RAGAYAR DUTSE

PAGE 5

by @nanahaleema11

  *RAGAYAR DUTSE.*


            ©️ *Nana Haleema.*


*Book 1*

*Page 005.*



Saheer yana fita ya shiga motar da take ajjiye a ƙofar gidansu. Yana shiga wanda yake cikin a zaune a motar ya ce, "ka kirani a daren nan, ga sanyi." 


Ya ɗan yi tsaki ya ce, "ka cika mita wallahi, Islaha ce a ɗakina shiyasa zamu tafi tare." 


Sadik ya buɗe ido ya ce, "Wow, ka ga masoya, har kwana take a ɗakinka ashe. Kana nunawa yarinyar nan soyayya, ko da yake itama tana sonka. To meyasa baza ka kwana tare da ita ba?."


"Sai aurena ya hau kanta, sannan hakan zai faru." 


Sadik ya bi sa da harara ya ce, "Kamar wani mutumin kirki, mtsww. Meye dan kun kwana tare? Ai normal ne."


Saherr ya ce, "babu ra'ayin yin hakan" ya faɗa yana duba wayarsa. 


Sai ya ce, "kai boss ya kira ni, mu je duk yadda aka yi akwai wani abun." 


Sadik ya fara jan motar sannan ya ce, "wai meyasa baza ka shigo da Ishala cikinmu ba?." 


Saheer ya yi masa banza kallo ya ce, "Matar da zan aura ce fa."


"So what dan zaka aure ta? Mata nawa ne a cikin mu suke da auren?."


"Baka da hankali."


"Na san daman haka zaka ce, amma da zata shigo zata kawo haske sosai."


"Ka daina wannan tunanin, domin kuwa har abada!."


Sadik ya yi dariya ya ce, "Allah ya sa kar boss ya gano ta, kuma ka san in ya gano ta ko wacece ita  sai ta shigo." 


Saheer ya wani kalle sa, sannan ya ce, "ta ya zai ganta?."


"Itace take gabatar da shirin Rayuwarmu talkshow, ko ɗazu na ji wani yana kallon shirin har yana yabonta, fuskarta ba ɓoyayyiya ba ce, tsaf zai iya ganinta."


Saheer ya ce, "Don Allah ka bar maganar nan, bana so wallahi. Harka kasuwancina daban, matata daman, ka daina haɗa min ita dashi." 


Sadik ya ce, "Allah sarki, ashe mu duk bamu san abinda mu ke yi ba" ya faɗa yana hararasa shi dai bai ce masa komai ba suka cigaba da tafiya.


                 Washe gari.


Slowly take tafiya zuwa cikin falon, bata so ta ga wani daga cikin gidan a zaune, bata shiryawa tashin hankali ba. 


Tana zuwa tsakiya ta ji muryar Mama, cikin ɗaga murya ta ce, "dawo nan!." 


Islaha ta runtse ido, ta dawo a sanyaye ta zauna a akan carpet ta ce, "Ina kwana." 


A fusace ta ce, "da ban kwana ba zaki ganni? Shegiyar yarinya ƙaramar karuwa, ni za ki kawowa bariki har cikin gida? Kuma ki rasa da wanda za ki yi barikin sai da ɗan cikina?. Kina cikin hankalinki kuwa?."


Islaha ta kalle ta ta ce, "Wallahi Mama ba abinda ki ke tunani ba ne, kawai....."


Bata ƙarasa ba, Mama ta tsinke ta da marin da ya saka ta yin shiru tana dafe fuskarta. Ta dinga bin Mama da kallo cikin mamaki, ba dan matsayin mahaifiyar Saheer da take dashi ba, wallahi sai ta rama. Amma baza ta iya ba, ko babu komai Mamansa ce.


Mama ta sake fusata ta ce, "in ki ka kuma yi min magana wallahi sai na yi miki dukan tsiya a gidan nan...." Islaha ta yi shiru hawaye ya cika mata ido, suka fara sauka akan fuskarta.


"Ni za ki kawowa iskaci har gida? Ki shiga ɗakin ɗana ku kwana tare, sannan ki dawo min yanzu ki shigo min falo, dan ba ki da kunya ba ki da mutumci? Uban me Saheer ɗin ya yi miki?." 


Bata amsa ba sai kukan da take yi a hankali cikin ƙunar rai da baƙin ciki. Ta so ace wata ce ba Mama ba, da ta faɗa mata abinda kunnenta zai toshe gabaɗaya.


Hanan da hayaniyar Mama ta tashe ta daga bacci, ta fito tana kallonsu ta ce, "To Mama sai kin tambaya? Me ta yi masa za ki ce, ba me ya yi mata ba. Da yawan wanda suka tashi a wani waje inda ba gaban iyayensu ba meye basa yi? Balle Islaha, yarinyar da kowa ya san halinta. Ai kawai ki saka a ranki ta gama lalube miki ɗa, daga ganin yanayinta kin san ta gama dashi wallahi."


