JANNAH YAR GIDAN ANDERSON

Immune to pain ( free chapter as Barka dai sallah )

by @zahrabmrs02


A hankali Jannah ta fara buɗe idanuwanta wadanda suka yi mata nauyi saboda tsabar kukan da ta sha da kuma jirin da ya kwashe ta. Kamshin dakin ya tabbatar mata da cewa tana cikin babban Penthouse dinta na alfarma dake Kano, gurin da babu mai takura mata.

Ta yunkura zata tashi zaune, sai ta ji wani irin zafi a  hannunta; ta duba ta gani ashe drip ne (ruwa) aka sanya mata A gefen gadon kuma, Amani ce zaune fuskarta cike da tsantsar damuwa da worry (fargaba), tana kallonta cikin tausayawa.

Jannah ta gyara muryarta da ta dashe, ta kalli amintacciyar kawar tata tace, "Amani... ya akayi nazo gida? Me ya faru a ofis ?


Amani ta sauke nannauyan numfashi, ta matso ta gyara wa Jannah lafiyayyan bargon dake jikinta, muryarta   sanyaye tace, "Alhamdulillah da kika farfado Jannah. Zuwa nayi na sameki a ofis dinki a yashe dama sanda na Kira ki Ina hanyar Karasowa 

Amani ta cigaba da bayyana mata dabarar da suka yi, "Ganin halin da ake ciki, na san muddin aka barki a gurin, kafofin yada labarai za su zo su dauke ki a wulakance. Shi yasa na nemo your trusted boy Sule (Suleman). Shi ya tayani muka dauko ki da sauri, muka fita dake ta back door (kofar baya) ta kamfanin baki daya, ba tare da kowa ya ganmu ba ko ya dauki hotonki!"

"Muna zuwa nan gida," Amani ta nuna robar ruwan dake diga, "Na kira Dr. yunus  ya zo duba ki, shi ne ya ce jinin ki ya hau sosai saboda shock, shi yasa ya kara miki wannan ruwan domin ki samu natsuwa."


Jannah ta kalli Amani cikin mamaki, "Amani... Why are you still here? (Me yasa har yanzu kina nan?) Ba ki ji allegations (zarge-zarge) da kazafin da duniya ke faɗa a kaina ba a Twitter?"

Amani ta saki wata 'yar gajeruwar dariya mai daci, ta dubi Jannah ta ce, "Come on, Jannah! Ina ruwana da wani maganganun mutanen gari? Ko da gaske ne ke kika kashe su Mr. and Mrs. Anderson ɗin—wanda na sani sarai ba hakan ba ne—ai wallahi ba zan taɓa guje miki ba!

Fuskar Amani ta juye zuwa bacin rai lokacin da ta tuna asalin tushen matsalar. "Ni dai yanzu abin da ke damuna... ya aka yi har kika yi trusting (yarda da) wannan foolish boy ɗin can, Aliyu, har ya sami damar yaudararki haka? Mutumin da kika bama kariya, shi ne zai watsa sirinki a duniya?"

Jannah ta lumshe idanuwanta wadanda suka yi nauyi, ta dafe daidai saitin zuciyarta da ke mata zafi. "Mu bar maganar Aliyu, Amani... it's past now (ya zama tarihi yanzu). Na gode sosai, na gode kwarai da kika tsaya da ni."


Jannah ta ɗan waiga dakin, ta tuna wata dambarwar daban ta ce, "Ina Salma?"

"Oh, that whore ? (Waccan  karuwa ?)" Amani ta faɗa cikin lallausan murmushi mai cike da ma'anoni da yawa. "Ta kirani tana ta kuka kina bacci. Wai dazu-ɗazun nan suka tafi London ita da bilal mijinta  jikinsa ya yi tsanani sosai! Har ta tura mini pictures (hotuna) dinta a airport suna shirin shiga jirgi."


Jannah ta mika hannunta dake rawa kadan amma fuskarta babu alamun tsoro, ta kalli Amani tace, "Miko min wayata  Amani."

Amani ta ja baya da sauri, ta boye wayar a bayanta tace, "Waya kuma Jannah? Don Allah please (ki yi hakuri), kada ki duba komai yanzu."

Jannah ta saki wata 'yar gajeruwar dariya mai cike da daci, ta dubi kwan mika na drip din dake jikinta tace, "Kar ki damu Amani. Kina ganin akwai abin da ya rage da ban gani ba a duniyar nan? Kar ki damu, I am immune to pain (na dade da dorewa da radadin zafi, ba zai min komai ba)."

Amani ta mika mata wayar cikin sanyin jiki. Tana budewa, sakon Alhaji Bashir ne ya fara bayyana radau a allon wayar:


"I told you, you won't see me coming! Shame on you Jannah Anderson... ooops Jamila yar kauye! And one more thing, Anderson Global ya kusa zama nawa baki daya!"


Tana gama karantawa, sai ga na gaba daga gurin Nadiya:


"How far Jannah? Oh Jamila, your real name! Arziki ya miki kyau fa 😂 da emoji din dariya Yanzu ya zaki yi da wannan public humiliation din (wulakancin da duniya ke miki)? Da nice ke, da yanzu na rataye kaina, shi ne mafi sauki da mutunci. Best advice kenan da zan iya baki!"


Assalamu Alaikum masoyana da masu karanta littattafai na. Ina muku  gaisuwa mai cike da farin da fatan alkhairi a wannan babbar rana ta Eid al-Adha. Allah ya maimaita mana   Barka da Sallah! fam ❤️

ga masu kirana a waya suna jiran update to gashi ya sauka 
kun dai hanani sallah break 🥹