BARRISTER SUHAIL

BARRISTER SUHAIL

by @officialkhadeey

🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾

Mallakar

KHADIJA WRITES

YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION
(YOTA)


💖 Dedicated To My Mom 💖

BARKA DA SALLAH DA FATAN KUNYI SALLAH LAFIYA


بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

🅿️----17 

yana shiga ciki Iman ta koma bakin gado ta zauna wayar ta , ta dauko tana san kiran Ammi ganin karfe bakwai na safe yasa ta bari sai anjima dan kar tayi tunanin ko ba lafiya ba.

tashi tayi ta fita falo tana karewa gida kallo kofar da ta gani a rufe ta tabbatar da nan ne Kitchen ta shiga mutuwar tsaye tayi ganin irin kayan Kitchen din da Malan ya zuba mata a ciki babu Abinda babu na more Rayuwa haƙiƙa sai yau ta tabbatar da yar gata ce ita gaba da baya Hannu ta daga tayi addu'ar masu addu'ar gama da duniya lafiya 

ta fara duba abubuwan da basu yi mata ba ta gyara har karfe tara kafin ta koma dakin ta wanka tayi ta fito daure da towel bakin mirror ta nufa ta fara shafe jikin da wasu lotions masu masifar kyau da tsada iya kamshin su masu tsada hankali ji tayi kawai tana son tayi light make up duk da ko a gida kwalliya ba wani damun ta tayi ba.

bayan ta gama ta fito da wani dark and light purple lace dinkin riga da siket bakin mirror ta nufa ta daura dankwalin ta

ko ba'a faɗa ba ita kanta tasan tayi kyau light purple veil ta dauko ta yafa ta koma bakin gado ta zauna Muryar yaya Mubarak kawai take san ji wayar ta dauko tayi dailing Number cikin Sa'a ko ya Daga

"Amarya na dauka kin manta da yayan naki"

ido ta zaro tamkar tana gaban sa ta ce"haka Yaya mubarak ya  za'ayi na manta dakaii"

murmushi yayi yace"nima wasa nake maki Autar ya kike ya gidan munyi kewar ki sosai"

"nima haka yaya ina Malan da Ammi"

"suna gida, ina cikin mota zani kano aikin da na cile jiya suka kirani nazo na amshi offer kuma next week zan fara aiki"

Wani irin kara ta saki dan da yaya Mubarak na kusa da ita  babu abinda zai haka ta rungume sa tsabar farin ciki da take ciki ,tasan yadda yayanta ya damu da aikin nan kullin addu'ar sa Allah ya sa ya samu aiki a wannan ma'aikatar"

sai da tayi controlling kanta ta ce"Alhamdullilah yaya Allah ya bada sa'a da rabo mai amfani"

"Amin iman sai anjima ki gaida mai gidan naki"

bai jira ta kara magana ba ya kashe wayar.

ajiye wayar tayi tana ta fara'a tare da godewa Allah da ya ba yayan ta Sa'ar samun aikin da ya jima yana mafarkin samu.

Suhail ne  tsaye gaban mirror yana taje sumar kansa sanye yake cikin wani dark green din yadi dinkin Captain yayi matukar yi masa kyau agogon dake sanye a hannun sa ya duba ganin karfe goma saura yasan zuwa yanzu iman zata ji yunwa kuma yana da yaƙinin mami bazata aiko masu komai ba ,baya da wani option ila kawai yaje resturarant ya samo masu abinda zasu ci.

key din motarsa ya dauka da Atm card dinsa ya fita falo sai kuma ya dawo kofar Dakin iman ji yayi ya kamata ya tambaye abinda zata ci gudun kar ya siyo mata abinda bata da ra'ayi knocking yayi a bakin kofar Iman dake zaune bakin gado ta tashi ta nufi baƙin Kofar haka kawai taji zuciyarta na bugawa sai da ya sake knocking a karo na biyu ta buɗe.

hade ido suka da sauri ta dauke idanunta ta rasa miyasa Suhail keyi mata kwarjini  kawar da idanun ta tayi kusan mintuna  biyu suka kwashe a haka Suhail na kallon ta tun daga sama har kasa kamshin humrar ta na rasa zuciyar sa karon farko da ya ji turaren wata mace ya birgesa. 

ji tayi ta Tukura da kallon da yake yi mata "ina kwana ta faɗa cikin wani irin cool voice"

