40
*KUNDINA*
*SASAAL*
***
40
FATIMA;
Ban tanka mata, sai ƙasa da nayi da kaina..
Tana yunƙurin ƙara sako wata maganar.. wayata ta fara ringing.
Da sauri nayi gaba na bar su a baya..
Baba ne yake kirana, ban ɓata lokaci ba, na ɗaga..
Sai da ya bari na gaishe shi ya amsa tukunna, sannan ya fara yimin faɗan tunda muka sauka babu wanda ya kirashi..
Haƙuri na bashi, ya yi min yaya jiki haɗe da tambayata babu wata matsa daga su Hajiya Babba ko?
"Eh" nace masa, nayi masa bayanin Asibitin da Aunty Amarya ta kai ni.. sakin muryarsa yayi alamar ya ji daɗi, ba kamar sanda ya kira muryarsa ciki-ciki ba.
Mun jima muna magana ina bashi labarin irin tarbar da ƴan uwanta Aunty Amarya suka yi mana..
Ba muyi sallama ba, sai da naga an fara ɗiban mutane..
Yanke shawarar kiran Mama nayi kar itama tayi fushin mun sauka ban kirata ba..
Maganar sakan talatin muka yi da ita, nayi mata sallama na nufi inda mutane suke ta shiga motoci..
Hajiya Babba na hango a jikin wata mota a tsaye, Farida da wata matashiya suna zaune a ciki.. kamar zan juya saboda gudun magana mara daɗi daga wajenta, sai kuma na tuna binsu zai fi min sauƙi, tunda ko ba komai tare muke da su..
Ina ƙarasawa jikin Motar Hajiya Babba ta hantare ni da cewa;
"Ina zuwa Hajajju? Ba zaki tafi wajen danginki da kuka yi anko irin ɗaya ba?"
Shiru nayi mata kamar ɗazun nayi ƙasa da kaina..
"Bakya ji na ne? Ashe shiyasa ki ka ƙi gaisheni, tunda kin samu matsayin saka leshin masu kuɗi" ta ƙarasa faɗa muryarta har rawa yake yi, da alama leshin da saka yayi mata ciwo.
Ban ɗago kaina ba, na juya domin tafiya na nemo Aunty Amarya ko na kirata a waya..
Karaf Hajiya Babba ta ɗaga murya yadda zan jiyota da kyau ta ce;
"Ai Gara ki nemi wata motar, saboda wannan motar ƴammata ne a ciki, ba Zawarawan da aka saki ranar auren su ba"
Kalamanta sun soki zuciyata matuƙa, amma ban tsaya ba na cigaba da tafiya...
Duk na laluba cikin ƴan uwan Aunty Amarya ban ganta ba, don haka na kira wayarta, shima bata ɗaga ba.. yanke shawarar komawa ciki nayi, sai kuma ga kiranta ya shigo wayata..
Da ɗaya daga cikin ƴammatan da suka zo bikin ta haɗani.. na shiga mota muka kama hanya...
Wajen taron yayi kyau, Amaryar Sarfaraz Masha Allah da ita kamar dai Angon, an ci an sha anyi kiɗe-kiɗe masu taushin da babu hayaniya.. ba a gama taron ba, sai ƙarfe goma sha biyu..
Da zamu dawo gida ban nemi kowa ba, na samu Mota na shiga..
Muna zuwa gida na shige ɗakin da aka bani.. wanka na fara yi da ruwa mai zafi, na ɗoro alola nayi sallar Isha duk jikina a mace, ga zazzaɓin jikina da bai gama tafiya ba.. ina nan zaune aka ƙwanƙwasa ƙofa..
Sai da nayi ƙoƙarin saita fuskata kar na je Aunty Amarya ce, saboda muryar mace na ji sannan na buɗe..
Daga uniform ɗin jikinta na gane ɗaya daga cikin masu hidimar gidan ce..
Matsa mata nayi ta shigo, ta ajiye tiren abincin da ta riƙo..
Ta yi min sai da safe na kullo ƙofar.. yadda ta ajiye abincin haka na barshi, ko magani na kasa sha saboda ji nake yi kamar idan nasha amai zan yi...
Ina kwance lulluɓe cikin bargo, barci mai nauyi ya ɗauke ni..
