RAGAYAR DUTSE

PAGE 4

by @nanahaleema11

*RAGAYAR DUTSE.*


                ©️ *Nana Haleema.*


*Book 1*

*Page 004.*



Da mamaki Baba yake kallon ta jin abinda take faɗa, ya yi shiru ya zuba mata ido har ta gama bayaninta yana girgiza kai.


Ya bita da kallo ya ce, "Maimuna kin san abinda ki ke faɗa kuwa?." 


Umma ta kalle sa ta ce, "na sani mana." 


Baba ya ce, "kuma kina cikin hankalinki?." 


Itama da mamaki ta ce, "in bana ciki ai bazan faɗa ba. "


Baba ya ce, "na fi tunanin bakya hankalin naki, dan mai hankali bazai faɗi abinda ki ka faɗa ba. Cewa ki ke yi za ki tura Safeera ƙasar waje aiki, a gidajen fararen fata fa." 


Umma ta ce, "eh haka na ce. Kuɗi ake samu, kai ka san ba halin aurar da ita muke dashi ba. In ta je ta yi aikin koda na shekara ɗaya ne, abinda ta samu ba sai a aurar da ita dashi ba?." 


Baba ya girgiza kai cikin mamaki, dan shi gani yake kamar bata cikin nutsuwarta, ya ce, "Safeera za a tura aikatau wata ƙasar? Ni tantama nake yi; anya kina cikin hankalinki?."


"Haba don Allah, ina hankalina mana, mahaukaciya ce ni?. Duk wata akwai gidan da ake biyan miliyan ɗaya a kuɗin nigeria, ko da dubu ɗari biyar za a dinga bata, a wata sha biyu nawa mu ke dashi?. In ta je ta yi na shekara ɗaya ba sai ta dawo ba?. Wannan banzar tashar da suke aiki ita da Islaha uwar me suke samu? Tashar tasu har yanzu bata wani ɗaukaka ba, albashin bai wuce dubu hamsin ba. Kai kana gida ba aikin kirki ka ke yi ba, nima ɗan buge-bugen da nake yi ba samu ake yi ba. Ga yara, ga Safeera budurwa wacce aka yiwa baiko, shi kansa wanda zata aura ɗin ba wani abin hannu ne dashi ba. Ya ka ke so na yi?."


Baba ya girgiza kai ya ce, "kuma kawai sai na sallama ƴata ta tafi wata ƙasar aiki, saboda a kaina aka ƙare talauci ko?." 


Ta yi shiru bata ce komai ba, Baba ya gyara zama ya ce, "Ai wallahi ko bara nake yi akan titi, bazan amince Safeera ta yi aikatau a garin nan ba, balle har sai an bar ƙasar nan. Ita woman leader ɗin da ta zugo ki, ki faɗa mata ita ta tura ƴaƴanta mana, sai ke za ki tura naki dan baki da hankali?."


Umma ta ɗaure fuska ta ce, "ina fa da hankali Malam, ka daina cemi bani da hankali. Kuma in Safeera ta je aikin nan ai cigaban mu ne."


"Cigabanki dai, amma ni ban dani. Kuma baza ta je ba, wallahi Allah Safeera baza ta je aiki wata ƙasar ba, matuƙar ina da rai ina numfashi. Ke ko na mutu ban yafe ba in ki ka turata. Tunda na lura abin naki ya tashi daga na masu hankali, ya tsallaka ya koma na mahaukata."


"Ka ji ai, matsalar talaka kenan wallahi. Baka dashi ka ce baza ka bi hanyar samu ba." 


Baba ya girgiz kai bai ce komai ba, dan ba ya so ya biye mata saboda yara, ba ya son yin abinda zai bar musu suna tunawa dashi.


A lokacin Safeera ta shiga da sallama cikin hijjab. Baba ya amsa yana kallonta, ta durƙusa ta ce, "Baba zan miƙawa Islaha wainar fulawa na dawo."


Baba ya kalli agogo ya ce, "ƙarfe tara ta yi Safeera, in kin je ki dawo, ban da zaman hira." 


Ta yi murmushi ta ce, "To Baba" ta faɗa tana miƙe ta fita. 


Umma ta ja tsaki ta ce, "yarinya budurwa kamar wannan ace baza a amfana da ita ba. Woman leader ƴaƴanta ne suke kawo mata kuɗi kullum, kuma ba neman maza suke yi ba, da dabara irin ta mata suke samu su kawo. Amma ni aiki na ce zata yi ka ce baza ta yi ba. Ni sai na wanke ƙafata na tafi, ai baza a hana ni ba!. In ka hana ƴarka, ni ai ba haifata ka yi ba!" Ta faɗa tana miƙewa.