Mama ta sake fusata, ta kalli Islaha ta ce, "za ki faɗa min abinda ki ka yi masa ko sai na ci uban ki a gidan nan?." 


Islaha ta goge ido, tana ji ko Maman ce fa sai ta miƙe ta ɗauki mataki, in ba haka ba rainin zai yi yawa. Ta haɗe rai ta ce, "ni babu abinda ya faru, kuma ba a ɗakin ma ya kwana ba." 


Hanan ta ce, "ƙarya ki ke munafuka, wanne halinki ne ban sani ba? Babu irin abinda bakya aikatawa a wajan aikin ku." 


Islaha ta ɗaga ido, ta harari Hanan cikin fusata  ta ce, "ba da ke nake magana ba, ki ƙyale wacce ta isa da ni ta yi min magana amma ba ke ba. Kar ki ga Mama ta faɗa na yi shiru, ki yi tunanin ke in kin faɗa zan yi shiru. Duk abinda mu ka yi ina ruwanki? Ai mun kai mu yi ɗin ne.”


Mama ta fara tafa hannu tana salati. Sai da ta gama salatin sannan ta ce, "shikenan komai ya ƙare, tunda har ki ka iya buɗe baki haka a gabana, kina faɗawa mai bin mijinki magana abinda nake zargi ya tabbata, babu abinda ya rage wanda baki sani ba. Islaha kin san maza, kin cuce ni, kin lalata min ɗa."


"Ko ya lalata ni ba" ta faɗa ƙasa-ƙasa tana goge idonta. 


Hannan ta buɗe ido ta ce, "Mama kin ji me ta ce? Wai ko ya lalata ba." 


Mama ta miƙe tsaye ta ƙarasa wajan Islaha, tana zuwa kusa da ita ƙhamshin turaren Saheer ya mamaye ta, ta ce, "Ke ɗago ki kalle ni." 


Islaha ta sauke kai ƙasa bata ɗago ba, ba dan bazata iya ba sai dan tana ɗan girmama Maman kaɗan. 


Mama ta ce, "yau sai kin bar gidan nan dan ubanki, ai ba a gidan nan aka haife ki ba ko? Ba a nan aka haifi uwarki ba. Aure kuma tsakaninki da Saheer babu shi, na soke shi!. Bazan bari ki zauna kina cigaba da lalata min yaro ba, dole ki bar gidan ko bakya so. Karuwar banza karuwar wofi, daman daga ganinki ni na san ba mutuniyar kirki ba ce."


Islaha ta ji ɗaci ya mamaye mata zuciya, ta kalli Mama ta ce, "Mama ki daina kirana da wannanan sunan, ni ba karuwa ba ce. Kuma in lalatawa ne sai dai shi ya lalata ni, ba ni zan lalata sa ba. Ban taɓa jin tarihin da aka ce mace ta lalata namiji ba, sai dai shi."


Labiba da ta fito a lokacin ta ce, "ke Islaha! Maman ki ke faɗawa haka? Wacece ke in ba karuwar ba, wacece take kwana a ɗakin wanda ba mijinta ba, faɗa min sunan sunanta?." 


Islaha ta kalli Labiba, ta bita da banzan kallo ta ce, "ke za a tambaya, wannan harka ki ce ba tawa....." 


Maganar ta katse saboda marinta da Mama ta sake yi mata cikin fusata. Islaha ta fashe da kuka mai tsananin sauti, zuciyarta tana zugata akan kawai ta rama. 


Mama ta ce, "ita ce karuwar ki ke nufi?. Tabɗijam! Lallai yau mai raba ni dake a gidan nan sai Allah, sai na nuna miki banbancin tsakanina dake, sai na nuna miki na dame ki a iskanci na shanye. Lokacin da na yi nawa ba a haife ki ba, ba ki san komai akaina ba. Shegiya ƴar gaba da fatiha, wacce iyayenki suka yi cikin ki suka cillar dake. To daman ta ya za a samu tarbiyya a wajanki? Ta ya tarbiyya zata wanzu a wajanki?."


Islaha ƙunci ya mamaye mata zuciya, ta tafi tunanin kenan waɗanda suka girma a gidan marayu dukkansu ba ta hanyar aure aka same su ba? Mutane basa tunanin akwai ƙaddarar da zata iya kawo mutum ciki?. Meyasa ake yi musu kallon waɗanda iyayensu suka haifa suka cillar?.


          "Mama me ya faru.?" 


Saheer ya shigo yana tambaya, yana kallon Islaha da take durƙushe a ƙasa tana kuka. 


