PAGE 3
*RAGAYAR DUTSE.*
©️ *Nana Haleema.*
*Book 1*
*Page 003.*
Ƴan mata guda goma ne a tsaye, kyawawa masu ji da haske. Kallo ɗaya zaka yi musu ka san jinin fulani ne, duba da yadda suke da kyau mai sanyi. Dukkansu basu wuce shekaru ashirin ba, babu wacce zata ɗara daga ashirin, sai dai ƙasa da haka.
Suna zaune a babban falo, sai wata babbar mace a zaune tana kallonsu tana murmushi.
Ta ajjiye wayar hannunta ta ce, "bakwa burin zama a irin wannan gidan don Allah?."
Suka yi shiru basu ce komai ba, ta sake yin dariya ta ce, "ku saki jikinku, babu abinda zai faru a nan. Na san kun ji daɗin kuɗaɗen da ake baku ko?."
A tare suka ɗaga kai alamun eh, ta ce, "To kun gani. Da kuna gidan marayu kuna rayuwa kamar ta bayi, abinci ma ba wani mai kyau ake samu ba. Ku kalli yadda ku ka canja, ku ka yi kyau kamar ba ku ba. Ni kaina yanzu na tabbatar muna da ƴan mata kyawawa, da an dakusar daku a waje ɗaya."
Gyaran murya suka ji, ta yi musu alamu duk su miƙe suka miƙe tsaye.
Babban mutum ne ya shigo sanye da shadda fara harda babbar riga. Kana ganinsa ka ga alhaji, wanda kuɗi ya zauna yake shigowa.
Ganin ƴan matan sai ya yi murmushi yana binsu da kallo, ya kaɗa kai ya ce, Kai! Kai! Kai!!. Daman haka mu ke da kyawawa ƴan mata a garin Yola kamar haka?. Jamila aikin ki yana yin kyau."
Ta yi dariyar farin ciki ta ce, "Godiya nake yallaɓai."
Ya murmusa ya ce, "ku zauna ƴan mata adon gari."
Suka zauna gabaɗayansu, ya bi su da kallo yana murmushi.
Kafin ya kalli Jamila ya ce, "waɗanan sun yi."
Ta ɗan rusuna ta ce, "Godiya nake yallaɓai."
"Ina fatan komai daidai."
"Komai daidai yallaɓai, komai zai tafi yadda ake so. Dukkansu babu matsala, na yarda dasu ɗari bisa ɗari."
Ya kalle su ya ce, "ai daga ganinsu, wayayyu ne basu da duhun kai. Kuna ji ƴan mata?."
Duk suka kalle sa, ya gyara zama ya ce, "Za a kai ku inda zaku samu cigaban rayuwa. Yin karatu a babbar makaranta, hawa mota, riƙe waya mai tsada, kwana a waje mai kyau, da komai za ku zamu. Abinda mu ke so da ku, bama son yawan surutu, ku yi shiru da bakunan ku. Ba ku da iyayen da zasu takura mu ku, abinda ku ke so shi za ku yi."
Jamila ta ce, "in ku ka yi haka, za ku samu abinda baku taɓa tunani ba. Fita ƙasar waje, da komai ma za ku samu. Kun amince?."
Dukkansu suka ɗaga kai alamun sun amince. Ya yi murmushi ya ce, "ku shiga ciki, akwai mai dafa abinci, ku faɗa mata duk abinda ku ke so za a yi mu ku. Akwai driver a waje, in kuna ƙwaɗayin kayan ciye-ciye duk za a baku." Suka miƙe suka shiga inda ya nuna musu, ya bisu da kallo yana murmusui har suka ɓace.
Ya kalle ta ya ce, "ba a taɓa samu team mai kyau kamar wannan ba, kin yi haɗi yadda ya kamata. Kuma da alama dukkansu lafiyayyu ne, za a samu abinda ake so."
Daɗi ya kamata, ta ce, "sai da na zauna sannan na zaɓa, na fiddo su."
Ya ce, "na san za ki iya. Amma ina yarinyar nan da na gani?."
Ta ɗan sauke numfashi sannan ta ce, "Hafsa ko?."