HAJIYA BABBA;
Har aka gama taron ba ta daina jin takaici ankon da Hanifah da yiwa Fatima, Farida tana ƙara ingizata..
Da suka dawo gida ma, Farida baro ɗakinta tayi ta dawo na Hajiya Babba, suka yi ta kwashewa Aunty Amarya albarka, Hajiya Babba har da cewa ai kina gani asiri tayiwa danginta, baki ga yadda suke ji da ita ba..
Ɓatanci bai tsaya a iya su biyu ba, sai da suka kira su Aunty Ummi suka share hour suna mayar da labarin duk abinda ya faru..
Aunty ummi har da cewa, Allah Ya sa kar Farida ta samu miji, Aunty Amarya tayi mata hassada ta hana auren.. cikin faɗa Hajiya Babba ta ce wane ita?
Ko da suka katse wayar Farida bata koma ɗakinta ba anan ta kwana..
★washe gari basu tashi ba, sai ƙarfe bakwai, suna idar da Sallah Hajiya Babba ta ɗora da mitar wataƙila ma kiga dukka ankon bikin tayi mata..
Karaf Farida ta ce;
"Ai ki daina ma nanatawa Hajiya, ita fa Aunty Amarya tana yin haka ne duk don Baba ya ƙara sonta"
Baki Hajiya Babba ta taɓe ta ce;
"Indai Umaru ne na bar mata shi, banda ma rashin tunani ina da dangi irin wannan me zanyi da wani Umaru, mtwsss"
Ta ja dogon tsaki.
Da ire-iren waɗannan hirarrakin barci ya ƙara ɗauke su..
FATIMA;
tun ƙarfe huɗu na tashi na kasa komawa barci, jikina zafi zau.. ina nan kwance idona biyu har aka fara kiran assalatu... Da bin bango na miƙe na shiga Washroom na ɗoro alola..
Sallar ma a zaune nayi, bayan na idar na rarrafa na ɗauki toothbrush da toothpaste na miƙe na koma Washroom.. a tsugunne na wanke baki, na fito na zauna a inda aka ajiyemin abincin daren jiya.. loma uku nayi na ɗauko magunguna nasha na ƙara yin loma ɗaya na koma kan gado na kwanta...
Ban jima ba, barci mai nauyi ya ɗaukeni..
Kafin na farka nayi sa'a zazzaɓin ya sauka, sai dai jikina babu ƙarfi...
Kamar jiya haka aka ƙara kawomin abin kari a ka kwashe na daren jiya..
Bayan na gama uzurina na fito muka gaisa da su Aunty Amarya ban nuna ina jin komai ba...
A sashen Hajiya Ni'ima na wuni, suna hira ina kallonsu gwanin sha'awa, sai nake ganin kamar basu da matsalar komai a rayuwar su..
Da dare yayi mata masu ƙananun shekaru har da su Aunty Amarya suka shirya zuwa Dinner da Ango ya shiryawa mutanensa da ba zasu samu zuwa Yola ba..
Ban so zuwa ba, amma Aunty Amarya ta tilastani na shirya, cikin wasu kayan daban, saboda babu anko, kowa kayan da yaga dama zai sa.
Abun mamaki har da Hajiya Babba na hango a masu shiga motar zuwa wajen Dinner, hannunta riƙe gam dana Farida...
Ban kalli gefen su ba, na shige mota muka kama hanya.
Ɗakin taron shima mai kyau ne, ga maza da mata ƴan gayu ta ko ina, kiɗa kuwa kamar zai toshemin dodon kunne, ba kamar irin na taron jiya ba.. Amarya da Ango sunyi kyau Masha Allah...
Kamar taron jiya shima haka kowa ya samu cima mai rai da lafiya da kyaututtukan dake ɗauke da hoton ango da amarya..
Ba mu baro wajen taron ba, sai ƙarfe ɗaya na dare... Ko kusa ban raɓi su Hajiya Babba ba har muka iso gida...
Da zazzaɓi na ƙara kwanciya sai dai bai kai zafin na jiya ba..
★washe gari basu yi ko wani taro ba, sai kimtse-kimtsen tafiya Yola da kowannensu ya wuni ya na yi..
A ranar ni da Farida aka yi mana lallan sudan mai kyau a ido..
