PAGE 2
*RAGAYAR DUTSE.*
©️ *Nana Haleema.*
Wattapad@NanaHaleema
ArewaPen@nanahaleema11
Tiktok@Nanahaleemawriter
Ig@nana_haleema_writer.
*Book 1*
*Page 002.*
Mama tana shiga ɗakin ta kalli Labiba ta ce, "ke bana ciki da iskanci, ki bani abinda ki ka samo ko na saɓa miki."
Labiba a gajiye da maganar ta ce, "Mama na faɗa miki waya zan canja, don Allah ki bar maganar nan. In na samu ai ina kawowa, dan yau kaɗai ban kawo ba bazai zama matsala ba."
Mama ta harare ta ce, "wallahi sai kin kawo su, ko kina so, ko bakya so sai kin kawo kuɗin nan."
Ta yi ajiyar zuciya ta ce, "shikenan zan kawo."
Ta yi tsaki ta ce, "ya fi miki."
Mama ta fita ta shiga ɗakin da aka mallakawa Islaha. Ta same ta a tsaye tana ninke kayan da ta cire, ta bita da harara ta ce, "saura ke, kar ki ga na yi miki shiru ki ɗauka na yafe miki. Dole ki kawo na yau."
Islaha bata son magana, hakan ya saka ta ce,"to Mama" ta fada tana ajjiye abinda yake hannunta ta shiga banɗaki.
Hanan da Labiba da suka biyo bayan Mama, suna daga tsaye Hanan ta ce, "wai Mama kanmu ɗaya da yarinyar nan a cikin gidan nan?."
Mama ta ce, "ta ya zata zama kai ɗaya da ku? Itafa ƴar riƙo ce."
Labiba ta ce, "Amma itace wacce Hammanmu zai aura ko?."
Mama ta Harare ta ce, "da zata auri Saheer sai ta zama ƴar gidan nan?. Ke kin ga an yi aurensa da ita din ne, kin ga ya aure ta ɗin ne, gwana ta gwanaye?" Ta faɗa tana harararta ta fita.
A lokacin Islaha ta fito daga banɗaki ta saka hijjab ta kalli gabas ta tayar da sallah. Bayan ta idar ta ɗauki wayar ta ta fita daga falon zuwa kitchen.
Aiki take yi tana tunani, dole ce ta saka take zaune a gidansu Hamma, in ba dole ba da yanzu ta tattara kayanta ta gudu. Amma baza ta iya hakan ba, saboda Hamma. In ta yi masa haka bata kyauta ba, kuma ta yi butulci. Bata so ta cigaba da zaman gidan, dan wata ran baza ta iya barwa Mama ba. In tana faɗa tana shiru, wata ran bazata iya yin shirun ba.
Hankalinta yana kan aikin da yake gabanta, ga tunanin da yake zuciyarta, tana ta gyara kayan miya tana wankewa.
Ƙhamshin turaren da ta ji a bayanta ya saka ta murmushin farin ciki, lokaci ɗaya zuciyarta ta mamaye da farin ciki, ta ji daɗi kamar ta buga tsalle.
Ta ɗan sauke numfashi, cikin muryarta mai daɗin saurare ta ce, "Hamma!."
A lokacin kyakykyawan sarauyi fari tass ya shigo kitchen ɗin yana murmushin. Bazai wuce shekaru talatin da uku ba, yana da tsayi sosai, dan da ya tsaya a kusa da ita sai ta zama ƴar ƙarama.
Fari ne sosai, kyakykawa mai kyaun fulani. Yana da hanci dogo, da kyakykyawan gashi a fuskarsa, duk da babu yawa kaɗan ne.
SAHEER kenan, Hamman Islaha, abokinta, masoyinta, abokin shawararta.
Ya jingina da cabinet, ya harɗe hannu a ƙirji yana kallonta ya ce, "ya aka yi ki ka san nazo?."
Ta juyo tana kallonsa ta ce, "tun kafin ka zo turarenka ya ri ga ka zuwa."
