HADIN KADDARA

Chapter 27

by @aishanalado88

🌀 *HAƊIN ƘADDARA* 🌀

                     By

         
           AyshaNalado


Sadaukarwa ne a gareki ƴar uwa rabin jiki *RUKAYYATU* (Aunty Ummi) Son so fisabilillah😍


BOOK 1


Page  27



*BARKA DA SALLAH*

Rass! Gabanta ya yanke ya faɗi, Da sauri ta kalli Ammie, sai dai ga mamakinta babu wani sauyi ko razani a tare da ita ba,  sai ma juyowa 
da ta yi tana kallonta har lokacin da sanyayyar  murmushi a fuskarta, ta sake juyawa  ga Salmah da tun shigowarsu ta nemi waje ta zauna akan extra bed din dake dakin, da kuma Ya Ammar dake  tsaye daga bakin kofa jingine da bango,  kafin ta hadiyi wani busashen miyau, ta kallesa ta saki wani gajeren murmushi wanda iyakarsa laɓɓanta, ta amsa masa da faɗin “Na'am Yayana, Oyoyo.” Murmushi  ya yi yana sake narke idanunsa a kanta ya ce “Gawa ta ƙi rami. Ya jikin?” “Da sauƙi Alhamdulillah.” Ta amsa a sanyaye da muryarta  ta marasa lafiya, “Ma sha Allah, Allah ya kara miki sauki Ayush, duk da nasan don kar ki tarbe ni ne, kika langwabe ki ka kwanta ciwo har gadon asibiti.” Murmushi kawai ta yi ba tare da ta amsa masa ba,  ta riga ta saba da yanayinsa na barkwanci, haka yake very simple, har ma yafi Salman sakin fuska da sauƙin kai, duk yanayinsu ɗaya da Abie.   “ Ina wuni Ammie?” Ammar ya tsuguna daga inda yake tsaye ya gaisheta, “Laa Ammar ashe tare ku ke, wallahi ban kula ba.”  yana murmushi ya ce “Tare muke Ammie ya mai jikin?” “To gata nan da sauƙi dai zance Ammar.” “Allah ya kara sauki. Sannu  Sister, ya jikin naki?”  Ya mayar da gasiuwar kan Aysha, “Da sauki Ya Ammar ina wuni?”  “Ina gajiya mai babban suna, Sannu Allah ya kara miki lafiya.” Da Amin duk suka amsa. Sai sannan Anas ya mike daga gaban Ammie ya koma kusa da Salmah ya zauna, Ammar kuma ya ja farin kujerar roba irin wanda Ammie ke kai ya zauna shima,  nan take hira ta barke , a tsananin Ammar da Anas, irinta abokan da suka dade ba su ga juna ba,  hirar tafi karkata ne akan labarin kasar da ya baro Singapore, yadda ya dinga gudanar da rayuwarsa a can, kalubalen da ya ɗan fuskanta da farko kafin ya saba da kasar,  hakan ya sa daƙin ya yi tsit,  suna saurarensa, sai Ammar da ke yi masa tambayoyi da sharhi, Ammie na saka musu baki jefi jefi.  Salmah kam kasa sakewa ta yi saboda idanun Ammar da ke yawo a kanta, ta takura sosai ga wani irin kunyarsa da take ji, ita kanta har mamakin kanta take yi, kamar ba ita ba, wayarta ce ta ɗauki vibaration, alamar shigowar kira, da sauri ta  katse kiran, ta ɗago  a ɗan diririce kamar mara gaskiya ta kalli mutanen ɗakin. Duk babu wanda ya kula da yanayinta, illah Ammar da rabin hankalinsa ke gareta,  ganin haka yasa  ta lallaɓa ta haye  can karshen gadon ta shiga latsa wayar, kimanin mintuna goma, ta gado kaɗan cikin dabara  ta shiga yiwa Aysha da ta koma ta kwanta lamo ta lumshe ido kamar mai barci tana sauraren muryar Ya Anas  da ke sanya zuciyarta girgiza bidiyo ba tare da sanin kowa ba.  Mintuna ashirin suka kuma shuɗewa a haka kafin a turo kafar ɗakin, Salman ya shigo bakinsa dauke da sallama can ƙasar maƙoshi, fuskar nan tasa turbune, babu alamar Rahama, duk ido suka zuba masa yayinda Ammie da ita kadai ce ta ji sallamarsa ta amsa masa, bai kula da baƙin da ke cikin dakin ba har sai da ya mayar da kofar ya rufe ya yi taku biyu, kafin idanunsa suka hasko masa ya Anas zaune a bakin gado yana sakar masa sanyayyar murmushin nan nasa mai kwantar musu da hankali. Turus ya yi irin na ganin bazata, sai kuma ya juya ya kalli Ammie, ya miƙa hannu ya murza ido ya sake juyawa gefen da yaga Anas still ya sake ganinsa, sai kawai ya nufesa da sauri suka rungume juna suna dariya, Ammie da Ammar na tayasu, Aysha da har lokacin idanunta ke lumshe, ta kasa budewa saboda gani take kamar za su gane halin da zuciyarts ke ciki ta kwayoyi idanunta, ita ma murmushi take yi, don tana hasaso mai ke faruwa a zuciyarta, Salmah kam ɗauke  kai ta yi, tare da taɓe baki, duk da zuciyarta cike take da shauƙi da farin ciki.

