Nadama page 2
by @mrsomar
NADAMAR DA NA YI 🙆🏼
Fatima Isa
Edit..2026
Love story 2015🥰
Free book
PAGE 2
Kai ta ɗago itama ta kura mashi manyan idannunta, fuska ta yatsina kafin ta ce.
"Ina kwana?"
Murmushi ya yi kafin ya girgiza kai ya cije leɓensa ya aje phone nashi a gefan kujera haɗi da lumshe ido, a hankali ya wani juya kwayar idonshi ya ce.
"Humm ashe kina magana? ai ji nake ke kurma ce."
Ya faɗa yana kallon kwayar idonta.
Fuska ta yatsina ta turo baki.
"Fatima kenan wai sai yaushe za ki gane Allah ɗaya ne? ki amince dani nazama uban ya'yanki."
Kai ta girgiza cike da bakin ciki ta ce
”Ai kam babu rana ba lokaci, dan zuciyata mutum ɗaya na mallakawa ita, Yaya Faruok kasani bazan taɓa amincewa da kai a matsayin mijina ba."
Sake girgiza kai ya yi dan jin kallamanta masu zafi, ya murmusa sannan ya fara magana cikin rarrashi.
"Please Fatima ki tausayawa zuciyata wallahi duk duniya babu macen dana taɓa so sama dake, idan na rasaki zan shiga babban hadari please ki faimce ni Fatima. Kinji?"
Baki ta taɓe ta ce
"Ji yazama dole amma yarda bata zama dole ba."
Murmushin takaici ya yi wanda daka kalli fuskarshi kasan baikai zuci ba.
"Fatima yanzu abinda zaki ce kenan? zamana dake baki taɓa faɗa min magana ba, haka yasa na yi wa Dad tayin auranki dan irin tarbiyar da ki ka samu."
Tsoki tayi, ta saki murmushin takaici wanda baikai zuci ba ta ce.
"Yaya Faruq kenan u will never understand me. Ta yaya bazaka fahimci abinda nake ji a zuciya ta ba, wallahi duk lokacin da kayi kuskuran aure na to wallahi zaka tafka babban kuskuren da baka taɓa yi a rayuwarka ba.."
Mai aikinsu ce ta shigo ɗauke da tire a hannunta, lemun kwaline da cup a kai, saman table ɗin gabansa ta aje har ta ɗaga kai zata juya Faruq yayi mata alama da ta zuba mashi, bayan ta juya ta fita ne ya ɗauka ya kafa a bakinshi bai wani sha da yawa ba ya aje cup ɗin, sai da ya aje kafin ya ce.
"Na sani Fatima zuciyarki babu so na a ciki, amma na tabbata idan kika aure ni zaki so n.."
"Never!!! idan ko haka ta faru to na tabbata ranar zakayi NADAMAR aure na, kuma daga ranar zaka tsani duk wata mace dake duniya dan sai n.."
"Dakata ba sai kin ida faɗin abinda zaki faɗa ba, Fatima har kina tunanin zan iya hakuri da auranki dan kawai ki auri wannan makahon yaron? kin manta tarin alkairin da mahaifinki yayi min? To wallahi Fatima yanzu ne ya kamata na nuna masu abinda sukayi min dan su tabbatar da ni ɗane ba butulu ba"
Tsoki taja ko kunyarshi bata jiba soyayya ta rife mata ido ta ce
"Aikin banza kai ake ji mahaukaci ya faɗa rijiya mtss fool." Ta ƙarasa tana murguda baki.
"What!? Fatima ni ki ke faɗawa wannan maganar har kina da bakin zagina? To bari ki ji yanzu na fara sonki ki yi duk yanda zakiyi. Don't call me that again because if u...... humm Fatima kinci sa'a wallahi ina sonki wallahi da yau kin gane shayi ruwa ne, haba Fatima bazaki tausayawa mahaifiyarki ba ko baki tunanin halin da zata saka kanta ne? Idan har kikaki aurena.."
