NADAMA page 1
by @mrsomar
NADAMAR DA NA YI 🙆🏼
Fatima Isa
Sabon Edit..2026
Littafin kyauta (Free book)
Love story 2016😍
PAGE 1
Da sunan Allah mai Rahama mai jinƙai ina godiya ga Allah subhanahu wata'ala Allah ka sa yanda na fara rubuta littafin nan lafiya, na gama shi lafiya amin.
GARGAD'I
Wannan littafin nawa ƘirƘirarre ne banyi shi dan cikin fuska wani ko wata ba na yishine dan ilimantarwa haɗi da nishadantarwa, ban yarda wani ko wata su ɗauki koda kalma ɗaya daga cikinshi da niyyar su juya min littafi ba, in ba tare da izinina ba, duk wanda yayi haka to ban yafe ba.
*********
Parlour ne na gani na faɗa wanda ya ke ɗauke da lautsa_lautsan kujeru, ƙayatuwar parlourn kawai zai tabbatar maka da gidan wani attajirin mai kuɗi ne. Parlourn tsit yake baka jin motsin komi sai sautin kuka ƙasa_ƙasa. Zaune yake akan kujera ya ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya, yayinda fuskarsa na kan wadda taketa faman kuka kanta a ƙasa yake sai dai hawaye kawai dake sauka akan hannayen ta. Ƙafarshi ya sauke ƙasa ya gyara zamanshi kafin ya sauke ajiyar zuciya ya ce.
"Fatima kada kiga ina maki faɗa kiyi tunanin kamar bana sonki ne a'a ina maki faɗa ne kawai dan irin son da nake maki, nasan bazaki gane hakan ba sai bayan ba raina, ni ina son na gina maki rayuwa mai inganci, kada ki manta ke ɗaya mahaifiyarki ta haifa, shiyasa na zaɓa maki miji da kaina, saboda na tabbata Faruq yaron kirki ne. Fatima a matsayina na mahaifinki ki ɗaure ki amshi Faruq a matsayin mijin auranki, idan kika yi min haka kin gama min komi a rayuwa please."
A hankali ta ɗago jajayin idannunta ta dubi mahaifin nata da duk hankalinshi na kanta cikin muryar kuka ta ce.
"Dad I know kana sona fiye da tunanina but Dad bani da burin da nakeso irin na k'yautata maka...Amma sai dai hakan ba mai yuwa ba ne, bazan iya hana abinda zuciyata ke so ba rabani da Musaddik tamkar rabani da rayuwata ne Allah na gani bazan iya auran Yaya Far....."
Marin da ya wanka matane ya sa ta haɗe sauran maganar da ke bakin ta. Tashi tsaye ta yi cikin zabura, da tsoron ganin fuskar mahaifin nata ta sauya lokaci ɗaya.
"Thanks Fatima da irin sakayar da kika nuna min a matsayina na mahaifinki wanda nasha wahalar tarbiyarta dake tun bakisan abinda duniya ke ciki ba, na gina maki rayuwa da har ta kaiki ga ganin wadda kike so har kike masayar yawu dani yau Fatima. To bari kiji da kyau Fatima no one can stop this marriage and it’s my final answer, zaki iya fitar min daga ɗaki."
Hannu yasa ya nuna mata hanyar fita da gudu tabar parlour ta nufi ɗakinta tana kuka, kan gado ta faɗa ta saki wani kuka mai sauti. Wayarta ta jawo da sauri jikinta na rawa ta danna wata number mai ɗauke da sunan NOOR HAYYAT ringing ɗaya aka daga, tamkar dama jiran ƙiran nata yake. Daga ɓangaran da ta kira naji ya wani sauke ajiyar zuciya mai sauti.
"Amincin Allah ya tabbata agareki yake sarauniyar matan duk duniya, haba tawa ina kika shige ne? ko kinsan zuciyata zata iya tarwatsewa a duk lokacin da na rasa wannan muryar taki mai daɗi kamar sarewa, banida wani buri da ya wuce injini kusa dake, a kullum ina rukon Allah ya nuna min lokakacin da zamu zama miji da mata, Sahiba lafiya naji kinyi shiru?"
