GADAR TSAUTSAYI 5
by @nusybee143
Page 5
Jiki a sanyaye Mama ta ɗago tana kallon Amra wadda ta yi maganar fuskarta a ɗaure,da alamun ɓacin rai ƙarara a kan fuskarta,don har ga Allah wannan mummunan gidan ya fara isarta,ga wari ga tsantsani da ya ishe ta,ta rasa yadda aka yi Roxy da ba ta Rayuwa a Nigeria ma ta san da irin wannan wajen a ciki
Kafin wani ya sake magana Roxy ta gyara zama tana murmushi ta ce"ba wani abu ai,komai ya yi gaba,amma idan aka koma baya za'a ga tushiyar dawa,ko na ce asalin ungulu,kusan kowacce mace a bariki musamman ƴar talaka za ki ga kuɗi ta zo nema ne, don bata sanshi ba,kuma tana son ɗanɗana daɗinsa,to ba kowa bane ba ya iya jurar talauci ya shiga duniya,kin ga dai kamar Mama,uwa ta gari"ta karasa magana tana murmushi "
Kalaman Roxy kamar an watsa mata ruwan zafi a zuciya haka ta ji su,amma sanin halin Roxy na iya mayar da magana ya sa ta yi shiru,don sanin kanta ne Roxy sam bata da haƙuri,kuma bata da ɗaga ƙafa,muddin aka shiga gonarta,sannan ga tsananin wayo da hikima,ga basira, shiyasa take gudanar da rayuwarta yadda take so a ƙasashe zuwa garuruwa
Bata sake bi ta kan Amra ba, wadda ta yi kasaƙe tana kallonta,ta koma satar kallon Mama wadda fuskarta ta nuna alamun jin daɗin amsar da aka mayar mata sakamakon tsangwama da cin mutuncin da ta nemi ta yi mata
Hira suka cigaba da yi da Mama da Roxy, cikin hikima da wayon da Allah ya hore mata take jefa wa Mama tambayoyi game da Habu, bata yi mamakin jin cewa yana da larurar asthma ba,dama ta san da batun tun ba yanzu ba
Cikin damuwa Mama ta ɗora da batun "yanzu lokaci ne na damuna,ga yanayin zafi,ga kuma iskar gari,ciwon nashi yana yawan tashi,don ma wani lokacin sai mun haɗa da neman taimako a wajen mutanen arziƙi,kuma alhamdulillah ana samu,kin ga ko shekaranjiya da ciwon nashi ya tashi Musa ɗan maƙocinmu Malam Lado ne ya kai shi kyamis aka duba shi,ba ki ga magungunan da ya siyo ba,har da sabon abin zuƙar"
Roxy ta yi shiru na ɗan lokaci tana jinjina kai,tana shirin yin magana sallamar yara ta katse ta
Mama ce ta amsa sallamar,suka shigo yaran
Su biyar ne,biyu mata sai uku maza babban da me bi masa maza ne,sai mata biyu da suke bi musu,sai ɗan ƙaramin su da bai fi shekara uku ba, wanda duk da wahalar rayuwa da ƙangin talauci da suke ciki bai hana kyawunsa bayyana ba, wanda ya zarce ya yi fintinkau wa sauran
Kallon kayan jikinsa take yi,rigar gwanjo ce,sai wando yadi,su ma dai ragowar yayyen nasa babu wani mai sutura mai kyan gani, duk da cewa tsaf tsaf suke,amma ƙangin talauci ya ɓoye kaso mai yawa na tsaftar ta su
Da girmamawa suka gaida Roxy da Amra, Roxy ta amsa tana murmushi tana tambayarsu sunayensu ɗaya bayan ɗaya,duk da cewa ta gane Habu,suka gaya mata ɗaya bayan ɗaya Sannan suka wuce don ajiye allunansu
A jikinta ta rungume Habu tana cigaba da yi masa wasa tana murmushi,shi kuwa sai bin ta da kallo yake yi, kasancewar ba shi da sabo,kuma bai santa ba, gashi kuma ba mai yawan magana ba
Ta ɗan juma tana wasa da yaron,ji take yi kamar kar ta rabu da shi,ita dai Amra tana tsaye akanta kamar wata sanda tana kallon su cikin takaicin wannan ɓata lokacin da Roxy take yi musu
Sun ɓata wajen awa guda a gidan,har hira Roxy ta yi da yaran matar kafin ta yi musu sallama,ta direwa matar 100k ta ce a mayar da yaran makaranta, godiya sosai suka yi mata,ta janyo hannun Habu tana murmushi ta ce "autan Mama in tafi da kai?"