"Aikin banza ba'a son mutum amma bazai fahimta ba sai inda ba'a sonshi yake zuwa,."
Gaba ɗayansu suka juya suna kallon k'ofar dan ganin mai magana. Cikin isa ta iso gabansu tana wani karairaya kamar zata karye, ga wani uban make-up da tasha an kawo ɗaurin ɗan kwali gaban goshi, ta na wani yatsina sai kace itace sarkin kyawawan duka duniya. Baki Faruok ya saki yana kallon irin abinda take. Daidai inda yake zaune ta zauna saman hannun kujera ta wani murmusa kafin ta ce.
"Haba Yaya look at me and look at her dame tafi ni? Yaya inada duk wani abu da mace take bukata, ya kamata ka fahimci haka."
Sai da Faruok ya kalli Fatima yaga murmushi kwance a fuskarta kuma ya tabbatar ba murmushi wani abu bane illa na mugunta yasa ya tashi cikin isa da taƙama yana taku har ya iso daidai inda take ya zauna har suna gugur juna ya ce.
"Sahiba wai da gaske bamu dace da juna ba?"
Cikin rawar muryarta Fatima za tayi magana ya yi saurin ɗaura ɗan yatsansa a kan lips ɗinta ya ce.
"Sheeeeee.... Ba sai kin wahalar da bakinki ba."
Ido ɗaya ya kashe mata kafin ya ce.
"Humm Hafsat kinyi kuskure babba da zuciyarki ta zaɓa maki kiyi soyayya dani, har take saƙa maki zan iya auranki, wallahi Hafsat tunda nake ban taɓa jin sonki koda na sakan ɗaya a zuciyata ba, a kullum mafarkina shine naga na auri Fatima mace tamkar da dubu. Tun ranar da na fara gane kina shige min na san a rina, wai an saci zanin mahaukaciya. Hafsat ki sani shi so ɗaya ne ba'a sake masa suna.."
Fuska ta marairaice kamar za ta yi kuka ta ce.
"Amma yaya Faruok ya kamata ka fahimce ni sannan ka gane Fatima babu sonka ko kaɗan a cikin zuciyarta"
"Hafsat na tabbata idan Fatima ta aure ni wata rana zata so ni.."
Cikin sauri fatima ta mike tsaye ta ce.
"Kaga Yaya Faruok gaskiya Hafsat ta faɗa ya kamata ka fahimce ta ita ce daidai da kai nima ka barni na auri daidai dani."
Cikin fushi Faruok shima ya mike kamar zai daketa ya ce.
"Idan naki fa?"
"Zaka mutu kuwa bakayi aure ba indai ka ce Fatima zaka aura."
"Hafsat ki fita daga idona kafin na karyaki a ɗakin nan"
Tsoki Fatima tayi ta buga ƙafa kafin ta nufi hanyar ɗakinta.
Cikin isa Hafsat ko kunya babu ta ƙaraso wajen Faruok kamar zata shige cikin jikinshi har yana jin saukar lumfashinta. Ƙara shake murya tayi kamar ta babyn roba ta ce.
"Please Yaya Faruok ya kamata ka gane irin soyayyar da nake maka wallahi idan har ka amince zaka aure ni, to wallahi zan daina duk wani abinda nake please Yaya.."
"Stop Hafsat what are you doing ?"
Cikin fushi yayi mata wannan tambayar dan ganin zata faɗa saman ƙirjinshi wanda a kullum idan tana kallon wajen ke sata ƙara son shi saboda a rayuwarta tana son namiji mai faɗin ƙirji. Kuka ta fasa, ta faɗi ƙasa tasa hannu ta dafa zuciyarta kafin taci gaba da magana.
"Yaya Faruok kaine mutum na farko da ya kamata ka tausaya min karfa ka manta da irin tarin alkhairin da mahaifinmu yayi maka. Haba Yaya Faruok sonka ɗaya ne tak a cikin zuciyata wallahi idan har baka aure ni ba to zan.."
