BARRISTER SUHAIL
🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾
Mallakar
KHADIJA WRITES
YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION
(YOTA)
⸻
💖 Dedicated To My Mom 💖
⸻
بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
🅿️----18
hirar da yake da Amatullah taso mantar dashi abinda ya kawo shi tashi yayi zai fita Amatullah ta ce"Uncle zan bika"
juyowa yayi ya kalleta ya ce"ki same ni part din aunty Fauziya"
da gudu ta koma Dakin mami har lokacin bata gama jera kayan ba ganin Amatullah na kokarin saka takalmi ta ce"Amatullah ina kuma zaki je"
"Mami zan bi uncle ne"
da sauri ta fi ce daga dakin kar Mami ta hana ta zuwa
Suhail ne zaune falon aunty Fauziya suna gaisawa ta ce"Suhail ya gida ya amarya?"
murmushi gefen baki yayi ya ce"Lafiya qlau Aunty"
tashi tayi ta dauko breakfast din data shirya cikin wani kyatttacen basket ta dire a gaban sa
Amatullah ta shigo cikin shirin fita aunty Fauziya ta ce"Amatullah ina zakije da safiyar nan"
bata rai tayi ta ce"aunty ni Uncle zan bi"
"kuma tun da safe ki bari mana anjima da yamma idan su Zarah zasu ba sai ku tafi tare ba"
Kuka take son yi Suhail ya ce"aunty ki barta kawai mu tafi taren"
"to shikenan Suhail agaishe da amarya "
a back seat din motarsa ya saka basket din ya buɗe wa Amatullallah front ta shiga ya tada motar yayi gaba
Amatullah ta ce"Uncle baka fadamim sunan Aunty amarya ya ba"
Suhail ya ce"Nima ban sani ba amman yanzu idan munje sai ki tambayeta,kinga idan ta faɗa maki nima zan sani ko"
Amatullah badan ta yarda da Abinda suhail ya ce ba taya zai ce baisan sunan matar sa ba
a haka suka isa kofar gidan bayan ya shigar da motar ciki ya dauko basket din ya kama hannun Amatullah zuwa ciki a kan dinning ya ajiye ya koma falo ya Zauna
"Uncle ina aunty Amarya"
"her room" ya faɗa tare da mata nuni da kofar dakin
ya ce"ta fada mata ta fito ta ci abinci"
Iman ce kwance akan gado tana duba hotunan biki da hafsat ta turo mata yanzu ta whatapps
Amatullah ta murda kofar dakin ta shiga da sallama a bakin ta,iman dake kwance jin a buɗe kofar dakin ta juyo da mamakin ta taga yarinya karama ta nufo ta.
Amatullah ta zauna gefen gado tana murmushi ta kalli iman ta ce"good morning aunty Amarya"
"morning my dear ykk"
Amatullah ta ce"i'm fine"
shiru Iman tayi tana kallon ta ganin bata san ko daga ina take ba amman taji lokacin da Suhail ke shigowa da motar sa kila tare suke
Kusan mintuna biyu babu wanda yayi magana Amatullah ta ce"Aunty baki sani ba ko"
iman ta daga mata gira "Eh"
dariya tayi ta ce"my name is Amatullah momy na kuma Aunty Zarah yayar Uncle Suhail ce mijin ki"
Iman ta tuna da ranar da aka kawo kayan tabbas taji aunty zaituna ta amshi Sunan Zarah a wanda aka kawo lefen tare
murmushi tayi ta ce"Ina mamanki"
"sun tafi duba aunty meerah wai ciwon so ke damunta"
a yadda Amatullah tayi magana sai da ta ba iman dariya ita ko ina tasan wani abu wai ciwon so ko ita da take matured aka titsiyeta aka tambaye minene ciwon so bata san ma mi zata ce ba ko dan bata taɓa yin saurayin da taji ta kamu da san sa bane oho
Iman ta ce"to Allah ya bata lafiya"
Amatullah ta ce " Ameen Amman ke baki faɗamin sunanki ba"
iman ta dafa kanta ta ce" sunana Iman"
"wow nice name zan kiranki da Aunty iman ai yayi ko kinga yanzu ke matar Uncle ce"
har ta kai bakin kofa zata fita ta juyo ta ce"Aunty uncle ya ce kin fito kiyi breakfast"
Amatullah ta koma palor wajen Suhail yana zaune inda ta barsa yana danna wayar sa kusa dashi ta zauna ta ce"Uncle na tambayeta sunan ta she said iman"
Sai lokacin ya tuna da kusan haka ya gani Lokacin da yaga invitation din da Abba ya basa dan shi bai ma tsaya karantawa da kyau ba"
Amatullah ta katse masa tunani da cewa" Uncle you got a beautifull wife wallahi tana da kyau sosai blacks beauty and i like her cool voice"
Suhail ji yayi surutun Amatullah ya soma isar sa ya tashi zai koma dakin sa ya ce"wait for her ta zo kuyi breakfast"
har ya shiga daki tana kallan kawai dan tana yabon matarsa sai ya tashi ya wani shige turo baki tayi ta cigaba da kallon tv
shigar suhail daki kenan Iman fito plate ta dauko da cup a Kitchen tayi serving din su fried yam ce da pepper soup din kayan ciki sai ment tea tare suka ci abincin da Amatullah bayan sun kammalwa Iman ta kwashe kayan zuwa Kitchen Bedroom din suka koma.
Amatullah hannun ta rike da wayar Iman ta kunna mata game sai zuba mata surutu take sai ta bita da uhmm ko a'a dan ta soma gajiya da
Maganar ko dan bata saba bane.
Amatullallah ta ce"aunty iman nasan Favourite Food din uncle idan zakiyi launch i will help You mu girka masa nasan zaiji dad'i nima idan momy na ta girka wa daddy Favourite din kullin sai ya bata gift"
iman ta ce"okay tom shikenan"
suna zaune a haka har aka kira sallah Azahar Iman ta saka Amatullah tayi alwala ta bata hijab sukayi Sallah tare
bayan sun gama suka nufi Kitchen dora abincin rana fridge ta daga taga babu abinda babu nan suka fara dora faten doya da farfesun kayan ciki kamar yadda Amatullah ta ce shine fovourite food din Suhail da ko a ina ya aka bashi shi bazai iya denied ba.