"morning how was You night"

zuciyar ta ta buga tunawa da tayi da yadda ya shigo daki ya ganta jiya  ƙasa amsawa tayi ganin bazata yi magana ba ya ce"mi zaki ci for you break fast"

"Komai ma" ta fada 

fita yayi ta turo kofar dakin ta koma ta zauna har lokacin zuciyar ta bata daina bugawa ba 

Suhaila na shiga cikin motarsa kiran Aunty Fauziya ya shigo bayan sun Gaisa ta tambaye sa iman ya ce"lafiya qlau"

"dama breakfast din kune tun dazu na rasa wanda zai kawo Yawale driver kuma sun fita da Alhaji"

Suhail ya ce"okay Aunty on my way"

katse wayar yayi a zuciyar sa yake yaba kyawawan halayen Aunty Fauziya ina ma Mami ce da irin wannan halin da ta Zauna da kowa lafiya da wannan tunanin ya nufi bakin gate horn yayi mai gadi ya buɗe ya ja motar ya fita.

a Kofar gidan su yayi parking knocking yayi baba mai gadi ya buɗe masa yana ganin suhail fara'ar fuskarsa ta Karu har yana tsokanar sa da ango Suhail ya shiga ciki ba tare da ya biye baba haladu ba 

part din Mami ya shiga babu kowa  a palorn sai tv dake faman aiki upstair ya nufa Mami ce tsaye bakin wadrope tana jera kayan ta Amatullah na kan gado tana game da wayar mami.

bayan yayi sallama  ya shigo Amatullah na ganin sa da gudu ta ajiye wayar ta ruga tayi huging din sa tare da cewa "welcome Uncle i have been seraching for you all this While ban ganka ba naje dakin kama baka nan na tambayi Momy ta ce kana sabon gida kai da Amarya"

murmushi yayi yaja ta cikin Dakin dan Amatullah badai surutu ba duka duka shekarunta biyar kacal a duniya amman idan tana surutu zata rantse tafi shekarun Tana matuƙar son Suhail Fiye da tunani kullin tazo kaduna tana like da shi bacci kadai ke rabasu shima ta fanin Suhail haka ne yana matukar san yaran yan uwan sa more especially  Amatullah da jinin su yazo ɗaya kullin tazo sai ya fita da ita ya siya mata ice cream da kayan wasa hakan yasa take jin shi a ranta hatta yan class dinsu kullin tazo kaduna ta koma sai ta basu labarin Uncle Barrister.

Mutane da dama ma sun dauka Amatullah diyar sa ce 

Suhail mutun ne mai son yara sosai ko a hanya yaga yaro ya birge sa sai ya yi masa kyauta.

Kan kujerar dake cikin Dakin  ya zauna Amatullah ta haye jikin sa 
gaishe da mami yayi ta Amsa ba yaɓo ba fallasa haka ya kara ci zaman sa ya fita zuwa falon kasa Amatullah na biye dashi ya tambaye ta mamanta Aunty Zarah ta faɗa masa suna gidan Aunty Aisha ita da Naima sun je duba  Aunty meerah ba lafiya.

wajen zama ya samu a falon da alama bakin Amatullah da magana kallon ta yayi ya ce"miya samu meerah"

sai da ta juya bayan taga ba kowa ta kamo kunnen Suhail ta ce"naji aunty aisha na fadawa momy na wai ciwon so ne wai saurayin da take so yayi aure shine fa aunty meerah ta damu ko abinci bata ci duk ta rame
Dariya Suhail yayi ganin yadda Amatullah keyi masa raɗa a kunne murmushi yayi ya ce"Amatu wanene wannan saurayin kuma a ina yake"

buɗe hannu tayi Alamun bata sani ba itama 

"Uncle a Turancin ta ciwon so shine love sickenss ko amman what cause it"

Suhail ya ce "yana nufin idan kana son mutun baya sanka shine kake Kamuwa da ciwo"

Amatullah ta fashe da dariya ta ce"uhmm su yaya meerah iyayen soyyaya ni fa Uncle tunda naga bata maka magana nima shiyasa ba Ruwa na da ita koda momy ta ce na raka su na ce no"

"Why,ki rinka mata magana she is You sister kuma nima tamin magana kawai da bata yi gaban mutane ne bata yi"