Mama ta bisa da harata ta ce, "ka je ka baje jiki, yarinya ƙarama kamar wananan ta gama lalata min kai. Sai da ta san yadda ta yi maka wayo ta bi ka ɗakinka ko?."


Saheer takaici ya kamasa, ya ce, "Mama ni na ce mata mu je ta kwana a ciki saboda bata yanayin jikinta, kuma ni ba a gidan nan na kwana ba, yanzu na shigo gidan."


"Yi min shiru, daman ai baza ka faɗa min gaskiya ba, ɓoye min zaka yi saboda ita ƴar gwal ce a wajanka bata laifi. Kowa ya ga idon yarinyar nan ya san ta jima da sanin maza, kaima gashi ta lalata min kai ban ji ba ban gani ba. Shegen tausayinka na tsiya shine ya saka ka jajubo min ita da sunan amana, har ka ke zancen aurenta ubanka ya goya maka baya...."


"To yanzu na soke, dole ta bar gidan nan dan baza ta lalata min yara ba. Tunda har ta san ta kwana a ɗakin ɗaya da namiji, gwara ta tattara ta bar min gidana."


Hanan ta ce, "ta je can ta ƙarata da gajojin samarinta." 


Saheer ya fusata ya yi kan Hanan zai dake ta, ya ɗaga hannu sama ya ce, "sai na fasa miki baki, dake ake magana?." 


Mama ta ce, "ni zaka daka ba ita ba Saheer, ni zaka juyo ka daka, a nan zan tabbatar da wuyanka ya isa yanka. Ka ga sai fahimci Islaha ta fi ni daraja a wajanka."


Ya girgiza kai yana harararsu Labiba, ya kalli Mama ya ce, "Wallahi Mama ni ba a gidan nan na kwana ba, kuma koda na kwana ɗaki ɗaya da ita babu abinda zai faru a tsakaninmu, domin dukka mu mun san daidai, kuma muna da ilimi, mun san abinda mu ke yi. Dalilina na kai ta ɗakina na san yanayinta, zata iya samun attack. A haka ma sai da na siya mata magani ta sha, saboda sanyin ya shige ta. Don Allah Mama ki bar wannan maganar, ki ƙyale ta ta je ta yi abinda yake gabanta."


Mama ta ce, "Saheer! Yarinyar nan baza ta sake kwana a gidan nan ba, dole ta bar sa tunda ba na ubanta bane!." 


Saheer ya ce, "Don Allah Mama ki daina wannan maganar, ki yi haƙuri. Kin san amana ce a hannuna, ki bari ya sauke nauyin da na ɗaukarwa kaina."


Ta kalli Islaha da kanta yake ƙasa har lokacin bata ɗago ba, ta ce, "in dai nan gidan mijina ne, wallahi sai ta barshi. Ta shiga ta ɗauko tarkacenta tazo ta bar min gida. Riƙon amanar an fasa, aure tsakaninka da ita an fasa, daman ba so nake yi ba. Yanzu na samu gaɓar da zan kafa hujja da ita, bazan bawa ɗana mace irinta ba."


Islaha ta miƙe ta shiga ɗakinta, ba jimawa ta fito da handbag ko kaya bata canja ba ta fita daga falon tana kuka sosai. 


Mama ta bita da kallo baki buɗe, sai ta girgiza kai ta ce, "kutumeleci, ka ga shegiyar yarinya. To kar ki dawo min gida, ki je can Allah ya raka ta ki gona!" Ta faɗa cikin ɗaga murya dan Islaha ta jiyo ta. 


Saheer kamar zai yi kuka ya ce, "Mama meyasa ki ke yiwa Islaha haka? Amana ce a hannuna, meyasa baza ki ta ya ni riƙe amanar ba?. Lokaci kaɗan ne ya rage ta bar gidan gabaɗaya."


"Da kai da amanar zan haɗa na zaga Saheer. Kai! ka fita daga idona na rufe, daman can ba son zamanta nake yi ba, yanzu kuma ta nuna so take ta tafi, sai a ƙyale ta." 


Saheer ya ce, "Haba Mama, itama ƴa ce kamar kowa, baza ki so a yiwa su Labiba abinda ki ke yi mata ba." 


Mama ta ce, "su Labiba marayu ne? Ko a gidan marayu suka tashi?. Kar ka sake haɗa min yara da ita, ta ko ina sun fita, baza su haɗu ba ko a hanya." Ya sauke numfashi bai ce komai ba, ya bi bayan islaha da sauri. 


Labiba ta bisa da harara ta ce, "tabɗijam, gaskiya da sake wallahi. Tun kafin ta auresa ta mallake sa haka? Kalli yadda ya bar ki a tsaye kina magana, ya yi ficewarsa ya tafi wajan ta?. Allah sarki Mama, Hamma yana auren Eslaha kin zama sorry, wallahi ganinsa ma baza ta bar ki ki yi ba."