Tunda ya fara magana Fatima ta lumshe idonta bata buɗe ba sai yanzu da ta saki sabon kuka.
"Ya salam haba SANYIN IDANIYATA wa ya taɓa minke? wallahi ko waye sai yaga b'acin raina dan ban haɗaki da kowa ba!"
Kuka ta k'ara fashewa dashi muryarta na rawa ta fara magana.
"Musaddik na shiga uku! Dad naso ya tarwatsa min zuciyata, ba susan cewa rabani da kai tamkar rasa rayuta...."
"Dakata Teema! ban gane abinda kike faɗi ba."
"Musaddik Dad yace zai aurar dani ga ɗan d'an uwansa Yaya Faruq..."
Wata irin tsawa yayi tamkar tana kusa dashi
"What! Faruq? No!!! dear impossible taya Dad zai raba anta da jini!? ko yasan rabamu babban kuskure ne. Ba komi Sahiba nasan ba komi yasa Dad yatsaneni ba dan kawai ya ga ni makaho ne ba ido shiyasa yake son rabamu, amma ki sani duk ranar da aka rabamu to daga ranar zan sha guba na mutu kowa ya hut..."
Da sauri ta daga murya cikin sautin kuka
"Na shiga uku haba Musaddik me yasa zaka faɗi haka ko ka manta zuciyata tamkar kitse ce Idan tanajin wannan kalaman naka zata iya narkewa, duk duniya bani da wani farin ciki da ya wuce na ganni a ɗakinka mun zama miji da mata a kullum mafarkina shine mukasance tare har abada, bani da wani buri daya wuce ka zama uban ya'yana ko bayan babu raina zanyi alfahari da haka"
Murmushi ya yi tare da gyara wayar a kunansa ya ce
Na sani rabin raina kece ke faɗa ana ji ai ni bakina bazai iya faɗin komi ba domin kuwa, zuciyata cike take da sonki babu macen da nake buri aura irin ki duk da na kasan ce ni ba kowa bane amma kika sadaukar min da rayuwarki"
"Dan Allah ka daina faɗin haka Noor hayat kai fa na daban ne buri na kawai muyi aure.."
"Ai kam babu rana babu kuma lokaci indai akan wannan dan iskan yaron ne dan haka idanma mafarki kike to ki farka idan kuma baki farka ba to tabbas wannan barcin naki ba lallai ki farka ba."
Da sauri ta ɗago kai tana kallon mai magana.
Wata mata ce fara 'yar kimanin shekara arba'in da wani abu, ta iso gabanta fuskarta a ɗaure babu alamar fara'a, a tare da ita.
"Wallahi Fatima kin bani mamaki, ashe har akwai lokacin da mahaifinki zai zaɓa miki abu ki ce a'a, har kina tunanin zamu so wani sama da Faruoq? ba mahaifinki ba koni ina mai farin cikin auranki da Faruoq saboda Faruoq yaron k'irki ne bazan taɓa man tawa da irin karamcin da Faruoq ya nuna min ba."
Kuka ta saki cikin sutin kuka ta ce.
"Haba Mom a matsayinki na mahaifiyata ya kamata ace kin goya min baya dan samun farin cikin rayuwata, Mom ina son Yaya Faruoq kamar yanda kike sonshi amma bada aure ba..."
Cikin fushi ta nufi wajan 'yar tata.
"Bada aure kike sonshi ba to da ubanki kike sonshi?"
"Mom baki fahimce ni ba nasan Yaya Faruoq yana da duk wani abu da ɗiya mace zata so shi, kuma wallahi da zuciyata babu son Musaddik a ciki wallahi da naso Faruoq Mom ki fahimce ne please Mom."
"Maganar banza."
Da sauri ta duka ƙasa ta kama ƙafar mahaifiyar tata tana rokonta.
"Please Mom listen to me, wallahi duk maganar da nake maki daga cikin zuciyata ne. Son Musaddik ya riga da ya mamaye zuciyata wanda yasa a duk lokacin da akayi gigin rabani dashi to wallahi zan iya rasa rayuwata."