Baba ya ce, "Allah ya kai ki lafiya, ƴaata dai baza ta je ba wallahi." 


Mama ta fita suka haɗu da Safeera tana kwashe kayan wankin da suka zube ƙasa saboda iskar sanyi.


Umma ta kalle ta ta ce, “Ke kina son zuwa ƙasar waje aiki?." 


Da mamaki ta ce, "Umma wanne aiki kenan?."


"Aikin Saudia, na gidan larabawa ko turawa.Kina so?."


Safeera mamaki ya hana ta magana, ta dinga bin Umma da kallo ganin yadda ta canja kamar ba ita ba. 


Umma ganin ta tafi tunani sai ta dafata, ta ce, "a wata ana samun albashi kusan miliyan ɗaya, to in ki ka je ki ka tara kuɗin ba sai a zo a ajiiye, kin ga in bikinki ya zo an huta da babu wannan babu wancan. Kin san ba ƙarfi ne da ni ba, babanki ma haka. In ki ka je ki ka samo kuɗin, sai a rufawa juna asiri. Shi kansa Saleem ɗin naki ba kuɗi ne dashi ba, kin ga sai a taimaka masa da wani abun in an samu, ko ya ki ka gani?."



Safeera a sanyaye ta ce, "Umma wai da gaske ki ke?."


"Da gaske nake mana. Kuɗi ake samu, musamman ke da ki ke jin turanci, za ki iya zama a ko ina. Ga ki fara, kyakykyawa."


"Umma ni bani da ra'ayin zuwa aikatau wata ƙasar gaskiya." 


Umma ta yi murmuahi ta ce, "jeki ki kai mata ki dawo mu tattauna, bazan bar wannan alkhairi ya wuce mu ba. In ki ka yi katari ki ka samu gidan aiki a saudia riba biyu, ga ki a garin ma'aiki, ga kuɗi, sannan ga labarawa da kyauta. Me ki ka manta?." 


Safeera ta yi ajiyar zuciya bata ce komai ba ta fita, dan ta ga yanayin Umma baza ta fahimce ta wuri ba.



      Islaha tana zaune a kan kujerun da aka yi su na gini a compund ɗin gidan sanyi yana ratsata, ta ƙanƙame jikinta tana rawar sanyi cikin rashin mafita. 


Ta kalli ƙofar da zata kai falo, ta ɗauke kai tana lumshe ido tana jin numfashinta yana yin sama. 


Ta san ko me zata cewa Mama baza ta bar ta ta shiga ba sai ta ga dama. Mama indai akan kuɗi ne bata ɗaga ƙafa, bata damu da inda zaki samo ba, ita dai kawaai  ki bata shine kwanciyar hankalinta. 


Sau da dama Islaha tana ji har gwara zaman gidan marayu akan gidan Mama. Can babu mai takura mata ta kawo kuɗi, in ta gama abinda take yi ta dawo ta kwanta shikenan. 


Duk da can ɗin ma akwai ƙananun ƙalubale, ta buɗe ido kawai ta ganta a gidansu Saheer, bata san ya aka yi ta amince ta biyosa ba. Dan ta san a dokar gidan marayu, in dai mutum zai yi adopting ɗinka, kuma ka wuce shekara sha biyu, dole sai da amincewarka kafin hukumar gida ta yarda. Balle ita, da ta kusa gama university a lokacin. 


Da kanta ta amince masa ta biyosa, ba ta san meyasa ya yi adopting ɗinta a lokacin ba, ta san shaƙuwar da suka yi ne sila, amma wani lokacin tana danasani.


In Mama ta yi wani abun, sai ta ji kamar ta haɗa kayanta ta koma, duk da ta san baza a karɓe ta ba, kamar an yaye ta ne. Amma tana da yayyun da ƙawayen da suka tashi tare, suka yi aure a manyan gidajen da zata iya zuwa can ta zauna. Kawai bata son zubawa Hamma ƙasa a ido ne, da wata ran sai dai ya buɗe ido ya ga bata nan.


Ɗankwalinta ta jawo ta rufe kunnenta ta jin sanyi yana shigar mata kunne ta ko wanne ɓangare. 


