa.

Sai da suka gaisa a mutunce tukunna sannan ta ɗan ɗaga murya yanda kowa zai ji ta ta ce;

"Ga abokiyar zaman Hanifah da ƴaƴanta"

Sai a lokacin Aunty Amarya taji bata kyauta ba..

Abun mamaki haka kowa ya dinga zuwa yana gaishe da Hajiya Babba...

Ba iya Hajiya Babba ba, har Farida sai ta tambayi kanta, wacece Aunty Amarya? Menene matsayinta a cikin zuri'arsu duk da tana Aure Miji irin Baba???


*Bari mu waiwaya Shekaru masu yawa baya*

Zuri'ar Hamza Ɗan fillo, zuri'ah ce data tara ƙabilar Fulani daban-daban har ma da wasu ƙabilun kamar su Shuwa, kanuri da sauransu, duk sanadiyyar aure daga wasu sassa na arewacin Nigeria.. amma asalin tushensu garin Yola ne, kuma anan yawancin su, suke rayuwa.

 Suna auren dangi kuma suna aure bare, sai dai kyansu yasa dayawa sukafi auren masu wadata..

Gudun gori da kushe da kuma son nuna matata tafi ta wannan Mijina yafi na na waccen, yasa Mazansu basa auro mata masu rangwamen kyau, haka suma Matan, duk kuɗin Namiji basa sa auren mai rangwamen kyan halitta.

Duk da wannan kyan da suke taƙama da shi Sarah itace  matashiyar yarinya da dangi ke labarin kyanta, ƴa ce a wajen Muhammad ɗaya daga cikin ƴaƴan Ɗan fillo da Allah yayiwa rasuwa tuntuni..

Sarah tana ɗan ƙaramin ƙani Misbah tare suke komai, tunda Mahaifiyarsu ta fita tayi aure a wani garin..

Kyan Sarah yasa dangi ake ta rububinta, har Mazan waje ma ba'a barsu a baya ba.. sai dai ita wani ɓako take so a unguwarsu mai tasho irin na fulanin Niger sai dai sam bashi da kyan fuska, kuma alamun da yawa sun  nuna bashi  da ko sisi sai dai rufin asiri.. sunansa Muzaffar..

Babu yadda dangi basu yi da Sarah ba, amma kafe tace ita dai ta ɓakon Niger take so..

Ƙarshe haka kowa ya haƙura.

Babu wanda ya goyi bayan auren, domin ko da aka tashi auren babu wanda ya tsaya mata ayi binciken waye Muzaffar da sauran binciken da ake yiwa mace ƴar gata a waccen lokacin..

Burin ƴan uwanta taje tasha wahala ƙarshe ya gudu ya barta tunda taƙi jin maganarsu.


Ko kayan ɗakin da akewa yi na nuna bajinta a zuri'arsu, ba'ayi mata ba, haka suka aura mata Muzaffar suka miƙata matsakaicin gidansa..

Sarah tayi rayuwar farin ciki da Muzaffar sama da yanda take hasashe, a gidanta misbah yake zuwa cin abinci kullum..

Shekarun su biyu da aure, ta haifi Ni'ima mai kama da ita, har rashin tsaho da haske fata, kamar ba ƴar Muzaffar ba.. wannan lamari ba ƙaramin ciwo yayiwa danginta ba.. ko Barka babu wanda ya zo mata..

Sarah ita take biyawa misbah kuɗin makaranta, domin akwai tazarar shekaru mai yawan gaske a tsakaninsu..

Daga kan Ni'ima basu ƙara samun wani rabon ba, kuma Muzaffar bai taɓa yi mata hirar danginsa ba, ya dai faɗa mata shi ɗan Niger ne, iyayensa sun rasu, rigimar dangin ne yasa yasa ya baro gida..

Duk wani abu da za'ayi na dangin Sarah babu sunanta a ciki,  ba'a gayyatarta biki, ba'a faɗa mata suna, mutuwa ma sai dai taji a bakin Misbah..

 Kwanci tashi Ni'ima takai shekaru goma sha biyu, kyanta ya fito ɗas gwanin sha'awa, maza suka fara rububin nuna suna Sonta, a cikinsu ta sasanta da Muhammad Jiddah, kyakkyawa ne na liƙawa a goshi, ɗan ƙabilar shuwa, ƙaramin jam'in soji.. 

Duk da kushe irin na dangin Sarah ba'a fasa auren Ni'ima da Muhammad Jiddah ba.

Daga Muhammad Jiddah sai Ni'ima suka  kama hanyar Lagos garin da yake aiki...

A lokacin Misbah ya kammala karatunsa yana fafutukar neman aiki shima ya samu yayi aure..

