KUNDINA

39

by @nafisatusasaal01

*KUNDINA*

   39



Bayan kwana biyu maraici da gorin rashin asalin uba ya addabi Aliyu daga mutanen unguwa, har ma da ƴan makarantarsu....

Duk wannan bai sa ya karaya ba, da kansa yake soya gyaɗa ya fito ƙofar gida idan ya dawo daga makaranta, kafin kace kwabo ya ƙare..

Salon muryoyi masu daɗi, da waƙoƙi baka kala-kala ya ƙara koya, idan ka zo siyan gyaɗa yasan sunanki haka zai yi raira miki waƙoƙi da sunanki.. 

Wasu sukan yi mai dariyar ya zama ɗan maula, amma bai damu ba.

Mijin Ni'ima ya jima da samu labarin rasuwar Sarah, amma gudun halin da Ni'ima zata shiga yasa ya ƙi faɗamata kuma ya hanata zuwa gida, yace ta bari sai Hanifah tayi wayo.. 


Bayan Ni'ima ta yaye Hanifah ta ƙara haihuwar ƴa mace, bata jima ba ta ƙara haifar Namijin da dangi suka ruɗe da farin ciki.

 Har su Misbah duk labari yaje musu, sai dai basu je ba.. ranar suna aka raɗawa jariri Sarfaraz...

Bayan watanni Jiddah ya samu ƙarin girma, suka canza muhalli mai kyan da yafi na baya..

Ni'ima bata waiwayi gida ba, sai da Hanifah ta isa sakawa a makaranta... Da murnarta  ta lodawa Mahaifiyar, Misbah da Aliyu, tsaraba.

 Ƴaƴanta duk sun kyau har da Hanifah cikin surutu gwannin sha'awa..

Sai dai labarin da ta tarar, sam bai yi mata daɗi ba, har suma tayi, tayi kuma fushi da kowa.

Acewarta ko addu'a suka gayamata tayiwa mahaifiyarta ai da sauƙi, amma tayaya mahaifiyarta zata mutu kowa ya yi mata shiru..

Saboda takaici ko gidan kakannin bata biya ba, ta ƙara komawa Lagos da Hanifah..

Tsananin gorin da Aliyu yake fuskanta daga mutane ne, yasa Misbah da har lokacin bai ƙara aure ba, yanke shawarar ƙara komawa  Niger da Aliyu wajen dangin Muzaffar..

Wataƙila idan suka ga Ɗansa zasu sassauta masa...

Ba ƙaramin fama Misbah yayi da Aliyu ba, kafin ya amince..

Da guziri mai yawan gaske suka kama hanya..

Misbah bai sha wahalar gano inda ya taɓa zuwa shekarun baya ba..

Ga mamakinsa hannu bibbiyu suka karɓi Aliyu, wasu kuma suka ƙaryata tayaya Muzaffar zai haifi Ɗa mai kyan wannan, sharri ne kawai irin na Misbah..

Hoton Aliyu da shi da Mahaifansu har da Ni'ima Misbah ya nuna musu..

A take rigima ya kaure a tsakaninsu, da yawa suka ce Baffan Muzaffar da dukiyarsa take hannunsa ya fito da su dukka a bawa ƴaƴansa, wasu suka ce ai ba lallai ƴaƴansa ba ne...

A daren ranar Misbah ya samu labari daga bakin ɗan Yayan mahaifin Muzaffar cewa Muzaffar ɗin ya bar gidane, saboda sihirce-sihircen da Baffansa da ɗan uwan Muzaffar ɗin da suke uba ɗaya suka dame shi da shi, akan dukiyar da ya tara na aikin noma da yake yi tuƙuru.. burinsu ya mutu su gada, tunda Muzaffar ba shi da Iyaye..

Amma idan Misbah zai bashi wani abun, zai taimaka musu wajen dawo da dukiyar hannunsu...

Ba tare da wani dogon tunani ba, Misbah ya ce amince..

Wahala babu irin wanda basu sha ba, daga cewa zasu yi sati ɗaya, sai gasu sun share watanni biyu da ƴan kwanaki.

Da ƙyar da roƙon Allah dukiyar ta dawo hannunsa..

Dukka arziƙin ƙasa ne, don haka Misbah ya samu masu siya, suka yi masa siyar ganin dama, ya sallami ɗan uwan Muzaffar suka kamo hanyar Yola...

Wahala tasa Misbah ramewa yayi baƙi.. kafin su iso Yola zazzaɓi mai zafi ya rufe shi..

Dukka da haka bai gajiya ba, suna dawowa da kwana ɗaya, ya ƙara shirya musu tafiya Lagos gidan Ni'ima.. saboda wayar hannu yayi ƙaranci a lokacin..

 A ranar da suka isa Lagos da yamma Allah yayiwa Misbah cikawa..

Aliyu yafi kowa jin mutuwar Misbah, saboda shi kaɗai yasan irin wahalar da yasha a garin Mahaifinsu...

Ni'ima ma taji mutuwar.

 Rashin danginsu a lamuran da ya shafe su ba sabon abu ne, wannan yasa basu wahalar da kansu wajen dole sai angayawa dangi ba, aka kai Misbah makwancinsa...

