BARRISTER SUHAIL

BARRISTER SUHAIL

by @officialkhadeey

🐾 BARRISTER SUHAIL 🐾

Mallakar

KHADIJA WRITES

YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION
(YOTA)


💖 Dedicated To My Mom 💖


Wannan paging Mamah beb ina jin daɗin sharhin ki Har cikin raina kuma nake jin ki wlh😩♥️

بِسْمِ اللهِ الرَّحْمٰنِ الرَّحِيْمِ

🅿️----21

Suhail na fita daga dakin Iman zuciyarsa cike da wani irin yanayi Bai taba tunanin zai rasa nutsuwarsa haka ba a hankali ya koma dakinsa ya zauna gefen gado yana shafa goshinsa 

A ransa yake cewa,

Me yasa na kasa controlling kaina haka dan karamin tsaki yaja ya koma bathroom yayi wanka

A bangaren Iman kuwa, har yanzu zaune take bakin gado tana kokarin daidaita numfashinta. Ba wai tsanar Suhail take ba, amma komai sabo ne a gare ta Tun tana karama tarbiyyar da aka yi mata ta sa bata saba kusanci da namiji ba haka ba

Duvet ta jawo ta kwanta amma bacci ya gagare ta gani take kamar Suhail zai dawo ya kara yi mata wani abun duk da ta rufe dakin 

Da asubah ta tashi tayi alwala ta tada sallah Bayan ta idar sai ta zauna tana karatun Al-Qur’ani cikin sanyin murya 

sai Wajen karfe 8 ta rufe Alqur'ani ta tashi ta nufi Kitchen dan dora breakfast kofar dakin Suhail tabi da kallo tana jin yau ko Sallar Asuba bai fito ba.

tea da bread sai omlette kawai ta iya hadawa ta jera komai kan dinning tana tsaka da jera cups Suhail ya fito sanye yake da wani ash din yard yayi matukar kyau a jikin sa.

wata kunya taji ta lulluɓe ta tinawa da Abinda ya faru daren jiya tsananin ta da shi,ta kasa ko bude baki bare ta. gaishe shi 

duk Suhail na lura da hakan a ransa yayi kansa Alƙawarin ya zama dole ya raba ta da wannan kunyar.

ta gefen ta ya wuce zuwa dining din zata koma daki ya ce"come and serving me"

ji tayi kamar ta ce"bazata tayi ba"

tunawa da nasihar mahaifin ta da kuma ta aunty zaituna yasa ta koma ta fara hada masa

wayar dake ajiye gefen sa ta fara Ringing sunan zeenah ya bayyana tare da alamar white heart a gaban sunanta

da sauri ya janye wayar ya katse kiran iman ta daga ido ta kallesa ba tare da ta ce komai ba ta gama hada masa ta koma ciki

duk ranta babu dad'i miyasa zai yi rejecting call din to kodai yar uwar sa ce amman idan yar uwarsa ce ai bazai ji kunyar daga wa gaban ta ba kuma tana kula da yadda hankalin aa ya tashi bayan tabbatae da taga sunan wanda ta kirasa.

kayan bacci jikinta ta cire ta daura towel ta nufi toilet fitowar daga wanka kenan taji fitar Suhail a mota ta window ta leka sa already har ya riga ya fita.

fita tayi zuwa dining taga abincin ma ba wani cin kirki yayi masa ba kuma. ta tabbatar fitar sa nada nasa ba da kiran wayar da akayi masa

ji tayi kawai ranta ya ɓaci wanda idan za'a tambayeta Dalilin ɓacin ranta baza ta iya fada ba.

a haka ta gama shafa manta ta saka wata brown din atamfa dinkin riga da siket dinkin yayi mata kyau sosai a jikin ta humrar da aunty Fauziya ta bata ta shafa tare da sauran perfumes dake jere akan mirror .

Kitchen ta koma ta hado nata breakfast din ta zauna a falo tea kawai ta iya sha shima ba wani da yawa ba ta kwashe ta maida

zama tayi ta saka kallo a gaba ba ,ba wai dan tana fahimtar Abinda take kallo ba

waya ta dauka ta kira hafsat cikin Sa'a ta same ta bayan ta daga "Amarya sai yau kika tuna dani ko dadin miji yasa kin mata damu" Hafsat ta yi maganar cike da zolaya

Iman ta ce"wani dadi kuma Hafsat"

"ke karfa ki raina min wayo ai duk musan abinda ke faru ai waya sani ma war haka ko yaya Suhail ya jefa kwallon sa cikin raga"

a wannan gabar Iman ta rasa mi zata cewa Hafsat dan indai ita ce zatayi abinda ya fi haka

Iman ta ce"Ina aunty zaituna"

"tana nan lafiya qlau ina school yanzu haka"

"Allah ya bada sa'a"

"Amin ina yaya Suhail din"

"ya fita" kawai iman ta faɗa

hafsat ta ce"har ya gama cin amarcin nasa kenan"

Iman ta ce"kinga sai anjima idan kin koma gida ki gaishe min da aunty Fauziya da baba"

bata jira mai hafsat zata ce ba ta kashe wayar.

anan bacci yayi awon gaba da ita cikin baccin taji kamar an tsikare ta ƙasar marar da sauri ta tashi jin kamar ciwon na karuwa  sako wa tayi daga kan kujerar tana ta juye juye ta dafe marar da hannun ta kusan awa daya ta shafe a haka tun tana kukann har taji sai zufa ke karyo mata duk da sanyi Ac dake dakin 

a haka Suhail ya dawo ya iske ko motsin kirki bata iyayi da sauri ya ƙaro ida take hannu ya kai zai kamata da sauri ya sauki jin zafin jikin tamkar an dora garwashi hawaye ke ta zuba daga idanun ta har lokacin hannun ta na kan cikin ta.

Suhail ya ce"miya same ki"

nuni tayi masa da cikin ta

a rude ya ce" tashi mu je asibiti"

mikar da ita da yayi yaga jikin duk ya ɓaci da jini har kan tiles sai zuba yake kamar a buɗe famfo

ajiyar zuciya yayi ganin abinda ya sa mata ciwon marar kenan

kallon ta yayi cike da tausayawa ya ce" dama duk wata kina irin wannan ciwon cikin"

kai kadai ta iya daga masa 

"wani magani kike sha"

"Ammi ke kaini asibiti ko yaya Mubarak"

kwantar da iyayi yayi Sameer kadai ya fado ran sa tunawa da yayi matar sa nurse ce kiran sa yayi bayan sun gaisa Suhail ya ce"Iman ce bata da lafiya ko maryam zata so ta duba ta Please"

Sameer ya ce"ba damuwa bari sai na kawo ta

wajen iman ya koma ya ce"muje ciki ki gyara jikin lafin tazo"

da taimakon Suhail ya kaita dakin ta cire kayan jinkin ta shiga toilet kan ta fito ya dauko mata wata riga marar nauyi tare da pad dake cikin lefen da kuma sabon pant ya ajiye mata.

ya koma palorn ya gyara duk inda ta ɓata