BARRISTER SUHAIL
🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾
Mallakar
KHADIJA WRITES
YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION
(YOTA)
⸻
💖 Dedicated To My Mom 💖
⸻
Follow me on Arewapen
@Officialkhadeey
Sai Nayi posting Chan tun nake a sauran social media platforms
بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ
🅿️----19
Cikin kasa a awa biyu suka kammala komai suka jera abincin kan dining da taimakon Amatullah
Suhail ne ya fito zuwa masallaci sallar la’asar Kamshi girki daya mamaye falon yasa shi lumshe idanun sa tare da kallo kofar Kitchen
Amatullah da ita kadai ta hango tsaye ta fito da gudu ta ce"Uncle aunty Iman ta girka maka Favourite Food dinka muje kaci"
tana kokarin kama hannunsa ya ce"Sallah zanje idan na dawo zanci"
ido suka hada Iman dake tsaye bakin sink tana wanke-wanke.
kan ya dawo ta gama kammala komai ta koma dakin ta Amatullah kuma na zaune a falo tana jiran dawowar Suhail.
ba jimawa ya dawo Amatullah ce tayi serving dinsa aroma din dake tashi cikin abincin kadai ya isa ya tabbatar da dadin abincin
spoon ya dauka ya diba ya kai bakin sa da kyar da iya hadiƴe wa tsabar dadin da girki yayi masa ya sha banban da duk abincin da yake ci a resturant ko wanda yake saka cookers din Mami suyi masa Abincin yayi masifar dad'i"
Ajiye spoon din yayi yana kallon Amatullah da ta saka wa reaction din sa ido "who cook the Food"
washe baki tayi ta ce"ni da aunty Iman Ni na faɗa mata Favourite Food dinka"
jinjina kaii ya cigaba da cin abincin sai da ya cinye abinci da Amatullah ta zuba masa tass ya mike zai tafi Amatullah ta ce"Uncle Abincin yayi dad'i ko"
kaii ya daga mata ya ce"no bad"
"yawwa Uncle sai ka bada tukwuici a kaiwa aunty iman kaga gobe sai ta girka wanda yafi wannan ko"
Hannun ya saka a aljihu ya fito da bandir din yan dari bibiyu ya mika mata da sauri ta Amsa ta ruga da gudu dakin Iman cike da murna Iman na tsaye bakin mirror daure da towel fitowar daga wanka kenan tana parking gashin ta da ribbon.
Amatullah ta mika mata kudin Iman ta ce"Amatullah wannan"
murmushi tayi "Uncle ya bada ya ce na kawo maki tukwuicin girkin da kikayi masa"
mutuwar tsaye Iman tayi ta kalli Amatullah ta ce"rokon sa kikayi ko"
kaii ta girgiza ganin kamar iman bataji dadin abinda tayi ba ta ce"a'a fa shine ya bani na kawo maki"
Iman ta kamo hannunta ta saka mata kudin ta ce"okay ki rike ni ba Abinda zanyi dasu"
amsa tayi ta koma bakin gado tana kallon kudin tana hawaye iman bama ta lura da mi take ba har ta gama shiryawa ta nufin closet ta fito da wata marron din abaya tayi rooling da mayafin ta tayi kyau sossai juyawar da zatayi ta ga Amatullah sai share hawaye take da bayan hannu.
da sauri ta nufi bakin gadon ta rage tsayin ta daidai na amatu ta na kallon yadda ta tisa kudin a hannun tana kukan ya daga mata hannu ta ce"Amatullah miya faru"
"Aunty Iman ba ke bace kika ki amsar kudin da Uncle ya baki"
dariya ta kusa subuce wa iman ta ce"haba Amatu kawai dan na ki amsar kudi sai kizo ki rinka kuka,yanzu idan na amshi kudin shikenan"
kai ta daga Iman ta amshi kudin ta ce"tashi kije kiyi sallah na kawo mana abinci muci ko"
bathroom ta shige Amatullah ta koma Kitchen ta zubo masu abincin a tray ta kawo masu daki sai da ta jira Amatullah ta gama sallah suka fara cin abinci duk da ita ba ma wani sosai taci ba Amatullah ta cinye komai dake ciki ta dauki plate din ta fitar zuwa Kitchen ta fito kenan idanun suka sauka kan Suhail dake zaune kan kujera yana dannan wayar sa gaban ta ya fadi dan bata san ma tun yaushe yake zaune a nan ba ya kafe ta da ido "ina wuni " ta faɗa tana wasa da veil din jikin ta
Suhail ya ce"lafiya qlau"
juyawa tayi ta koma dakin
suhail na zaune a falo yaji ana knocking kofar ya tashi ya buɗe Zarah ce da naima.