Zuwan Salman ya kara rikita ɗakin, tuni ya mance da buhuhunan masifar da ya yi dako ya niko gari takanas ya bar lecture don ya zo ya sauke su akan Salmah. Nan da nan ya ɗauki waya ya kira Abie ya mai albishir ya kira Hajiya Saude da Aunty Aina'u, ya shiga kiran dangi makusanta yana sanar da su, har ya gangaro kan lambar Suraj, nan take abinda ya faru da safe ya dawo, yanayinsa ya canza har hakan ya bayyana a fuskarsa ya ɗago ya kalli Salmah, cikin sa'a itama ta kallosa ya watsa mata wani shegen kallo da ita kaɗai ta san ka menene, bata yi ƙasa a gwiwa ba ta balla masa harara tare da jan dogon tsaki mara sauti, ya yi ƙwafa tare da kau da kai, ya kara waya a kunnensa ya fara magana da Uncle Adam, da ya mayar da akalar kiran Suraj kansa.

Ammie ce kaɗai ta kula da abin da ya faru, bata tanka ba, a zuciyarta ta ce “Allah ya yaye muku.”  a zahiri kuwa ta ce, “Salmah taso ki zuzzubawa mutane abinci mana, sam baki da wayo, komai zai an koya miki.”   Dan turo baki ta yi kasancewar Ammie ta bata baya, sai kuma ta saci kallon Ammar cikin sa'a suka hada ido, da sauri ta sunne kai, a diririce ta shiga kokarin zamowa daga gadon. Murmushi ya saki tare da kawar da kai, ya mayar kan agogon hannunsa, ganin lokacin sallah ya yi, ya ce, “Ammie ai ina ganin a bari mu yi sallah.”  Ya yi  maganar tare da miƙewa, “Gaskiya kam.”  Anas ya faɗa shina yana kallon agogo “Lokaci ya yi ko? To babu laifi, muma bari mu yi namu tukunnah.” Cewar Ammie. Mikewa Anas ya yi ya kama hannun Salman ya ja shi suka fice a tare su uku.


*************


Yanayin shigowar Suraj ya yi matukar tayarwa Mother da hankali,  da sauri ta saki jaka da gyalen da ke rike a hannunta tana kokarin yafawa, domin cikin shiri fita take. Ta nufosa da sauri tana faɗin, “Innalillahi wa Inna ilahi raji'un! Surajudeen! What's happening, me ya sameka haka?” Ta sake bin ƙafarsa da ya yi futu futu da ƙura da kallo, ga dukkan alamu tafiyar kasa ya yi mai nisan gaske kafin ya iso gida, ga idanunsa a zurme sun ƙanƙance sun rine, fuskarsa ta yi jajur musamman siɗe ɗin da Salmah ta mare shi, farar rigarsa a cukurkude duk jirwayen datti da hawaye kamar ba ita ya saka tana ɗaukar ido kafin ya bar gidan ɗazu ba.  “Ka gaya mini Suraj, na ce meya faru baka da lafiya ne?” ta sake yi masa tambayar tare da miƙa hannu kasancewar ya fita tsawo ta shiga taɓa wuyansa zuwa goshinsa don ta tabbatar da abin da take zargi, jikin da zafi kuwa don da gaske zazzaɓin yake. Murmushi karfin hali  ya sakar mata tare da rike hannuta, muryarsa a dusashe ƙasa-ƙasa ya ce, “Babu komai Mother, I'm fine.” sai kuma ya saki hannunta ya raɓa gefenta ya haura sama zuwa dakinsa. Kamar mutum mutumin tabi bayansa da kallo har ya ɓacewa ganinta, sai kuma kamar wacce ta farfaɗo daga suma, ta zabura ta zura da gudu ta bi bayansa, sai dai kafin ta iskesa, har ya banko kofa ya murza key. 