★washe gari ƙarfe bakwai da ƴan mintina, Aunty Amarya ta kirani na shirya...
A ɗaya daga cikin Abayoyin da na taho da su, na yi wanka na kimtsa.. ina nan zaune aka kawo min abin kari...
Ƙarfe 8 da ƴan mintina muka bar gida..
Nayi tunanin saboda yawan mutane a mota za'a tafi, amma sai na saɓanin haka, kowa jirgi ya shiga.
Hannuna riƙe da na Aunty Amarya, muka shiga jirgi... Ba irin wanda da muka zo daga Kano ba ne, irin private jet ɗin da nake gani a social media ne..
Ba tare da su Hajiya Babba ba muka tafi ba, ko haɗuwa da su ban yi ba...
Da muka sauka, motoci Masu yawan da zasu ishi kowa ya zauna a wadace a aka turo, suka kwashe mu...
Sai a lokacin na hango Hajiya Babba ita da Farida a ɗan nesa da ni..
Mota daban daban muka shiga...
Babban gida mai ɗauke da ɓangare ɓangaren da aka yiwa gyaran zamani motocin da suka kwaso mu suka faka..
Ƴan uwana ne maƙil cike da ƙaton gidan, kowannensu Masha Allah da kalan baiwar kyan da Allah Ya yi masa cikin sutura na wadata...
Sarfaraz suka tararwa ana tsokanarshi yana dariya..
A nan ma dai kowa ji yake yi da Aunty Amarya, abu kaɗan sa ambaci sunanta...
Ni da su Hajiya Babba ne bare, don haka aka kai mu parlo mai kyau, ƙamshi sai tashi yake..
Ko kallon gefena su Hajiya Babba basu yi ba, ko da na gaisheta da ƙyar ta amsa suna hirarsu murya ƙasa-ƙasa ita da Farida..
Ni ma wayata na zaro, ina ta scrolling don rage kaɗaici..
Muna nan zaune aka jera mana abinci kala daban-daban..
Ban wani ci ba saboda har lokacin jikina bai gama dawowa daidai ba..
Farida da Hajiya Babba kuwa zaƙewa suka yi, suka cika tumbinsu..
Bayan sun gama ci, suka ja gefe suka cigaba da hirarsu..
Wayata ce tayi ringing suka dawo da hankalinsu kai na..
Aunty Amarya ce, ina ɗagawa ta ce min na fito Hajiya Ni'ima tace tare zata tafi da ni gidansu..
Tana katsewa na miƙe, na gyara zaman mayafin jikina, ina jin Hajiya Babba tana cewa;
"Mayya ƴar maula kawai"
Kamar ban ji ta ba, haka na fice na bar su..
Ina fita na ci karo da Aunty Amarya, ta kama hannuna har parlon da su Hajiya Ni'ima suke..
Hajiya Ni'ima tana ganina tace;
"Yauwa ƴar albarka, nasan ba zaki ƙi bina ba, tunda kowa ya ce anan zai zauna"
Ban fahimci abinda take nufi ba, kawai nayi murmushi...
Ban zauna ba ta miƙe muka fito tare..
Mota muka shiga, ta tuƙa da kanta, tana ɗan jana da hirar gidansu zata je ta zauna a can, ba zata iya zaman nan ba.. a cikin zuciyata nake mamakin to dama gidansu daban gidansu Aunty Amarya daban..
Babu tazara sosai tsakanin gidan da wanda muka baro... Shima dai mai kyau ne, amma ko rabin waccen bai kai ba a girma, anyi masa gyara irin na zamani...
Mai gadi ne ya buɗe mana Gate... Bayan ta faka muka fito, ko ina na gidan fes, ƙamshi na ta tashi.. masu hidima biyu muka samu Mace matashiya da kuma babbar mace mai shekaru..
Da yake tana son hira, labari ta fara bani kan gidan iyayensu ne, sun rasu da daɗewa, maimakon a siyar da gidan shine suka gyara suka saka masu kula da gidan suna biyansu duk wata..
Addu'ar Allah ya jiƙan iyayensu nayi mata.. ba ƙaramin daɗi ta ji ba, tayi ta samin albarka..