Bai yi mata kara ba ya girgiza mata kai yana komawa jikin Mama ya rungume ta,suka yi ƴar dariya, Mama ta ce "ai shi wannan ba'a bayar da aron shi,na Mamansa ne,daga shi sai ita"
Roxy ta yi ƴar dariya tana faɗin "to yaran mamansa, Allah ya bar ƙauna tsakaninka da Mama,ga wannan ku sha Sweet kai da yan'uwanka"ta faɗa tana miƙa masa rafar ɗari biyar
Tsayawa ya yi yana kallonta, Mama ta ce"a haba!
Kin biya musu kuɗin makaranta yanzu kuma za ki ƙara wani kuɗin?
Don Allah ki bar shi, wallahi mun gode Allah ya saka da alkhairi"
Roxy tana murmushi ta ce"ayya Mama!abin da ba ki sani ba ni ƙawar Fauziyya ce kafin rasuwarta,mun haɗu da ita a secondary,a wancan lokacin Allah bai taɓa nufa na zo gidansu ba,amma bayan rasuwarta na ji ina sha'awar zuwa na ganku,sai na same ku a cikin jarrabawar ubangiji,kuma kin ga Fauziyya ta yi min babban taimako lokacin da tana makaranta,duk sanda na samu matsala a makaranta ita take taimako na ta fitar da ni daga ciki,ba zan manta halaccinta ba
Ni dai yanzu roƙon da nake yi miki shine ki ɗauke ni a yadda kika ɗauke ta"
Murmushi sosai Mama ta yi,tana tuna babbar ƴarta Fauziyya, wadda ta rasu shekaru bakwai baya yanzu,a hankali ta ce"to Allah ya saka miki da mafificin alkhairi"
Roxy ta ce"Ameen Mama, Allah ya ji ƙan Fauziyya da baba, Allah ya albarkaci rayuwar ƙannenta
Wannan jihadi da kika yi Allah ya saka miki da alkhairi "
Mama ta yi ɗan murmushi ta ce"har zuwa yanzu ba ki sanar da ni sunanki ba"
Roxy ta ce"kin manta sanda na zo wancan karon na gaya miki?
Sunana Zainab, kuma a yanzu ina jihar Kaduna ne da zama"
"Allah sarki!
A wanne gari kike a Kadunan?ai mahaifinsu ma ɗan can ne"
Roxy ta ce"a cikin garin Kaduna nake,a unguwar dosa,to Mama za mu tafi,sai idan na sake dawowa "Mama ta fara yi wa Roxy godiya sosai,ita dai Amra har yanzu tana tsaye tana kallon Roxy da tsananin mamakin yadda halayenta da dabi'unta suke canjawa kusan kowacce daƙiƙa a rayuwarta
Babu abin da Roxy ta tsana a duniya sama da ƙarya, ƙarya ba ɗabi'arta ba ce ko kaɗan, kuma bata jituwa da mai yinta,amma sai gashi tana ta zubo bayanin da take da yaƙinin duka ƙarya ne,a gaban waɗannan mutanen da take kallon basu da maraba da bola a wajenta
Ba su sake ɗaukar lokaci ba suka yi wa Mama da yaranta sallama suka fice daga gidan, zuciyar Amra fal da tambayoyi kala-kala
Adaidaita sahu ɗaya suka shiga,sai dai ba su yi nisa ba Roxy ta sauka,ta shige wasu lunguna ta ɓacewa ganinsu, Amra ta bi ta da kallo tana taɓe baki
*MALIYA ESTATE*
"Hooo Hajiya innayyo tamu,ko kewarmu ba ki fara yi ba ne?
