Fight for Dignity
by @zahrabmrs02
The Interrogation Room
gari ya waye cikin wani irin yanayi mai cike da fargaba. Jannah ta shirya tsaf cikin wata hadaddiyar shiga ta alfarma, amma domin ta guje wa taron ’yan jarida (Press) dake ta faman kishin-kishin a kofofin waje, ta saka baƙar safar fuska (Face Mask) gami da canza kama gaba ɗaya.
Suna isa, aka bar Amani a can gurin jiran baki (Reception) tana ta faman rarraba idanu cike da fargaba, yayin da aka shigar da Jannah cikin babban ɗakin bincike na sirri (Interrogation Room).
Oga Nura ne zaune a gaban babban teburin, ya sanya aka kawo wa Jannah ruwan sha mai sanyi, sannan ya kalle ta da kwayar idanunsa da suka nuna kwarewa, ya ce:
"Miss Jannah Anderson... muna so ki bamu cikakken haɗin kai a cikin binciken nan. Ki faɗa mana gaskiyar yadda aka yi Mr. and Mrs. Anderson suka rasu a ainihin daren nan."
Maimakon ta firgita ko ta yi in-ina, Jannah ta gyara zamanta cikin tsantsar compose da kuma steez na takama. Ta kalli Oga Nura kai-tsaye ba tare da fargaba ba, ta ce:
"Kamar yadda kuka ji a cikin viral recording (muryar sirrin nan da ta bazu a duniya) wacce agent ɗinku Aliyu ya ɗauka... abinda na faɗa a ciki haka ne ya faru, babu ragi ba ƙari. No need na sake maimaita kaina ."
Oga Nura ya gyada kansa a hankali, yana mai tsananin mamakin yadda mace take da irin wannan juriya da dakiya a gaban jami'an tsaro. Ya numfasa ya ce, "Shi ke nan, Miss Anderson. Shin za mu iya ganin ainihin asalin takardun (Original Copy) na yarjejeniyar ɗaukarki da aka yi a matsayin ɗiya ta halak (Adoption Paperwork) wanda Mrs. Anderson ta sanya hannu a kai?"
Jannah ba ta yi wata-wata ba, ta buɗe haɗarriyar jakar hannunta, ta ciro takardun masu asalin tambari ta ajiye a gabansa.
Oga Nura ya sake matsawa, "To ko za mu iya ganin takardar gadon dukiya baki ɗaya (Will) na iyayen naki, wanda ke nuna cewa ke ce ainihin magajiyar (Heiress) dukkan dukiyar Anderson Global?"
Jannah ta saki wani lallausan murmushi na isa, ta sake fito da babban fayil ɗin takardar gadon ta ajiye a kan teburin.
"Ga shi nan," Jannah ta faɗa . "Wannan ita ce takardar Will ɗinsu. Ga sa hannun Mr. Anderson, ga na Mrs. Anderson, ga nawa a matsayina na magajiya, sannan kuma ga asalin sa hannun babban lauyanmu na kamfani (Lawyer)."
Oga Nura ya zuba wa takardun ido yana duba kowace sa hannu da tambari cikin fargaba da mamaki, domin duka takardun sun fito
, babu alamar bogi
Oga Nura ya gyara zaman gilashinsa, ya kalli takardun dake gabansa, sannan ya dawo da idanunsa kan Jannah cikin rashin wasa. "Duk da wadannan takardun naki sun nuna halaccin gadonki, Miss Anderson, kotu da jama'ar gari suna matsa mana lamba. Don haka, hukumar DSS ta yanke shawarar cewa dole ne mu sake gudanar da binciken gawa (Autopsy) a kan Marigayi Mr. and Mrs. Anderson baki ɗaya domin tabbatar da musabbabin mutuwarsu."
Jin wannan maganar ya sanya Jannah ta ji kamar an soka mata mashi a ƙirji. Ta kure Oga Nura da idanunta dake ta faman kawo ruwa saboda tsananin faɗuwar gaba.