Sosai hankalin Mother ya tashi domin tunda take da Suraj, yau yana neman shekara ashirin da biyar a duniya  bata taɓa ganinsa cikin irin wannan yanayin ba, ko bashi da lafiya jikinta yake kanannaɗewa, kamar sabon ɗan yaye, ya yi ta zuba mata shagwaɓa. Tana da tabbacin  koka menene yake damunsa, ba ƙarami ba ne. Sai da ta yi tsayuwar kusan mintuna goma tana knocking tana kiran sunansa amma shiru ko motsinsa bata sake ji ba, jiki a sanyaye  ta koma ta zauna ta zuba tagumi, ta rasa me ke yi mata daɗi, tuni ta manta da fitar da shirya yi, kimanin mintinan ashirin ta kwashe a haka, kafin ta zabura ta ɗauki wayarta ta shiga kiran layin Salman, domin tana da tabbacin a wajensa kaɗai za ta iya sanin meke faruwa, sai dai cikin rashin sa'a wayar ta ƙi shiga, sai ta mayar da akalar kiran kan Bunayyah.

A daidai wannan lokacin Mr AA, yana zaune a gaban Abba da kuma baban aminin Abba wanda suke tamkar, tif da taya saboda shakuwa da sanin juna, Alhaji Kabiru , abokinsa ne tun na yarinta irin abotarnan da ɗaya baya iya aiwatar da wani abu a rayuwarsa sai da sanin ɗayan, duk wani gwagwarmaya  da faɗi tashin rayuwa tare su ka yi, har kawo zuwa yanzu. Tattaunawa su ke yi akan yarinyar da  Abba ya sanya  ya yi masa bincike a kanta wato Aysha. Be ɓoye musu komai game da abinda ya faru tsananinsu ranar da ya sanya su Ussy suka dauko masa ita ba, duk shiru su ka yi suna nazarin lamarin, zuciyoyinsu cike da al'ajabi. A haka wayar AA ta ɗauki ruri,  ganin sunan Mother yasa ya nemi iznin su Abba, kafin ya daga wayar. Yadda ya ji muryarta yasa gabansa ya faɗi, ya shiga tambayarta abinda ke faruwa hankalinsa a ɗan tashe, hakan ya sa su Abba suka zuba masa idanu, “ Surajudeen ne, Bunayyah.” Iya abinda ta faɗa kenan ta dakata saboda muryarta da yake rawa kamar tana shirin fashewa da kuka, miƙawa tsaye ya yi yana faɗin “Gani nan zuwa gidan yanzu.” Ya katse wayar ta mayar aljihu, ya kalli Su Abba cike da ladabi  ya ce, “ Afuwan Abba, ina tunanin babu lafiya zan je na ga mai ke faruwa.” Gyaɗa masa kai Abba yayinda Abba Kabir, ya ce, “Ashha! Jeka maza Ahmad Allah ya sauƙaƙa, ka gaida Asma'un”. “To Abba.”  ya Amsa tare da ficewa da sauri, hakalinsa  a ɗan tashe, sai dai kwata kwata hakan bai nuna a yanayinsa na zahiri ba saboda tsabar iya kamewa.