Daga wannan rana Aliyu ya ɗora ɗamara da neman kuɗi Mijin Ni'ima mai zuciyar ƙwarai shi ya tsaya mai, sam bai nuna zalamarsa akan dukiyar da suka samu ba, tunda ba wani abun azo a gani suka samu ba..

Babu jin kunya babu tsoro babu girman kai, haka Aliyu yake tallata kayan kolin da yake siyarwa a cikin kasuwar Lagos..dama gashi gwanin iya muryoyi kala-kala ne. 

Ko da ya kai shekaru 20 muryarsa ta zama mai nauyi da amo, hakan bai hanashi sarrafata  yanda yake so ba, duk dan a siyi kayanshi.. a lokacin ne ya samu nasarar shiga jami'ar Lagos..

Buɗi kam haka yake ganinsa ta ko ina, hakan ba ƙaramin ƙara masa ƙaimin nema yayi ba..har Yara ne da shi, da suka girme mai a shekaru..

A wannan gaɓar ne, uban gidan Jiddah ya samu matsala a ƙafa, suka tafi dubashi dukkansu..

Uban gidan Jiddah tunda yaga Aliyu da yanayin ƙirarsa ya ji yaron ya birgeshi.

Bai yi nauyin baki ba, ya cewa Ni'ima su ba shi Aliyu ya saka shi aikin soji.

Ba tare da tsoro ba, Aliyu ya ce shi kasuwanci yake so, ya zama shararren mai kuɗi..

Dariya Uban gidan Jiddah ya saka, ya ce Aliyu yaje yayi tunani..

Basu baro gidan ba sai dare..

Ba ƙaramin fama Jiddah da Ni'ima suka sha da Aliyu ba, acewarsu ai yana da Yaran da zai iya ɗorawa akan kasuwancinsa...

Akan haka suka shawo kanshi...



Bayan wasu shekaru, Aliyu yayi irin kuɗin da yake buri da taimakon yayarsa Ni'ima da Mijinta Jiddah.. haka a aikinsa ya take muƙamin da kowani soja yake burin kai wa.. Dangi daga ko ina suka yayyame su, suna neman yafiya, ba wai don sun talauce ba, sai don burin ace suma su Aliyu nasu ne...

Ni'ima ta zama babbar Mace ƴaƴanta mata duk sun yi aure..

Farko da Hanifah da kawo Babansu Fatima Hajiya Ni'ima ba ta amince ba.. amma tuna rayuwar farin ciki Hanifah take buƙata ba na kuɗi ba, tunda su suna da shi yasa ta amince..

Gaba ɗaya sai ya zamana Aliyu shine wanda dangi suke taƙama da shi, ya zama Breadwinner... 

Zainab bata iya zuwa wajen Hanifah, duk da tayi nadama saboda kunya, sai dai ta aike mata da saƙo.. 

Hanifah ba tana wofintar da ita ba, indai taje Yola sai ta kai mata ziyara..

Aliyu kyakkyawan Matashin soji mai shekaru 39 a duniya hannunsa a buɗe yake, musamman idan ka kara sunan Hanifah wajen tambayarsa kuɗi, babu jinkiri yake bayar da abinda aka tambaya.. don ko gidanta kace zaka je, indai ka sameshi a waya, sai ya baka  kuɗin shan mai.

Ya sha yiwa danginsa kyautar mota ga waɗan da basu da shi idan suka ce zasu je gaishe da Hanifah a Kano..

Yana son Hanifah sama da kowa a rayuwarsa, kowa shaida ne, shiyasa Hanifah ta zama abar so a wajen kowa..




*DAWOWAR LABARI*
Haka su Hajiya Babba suka yi ta gaisawa da mutane, daga baya aka kai su ɗakin da zasu zauna, kowa nashi daban..

FATIMA; nima ɗaki daban aka kaini.

Ko zama ban yi ba, na shiga wanka,  ina fitowa  Aunty Amarya ta kirani na fito mu tafi Asibiti..


Kayan da na sako na mayar.  Ina fitowa na same ta a Parlo cikin ƴan uwa..

Tasowa tayi muka fito Harabar gidan tare..

Jamil ne ya tuƙa mu, ba mu sha wahalar ganin likita ba... Ya lodomin magungunan zazaɓi masu kyau muka dawo gida..

Kai tsaye ɗakin da aka bani na wuce, ban jima da shiga ba, aka kawomin abinci kala da biyu da lemo har da fresh fruits masu kyau gani a ido...

Da ƙyar na tsakuri abincin nasha magani...

Da dare yayi aka fara shirye-shiryen tafiya taron da Hajiya Ni'ima ta shirya da ƙawayenta kafin su wuce Yola..

FARIDA rasa kayan sawa tayi musamman da ta ji ance har da abokanan ango.. sai dai tuna asalin masu kuɗin wataƙila bikin Yola zasu je yasa ta sassautawa kanta, tayi adonta cikin leshi mai kyau...

FATIMA; Aunty Amarya ta waya ta gayamin kalan kayan da zan saka..

Ai kuwa ba ƙaramin kyau na yi ba.. ina fitowa nayi karo da Farida ita da Hajiya Babba dukkansu sunyi ado cikin leshinsu mai tsada...

Harara Hajiya Babba ta banka min a hankali ina jinta ta ce;

"Makira saboda kinga za'a zo gidan arziƙi shine kika tsiri ciwon munafurci don su tausayamiki, Allah dai ya wadaran naka ya lalace"....✍🏻