BARRISTER SUHAIL

BARRISTER SUHAIL

by @officialkhadeey

🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾

Mallakar

KHADIJA WRITES

YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION
(YOTA)


💖 Dedicated To My Mom 💖


follow me on arewapen 
@officialkhadeey


بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

🅿️----20

Bayan sallar Isha'i Suhail ya dawo a falo ya iske Amatullah da iman suna kallon cartoon Amatullah na ganin sa ta miƙe ta ce"Uncle kai maidani gidan Mami"

kallon Iman yayi ya ce"ki shirya mu kaita tare"

"tom" kawai ta ce

ta koma ciki rolling tayi da veil din jikin ta gyara fuskar ta fito da handbang da flatshoe da sukayi matching da kayan jikin ta fito.

koda ta fito har sun shiga mota back seat ta shiga yaja motar sukayi tafi tunda suka shiga mota Amatullah kewa Suhail surutu 

iman na zaune a kujera baya tana binsu da ido 

a haka suka isa kofar gidan zuciyar Iman ke ta bugawa ba tare da tasan dallilin haka ba da kyar ta fito daga cikin motar suka shiga gidan tana biye dasu a baya 

har suka isa part din mami tana zaune a falon kasa tare da Naima dake feeding Ayla da town brown suka shiga kan carpet iman ta zauna Suhail ya samu kujera nesa da ta Mami ya zauna Amatullah ta haye cinyar mami tana mata nuni da Iman wai tazo ta gaishe ta.

Mami da tun shigowar su ta haɗe girar sama da ƙasa Suhail ya fara gaishe ta Sannan Iman ta ɗago kan ta a hankali ta ce"Ina wuni"

"Lafiya" kadai mami tace a yanayin data amsa mata hatta Suhail saibda yaji bai ji dadi ba ganin kamar ma batayi farin ciki da zuwan ta ba

Amatullah ta kalli mami ta ce"Mami aunty Iman is so kind she take care of me"

Naima ta wurga wa Amatu harara ta ce"talktive waya tambaye ki Mutun sai dan banzan surutu"

Suhail ya dago ya kalleta  alamar kallon warning hakan yasa Naima yin shiru.

Mami ta tashi ta kalli Suhail ta ce"idan kun gama zaman naku zaka iya daukar ƴar malan din ku tafi"

bata jira amsa ba ta nufi upstair ran Suhail idan yayi dubu a bace yake da yasan Wannan wulakanci mami zatawa iman da ba abinda zai tasa ya nemi ta rako su.

Naima ma ta tashi ta dauki Ayla ta koma dakin su 

Iman da kanta ke duke a kasa bata san lokacin da hawaye ya soma fita daga idanun ta Wannan wani irin ahali ne Allah ya kawo ta tana jin ƙiyyaryar uwar miji amman ba irin wannan ba yau ne ranar farko da suka fara haduwa amman tayi mata kalar wannan tarbar.

Amatullah bata lura da Kukan da iman keyi ba amman duk wani motsin ta akan idannun Suhail lokacin zuwa lokacin take goge hawayen da mayafin jikin ta.

miƙe yayi ya ce"muje"

Amatullah har bakin kofa ta rako su ta koma ciki 

part Aunty Fauziya ya Kaita tana zaune kan kujera tare da junaid tana sa mashi Pampers tana ganin ta. miƙe cike da kulawa ta tarbesu Iman na kokarin zama a kasa ta kamo ta zaunar da ita kan kujera.

Iman ta gaishe ta cike da girmamawa ta amsa Suhail ma ya gaishe ta ta ce"yanzu kuke tafe"

"Eh aunty na kawo ku gaisa"

"aiko ka kyauta Suhail Allah ya maku albarka ya baku zaman lafiya da zuri'a dayyiba"

"Da Ameen" duka amsa 

Suhail ya ce"ina aunty Zarah naga junaiid anan"

"ta tafi shopping siyayya kasan gobe Sadeeq din zaizo su wuce"

jinjina kai yayi ta kwantar da junaid ta shiga Kitchen ta hado masu drinks da snacks

Suhail ya ce"Aunty da kin barshi tafiya zamuyi"

"Da wuri haka,Amman ai ka bari Zarah tazo kuyi sallama ko"

"da safe zan dawo in sha Allah"

Aunty Fauziya ta shiga daki ta hado wasu turrarrukan wuta masu tsada da Kamshi da humra masu kyau ta ba Iman har ƙasa ta duka tayi mata godiya suka fito har bakin gate ta rako su suka tafi.