Ni'ima nayin aure, Sarah ta samu juna biyu, itama Ni'ima ko wata biyu bata yi  Allah Ya basu rabo..

Tsakanin haihuwar Sarah da ƴarta Ni'ima kwanaki arba'in ne kacal..

Sarah kyakyawa  jariri mai tsananin kama da ita sama da Ni'ima ta haifo sai dai bai kai Ni'ima haske ba lokacin da tana jaririya.. ranar sunan da babu danginta ko mutum ɗaya sai abokannan arziƙi jariri yaci sunan Aliyu..

Itama Ni'ima kyakkyawar ƴarta Mace ta haifa, bazaka ce ga da wanda take kama ba,  itama Abokanan arziƙi da dangin Jiddah ne suka kula da ita, sai misbah da Muzaffar yayiwa kuɗin Mota yaje ya dubasu ya yi kwana biyu ya dawo.

Haka rayuwa ta miƙa musu, da daɗi babu ɗadi.. har Misbah ya samu aikin koyarwa a makarantar primary gwamnati..
Saboda haushin Sara yasa dangin kowa ya zame hannunsa akan lamuransu, balle ya saka ran zasu taimakamai da aiki mai gama tunda suna da hanya..

A sashen da suka gada a wajen mahaifinsu, falle ɗaya da parlo yayi auren da sam babu armashi, bai zafafawa kansa ba, ya nemo ƴar masu rangwamen ƙarfi..

Zainab matar Misbah rabinta Fulani rabinta shuwa, tun asali macece mai burin samun duniya, sai dai son misbah ya danne waccen burin nata har ta yarda ta aure shi..

Kishi yasa matan ƴan uwan misbah suka dinga zugata, gashi mazansu suyi ta kawo musu kayan daɗi ban da ita.. 

cikin ƙanƙanin lokaci ta sauya kai tsaye ta nunawa Misbah ita fa ba zata iya zama da shi ba ta gaji..

Mamaki ta bawa Misbah, don aurensu ko shekara bai yi ba, haƙuri yayi ta bata suka ci-gaba da lallaɓawa..


A lokacin da Aliyu ya cika shekaru shida wanda yayi daidai da shekaru biyu da auren misbah da Zainab, Zainab ta samu juna biyu.. sai dai ko wata biyu bai ba ya zube.. haka ta jera shekara ɗaya da rabi tana samun juna biyu akai-akai yana zubewa..

Zainab bata ƙara birkicewa misbah ba, sai da Ni'ima ta haifi ƴarta ta biyu mace, suka je suna, taga rin kayan daɗin da su Ni'ima suke ci, acewarta ai Ni'ima ba finta kyau da gata tayi ba, amma gata nan ta samu mijin da suke cin kayan daɗi..

Da suka dawo Yola ta ƙara samun wani juna biyun
tattara kayanta tayi tace ta gaji da zama da shi, rashin cin kayan daɗi ne yasa cikinta yake zubewa, ba zata zauna ta ƙara asarar na jikinta ba..

Babu irin magiyar da misbah bai yi ba mata ba, ta nuna sam bata san zancen ba..

Aliyu kyakkyawan yaron liƙawa a goshi, yana zuwa makaranta, idan yamma tayi ya dawo daga Makaranta muhamdiyya sai ya ɗauki soyayyar gyaɗan Innarsu ya fitar da shi ƙofar gida..
Yara mata sa'anninsa su yi ta siya, don kawai su yi hira da shi.. da ya fahimci gyaɗar Innarsa ta na saurin ƙarewa idan ya saki jiki ya yi hira, sai ya zauna ya tsara labarai masu daɗi da tatsuniyoyi kala-kala, har muryoyi kala-kala ya koya, yara mata har da maza su taru ana ta siyan gyaɗarsa suna saurarar labaransa masu daɗi...

Ni'ima bata waiwayi gida ba, sai da ƴarta ta yi watanni goma, saboda nisan gida.. don rabonta da gida tun Aliyu na ɗan shekaru biyu..

A ranar kasa barci suka yi sukayi saboda farin ciki, ta kuwa taho da tsaraba kala-kala...

Mamakin girma da tsahon Aliyu take ta yi, har tsahonsa ta gwada da na ta  iyayensu suna ta dariya...

Washe gari taje gidan kakanninta na ɓangaren uwa, bata jima ba ta wuce gidan iyayen mijinta...

A ranar da Ni'ima ta tafi gidan Iyayen mijinta da yamma Babansu yana dawowa daga kasuwa mota ta bigeshi..

Cikin jini aka kaishi babban Asibiti.. 

Kwanan Asibiti, Sarah da su Ni'ima har da misbah suka yi..