Murmushi ya sake yi yana kallon fuskar ta da take fitar da murmushi, ya ce, "Ba wani nan, kin ji shigowata ne kawai."
Ta ɗago kyakyawan idaunta ta kallesa ta ce, "A jikina na ji zuwan ka Hamma. Sannu da zuwa, daman yau zaka dawo baka faɗa min ba?."
"Na kira matar Hamma bata ɗauka ba, sai na ƙyaleta na ce kar na je na yi laifi."
Ta jingina da cabinet itama ta ce, "Hammana ba ya laifi a wajena."
Murmushi ya sake yi, cikin ƙauna da soyayyarta ya ce, "me ake dafa mana matar Hamma?" Ya faɗa yana karasowa kusa ita ya buɗe tuukunyar da ta ɗora.
Islaha ta ce, "couscous Mama ta ce a dafa. Kamar ta san zaka dawo."
Ya juyo ya kalle ta ya ce, "baki je aiki ba ne?."
"na je."
"Amma ki ke a tsaye a kitchen kina aiki? Ina Labiba ko Hanan, su baza su yi girkin ba sai ke?."
Ta ɗan sauke numfashi ta kalle sa, sai ta ɗauke kai ta yi murmushi bata ce komai ba.
Ta ce, "Mama ce ta saka ni."
Ya sauke ajiyar zuciya yana kallonta cikin rashin jin daɗin abinda Mama take yi mata a gidan, ya cize baki yana girgiza kai tare da zuba mata ido.
Calmly ya ce, "ki yi haƙuri Islahaa! In sha Allah komai ya kusa ƙarewa, da mun yi aure na ɗauke ki shikenan babu mai takura miki. Da kaina zan dingayi mana girki, bazan bari ki takura kan ki ba."
Kunya ta kamata, ta saka dogayen hannayenta ta rufe fuska. Sautin murmushinsa ta ji yana kallon hannunta ya ce, "yaushe aka aka miki red henna? Yana yi miki kyau Islaha, Ina so na gansa a hannunki, ke kaɗai" ya faɗa yana riƙon hannunta yana kallon zanen red hennan da yake fatar hannunta.
"Dakyau Saheer! Ashe ka dawo, ni uwarka Ina ɗaki baki a sake Ina jiranka, ashe kai kana nan ka saka ƴar gold a gaba. Wato ta fi ni mahimmaci a wajan ka, wajanta ka fara zuwa kafin ka zo wajena ko!?."
Da sauri ya saki hannun Islaha, ya juyo yana kallon Mama.
A sanyaye ya ce, "Mama na shiga kina sallah." Ta harare sa, ta juya ta bar wajan.
Ajiyar zuciya ya yi ya kalli Islaha ya ce, "Zamu yi waya" ya faɗa murya a can ƙasa yana fita ya bi bayan Mama.
Islaha ta bi sa da kallo kafin ta cigaba da aikinta, rayuwar gidan sam bata yi mata daɗi, tana manage kawai dai bata da inda ya fi gidan. Shiyasa take jin daɗi in ta fita aiki, wani lokacin ko lokacin barinta aikin ne ya yi bata dawowa, zama take yi a can ta huta da bala'in Mama.
Dan gidan indai ba Baffa yana nan ba ya yi mata daɗi. Babu mai sonta a gidan, daga Baffa sai Saheer sai babbar gidan wacce ta yi aure. Baayan su babu wanda yake nuna mata so.
Ta san ita ba kowa ba ce a gidan, bata da kowa sai Hamma Saheer, shine uwa kuma shine uba a gare ta, Yayanta kuma mijin da zata aura.
Kallonsa kaɗai yana ƙara mata farin ciki da jin daɗi a zuciyarta, shi kaɗai ne mai tausayawa rayuwarta da son ganin ta je matakin nasara. Ya jure ƙalubale da yawa akanta, ya jure ɓatawa da kowa kawai dan ya riƙe ta a gidansu ba tare da sun haɗa jini ba.