cike da sakin fuska ya tarbi yan uwan nasa zuwa cikin dakin bayan sun zauna ya gaishe da aunty Zarah ta amsa Naima ko da tun ta shigo take karewa dakin kalo da kyar ta buɗe baki ta ce"ya Suhail ina wuni"
"lafiya" kawai ya ce dan duk abinda Naima tayi gidan surukan sa saida aunty Zarah ta fada masa tun lokacin yake jin haushi ta
juyawa yayi wajen aunty Zarah "suna ciki ku shiga"
Murmushi tayi ta ce"a'a kadai kirata mu gaisa"
tashi yayi ya nufi Dakin Iman knocking yayi Amatullah ya buɗe ya faɗa mata suje da Iman falo momyn tazo tare suka fito Imam sai nokar da kai take waje ta samu akan carpet ta zauna Aunty Zarah ta ce"Iman ki hau kan kujera mana"
kaii ta girgiza ta ce"nan ma ya isa"
Suhail na kallon ganin yadda ta kasa hado ido da yan uwansa haka tafi ta gaishe su ɗaya bayan daya a yadda naima ta amsa kadai ya tabbatar mata ita ce wanda aunty zaituna ke magana akan ta bata da kirki
suhail ya tashi ya koma ciki Amatullah ta amso junaiid dake hannun aunty Zarah ta mikawa iman ta ce"kai ka gaishe da matar Uncle"
amsar shi tayi kamar yaji abinda tace ya taba fuskar iman yana ta mata dariya bayan sun gama ta maida wajen aunty Zarah ta nufii Naima zata amso ayla da sauri ta janye ta Amatullah duk sai taji jikin yayi sanyi haka ta dawo kusa sa iman ta zauna.
Iman ta tashi ta koma cikin ta dawo masu snacks da drinks masu yawa ta ajiye a gaban su.
Aunty Zarah kawai ta ci bayan ta gama ta kalli iman ta ce"sunana Zarah ni yayar Suhail ce ta nuna naima ta ce wannan kuma. Naima kanwar sace"
jinjina kaii Iman tayi ta tashi ta ce"Aunty bari na shiga ciki kan ku gama"
Zarah ta kalli Naima da tun shigowar waya ce a hannun ta ta ce"bazaki cin bane"
hade rai tayi "bashi ya kawo ni ba"
Aunty Zarah bata ƙara magana gudun kar su raba hali anan ma bayan ta gama ci ta nufi Dakin Iman suna kwance kan gado tare da Amatullah tana ganin ta miƙe zaune Aunty Zarah ta da Amatullah ta koma falo ta kula da junaid ba musu ta fita
Aunty Zarah ta karasa bakin gadon ta fito da nylon din dake hannun ta ta fito da wasu magungunan mata masu masifar tsada ta ba Iman tare dayi mata bayanin yadda zatayi Amfani dasu amsa iman tayi dan ita bama tasan amfanin su ba ta wa Aunty Zarah godiya
dafa kaffadar ta tayi ta ce"bakomai inaso ki kalli Matsayin yaya ba sirika duk sanda kike bukatar wani abu ki faɗamin" wayar Iman ta amsa ta saka mata lambar.
tare suka fito falon Naima na zaune inda suka barta hararar Zarah tayi a ranta ta ce"Mutun sai shegen shishigi"
Suhail ne ya fito zuwa sallar magariba Aunty Zarah ta ce"ai tafiya ma zasu yi"
Amatullah ta ce"Aunty ni anan zan kwana"
hade rai tayi ta ce"baki da hankali ko Amatu duk wunin da kikayi bai ishe ki ba zaki wuce mu tafi ko sai ranki ya ɓaci"
Suhail ya ce"ki barta gobe da safe zan kawo ta"
"a'a Suhail gobe zamuje wuce Abuja koma Flight din safe zamu bi"
"okay tom anjima zan kawo ta da kaina"
da kyar aunty Zarah ta yarda ta bar Amatullah har bakin gate suka musu rakiya Suhail ya wuce masallaci Iman da Amatullah suka koma ciki