 Gabannin Asuba Muzaffar ya ce likita ya kira masa misbah..

 Da muryarsa da bata fita da kyau ya ce  yana son Misbah yayi masa alfarma zai bashi addireshi yaje ƙasarsu kuɗi na ƙasar katifarshi ya gaya musu bashi da lafiya yayi hatsari, su zo ya gansu..

Misbah bai musu ba, bai kuma gayawa kowa zai yi tafiya mai nisa ba, sai Ni'ima saboda yasan Sarah bazata barshi ba...

Da taimakon Ni'ima ya ɗako kuɗin Mota a ƙarƙashin katifar Muzaffar, ya kama hanya..


Kwanan Misbah biyu da tafiya ƙasar niger ɗauke da addireshin da Muzzafar ya bashi, Allah yayiwa Muzaffar rasuwa...

Ƙuncin da wannan zuri'a suka shiga ɓata bakine.
A ranar Sarah ta samu labarin inda mishah ya tafi a bakin Ni'ima...

Abokanan arziƙine suka kai Muzaffar makwanci, babu wani ɗan uwa na jini, sai Jiddah da wasu ƴan uwansa...

A nan gidan rasuwar maƙota suka fara gulmar ai ga abinda ake jiyewa Sarah nan, ta biyewa soyayya yanzu gashi ya mutu ya barta babu danginsa..

A kaf danginta babu wanda ya zo mata gaisuwa, kuma duk sun ji labari...

Suna cikin wannan jimamin Zainab ta zo da sabuwar  jaririyarta haihuwar ranar, ita da ƴan uwanta mata biyu..

Daƙyar suka yi musu gaisuwa sannan suka ɗora da bayanin sun kawowa Misbah jaririyarsa tun da bashi da kirki, baya zuwa kullum duba jikin Zainab har ta haihu..

Sarah tana kuka take roƙonsu su rufa mata asiri, ina zata kai Jaririya?.. basu saurareta ba suka tafi suka barsu da jaririya tana barci.. Aliyu shi ya ɗauki jaririyar ya rungume ya ce shi yana so, zai yi cinikin gyaɗa ya siyo mata  abinci...

Ni'ima shawarar shayar da jariryar ta yanke, ko da ta tambayi Mijinta da ya zo da Daddare bai musa ba, saboda tausayinsu da yake ji..

MISBAH; ya samu dangin Muzaffar Talakawa ne fitik, masu kafiyar tsiya.

 Daƙyar da magiya ya samu  baffan Muzaffar ya karɓi addireshin inda Muzaffar yake, ya ce masa zasu zo In sha Allahu...

Misbah bai ƙara kwana ba ya kamo hanya da addu'ar Allah Ya sa dagaske su waiwayi Muzzafar..

Ya na dawo gida ya samu labaran da suka gigitashi Fuskarta ta ƙara dawowa ƴar ƙarama...

Ya samu Ni'ima har ta fara shayar da jaririyarsa.. 

Yayi kukan mutuwar Muzaffar, bai gayawa yayarsa gaskiya ba, cewa mata yayi da dangin muzaffar suna nan zuwa jibi...

Aliyu shi ya kafe aka raɗawa jaririyar suna Hanifah, sunan wata yarinya ƴar gidan mai garin da suke zaune a ƙasar waje, da ta taɓa zuwa wajensa siyan gyaɗa..

Tun Sarah tana saka ran zuwar dangin Muzaffar har ta cire rai, saboda satin Misbah ɗaya da cema mata jibi zasu zo..

Har lokacin zainab bata waiwayi Hanifah ba.

Ana saura kwana ɗaya su Ni'ima zasu tafi.. Mijinta ya kawo shawarar zasu tafi da Hanifah idan tayi ƙwari sai su dawo da ita...

Sarah da duk ta rame ta dawo wani iri tana kuka ta yiwa Jiddah godiya da addu'ar Allah Ya raya masa zuri'arsa...

Sai dai a ranar da suka tafi da Daddare Allah yayiwa Sarah cikawa.. daga faɗuwa bata motsa ba..

Aliyu da Misbah sunyi kuka, kamar su ma zasu bita...

Aliyu da kansa yaje gidan kankaninsa ya faɗa musu Mahaifiyarsa ta rasu, amma babu wanda ya zo a cikinsu sai washe gari...

Haka akai Sara makwancinta, Ni'ima tana can babu wanda ya aike mata da saƙo, gudu halin da zata shiga tunda ga ƴaƴa har huɗu a tare da ita..


zafin zuciya irin na Aliyu yasa bai bi Misbah ba can gidansu ba, ya ce shi a gidan Ubansa zai zauna.. dole haka Misbah ya ƙyaleshi...✍🏻