Murmushi Mom tayi ta girgiza kai.
"Humm Fatima what did your father say? You know no one can change him. Dan haka kawai kiyi hakuri ki amshi zaɓinshi."
Kai ta girgiza zuciyarta kamar zata fashi ta ce
"Toh ni dai gaskiya Mom bazan iya zama da ko wane miji ba in ba Musaddik ba."
Cike da lalashi mom ta ɗan dafa kafaɗarta ta ce.
"Fatima kenan aure duk sunansa aure na tabbata idan kika aure Faruoq zaki soshi fiyi da son da kikewa wannan yaron."
Tashi Fatima tayi daga durkushin da take ta koma kan gado ta zauna taja majina ta ce.
"Mom na tabbata ke da Dad bazaku taɓa fahimta ta ba, wanda ya taɓa soyayya ne kawai zai fahimce ni. Mom kada ki manta duk sauran 'yan uwana babu wanda aka taɓa yi mashi auran dole sai ni Mom yanzu za'ayi min?"
Bakin gado Mom tazo dai-dai kusa da ita ta zauna tasa hannu ta dafa ta.
"Please Fatima promise me, bazaki taɓa kin wannan zaɓin na mahaifinki ba, wallahi Fatima saboda so da ƙauna da Alhaji ke maki yasa ya zaɓa maki miji mai NAGARTA kamar Faruoq.."
Ɗan lumfasawa tayi kafin ta ci gaba da magana.
"Sauran da kike faɗi bai yi masu auran dole ba idan kinyi tunani ai za kiga ba tarbiyarku ɗaya ba, abinda yasa Alhaji ya zaɓa maki Faruoq kenan dan irin tarbiyar da ya ga na baki. Humm Fatima sai gashi yanzu soyayya nason rufe maki ido ki manta da alkairin mahaifinki. Dan Allah Fatima ki taimaka ki tausaya min kada mutan gidan nan suyi mana dariya wallahi Fatima da ina da wata y'ar dana bama Faruoq ita dan ki samu farin cikin rayuwarki."
Magana Mom take kamar zatayi kuka haƙika Fatima ta tausayawa mahaifiyarta dan dai kawai babu yanda zatayi da soyayyar Musaddik a zuciyarta ne.
Gani ta yi ɗiyar tata bata da niyar ƙara magana yasa tatashi sai da ta kai daidai bakin ƙofar fita kafin ta ce.
"Idan kinga dama ki fita ga Faruoq can a parlour yana jiranki salan idan kinje kiyi mashi yanda kika saba a koda yaushe.
Baki ta turo kamar zinguro. Mom bata tsaya jin amsarta ba ta fita da sauri.
Cikin fushi taja mayafinta ta nufi parlour kamar zata tashi sama.
Zaune yake kan sofa one sites yayinda ya ɗaura k'afarshi ɗaya kan ɗaya, sanye yake da kakinshi na soja color army green, sunyi mashi kyau sosai kamar dan jikinshi akayi kayan, kyakkyawan matashi ne mai jini a jika dogo ne marar jiki sai dai yana da cikar gaba, shiba baƙi ba kuma ba fari ba, zamu iya kiransa da chocolat color watau (wankan tarwaɗa ) yanada hanci kamar biro fuskarshi dogowa ce yanada manyan idanuwa bakinshi ɗan k'arami ne ga wata suma mai laushin gaske a kanshi ba irin mai yawa ba saboda aikinsu ba'a barin gashi kai da yawa. daga nesa yana da cika ido. FARUOK AHMED LAMIDO kenan namijin duniya.
Tunda ta shigo kanshi ke duke a kan wayarsa yana dannawa, yayi kamar baisan ta shigo ba dan kuwa ko sallama batayi ba. Sai da yaga bata da niyar magana ya ɗaga kansa ya kora mata ido kamar zai cinye ta.
#Love
#yaudara
#Cin amana
#Kiyayya
#Fatima
#Farouq
#Musadiq
#Hafsat
#Bilal
#Aunty zee