Nadama page 3
by @mrsomar
*NADAMAR DA NA YI*🙆🏼
Fatima Isa
Edit...2026
Love story 2015🥰
Free Book
_Page 3_
Tsaye yake daidai harabar gidan su Fatima gidan da ya amsa sunansa gida.
Da kaga gidan kasan gidan attajirin mai kuɗi ne wanda ya tada kai da naira, da kaga gidan zaka tabbatar da gidan suda talauci har abada sunyi hannun riga dashi.
Kai basu ba har ya'yan ya'yansu basu ba talauci sunyi hannun riga dashi saboda a kalla gidan zai kai 500billions sai ga wasu manyan motoci a harabar gidan sun kai 30, a kalla duk ɗaya zata kai 50million ko wace da colour ta. Gidan dan kyau yayi kyau ba'a magana.
Matashi ne fari dogo yana da dan jiki fari ne tas yana da hanci babu laifi ga saje kwance a fuskarshi banga colour ɗin idonshi ba saboda rufe suke da bakin glass. Daidai inda yake tsaye gefe ɗaya ga roba-roba wani matashin yaro na zaune a kai da alama shi yaron ya kawo akai. Basu wani 6ata lokaci ba Fatima ta fito direct wajansu ta nufa yanayin yanda fuskarta ta faɗaɗa murmushinta ne ya tabbatar da cewa wannan matashin saurayin mai glass shine Musaddik.
"Na yi fushi ai ji nake baka zuwa?"
Murmushi yayi ya fuskanci ta tamkar yana kallonta cikin sanyi murya ya fara magana.
"Haba sweetheart wane ni ai dole nazo naga lafiyar Sahiba ta saboda na tabbatar da yau an ɓata mata rai."
Ɗan gyarawa tayi daga inda take ta ɗan jingina da motar dake kusa dasu ta ce.
"Humm Musaddik Dady naso ya ruguzamin mafarkina wanda a kullum nake fata ya zama gaskiya. Dan banda wani buri daya wuce na auranka a duk halin da kake ciki.. Humm saidai iyayena nason rabani da farin cikin ruhina."
"Fatima ki amince to kawai zaifi."
Yana faɗin haka tamkar ya faɗa mata sakon mutuwa tayi wata zabura ta kalleshi shima dukda ba gani yake ba fuskarshi na fuskantar tata. Take hawaye ya fara bin fuskarta cikin muryar kuka take magana yanzu.
"Haba Musaddik ya zanyi da rayuwata ko kasan sonka zai iya rabani da rayuwata a duk lokacin da na wayi gari na samu kaina a ɗakin wani namiji ba kai ba? to wallahi ina faɗa maka a ranar zan...."
"Dakata Fatima."
Ya ɗaga mata hannu tamkar yana kallonta shima ya fara magana cikin zafin zuciya.
"Fatima kenan ai kece iya faɗin abinda ke zuciyarki dan kuwa idan ni nake faɗin abinda ke cikin zuciyata to tabbas da yanzu sai dai aga gawata a ƙasa, Fatima ai ke mace ce tamkar ke ɗaya ce mace a duka duniya fatima kece farin cikin ruhina hasken zuciyata, kece mace ta farko dana fara so a duniya, ina rokon Allah duk lokacin da idona ya buɗe na fara saki a idona, dan ke tauraruwar duk matan duniya ce duk da bansan fuskarki ba amma na tabbata ke kyakkyawa ce."
Ɗan shiru ya yi ya numfasa kafin ya ci gaba da magana.
"To wai Fatima dan me Dad ke son rabamu ko dan ya ganni makaho ba ido? Wayyo Allah Fatima zuciyata zata buga.."
Da sauri ya dafe zuciyarshi saura kiris glass ɗin fuskarshi da ya faɗi ƙasa. Da sauri Fatima tasa hannu ta tallaboshi wanda ya yi daidai da fitowar Dady a harabar wajan can ya tsaya yana kallonsu cikin ɓacin rai ya yi mata wata irin gigitaciyar tsawa wanda tasa jikinta ya fara rawa.
Daga window ɗakin Faruok yaji tsawar da Dady yayi mata da sauri shida Mom suka nufi hanyar waje.
Cikin zafin rai Faruok ya nufi inda Fatima take tsaye dan ganin duk illa hirin jikinta na kan jikin Musaddik harta dukiyar fulaninta na gogar gefan jikinshi. har zuwa yanzu tana rike dashi Tana kallon su.
Wata irin wawar fizga Faruok yayi mata da ƙarfi ta faɗa saman kirjinshi cikin zafin zuciya ya ɗago fuskarta daga samanshi yana magana kamar zai ɗaura hannu a ka ya yi kuka.
"Fatima are you crazy? What's wrong with you? Kina hauka ne har zaki kama wani kato a cikin gidan nan gaban idonmu."
Baki ta turo cike da rashin kunya soyayya ta rufe mata ido ta ce
"Wallahi Yaya Faruok kada ka ƙara kiran Musaddik wani kato ko ka manta Musaddik mijin da zan aura n..."
Bata karasa maganar da take ba ta diga jin saukar mari a fuskarta. Dady ne cikin fushi haɗi da zafin zuciya, wata irin shaka yayi mata yana faɗi.
“Ki kuma maimaita abin da kika ce i said, repeat what you said again,”
Shakar da yayi mata ne idonta duk sunyi waje yasa Faruok ya yi sauri ya faɗi ƙasa yana bashi hakuri itako Mom tsaye take kamar hoto ta kasa komi juyawar da Faruok zai yi yaga yaran da yazo da Musaddik ya ɗaukeshi har sun bar harabar gidan. Kallon daya zakayiwa fuskar Daddy ka tabbatar da ranshi ya ɓace sosai. Rukon da Faruok ke yi masa ne yasa a hankali ya saketa yana huci ya fara nunata da yatsanshi.
"Fatima tunda naga take-takenki bamai karewa bane zan kawo karshenshi tunda ina tausaya maki baki gani ya yi kyau. Sati mai zuwa insha Allahu za'a ɗaura maki aure da Faruok idan yaso sai ki mutu idan anyi."
Wata irin ƙara Fatima ta fasa kamar an aiko mata da sakon mutuwa ta faɗi ƙasa tana faɗi.
"Please Daddy kada kayi min auran dole wallahi idan na auri Yaya Faruok mutuwa zanyi please Daddy help me."
Babbar rigarsa ya kaɗe cike da fushi ya ce
"Aikin banza ai ni dama nafi son idan an kaiki to a kawo min gawar taki zaifi, da irin wannan abin kunyar da kike so nuna mana."
Ƙafarshi taje zata kama ya yi saurin janyewa yabar wajan da sauri Mom ta mara mashi baya. Wani irin tausayinta ne yakama Faruok take yaji zuciyarshi ta karaya a hankali ya nufi wajanta yasa hannu zai kamata cikin zafin rai ta ce.
"Stop ya Faruok don't touch me."
"Why?"
Hon din da akayi ne yasa sukayi saurin juyawa dan ganin ko waye..
#Love
#yaudara
#Cin amana
#Kiyayya
#Fatima
#Farouq
#Musadiq
#Hafsat
#bilal
#Aunty zee