Bata san shi ba, shima bai santa ba. Sanadin zuwa gidan marayu ziyara ya haɗa su, daga nan ta tsinci kanta a cikin gidansu da amincewarta.
Saboda shi take ɗagawa Mama ƙafa, tana sharewa in aka yi mata ba daidai ba. Amma ba dan shi ba, wata ran sai dai azo aga tana dambe da Hanan ko Labiba. Bata son raini da wulaƙanci ko kusa.
Saheer kuwa ɗaki ya shiga wajan Mama, ya same ta zata fito daga ɗakin, bata kula sa ba ta dawo falo ta zauna, shima ya zauna.
Ya ce, "Mama barka da dare." Bata kula sa ba ta yi masa banza.
Saheer ya ce, "ki yi haƙuri, na shiga kina sallah."
"Sai da ka gama gaisawa da ƴar gold sannan zaka zo inda nake ko Saheer?."
Ya sauke numfashi ya ce, "ba haka bane Mama, wallahi na shiga kina sallah."
"Ƙarya ka ke yi Saheer, ka nuna min son da ka ke yi mata ya fi wanda ka ke yi min. Ka ga in ka aure ta, wata ran ma daina kula ni zata ce ka yi."
Saheer cikin damuwa ya ce, "ki yi haƙuri Mama."
Ta ja tsaki cikin faɗa ta ce, "ni fa tun yarinyar nan bata kai haka ba ba sonta nake yi ba, saboda kai na amince take zaune a gidan nan tun ba a kai haka ba. Haka kawai babu dangi uba da uwa, ka kwaso mana yarinya ka kawo mana?."
"Mahaifinka da yake bakin ku ɗaya, ya goya maka baya harda shige maka gaba a aurenta. Wataƙila yarinyar nan mayya ce, wataƙila ba ta hanyar aure aka same ta ba. Tun farko laifina ne da na amince wallahi, gashi yarinyar tana neman ƙwace min kai, tun kafin ka aure ta!."
A sanyaye ya ce, "har abada babu wanda zai ƙwace miki ni, ke ki ka haife ni fa Mama, bani da wata sama dake."
"Ƙarya ka ke yi, ka fi sonta dani."
"Ina son Islaha Mama, amma bata kama ƙafar son da nake yi miki ba. Ki yi haƙuri" ya faɗa yana saka hannu a aljihu ya ɗauko rafar ɗari biyar ya ajjiye mata.
Sannan ya ce, "a yi haƙuri Mama." Dan ya san indai da kuɗi yanzu zata sauka.
Ganin ya ajjiye mata kuɗi masoyanta, sai ta basar ta girgiza kai, ta ja kuɗin kusa da ita ta ce, "shikenan ai. Ka je ka huta."
Ya miƙe ya fita, yana so ya ga yanayin da Islaha take ciki, dan yana da tabbacin ta ji kalaman Mama.
Islaha ba jimawa ta gama girkin, ta fito ta wuce ɗaki ta ɗauki wayarta a lokacin ta ga kiran chairman.
Kiransa ta yi, yana ɗauka ya ce, "Islaha gobe ki zo office da wuri, akwai aikin da nake so mu yi." Ta amsa da to ta kashe wayar ta ajjiye tana sauke numfashi.
Falon ta dawo ta tarar kowa ya zuba abinci yana ci, bata ce komai ba ta zuba nata ta zauna a gefe tana ci a nutse. Tana ganin irin kallon da Saheer yake yi mata, amma ta basar ta cigaba da cin abincin ta bata sake kallonsa ba. Bata so ya jawo mata hayaniya, dan Mama bata raina ƙaramin abu.
Wayar Mama aka kira, ta ɗauka tana cewa, "Kin faɗa mata gobe ne tafiyar?."
Daga can ɓangaren aka ce, "eh ta sani."
"Yauwa, ta san tsarin dai?."
"Ta sani."
"Yauwa, sannan ki faɗa mata, ni ban damu da alkhairin da fararen fata suke yi ba, kawai a haɗa min kuɗina. Dan wallahi bazan ɗaga ƙafa ba." Mama ta yanke wayar.