Wani ɗaki ta kaini matsakaici mai kyau, tace na kwanta na huta, anjima zata sa Hanifah ta bawa driver kayana ya kawomin...
Daga ɗan kwanciya barci ya ɗaukeni, ban farka ba sai bayan azahar..
Haka muka wuni, ƴan uwa suna ta zuwar mata jefi-jefi..
Kamar yadda ta faɗa da yamma sai ga driver da akwatin kayana..
Tare muka ci abincin dare da ita, bayan mun ɗan yi kallo tana jana da hira, kowanne ya tafi ɗaki ya kwanta...
★washe gari, tunda Safe bayan mun karya, ƴan uwa suke ta zuwa, da alama akwai wani taron da zasu yi..
Ɗaki na koma nayi zamana, cin abinci ne kawai yake fito da ni...
Tunda mu ka rabu da Aunty Amarya bata kirani ba, nima ban kirata, wannan dalilin yasa bayan Magriba da Hajiya Ni'ima tace na shirya yau dangi zasu yi nasu Dinner na ɗauko blue ɗin material ɗin da Aunty Amarya ta bani na saka...
Ba ƙaramin kyau na yi ba, duk da babu kwalliya mai nauyi a saman fuskata..
Hajiya Ni'ima da na fito ta ganni murmushi tayi tana ta samin albarka tare da addu'ar Allah Ya bani miji na gari...
Tare muka fita, sai dai muna zuwa can Babban gidan na nemeta na rasa, na kira layin Aunty Amarya ma ba na samu..
Wata mota na hango nayi sauri na nufi wajen, ina addu'ar Allah Ya sa na samu waje...
Ina kuwa zuwa saura wajen mutum ɗaya, ban lura da waɗanda suke ciki ba, nayi Bismillah na shiga, sai dai ban kai ga zama ba, aka hankaɗoni waje, har sai da na faɗi ƙasa..
Ashe Hajiya Babba ce, da Farida sai wata matashiya guda ɗaya.
cikin faɗa Hajiya Babba take cewa;
"Duk gatanki a cikin dangin nasu, ba su ware miki driver da zai dinga fita da ke ba? Muguwa ƴar maula mai macacciyar zuciya, to wannan motar ni da Farida akace kawai driver ya kai, ban da Bazawara irin ki ƴar maula mai ƙaryar ciwo"
Maganganunta sun soke ni matuƙa sama da wanda ta saba yi min, cikin kuka na ce;
"Ni ba ƴar maula ba ce, kuma ni ba Bazawara ba ce"
Karaf ta ce "kya ji dashi, busasshiyar banza kawai, mai koɗaɗɗen fata"
Kamar na zabura na koma wuyar rigar jikinta haka naji, sai dai ba zan iya ba, wannan dalilin yasa na tsugunna na fashe da kuka..
Dariya tasa tace driver ya tuƙa su, su tafi...
HAJIYA BABBA; suna cikin tafiya aka kira driver ya dawo da su, masifa ta fara yi kamar zata taune harshenta, Farida na tayata, ita ma Matashiyar faɗa take yi, cikin gogaggen turanci kamar a ƙasar turai...
Driver bai sauraresu har sai da ya ƙara dawo da su inda ya ɗauke su..
Bayan tafiyarsu Hajiya Babba..
Fatima tana cikin kuka Mota mai ƙarfi fitilu sama dana gidan da ya haske ko ina ya haske Mata fuska, da sauri ta rufe Fuskarta ta miƙe tsaye a tsorace..
Bata tsaya jiran komai ba tayi hanyar fita daga gidan gaba ɗaya, titi ta hau.. tana tafiya da sauri don komawa gidan Hajiya Ni'ima, horn mai ƙarfin da ya Sata ƙamewa a tsaye jikinta na karkarwa ta ji a bayanta... Ba ta motsa ba har motar ya ƙaraso dab da bayanta..
A hankali ta juya kanta kamar mai ciwon wuya, idon bai faɗa ko ina ba sai lambar jikin motar...
A nan na kawo ƙarshen free pages ɗin Littafin KUNDINA.
₦700 ne ba tsada😅 Nafisat Aliyu Muhammad First Bank 3207955182, amma saboda Sallah zan rageshi zuwa 400 ga waɗanda suka yi payment daga yau zuwa ranar Sallah..