Bayan tafiyar AA Abba Kabir ya zakuɗa ya  kalli Abba ya ce, “Anya baka tunanin makirci a lamarin yarinyar nan, sam ban ji na gamsu da bayanan Ahmad ba.” Abba ya sauke ajiyar zuciya mai karfi kafin ya ce, “Ahmad yana da zurfin tunani da kaifin basira fiye da duk yadda  muke tunani, na san ba zai tasa mu a gaba ya fada mana son ransa ba, amma ni ma ina tantama game da wannan al'amari, idan babu rami me ya kawo zancen rami? Sai dai ba Ni da ja, domin ina da kyakkyawar yaƙini akan Ahmad.” cikin ɗan hasala Abba Kabir  ya tari numfashin Abba, “Bai kamata mu bar maganar nan haka ba Idris, wannan sanyin naka shi ya sanya har yau muka kasa yi wa wannan tufkar hanci, shekaru sama da arba'in ana abu ɗaya, ya ƙi ci ya ƙi cinyewa kamar cin kwan makauniya, idan har su sun gaza ganin bayanmu, to ya zama dole mu muga nasu, wannan karon ba zan goyi bayanka, rayuwar Ahmad tana da mahimmanci, a garemu da al'umma gaba ɗaya a yanzu haka shine kashin bayanmu, ya zama dole mu ba shi kariya da iya iyawarmu.”  Murmushi Abba ya yi,  ya ɗauki ruwa a cup dake ajiye kan table ɗin dake gabansu, ya kurɓa kaɗan ya mayar ya ajiye, ya fuskanci Abba Kabir da kyau ya ce “Ai ba za su taɓa iya cimmana ba, domin  mun riƙe Allah, kuma ya tsaya mana, ba domin haka ba, shekara arba'in ai ba kwana arba'in ba, ko ka tuna abin da ya faru shekaru takwas baya?” Ya karashe zancen da tamabaya idanunsa akan Abba Kabir alamar yana jiran amsa daga garesa. Gyaɗa masa kai ya yi, ba tare da ya iya bude baki ba. Abba ya sake yin murmushi ya ci gaba da cewa, “Wayon mu ne, ko iyawarmu?”  Ya girgiza kai sai kuma ya baiwa kansa amsa,   “Babu ɗaya Kabir, Allahn kenan ai, ina fatan ka gane.”   Gyaɗa kai Abba Kabir ya yi cike da gamsuwa fara'ar fuskarsa ta faɗaɗa, sai dai kafin ya kai ga sake furta wata kalma, Aunty Rukayya ta shigo falon bakinta ɗauke da sallama, kamar kullum cikin kwalliyarta na hamshaƙan mata, gaban Abba Kabir ta ɗan risina ta ce, “Ina kwana kawu.” Ya bita da kallo yana yar murmushi ya amsa, “Lafiya ƙalau Rukayya, fatan ki na lafiya.”  “Lafiya kawu, ya su Aunty Binta da sauran yara.” “Kowa na nan ƙalau duk suna gaishe ki.”   Shigowarta shane ya daƙile wancen hirar suka maye gurbinta da wata, Aunty Rukayya ɗiya take ga Alhaji Kabir, yar marigayi yayansa ce Malam Tukur, shi ya aurawa Abba ita bayan rasuwar matarsa Hajiya Zainaba mahaifiyar Ahmad, da shekara ɗaya, ita kuma lokacin tana zawarci, bayan mijinta mahaifin  tilon yarta, Na'eemarh, ya gudu ya barta daga cewa zai je ganin gida, ashe ya sayar da ɗan gidan da suke ciki sai watso mata kayanta aka yi wajen, a garin haka ne ta ci karo da takardar sakin da ya rubuta ya saƙale mata  a inda yake da tabbacin duk ranar da ta zo kwashe kaya za ta ci karo da shi....


*************


Cikin ƙanƙanin lokaci AA ya isa Kangiwa Estate, har lokacin Mother na zaune a falo,  ta zuba tagumi da dukkan hannayenta biyu, ta yi zurfi cikin tunani sai zaman shi kawai ta ji a kusa da ita, ta ɗago ta kallesa, da idanunta da suka kaɗa, hannunta ya kama, ya rike cikin ƙasa ƙasa da murya ya ce, “Me ya samu Surajudeen ɗin?”  Sai da ta ja dogon numfashi ta fesar, kafin ta shiga ba shi labarin halin da suke ciki, bai katse ta ba har ta dasa aya. Shi kansa ya cika da mamaki kuma yana da tabbacin koma menene to tabbas ba karamin abu ba ne, zai jefe Suraj a irin wannan yanayin, sai da ya kwantar mata da hankali, kafin ya mike ya haura sama zuwa ɗakin Suraj ɗin, turawa ya yi ya ji shi a kulle, sai ya shiga knocking kaɗan kaɗan, nan ma ba wani motsi, a hankali ya shiga kiran sunansa ya basa umarnin bude ƙofar. Jin muryar AA ya sanya Suraj dake zaune a tsakiyar gadonsa ya tankwashe kafa ya dukar da kai yana ta rubutu cikin wata ƙatuwar memo ya ɗago kai,  ya kalli kofar, “ Ya B!” Ya furta akan labbansa, sai kuma ya miƙe jiki a mace ya nufi kofar ya cire lock ɗin, jin haka yasa AA murɗa kofar dakin ya shiga bakinsa dauke da sallama. Kallo ɗaya Suraj da ya koma bakin gado ya zauna bayan ya bude kofar, ya yi masa kamar wani mara gaskiya ya yi ƙasa da kansa. Daga bakin kofa A A  ya yi tsaye yana karewa masa kallo, kusan mintuna biyar a haka, kafin ya sauke idanunsa a kan memo da pen ɗin dake a tsakiyar gadon ya ɗan kura musu ido suma, kafin ya taka a hankali ya isa gaban gadon ya miƙa hannu ya dauƙa yana dubawa............






Wacce ta shirya payment yanzu kafin mu gama Book 1  800₦ ne , a saka a wannan account ɗin 7041130088 Aisha Alhaji Yahaya Opay, a turo shedar biya ta ***.