Buɗe gate ɗin aka yi aka shigo, sai ta ɗaga kai ta kalli wanda ya shigo. 


Safeera ta gani, ganinta a zaune a wajan sai ta ƙaraso da roba a hannunta ta ce, "Islaha lafiya ki ke zaune a nan? Kin san dai wajan nan ba wajan zamanki bane, tunda ba cikakkiyar lafiya ce dake ba ko?." 


Islaha ta kalle ta tana ƙanƙame jikinta ta ce "Safeera Mama ce ta ce in fito na zauna."


"Akan me?."


"Akan ban kawo kuɗin ba, kuma bani da kuɗin ne shiyasa. Da meye dubu goma ko ashirin da na bata?."


Safeera ta zauna kusa da ita, cikin fusata ta ce, "Amma Maman nan ƴar...." 


Islaha ta dakatar da ita ta ce, "kar ki zage ta Safeera, ta yi min abinda babu wanda ya yi min irinsa a duniya. Duk da ba zaman daɗi nake yi ba, amma babu laifi ina kwana na tashi har na ci na sha. Ɗanta kamar shine bangona, shi nake kallo a matsayin Yayana, aboki, kuma mijin da zan aura. Ta cancanci girmamawa ko ya ya ne."


Safeera a ƙufule ta ce, "to neman maza take so ki fara ko me? Haka kawai namiji zai ɗauki kuɗi ya ba ki ba tare da kin bashi wani abun ba?."


Islaha ta ce, "duk yadda ki ke tunanin Mama akan son kuɗi ta wuce haka. Ita gani take yi haka yaranta suke yi, tunda suna fita su samo mata."


Safeera ta yi tsaki ta ce, "to ki zo mu tafi gidan mu kawai, in ba haka ba kin san sanyin nan zai cutar dake."


Ta girgiza kai ta ce, "a'a, ƙyale ni kawai Safeera. Me ya fito dake a daren nan."


Ta miƙa mata pack ɗin ta ce, "Wainar fulawa ce, na soya shine na kawo miki."


Islaha ta karɓa ta ce, "kamar kin san tun jiya nake muradin cinta wallahi, sai dai sanyin nan bazai bar ni ci ba." 


Safeera ta ce, "ki zo mu tafi gidanmu, yanzu numfashinki zai riƙe, kin san yanayinki kamar na masu asthama.”


Islaha ta ce, "ki bari kawai Safeera, na tabbata yanzu zata ce na zo na koma. Ki je gida, dare ya yi kar Baba ya yi miki faɗa."


"Ya san na fito ai, kuma in dai tare dake ne ba ya  yi min faɗa." 


Islaha ta bita da kallo ganin fuskarta babu walwala ta ce, "wai me ya faru?." 


Safeera ta ce, "Umma ce Islaha, wai zata tura ni aikatau ƙasar waje." 


Islaha ta zaro ido ta ce, "kamar ya?."


"Kamar yadda ki ka ji, kuma na san Mama ce ta zugata."


"Tabbas kuwa, dan ɗazu tare na dawo na tarar dasu a falo, kuma na san itace zata yi mata maganar."


"Lamarin Umma ai sai a hankali, ita bata ga bata tura nata yaran ba sai ita zata zugata tura ni?."


Islaha ta ce, "me ki ka ce to ke?." 


Ta kalle ta ta ce, "kema kin san ai bazan amince ba. Ni anya topic ɗin mu na ranar monday baza mu sake maimaitawa akan hakan ba?. Abin ya yi yawa Bestie, iyaye basu san inda yaransu suke zuwa ba, kawai kina nan kin tura ƴarki budurwa tana wata ƙasar aiki. Babu abinda ya dame ki da a hannun wa ta sauka, aikin me take yi, waye yake bata kuɗin, duk babu ruwansu. Kawai ta turo musu kuɗi. Wannan abun yana taɓa zuciyata Islaha, kuma wallahi iyaye mata sun fi wannan katoɓarar


Islaha ta ce, "hmmm! Kamar na fi ki tsanar wannan abun nan Safeera. In kin ga ƴan matan da Mama take turawa ƙasar waje sai abin ya ba ki mamaki. Kuma laifin iyayensu ne, sune suke bada damar wannan ɓarakar wallahi. Kuma da wahala ki ga uba mahaifi ya aikata irin haka, kamar yadda ki ka ce matan ne dai. Dan su za ki dinga gani a wajan Mama, ana washe mata baki zata kai ƴarsu Saudia. Zan yi magana da Chairman, zamu sake saka wannan a cikin topics ɗin mu in sha Allah."