Ya ɗaga kai ya ce, "ita. Ai na faɗa miki ina so a haɗo da ita, wannan da kaina zan ajjiyeta ba wani wajen zan kai ta ba."
"Hafsa da Zainab bana son taɓa su ko kaɗan, saboda yaran nan sune na hannun daman Islaha."
Ya bita da kallon mamaki ya ce, "Islaha kuma, ba mun gama da case ɗinta ba?."
"Mun gama Yallaɓai, amma ita bata gama damu ba. Daga ranar da ta buɗe ido babu ɗaya daga cikinsu, zata fara yi mana shige da fice a kan lamarinmu. A haka ma dan muna da maganinta a hannu ne, da ba mu san irin ɓarnar da zata yi mana ba."
"Wai wacece Islahan nan da mu ka kasa ganin bayanta?."
"Mun yi nasara yallaɓai, tunda ta bar gidan nan da jimawa. Barinta gidan shine ya dakusar da ita, har yanzu bata da hujja akan abinda mu ke aikatawa. Iya wannan ma nasara ce."
Ya ɗan gyaɗa kai ya ce, "A kashe ta mana, meye amfaninta?."
Ta yi murmushi ta ce, "ka bar komai a hannuna, indai ina da rai bata isa ta yi wani motsi ban saka ƙafa na fyaɗe ta ba. Ai bata isa ta yi wani abu na zuba mata ido ba."
"Na yarda dake Jamila, tunda muka fara harkar nan bamu samu matsala ba. Amma ina so ko ta wacce hanya Hafsa ta zo gidan nan, na yi miki alƙawarin mota, da kuɗi naira miliyan biyar, da kujerar hajj. bana. Amma in kin kawo min Hafsa kenan."
Ta yi dariya ta ce, "Wallahil azim, ka ji rantsuwar musulmai ko? Islaha ko ita ta haifi Hafsa sai na kawo maka ita, sai ka yi shagalinka da ita yadda ka ke so. Bata isa ta yi komai ba, babu abinda ta isa ta saka ko ta hana."
Ya yi dariya ya ce, "Idon naira, wato tunda na yi alƙawari za ki iya."
Ta yi dariya ta ce, "Yallaɓai babu abinda kuɗi ba sa sakawa."
Ya ɗaga kai ya ce, "wannan karo, baza mu fitar da yaran nan ba, a nan ƙasar zamu rabasu. An ɗan samu tangarɗa akan fitarsu ƙasar waje, tunda akwai mutanenmu a nan da suke da kuɗi a hannu zamu fanshe komai."
"Babu komai yallaɓai, amma kar a barsu a Adamawa ko kusa da Adamawa."
"Haba Jamila, na san abinda nake yi fa."
Ta yi masa jinjina ta ce, "tuba nake yi, matsala ce bana so."
Ya ɗaga kai ya ce, "na fi ki gudunta."
"Yallaɓai kowa da ɓangarensa, in ka duba yaran nan a hannun mu suke, binciken farko ta kaimu za a fara."
"Na ji. Ki je kawai, ki shirya min haɗuwa da Hafsa. Su kuma waɗanan, in anjima ko wacce zata san makomarta" ya faɗa yana miƙewa.
itama ta miƙe ta ce, "an gama ranka ya daɗe. Amma ina so a bani aron yaran nan mu tattauna." Ya nuna mata hanya alamun ta je, ta ce, "godiya nake."
Tana shiga ta kalle su ta ce, "Kyawawana, ku riƙe amana a duk inda aka kai ku, ban da sata, gulma, ko yiwa babban mutum video da waya. In aka kama ɗaya daga cikin ku da irin wannan laifin, za a ɗaure sa ne. In ku ka kwantar da kai, ƙasar waje sai ta zamar mu ku wajen zuwa ko yaushe."
Ɗaya daga ciki ta ce, "Baza ki taɓa samun mu, da irin wannan abubuwan ba."
Ta yi dariya ta yi musu jinjina ta ce, "sai mun yi waya" ta faɗa tana fita..
*****
Tunda ta koma ɓangarenta take kuka, ta dafe kai tana zubar da hawaye zuciyarta duk babu daɗi.