"Dakata Hafsat I don't know what u are talking about, kina 6ata yawun bakinki dan zuciyata bazata taɓa amincewa dake ba, dan zuciyata tsarkakakka ce tana son ta auri mace mai NAGARTA wallahi Allah Hafsat ko ban auri Fatima ba to bazan aureki ba."
Kaka ta fasa:
"Wayyo Allah na shiga uku Yaya Faruok ya zanyi da sonka a cikin zuciyata?"
Kafaɗarshi ya ɗaga ya taɓe baki ya ce.
"This is your problem."
Yana kai karshen maganarshi ya tafi ya barta nan tana kuka
cikin isa yake takunshi har ya isa upstairs ɗin da zai sadashi da bedroom ɗinshi, yana tafe yana ɓalle maɓallan rigarsa. Direct hannu yasa ya buɗe ɗakin, lokaci ɗaya kamshin turaren ɗakinshi ya gaurare ko ina.
Babu laifi kana shiga ɗakin kasan maishi dan gata ne, ɗauke yake da Italian bed yasha bedsheet mai ɗauke da flowers a gefe ɗaya kuma wardrobe daga hannun dama dressing mirror ne yasha kayan shafa iri-iri, tv kawai dake ɗakin abin kallo ce. Bayan ya shiga direct wajan gado ya nufa ya zauna gefan gadon ya fara cire booth ɗin ƙafarshi cikin lokaci kaɗan ya cire. A hankali ya kwanta yayi rigingine yana kallon sama sai da ya juya kwayar idonshi sannan ya lumshe idonsa.
'Oh ya Allah ka mallaka min Fatima ta zama uwar ya'yana Allah kasan abinda ke zuciyata Allah ka cika min wannan burin'
Knocking ɗin da yaji anayi ne yasashi dawowa daga dogon tunanin da yake.
Cikin isa ya nufi ƙofar hannunshi yasa mai ɗauke da gashi kwance yasa ya buɗe ƙofar ɗakin. Ganin Mom Fatima a tsaye yasashi saurin sakin fuskarshi yana faɗin
"A'a Mom kece da kanki? yanzu nake shirin na watsa ruwa kafin na shigo."
Fuskarta ɗauke da murmushi ta ce.
"Ba dole ba na shigo naga lafiyar ɗana."
"Kai Mom irin wannan kauna haka da kike nuna min ta yi yauwa."
Kai ta girgiza kafin ta zauna a gefan wata kujera dake gaban gadonsa. Daidai wajan ƙafarta ya zauna kan carpet kansa na kallon ƙasa tafara magana.
"Faruok babu abinda zance da kai sai dai na ce Allah ya saka maka da alkhairi hakiƙa kai ɗane wanda ko wane iyaye zasuyi alfahari dashi tun kana yaro kake sani farin ciki har zuwa yanzu. Faruok bansan da abinda zan saka maka ba, abinda kake so mallakina ne sai dai gashi yanaso yafi ƙarfina wallahi Faruok idan har Fatima bata aureka ba bazan tabba yaf..."
Cikin sauri Faruok baisan lokacin da yayi sauri kai hannunsa daidai bakin Mom Fatima ba kamar zaiyi kuka ya ce.
"Please Mom kada kiyi mata baki. Na tabbata in bacin soyayyar makahon nan da ta rufe mata ido wallahi da ta amince da zaɓin ku, amma duk da haka addu'a zamu dingayi mata har Allah yasa zuciyarta ta dawo wajena."
Tunda ya fara magana Mom Fatima ta kura mashi idanuwanta tana sauraron abinda yake fada.
"Amma Faruok kana ga haka zamu zuba mata ido muna kallonta sai kace ba 'yarmu ba, no! bazan bari y'ar dana haifa tafi ƙarfinaba.
#Love
#yaudara
#Cin amana
#Kiyayya
#Fatima
#Farouq
#Musadiq
#Hafsat
#bilal
#Aunty zee