GADAR TSAUTSAYI

GADAR TSAUTSAYI 4

by @nusybee143

Page 4



Shiru aunty Arfa ta yi tana kallonsu, Amina ta ja tsaki tana gyara zaman hular kanta,ta ce"dama wannan matar tana da wani hali wallahi, yanzu don Allah me zai ragu a jikinta idan ta yi mana fatan alkhairi saboda Allah?

Amma saboda wani hali sai ta kama wani fata?to ta Allah ba tata ba,za mu je abroad,za muyi karatu,za mu zama wasu,zamu zama manyan mutane in sha Allahu"ta ƙarasa maganar tana dariya,su ma suka hau dariya

Kallonsu kawai Arfa take yi, kafin ta taɓe baki ba tare da ta tanka ba,ita fa wannan gaba ta kai ta,ba don wannan abu da ya faru ba ita ai da bata cika burinta ba, don haka can ta matse musu, ita dai tunda ta samu biyan buƙatarta ai shikenan,su yi karatu ko kar su yi wannan damuwarsu ce

Surayya ce ta dube su ta ce"kuma fa ta ba ni tausayi "ta ƙyalƙyale da dariya,ta ce"maganar gaskiya,ita kenan yar,amma a dalilin karatu ta fanɗare "

Amina ta taɓe baki, Iman ta ce"ni ban damu da komai ba,ko tausayi ba ta bani ba

Abin takaicin shine lokacin da ƴar tata take cikin gidan nan ai fifita ta ake yi akan kowa na gidan 

Ba ƙaramin daɗi na ji ba da wannan abu ya faru

Yaya Safwan fa ya ba mu labarin lokacin da suke yara kiri-kiri Abba yake nuna ya fi sonta,gata yar wulaƙanci ta yi ta rashin mutunci kala-kala wai ita babbar yaya

Yanzu sai a je can,wa ya sani ma ko ta bar duniyar?"

Arfa ta kalle ta, Iman ta ce"tabbas haka yaya ya ce,kuma dama kin ga sai wani izza suke nunawa kamar su ɗin wasu tsiya ce"

Surayya ta ce"cheer up girls!

Mu dai burin mu ya cika,in sha Allah sai mun je abroad,mun yi karatu da yawa, mun yi amfani, sannan mu dawo gida mu auri musulmi wanda Abba ya zaɓa mana "suka yi dariya suka tafa

Arfa murmushi ta yi kawai,ta ɗauki ƴarta jaririya wadda bata wuce watanni uku ba ta fice daga ɗakin tana cigaba da murmushinta






*ROXY*

4:00pm......

A nutse take ɗaure dogon gashinta wanda yake da tsananin tsawo da cika,a hankali kuma ta dakata tana ƙurawa kanta kallo a jikin madubin da yake gabanta 

Ƙirjinta ne ya doka,a hankali ta lumshe idanu ta buɗe, saboda fuskar da take kalla,a hankali wani abu da ya shuɗe ya dawo mata ƙwaƙwalwa 

'Kalle ki sak gyatumarki,don haka wajenta za ki tafi '

'Abba na ni dai kai nake so ka ɗauke ni '

'Ba zan ɗauke ki ba, saboda mamanki ta yi son kai,ta kwashe kamanninta kaf ta liƙa miki don son kai!"

"Ummeena wai haka?

Dama ana iya ɗibar kamanni a zubawa mutum?'