Suhail lokaci zuwa lokaci yake satar kallon Iman amman taƙi bari su hada ido har suka isa gida dakin ta nufa har lokacin tana jin zafin abinda Mami tayi mata wato har ma suna ta saka mata ƴar Malan, aiko ta kira da hakan ma ba laifi tayi domin ba kowani mutun ke samun Matabar da za'a kirashi da Malan ba idan ma abinda yafi haka zata kirata dashi zata amsa kuma tayi Alfahari dashi.

bakin gado ta zauna ta fito da kayyan kamshi da aunty Fauziya ta bata tunda take bata taba gajin kamshin turaren wuta masu kamshin irin wannan ba haka ma humrar da ya hade dakin gaba daya kan mirror ta ajiye ta dauko wayar.

lambar Ammi tayi dailing har ta katse bata daga ba murmushi tayi ta ce"Allah sarki Ammi kila tana chan taskar gida tana aiki ta bar wayar a ɗaki so tari idan aka kira sai dai iman ta kai mata "


sake kira tayi a karo na biyu ta daga ta ce"Ammi na"

daga chan ɓangaren Ammi tayi murmushi ta ce"Autar Ammi ya kike muyi kewar ki sossai wuni daya da kwana daya amman gidan duk ya min shiru sai ni kadai babu ke babu Mubarak ko"

jin haka sai da ran Iman ya dan sosu tasan ammi na gida ita kadai ba Abokin hira malan tasan wannan lokacin yana wajen karatu

"Ammi nima nayi kewar ki sosai"

hira sukayi irin da ƴa da uwa Iman ji tayi duk bakin cikin da mami ta kunsa mata ya gushe a ranta kusan awa guda suka shafe suna wayar har katin Iman ya kare Ammi ta kira dan Mubarak baya taɓa barin wayoyinsu babu kati duk bayan kwana biyu sai ya saka masu.

har wajen karfe goma kafin Ammi ta kaishe ta ce"taje ta kula da mijin ta"

kayan jikin ta cire ta nufi bathroom wanka tayi ta saka rigar bacci har ta kwanta taji Kamar tana jin yunwa doguwar hijabi ta zura ta fita Kitchen dan samawa kanta Abinda zata ci.

indomie ta dafa da tea iya na mutun biyu koda ta gama ta jima tsaye a Kitchen tana tunanin ta yadda zata bashi abincin serving tayi a plate ta fito da cup din tea a falo ta iske Suhail yana kallon news ta ajiye masa a gaban sa.

"Iman" ya kira sunanta karin farko da taji sunanta yayi dadi a bakin wani 

juyo wa tayi ta kallesa 

"kiyi haƙuri da abinda Mami tayi maki"

"ni ai ba Abinda tayi man kuma ko tayi ma ba komai tunda a yanzu Matsayin uwa take a gare ni"

Wani irin girman Iman ya kara cika zuciyar Suhail.

Ba kowa zai iya daukar abinda Mami ta fada ya mayar da shi ba komai ba 

A karo na farko ya ji Abba ya zaba masa mace mai hankali fiye da yadda yake tunani 

Kitchen ta koma ta dauko nata abinci ta koma dakin ta 

duk da Suhail ba cika san indomie amman haka ya sa a gaba ya cinye ya kuma shanye tea gaba daya.

Iman na gama ci ta fito da plate Kitchen tayi Sa'a Suhail ya bar dakin 

ta ajiye ta koma ta haye gado bayan ta rage hasken dakin duvet taja ta rufe jikin ta take bacci yayi awon gaba da ita.

Suhail na Zaune a dakin sa ya tisa laptop a gaba yana aiki har kusan karfe sha biyu ya kashe ya nufi toilet ruwa ya sakar wa kansa ya fito ya zura jallabiyar sa ya nufi dakin Iman.

duhun daya mamaye dakin yashi kunna blue light tana kwace sai baccik take cikin sanda ya kara bakin gadon kusa da ita ya kwana har lumfashin ta na sauka Samar fuskarsa.

hannun ya kaii kan wuyanta a hankali ya soma shafa jikin har zuwa kan kirjin ta Iman dake bacci taji kamar alamun mutun a jikin da sauri ta ware idanunta iya kamshin turaren Suhail ya tabbatar da shine a hankali ta soma ja da baya yana binta har ta kaii karshen gado hannun ta sa ta fara kokarin turesa amman ko motsi ba yayi baki ta buɗe zatayi magana aiko kamar jira yake ya hade bakin waje guda ya fara kissing Tamkar yaro ya samu alewar tsinke.

tuni jikin ta ya fara kyarma kuka ta fasa amman Suhail bai ma san tanayi sai da gaji dan kansa ya cire bakin sa ya cika da shafa mata cikin

tuni jikin ta ya saki kukan ma ta kasa sai tanaji tana gani Suhail ya gama matse mata jikin kokari cire mata pant yake da sauri ta rike ta ce"Dan allah kayi haƙuri Please"

ganin taki bashi dama ya mike har wani jiri yake gani ya daga dakin da sauru ta bi bayan sa ta sawa kofar dakin key 

a bakin gado ta zauna tana safke ajiyar zuciya sai goge bakin take dan ji take har yanzu kamar bakin na hade jikinta sai ciwo yake sakamakon matsar da tasha wajen Suhail.