Kar ki manta fa, tafiya za mu yi, Allah ne kaɗai ya san lokacin da za mu sake waiwayar Nigeria"a cewar Iman tana rausayar da kanta tana yiwa innayyo magana, mahaifiyar Alhaji Yusuf Maliya
Wani kallo innayyo ta watsawa Iman, sannan ta sake jefawa su Surayya da suke dariya wani mugun kallo,ta ce"ko me za ki ce sai dai ki ce,duk wasu yan kayan da na siya saboda motsa baki kin sace kin cinye, to wannan ahir ɗinki"
Zaro idanu Iman ta yi,su kuma su Surayya suka kwashe da dariya, Amina har da taɓawa iman kunne, Iman ta galla mata harara,sannan ta dubi innayyo ta marairaice tana faɗin "haba innayyo ta!
Daga yau ne fa, gobe iwar haka ma mun bar ƙasar miki ƙasar ma"
Innayyo ta taɓe baki tana girgiza kai,ta ce"Ni wannan karatu naku da sai an tafi wata uwa duniya ba wai ina son shi bane,kawai dai ban yi magana bane saboda na ga baban naku ya dage, sannan kuma akwai masu yi muku baƙin ciki da hakan,tabbacin alkhairi ne karatun kenan"
Tuni suka mayar da hankalinsu gaba ɗaya kan innayyo, ba don sun yi mamaki da maganganun innayyo ba, dama sun saba da jin abin da ya fi haka daga bakin innayyo akan Ummeey, kasancewar kaf sirikanta babu wadda ta tsana kamar Ummeey,duk da biyayya da ladabin da take yi mata
Wannan sanannen abu ne a wajen iyalan Maliya gaba ɗaya,wani abin ma da ƙarin ƙiyayyarta baiwar Allah Ummeey take samu, inda kawai take samun sa'ada shine soyayyar da mijinta yake yi mata,duk da matansa uku kuma ita ce uwar gida amma soyayyar da yake yi mata dabam take
Surayya ta dubi innayyo sosai ta ce"wallahi fa innayyo,ki ji min mata da hassada, banda abin kunya ta rasa wanda zata yi wa hassada sai mu,to ta yi mana ma,ina ga iyayenmu mata kuma?su da suka haifi yara maza da mata?ba ita ba da ta tsaya akan guda ɗaya?ɗayar ma wadda ta lalace?"
Iman ta ce"saboda abin takaici ana saka sunayen mutanen kirki amma ni wai sai a saka min sunanta "ta ja tsaki cikin takaici
Amina ta yi ƴar dariya ta ce "ku yanzu kuka san halinta,mu mun daɗe da sanin halinta"
Iman ta ce"seriously Meena,ta kasa gane mugun halinta ne ya janyo mata lalacewar rayuwar tilon ƴarta,kuma Allah ya hana ta wasu yaran har zuwa yau,har da wani wai za mu lalace,to alhamdulillahi, Allah yana tare da mu, babu wanda ya isa ya yi mana lahani,ko boka ko malam "
Innayyo ta dube ta ta ce"in sha Allahu ma nan gani nan bari, shiyasa ma nake turara ku da maganin ƙaiƙayi koma kan masheƙiya amma ku rinka yi min surutu kuna cewa ina damunku da ƙauri,gashi nan kun ga amfaninsa yanzu ai"
Surayya ta rike haɓa ta ce"wai!