'ke rabu da ni da wannan shirmen,wuce mu tafi'

'Aa fa Hajiya,babu wanda zai saka yarinya ta tafiya da ƙafa,ba ni hannunki,zo nan na ɗauke ki'



Ƙasa ta yi da kanta tana ba wa ƙwallar da ta taru a idanunta damar zuba,bata da wani fata a duniya irin sake ganin mahaifiyarta kafin mutuwa ta ɗauki ɗayansu,bata da burin komai sama da hakan,komai na rayuwa yana tafiyar mata yadda take so amma banda wancan ɓangaren

Motsin da ta ji ne ya sa ta goge hawayenta,ta dake, saboda ta san Amra ce mai shigowa,gashi a duniyar nan tata babu wanda ta taɓa yadda ya ga rauninta, wannan ma yana ɗaya daga cikin abun da ya kassara mutanen da suke son ganin bayanta

"Hi Roxy!"ta ji muryar Amra tana yi mata magana 

"Hi!come in!"ta bata amsa idanunta akan madubin tana cigaba da gyara dogon gashinta

Shigowa Amra ta yi tana kallon Roxy kamar zata haɗiye ta,ita dai wallahi tana tsananin son wannan classic lady ɗin,bata taɓa jin tsananin sha'awar wani ko wata a duniya ba kamar yadda take jin ta Roxy 

Kyakkyawar mace ce,dirarriya,mai tsarin kyau da ƙawatuwa,ta ko'ina ta cika mace har mace

Amma duk da wannan kyan nata Amra sai dai ta kalla daga nesa, saboda ko da wasa bata ga fuskar da zata neme ta ba

"Hey! madam!!

Why are you staring at me?"muryar Roxy a tsawace ta katse ta daga dogon tunanin da ta lula 

Ajiyar zuciya mai nauyi Amra ta sauke tana ɗauke kanta, Roxy ta aika mata harara ta ce a fusace "ya zama na ƙarshe, kin sani tuntuni, Roxy bata san kallon ƙurilla,idan wani abu kike so ma a jikin Roxy to kin fi kowa sanin ba za ki samu ba"

Murmushi Amra ta yi ta ce"meyasa kike da ƙwarin gwiwar sanin ba zan samu ba?"

"Saboda wannan ita ce gaskiyar da za ki sani, da alamu har yanzu ba ki san wacece Roxy ba"ta ƙarashe magana tana shigewa cikin closet ɗinta don saka kaya

Murmushi sosai Amra ta yi tana faɗin "kar ki cika ƙwarin gwiwa Hermosa!

Nice Amra fa, wadda komai ta saka a gaba sai ta same shi 

Ba baƙuwa ba ce ni a bariki,a tsawon shekarun da na ɗauka ina bariki ban taɓa saɓa saiti ba"

Kallonta Roxy take yi tana jefa mata wani murmushi da ita kaɗai ta san ma'anarshi, kafin ta ce"Goodluck ƴan matan bariki!

With time za ki gane bariki tunani yake cinyewa,ba ƙwaƙwalwa yake buɗewa ba"bata bari amra ta sake magana ba ta jefa mata dogon hijabin da ta dauko,ta ce"tashi mu tafi, kar ki fita a haka "

Galala ta bi hijabin da kallo,kafin ta mayar da kallonta ga Roxy, wadda take sanye da doguwar rigar abaya,ta ɗaure dogon gashinta sannan ta fara ƙoƙarin saka dogon hijabin da ta ɗaukowa kanta 

"Ina zamu je haka ne?"Amra ta jefa mata tambaya tana tsare ta da idanu

Ba tare da ta kalle ta ba ta ce"tashi mu tafi"

"Na ce ina za mu tafi?"ta sake tambaya tana tsare ta da idanu 

Bata ba ta amsa ba,sai kammala saka hijabin da ta yi ta nufi hanyar fita daga parlourn,kan dole Amra ta miƙe,ta bi bayanta tana kallon yadda jikinta yake rausaya a cikin hijabin, kamar wadda take yi da gayya, Amra ta yi murmushi tana lashe baki,a ranta kuwa tana ɗaukar alwashi iri-iri 

Abin na Roxy bai sake bawa Amra mamaki ba sai da ta ga ta zaro niƙab ta ɗaura a fuskarta, Amra ta dube ta da mamaki,cike da rainin wayo ta ce"ikon Allah?