A fusace Mama ta ce, "ita ɗin banza, Wacece ita? Akwai wanda ya isa ya mallake min ɗa ne? Akwai macen da ta isa ta aurar min ɗa ta mallakesa na zuba mata ido ban ɗauki mataki a kanta ba?. Wallahi babu ita, ba a haifi uwarta ba balle ita."


Hanan ta ce, "to gashi dai Islaha ta fara nuna miki itace da zuciyarsa ba ke ba. Ni na fita, sai na dawo" ta faɗan tana niyar fita. 


Mama ta ce, "ban ce ki kwana a waje ba, in ki ka bawa namiji kanki ban yafe ba. Ki san dabarar da zaki yi ki samo mana kuɗi, amma ban da iskanci." 


Hanan ta kalle ta cike da mamaki, ta ɗan taɓe baki ta ce, "to" ta amsa a taƙaice tana barin falon.


      Saheer a bakin gate ya tarar da Islaha tana kuka, ya yi ajiyar zuciya cike da tausayinta da ƙauna. Ya ɗan sauke numfashi ya ce, "islaha zo mu je mota, akwai motar Sadik a hannuna, zo mu je" ya faɗa yana riƙo hannunta. 


Ta ƙwace hannunta ta ce, "daman kai nake jira ka fito, ni zan je na samu police, a binciko file ɗina in zai yu zan koma orphnage, in bazai yu ba bazan rasa inda zan zauna. Hamma, meyasa ma ka rabo ni da can, ya aka yi na yarda na biyo ka don Allah?. Shikenan duk wacce ta girma a gidan marayu cikin shege aka yi aka haife ta? Babu ƴar halak da ƙaddara ta kai ta can?.”


Cikin harshen fulani ya ce, "ki yi haƙuri, ki zo mu shiga mota." 


Itama cikin fulfulde ta ce, "Aiki zan tafi."


"Kayan jiya ne fa a jikinki."


"Zan shiga wajan Safeera in canja."


"To je ki, ina jiranki a nan. Kawo jakar in riƙe miki" ya faɗa yana miƙa mata hannu.


A sanyaye ta miƙa masa jakar, ya karɓa a daidai lokacin hannatu ta fito. 


Suka haɗa ido da ita, ya ɗaure fuska ya ce, "ina za ki?." Ta kalle sa ta ce, "Mama ce ta aike ni" daga haka ta bar wajan da sauri.


Islaha tana shiga soron gidansu Safeera suka haɗu, Safeera ta bita da kallo ta ce, "Lafiya? Me ya same ki?." 


Islaha ta ce, "Bestie na gaji da zaman gidansu Hamma, na gaji da zagi da cin fuskar Mamansu." 


Safeeraa cikin damuwa ta ce, "me ya faru?." 


Islaha ta ce, "jiyan nan bayan mun rabu ƙin buɗe min ƙofa suka yi, bawan Allah ya kai ni ɗakinsa ya siya min magani na sha, sannan ya fita ya bar ni na kwana a ciki. Ko wanka ban yi ba na koma can dan na shirya na tafi aiki, kin ji irin kalaman da Mama take faɗa min? Wai na lalata mata ɗa."


Safeera ta sauke numfashi ta ce, "wannan mata bata da kirki wallahi. Kuma itace mai zubi da ƴan barikin fa, ni zan tambayi Umma asalinta, daga ganinta ba ta kirki ba ce. Yanzu me ya faru?."


"Tana cikin yi min faɗan ya shigo. Ni na gaji da jurewa, dan in ta cigaba da marina tsaf zan rama, shiyasa na fito. Ni na gaji da zaman gidan, gwara  na koma inda na fito.“


Safeera ta yi ajiyar zuciya ta ce, "zo mu koma ki yi wanka ki canja kaya." Ba musu ta juya suka shiga tsakar gidan Umma tana dama kunu.


Islaha ta duƙa har ƙasa ta ce, "Umma ina kwana." Umma ta kalle ta ta watsar sannan ta ce, "lafiya." Umma ta kalli Safeera ta ce, "ke kuma me ya dawo dake?." 


Safeera ta ce, "Islaha ce zata shirya mu tafi."


"Kamar ya ta shirya, gidan da take babu wajan shiryawa sai a nan?." 


"A'a Islaha! Ke ce a gidan?" Baba ya faɗa da fara’a yana fitowa daga ɗaki. 


Islaha ta duƙusa har ƙasa ta ce, "Baba ina kwana." 


"Lafiya lau, ba ku tafi aikin ba?." Safeera ta ce, "yanzu zamu tafi, kaya zata saka." 


Baba ya ce, "ku shiga ciki mana." Suka wuce zuwa ɗakin Safeera.