Bata san me ta yiwa dangin mijinta da basa sonta ba, kawai dan ta kasance ba yarensu ba, dan ta kasance ba ƴar ƙasarsu ba, shikenan kowa ba ya sonta?.
Ba ita ta bawa Rehaan ɗaukaka ba, ba itace take sakawa ya zauna a ƙasar waje ba, ta fi kowa son ganinsa a kusa da ita. Amma da an tashi magana, duk laifinsa sai a juye ya dawo kanta gabaɗaya.
Babu mai kaunarta a cikin gidan sai Janan, wacce ta kasance age mate ɗin Riyya. Bayan ita babu wani, sai a fi sati ɗaya wani yaron gidan bai shigo inda take ba. Sun tsame ta daga gidan, sun mayar da ita kamar annoba.
A lokacin Riyya ta shigo, ganin tana kuka sai ta ƙaraso da sauri ta ce, "Mamy me ya faru, meyasa ki ke kuka?" Ta faɗa tana zama a kusa da ita hankali a tashe.
Ta sake cewa, "Mamy lafiya?."
Bata ce komai ba, ta goge idanunta ta kalli Riyya ta ce, "Riyya kira min Rehaan a waya."
Ba musu ta ɗauki waya ta kira number sa ta ƙasar uk amma bata shiga.
Ta kalli Mamy ta ce, "wayarsa bata shiga."
Mamy zata yi magana aka shigo ɗakin da sallama.
A tare suka amsa, suna kallon wanda ya shigo ɗakin. Riyya ganin Abba ne sai ta miƙe tana kallonsa, ba kasafai aka cika ganinsa a ɓangaren matansa ba, sai abu mai mahimmaci musamman rashin lafiya.
Riyya tunda ta gansa, ta san an ɓatawa Mamy rai a wajen meeting, shine ya biyo ta ya rarrashe ta.
Riyya ta ce, "Abba sannu da zuwa."
Ya kalle ta ya ce, "ina Banisha?."
"Ta yi bacci." Kai ya ɗaga Riyya kawai, ta fita daga ɗakin ta basu waje.
Abba ya sauke numfashi yana kallom matarsa da take zubar da hawaye har lokacin, kanta yana ƙasa bata ɗago ba.
Ya ɗan gyara tsayuwa ya ce, "NADIRA!."
Bata ɗago ta kalle sa ba sai goge idanunta da take yi, ya san an ɓata mata rai ne, hakan ya saka ya tako yazo inda take ya zauna.
Ya riƙe hannunta ya ce, "wannan kukan bashi da amfani, kin san bazan ja da hukuncin Daada a gidan nan ba. Kuma ba laifi bane da an ce Rehaan ya dawo gida."
Cikin harshen hindi, da take yi masa magana dashi ta ce, "Amma ka san duk lokacin da Rehaan ya dawo nigeria sai wani abun ya same sa ko? Ka san ba ya taɓa zama lafiya indai ya saka ƙafarsa a cikin ƙasar nan. Meyasa ake so ya dawo gabaɗaya, a manta a can yake aiki da kasuwancinsa?. In ya bar komai na sa ya dawo nan kenan ya haƙura da komai?. Ka san bana son wani abu ya samu Rehaan, bana so ko kaɗan."
Ya sauke numfashi bayan ya gama jin abinda ta ce. Duk da ba da yarensa ta yi magana ba, amma a zaman da suka yi ya iya yarenta sosai. Kamar yadda ta iya fulfulde da hausa. Yana fahimtar duk abinda ta ce, yadda ta yi maganar ya san abin yana taɓa mata zuciya.
Ya san macece da take da son ƴaƴanta, bata so ta ga wani abu ya same su. Hakan yana daga cikin dalilin ƙinta da Daada take yi, takance bata da fulako da yakana, su fulani ba haka suke nuna tsantsar son yara ba, suna ɓoyewa. Mamy kuwa bata san ɓoye son ɗanta ba, a gaban kowa take nuna masa soyayyar da iyaye suke nunawa yaransu.