Ai kuwa dai mun gani innayyo, Allah ya sawwaƙe,ya tsare mu sharrin mahassada kawai"
Sauran suka ce "Ameen!"Iman ta ɗora da faɗin"ya kamata a ce mun gama ɗaukar duk abin da za mu buƙata girls, let's go please "suka miƙe babu musu, Iman ta ce"to granny,zuwa gobe dai zan bar miki gidan,dama kin san min abin da kike ci,ai ba wani abu bane "innayyo ta ɗauki mafici ta jefe ta da shi,suka fice da gudu daga ɗakin suna dariya, innayyo ta ce"yan nema kai!"
*HAISAM*
Su biyar ne a zaune a cikin ɗakin sirrin, wanda ba'a shigarsa sai mamallakin ɗakin,wato CSO Haisam Abdulmalik Madaka ya buɗe shi da security ɗin idanunsa(eye Scan)ko na yatsansa(fingerprint scanner)
Hatta da Amna, ƴarshi ɗaya tilo baya barinta tana zuwa wajen ko da wasa, saboda tsananin muhimmancin da yake da shi a wajensa
Mutanensa ne na DSS su huɗu,dukansu yaransa ne da yake aiki tare da su,a gabansu computer ce wadda take taimaka musu don gudanar da binciken nasu
Hoton Roxy ne akan computer ɗin, Haisam ya ɗago yana kallon abokan aikin nasa, kafin ya fara jawabi
"Wannan ita ce wanted ɗin tamu,a halin yanzu babu abin da muka sani nata sai fuskarta
Ba mu san sunanta ba, ballantana wajen zamanta,daga ina take? menene bayani akan wacece ita? A'a!
Abu biyu kawai gare mu, fuskarta,sai kuma haruffan da take amfani da su,wato NOCCM, wadanda har zuwa wannan lokaci su ma ba mu san abin da suke nufi ba
Ita ɗin ana zarginta da aikata manyan laifuka a ƙasa,babbar hacker ce,ta ƙware sosai a sana'ar Yahoo, Sannan kuma cikakkiyar dealer ce ta cocain da miyagun ƙwayoyi
Manyan abin lura a tare da ita su ne,na farko ta raina hukuma,bata jin tsoron kowa, sannan ta goge akan wannan harkar tata
Duk da haka a matsayin mu na yan sanda maau bincike ya kamata a ce mun kama ta tabbas
Amma kafin nan kamata mu zama masu lura,ko da ya kasance ana zarginta da Laifuka dabam dabam amma babu kisan kai, hakan ba zai saka kai tsaye mu ce bata yi ba, don hatta da Safarar kwayoyi da Yahoo da take yi sai daga baya muka sani, wannan ɗin ma zata iya aikatawa
Abin da nake so shine mu yi taka tsantsan, sanannen abu ne a wajenmu cewa wannan matashiyar bata da suna a wajenmu,amma ina fatan za'a dace wajen samo ta a duk inda take a fadin duniya
A yanzu za mu duƙufa wajen nemo sunanta,da ma'anar haruffan NOCCM da take yawan amfani da shi,amma ku menene shawararku?
Ko kuna da wani hanzari?"
Ɗaya daga cikinsu mai suna Musa ya ɗago yana kallon Haisam,a hankali ya ɗaga hannu, Haisam ya ba shi damar magana,ya mike yana duban Haisam, kafin ya ce"sir!
Ina ganin ya kamata a fara mayar da hankali wajen gano ma'anar wadannan haruffan NOCCM,don ina kyautata zaton ƙungiya ce, wadda take daukar nauyin ta'addancin da take yi a duniya
Don har yanzu bana ji a raina cewa ƴarinyar nan tana aiwatar da duk abin da take so ba tare da tsayawar wani babba ba,a takaice ma,bata da ƙarfin ƙwaƙwalwar da zata iya yin hakan "
#Nusy_bee