Roxy ina kika koyi shigarmu ta musulmai?

Kuma fa kin yi kyau kamar ba ke ce mai shiga yadda ta ga dama ɗin nan ba"ta ƙarashe maganar tana wata ƴar dariya mau tarin ma'anoni 

Roxy ta ɗago ta kalle ta da wani yanayi a fuskarta,a karo na farko da ta ji ta muzanta irin wadda bata taɓa yi a rayuwarta ba,da wata iriyar murya ta ce"au?

Ke yanzu kallon musulma kike yi wa kanki dama?"

"Da mamaki Amra take duban Roxy ta ce"kamar ya kenan?

Ban gane maganar taki ba Roxy!

Ina kika san musulunci har da za ki san yaya musulmai suke gudanar da rayuwarsu "

Roxy tana wata ƴar dariya ta ce"of course a TV, programs da suka danganci musulunci ba sa wuce ni sam"

Amra ta ce"hakan bai amfane ki ba, tunda ba ki musulunta ba har yanzu "

Roxy ta yi murmushi ta ce"to ke menene shaidar da za ki kare kanki a wajena na cewa ke musulma ce?

Sallah?azumi?ko sauran ibada?

Kin ga ki wuce mu tafi,ina da wani abu mai muhimmanci da zan yi kafin na bar ƙasar nan,ina so na bi jirgin 4:00pm,so nake within 24 hours na sada Alejandro d kayansa, saboda bana son ya sake yi min hauka,saka hijabin nan "ta ƙarasa maganar da sigar bayar da umarni

Amra bata yi mata musu ba,ta saka hijabin,ita kuma Roxy ta ɗaura niƙab ɗin suka fice daga gidan 

Abin da ya ƙara ba wa Amra mamaki bai wuce ganin Roxy ta tsayar da daidaita sahu ba,duk da yawa da kuma ingancin motocinta da sauran ababen hawanta 

Amra bata samu damar yi mata wata tambaya ba,duk da yadda kanta ya cushe da tambayoyi saboda mamakin Roxy 

Kai tsaye wata unguwar talakawa suka nufa, unguwa ce ta masu ƙaramin ƙarfi,ƙananan gidaje,da ƙananan lunguna,ga kwatoci ko'ina, shara kuwa wajen kaca-kaca,ga tsamin kwata da yake tashi a kowacce kusurwa ta unguwar 

Ita dai Amra sai yatsine fuska take yi fuska a matuƙar ɗaure,a ranta tana jajen inda Roxy ta san wannan wajen,har ta iya kawo su

Wani tsuekukin mataccen gida suna nufa,wanda rabin katangar gidan ma ta zaizaye ta zube,da alamu ma gidan da har ƙasa aka yi,aka yi masa plaster,

Kai tsaye ba tare da damuwa ba Roxy ta kutsa kai cikin gidan, Amra ta bi ta da kallo tana cin birki a ƙofar gidan,sai da Roxy ta shiga soro sannan ta leƙo tana kallon Amra da ta ci birki tana bin ta da wani kallo 

Ba tare da damuwar komai ba ta ce"ki shigo mana,tsayuwar me kike yi a nan?"

"Ina ne nan?"ta jefa wa Roxy tambayar 

Kai tsaye Roxy ta ce"wannan abin da ya shafe ni ne,idan za ki shigo kawai ki shigo"

Kan dole Amra ta shiga gidan ba don ta so ba,tana kallon ko'ina a yatsine, gidanma ma ƙyanƙyami yake ba ta, saboda yanayin gidan,sai ya yi mata kana da ƙazanta,duk da cewa daidai gwargwado an gyara gidan

Da sallama Roxy ta shiga gidan, Amra ta kalli Roxy da tsananin mamaki jin tana yin sallama,abin da bata taɓa jin ta yi ba,wata mata da take zaune a tsakar gidan mai kama da wajen kiwon dabbobi ta ɗago tana kallon Roxy tana amsa sallamar da murmushi a fuskarta, Roxy ta ƙaraso ta durƙusa tana faɗin "Barka da yamma Mama"