"Nadira kin san dole gidan nan, shiyasa nake fɗa miki zamansa a England bazai yu ba. Dole ya dawo nan ya cigaba da zama kamar sauran ƴan uwansa."
"Kasuwancinsa fa? Ka san acan yake yin komai. In ban da yanzu, da ya kawo shopping mall da hospital nan ba, da bashi da komai a nan."
"Zai iya yi daga nan, ba sai a can ba. Muna zamanin da kana zaune daga gida zaka yi meeting, karatu, aika saƙo da komai da komai. Kasuwancinsa bazai dakushe dan ya dawo ba. Aiki da ki ke zance ke kan ki kin san ba yi yake yi ba, sai dai in ya samu contract da wata ƙasa ya je ya gama ya dawo. Bai ɗauki karatunsa na likitanci da mahimmaci ba, ya fi mayar da hankali akan kasuwanci."
Ya yi murmushi ya fuskance ta sosai, tare da riƙe ɗaya hannunta ya ce, "Nadira!."
Ya ɗago da fusksrta yana kallon kyakykyawar fuskarta ya ce, "na yi miki alƙawari, a wannan karo babu abinda zai samu Rehaan, ko da ya yi ciwon da ya saba baza a ɗauki lokaci ba zai samu lafiya. Aiki kuma zai cigaba da aikinsa a nan, tunda kin san ya fi mayar da hankali akan aikin in ya zo nan. Harkokin kasuwancina da nasa da suke a ƙasar da zai bari, za a cigaba da kula da komai daga nan. Don Allah kar ki samu damuwa, kin ji?."
Ta ɗaga kai alamun to, ta ce, "Ni daman ba damuwa nake yi akan zuwansa ba, gidansu ne, komai daɗewa dole ya dawo. Kawai rashin sakewar da ba ya yi ne bana so, ga kuma yawan ciwon cikin nan na sa."
"Babu abinda zai faru in sha Allah."
"Allah ya sa."
"Amin. Rehaan yana da wacce yake so ya aura ne?."
Ta ɗago ta kalle sa tare da girgiza kai, sannan ta ce, "bai taɓa bani labari akan hakan ba, sai dai ko yanzu."
Abba ya yi shiru yana kallon ta, sai ta ce, "Daada ta ce ya yi aure ne?."
Ya ɗaga mata kai ya ce, "ta ce a haɗa da aurensu Riyya."
Ta ɗan buɗe ido ta ce, "Riyya! Bikin Riyya ai ya kusa, har yaushe ya dawo da aka haɗa aurensu lokaci ɗaya?."
Ya ɗaga kai ya ce, "hakan za a yi Nadira. Za a san abinda ya kamata ayi."
"Ka zaɓar masa matar ne?."
"A'a, ke kina da zaɓi ne?."
"ko na faɗa ma baza a amince ba, baza a so na sake ɗauko hindi na kawo cikin fulani ba. Bani da zaɓi" ta faɗa a sanyaye.
Abba ya girgiza kai ya ce, "is okay, mu jira ya dawo, wataƙila yana da wacce yake so."
Mamy ta ce, "ina so in je gida, na jima ban je canja."
Ya miƙe tsaye yana cewa, "zaki je, amma ba yanzu ba Nadira. Ina jiran zuwa ki, ki kawo min tea" ya faɗa yana fita daga ɗakin. Mamy ta dafe kai tana tunani.
Tunaninta ɗaya wacce mata kuma za a zaɓa masa a cikin gaggawa haka? Ita fa bata son a aura masa wacce ba ya so, kuma bata so a aura masa wacce zata so shi dan kuɗi ko dan kyau. Shiyasa ta fi so ta zaɓa masa mata da kanta, amma ta san baza a taɓa bata dama ba.
Ko wacece wacce za a zaɓa masa, matuƙar baya sonta itama baza ta taɓa sonta ba har abada. Abinda Rehaan yake so shi take so, zaɓinsa shine zaɓinta. Ta sauke numfashi, ta miƙe ta shiga banɗaki cikin tunani.
Ɓangaren Daada Mama Saddiƙa ta nufa da sassarfa, ta shiga da sallama ta same a yadda suka bar ta.