Hanan ta ce, "Mama nima a tura ni aikin nan mana, ana samun kuɗi muna zaune a gida?."
Mama ta kalle ta ta ce, "ke da ki ke neman mijin aure ina ke ina tafiya wata ƙasar?."
Ta juya ta kalli Islaha ta ce, "Dama dai Islaha ce sai ta tafi, ko babu komai ta tattara kuɗin aurenta."
Saheer ya tarin numfashin Mama ya ce, "Allah ya kiyaye, me Islahaa zata je yi aiki wata ƙasar Mama? Babu inda zata je, komai da ake yi na aure zan yi mata."
"Indai babar Islaha ba mayya ba ce, to tabbas jikar ƴan bori ce. Ko sun lashe maka kurwa, ko sun tsafe ka" Mama ta faɗa tana kallonsa.
Shiru ya yi bai amsa ba, dan baya so maganar ta yi ta tsayi, a Islaha a wajan.
Mama bata dakata ba, ta ce, "tun kafin ayi auren har an asirce min kai? Wato ga mai kuɗin banza, kai zaka yi komai ko?." Shiru ya yi bai ce komai ba, kafin ta sake magana ya miƙe ya fita daga falon.
Labiba ta ce, "Mama kin haɗu da sirika tun yanzu. Wannan in ta auri Hamm wallahi sai ta hanasa gaishe ki" ta faɗa tana nuna Islaha sa yatsanta.
Mama ta ce, "ita ɗin banza, yaushe aka ƙyanƙyashe ta da zata hana Saheer gaishe ni?."
"Ga zahiri nan Mama. Kina gani yana katse ki kina magana, yana cewa shi zai yi mata komai?. Wallahi nan gaba zata iya saka ki kuka."
"In tana da iyaye a duniya, ko su ƙarya suke yi. In kuma yar titi ce, na fi iyayen nata tantiranci.."
Mama ta kalli Islaha da take aikawa da Labiba harara ta ce, "Ke Labiban ki ke harara?."
Islaha ta haɗe rai, cikin ɓacin rai ta ce, "bana so su dinga shiga harkata, in kina yi min faɗa su daina saka min baki, ai basu ne gaba da Hamma ba, shine gaba dasu."
Labiba ta buɗe baki, bata yi mamaki ba, dan ta san Islaha zata aikata fiye da haka. Ta ce, "Tabɗi, to ke a su wa?."
Islaha ta buɗe idanunta ta ce, "ni a matar Hamma."
Hananan ta ce, "to daman waye zai kwashe ki, Ai sai dai Hamman, in ba shi ba sai wa?. Waye zai ɗauki ragowar titi?. Ki bari a ɗaura ɗin, kafin ki fara kiransa da mijinki."
"Wanda ya ɗauki ragowar titi, shima ragowar titin ne Hanan. Kuma tunda har ake tsayar dake aka ta ya, Islaha ta wuce ace waye zai kwashe ta."
"Kutmar uba! Me ki ke nufi? Hamma ne ɗan iska?."
Zata yi magana suka haɗa ido da Mama, sai ta fasa ta ɗauke kai daga kallon Mama.
Mama ta ce, "mara kunya, kina gidan ubansu kina cin arzuƙi kina yi musu rashin mutunci. Zo nan."
Islaha a hankali ta ƙarasa ta zauna, Mama ta bita da harara ta ce,"ban ga kin bani komai ba yau, ko dan kin ga ɗazu ban yi miki magana ba, shiyasa ki ka ɗauka yau kin ci banza?."
Islaha ta rufe ido ta buɗe, ta ce, "Mama aiki na ke zuwa."
"Dan aiki ki ka je ina ruwana? Aiki ke ya dama ba ni ba, abinda na sani ki bani kuɗin yau kawai."
Islaha ta ce, "Mama ni bana zuwa wajan ko wanne namiji balle ya bani kuɗi."