Safeera ta ce, "gwara mu sake tattaunawa, dan da yawan yaran ba so suke yi ba, iyaye mata ne suke takura musu."


Islaha ta girgiza kai ta ce, "da na je aikatau wata ƙasar ba gwara na yi bara ba, Allah ya kiyaye." 


Safeera ta ce, "Amin Islaha. bara na wuce, sai mun haɗu gobe."


"Kamar kin san Chairman ya kira ni, wai yana so gobe na je da wuri zamu tattauna akan wata magana." 


Ta yi ƴar dariya ta ce, "Chairman dai yana ciki, amma na san bashi da space, wajan Hamma Saheer ne." 


Ta yi murmuahi ta ce, "gaskiya ne, bana iya kallon ko wanne namiji da fuskar soyayya sai Hammana, ina sonsa sosai Safeera." 


Ta yi dariya ta ce, "ya cancanta ki so shi ai Bestie, ya yi miki komai a rayuwar nan." 


Safeera ta miƙe ta ce, "sai mun haɗu, don Allah ki samu ki shiga ciki." 


Islaha ta ce, "To bestie, ki kwana lafiya." Daga haka suka yi sallama ta fita.


Wainar fulawar take son ci amma baza ta iya ba, sanyin ratsa ta yake yi, ga sauro da ya fara kawo mata hari. Duk da wajan akwai haske amma sauro ya dame ta sosai. 


Ta miƙe ta ƙarasa ƙofar sai ta tarar an kulle ƙofar,  ta ɗan yi knocking aka yi mata banza, kuma tana jin motsinsu. Ajiyar zuciya ta yi ta zauna a wajan tana tunani kala-kala.



     "Islaha!" 


Ya faɗa yana ƙarasowa wajan da sauri. Ta kalle sa, bata yi magana ba har ya ƙaraso. Ya bita da kallo ya ce, "me ki ke yi a wajan nan a zaune ga sanyi? In ki ka samu attack fa?."


Islaha ta karyar da kai, cikin shagwaɓa ta ce, "Mama ce ta ce in fito." 


Da mamaki ya ce, "ki fito kuma, to akan me?." 

Ta girgiza masa kai alamun bata sani ba. 


Ya ɗan yi tsaki ya ƙarasa yana buga ƙofar falon Mama amma aka ƙi buɗewa. Ya kira Maman a waya bata ɗauka ba, ya kira ƙannensa duk suka ƙi ɗauka. Ya dawo kusa da ita ya ce. "Taso."


Ta miƙewa tsaye, ya riƙe mata pack ɗin ya ce, "mu je ɗakina ki zauna, in wannan sanyin ya yi miki illa fa, mai lafiya ma ya cika balle ke?." 


Islaha ta bi bayansa, a hankali dan gaskiya bata son sanyi, tana da wani irin ciwo kamar asthma, duk da Hamma ya ce asthma ce, dan alamominta gabaɗaya ya bayyana a kanta, amma an je ayi test an ce babu. Hamma dai ya ce ƙarya suke yi, asthma ce da ita.


Ɗaki ne babba mai ɗauke da gado da komai na kayan gado, gashi a gyare babu tarkace sai takalmansa da laptop ɗin da yake aiki da ita. 


Ya nuna mata gefen gadon ya ce, "ki zauna." 


Ba musu ta zauna ya ce, "me zaki ci?." 


Ta fara sosa kunnenta da sanyim ya shiga ta ce, "Zan ci wainar fulawa, Bestie ce ta kawo....." ta kasa faɗa saboda atishawar da ta zo mata.


Saheer ya fusata, cikin faɗa ya ce, "meyasa ba ki zo nan kin zauna ba za ki bari sanyi ya yi mili illa? Gashi nan har kin fara atishawa, kin manta kina da asthma ne?. Haba Islaha, meyasa baza ki faɗa min ba?." 


Cikin sanyin murya ta ce, "ka yi haƙuri. Kuma har yanzu ba a tabbatar asthma ba ce.”


“Ni na tabbatar. Ƙarya likitocin suke yi, duk wanda ya ga yadda ki ke yi ya san itace.”


Ya sake yin tsaki ya ce, "ki ci wainar, zan fita na samo miki magani. Akwai ruwa a fridge ki ɗauka ki sha. Akwai abinda ki ke so in kawo miki?." Ta girgiza kai alamun babu sannan ya fita.