Matar tana ɗan murmushi ta ce"Barka dai, barkanku da zuwa,sannunku da zuwa"ta miƙe jikinta yana tsuma ya ɗauko tabarma, wadda yara sun kusa lalata rabi,ta shimfiɗa musu,ta ce "bismillah,ga waje ku zauna 

Ke ma zauna"ta ƙarasa maganar tana duban Amra wadda take tsaye ƙiƙam tana kallon su ba tare da ta yi magana ba

Still bata yi magana ba,sai na ɗan matsawa da ta yi baya tana ɗan yatsine fuska don kar matar ta taɓa ta,itama bata yi mata musu ba ta ja baya fara'ar fuskarta tana ɗan raguwa,alamun abin da Amra ta yi mata ya sosa mata rai,ita dai Roxy tuni ta hakimce akan tabarmar tana ɗage niƙab ɗinta 

"Mama ina yini!"ta gaida ita

"Lafiya ƙalau,ya hanya?ya iyali?ya kuka zo?"

Roxy ta yi murmushi ta ce"lafiya ƙalau, Mama na san ba ki gane ni ba ko?"

Mama tana ɗan murmushi ta ce"ban shaida ku ba wallahi 

Ku yi haƙuri gidan babu ruwa ne, gashi yaran suna islamiyya ballantana su karɓo muku a shagon ilyasu"

Murmushi sosai Roxy ta yi tana girgiza kai, ta ce"kar ki damu Mama,na san ba ki gane ni ba ko?

Kin tuna wadda ta kawo miki ziyara kwanaki kaɗan bayan samun Habu?"

Shiru Mama ta yi na some seconds, kafin ta ce"eh tabbas na tuna, Hajiya ya za'a yi na manta wadda ta yi min alkhairin da har yanzu nake mora?

Ai ni babu abin da zan ce miki ni da Habu sai fatan Allah ya biya ki da alkhairi, Allah ya saka miki da mafificin alkhairi"

Roxy ta yi murmushi tana faɗin "babu komai Mama,ina Habu da ƴan'uwan nashi suke?"

Mama ta ce"ai da yake an saka shi a allo ne,suna makarantar allo,sai zuwa anjuma za su dawo"

Roxy ta yi ɗan jimmm kafin ta ce"ba sa zuwa makarantar islamiyya ne Mama?"

Mama ta yi ɗan murmushi ta ce "da dai suna zuwa,amma kin san abu na yau da gobe,sai abubuwan suka fara yawa, abinki da hannu ɗaya, tunda kin ga mahaifin nasu ya rasu babu jumawa da tsintar Habu,to shine dalilin da ya sa suka koma allo kawai"

Roxy ta jinjina kai cike da jimami ta ce"Allah ya ji kan shi da rahama,to boko kuma fa?"

Mama ta ce"suna zuwa,habu ma ya fara zuwa wannan zangon da suka koma makarantar "

Roxy ta jinjina kai cike da gamsuwa ta ce "to Allah ya taimaka,zan samu ganinsa?"

Mama ta ce"eh sun kusa shigowa ma,ba za su wuce mintina goma ba, ƙarfe biyar suke tashi"

Roxy ta gyara zama ta ce"babu damuwa, bari na jira shi ya dawo,za mu gaisa"

Amra da take ta kallonsu cikin takaici ta dubi Roxy fuska a daure tana faɗin"Malama idan bata min lokaci za ki yi Just tell me,kin kawo ni wajen da za'a kashe ni da ƙazanta,ga warin talauci ya ko'ina,kin san ban saba rayuwa a irin wannan wajen ba,idan ke kin saba fine,but idan ba za ki taho ba ni sai na tafi "







#Nusy_bee