"You mean... gawar su za a tonu?!" Muryar Jannah ta canza gaba ɗaya, idanunta suna wata irin rawa ta tsantsar firgici da fargaba.
Ta tashi tsaye , ta dafe teburin Oga Nura, tana magana cikin rawar murya amma mai cike da uban dakiya:
"Please, don't do this! Wannan ai humiliation (wulaƙanci da cin mutunci) ne a gare ni da iyayena da suka mutu ! Ina da ainihin asalin sakamakon binciken gawar su (Original Result of Autopsy) wanda aka yi tun a baya kafin a binne su, ba sai kun tona mini gawarsu ba!"
Oga Nura ya so yin magana, amma Jannah ta ɗaga masa hannu, idanunta sun kawo ƙwallah na takaici. "If not... idan kuka kuskura kuka tona kabarin mahaifana, wallahi zan kai ka da daukacin hukumar ku ta DSS gaban kotu! Because ba ku da wannan damar ko haƙƙin (Right) a ƙarƙashin doka tunda an riga an yi bincike a baya!"
Jannah ta shaƙi numfashi, tana tuno wahalar da ta sha a baya, ta ci gaba:
"Kowa shaida ne a garin nan, sai da aka ɗauki tsawon mako biyu cif (2 weeks) ba a binne su ba bayan rasuwarsu! Ana ta faman gudanar da bincike kala-kala na kowane fanni a kan gawarwakin nasu kafin aka ba da izinin binne su! Ba zan taɓa barin ku sake wulaƙanta su a kabari ba
Oga Nura ya yi shiru, yana kallon yadda Jannah take huƙi da kishin iyayenta, lokacin guda yana auna gaskiyar kalaman muryarta da kuma takardun da ta ajiye a gabansa.
Oga Nura ya jingina da kujerarsa a hankali, ya kalli Jannah dake ta faman sauke numfashi na zafin kishin iyayenta. Ko kaɗan bai nuna alamar tsoro ko fargaba da barazanar kotu da ta yi masa ba, face ma wani sanyayyan murmushi na jami'an tsaro da ya subuce masa.
"Zaki iya tafiya, Miss Anderson," Oga Nura ya faɗa cikin muryar dakiya dake ratsa dakin.
Jannah ta ja ajiyar zuciya ta juya zata ɗauki jakarta, sai kuma kalaman Oga Nura na gaba suka sanya ta daskarewa a gurinta.
"Amma ki sani... remember bamu gama bincike ba gaba ɗaya," Oga Nura ya ci gaba da magana yana nuna ta da biro. "Don haka, baki da wani ikon doka ko haƙƙi (Right) na barin ƙasar har sai mun kammala daukacin bincikenmu . Sunanki yana nan daram a jikin jerin mutanen da aka hana fita waje."
Jannah ta juyo a hankali, idanunta suka sauka akan Oga Nura, fuskarta babu alamar tsoro sai dai kallon dake nuna tsantsar izza.
Oga Nura bai fasa ba, ya ƙara daddale mata gaskiyar lamarin: "Kuma duk lokacin da muke buƙata (anytime), zamu iya aiko da jami'anmu zuwa cikin babban Penthouse ɗinki ko babban kamfanin Anderson Global domin gudanar da bincike na kwatsam . Ki tabbatar kina gari."
Wani sashe na jikin Jannah ya so ya harzuƙa, amma da yake mace ce mai mugun ikon sarrafa fushi da sanya steez a gaba, sai kawai ta dake. Kalma ɗaya ba ta ce masa ba (kala jannah bata ce ba), ba ta kuma amsa barazanar tasa ba saboda ta san cewa nuna damuwa tawaye ne ga jarumtarta.
Ta juya cikin takunta na takama da izza, ƙofofin takalmanta suna amsa amon mulki a cikin ofis ɗin, ta nufi hanyar fita gaba ɗaya ba tare da ta waiwayo ba.
Tana tura ƙofar fita, ta iske Amani tana ta faman kai da kawowa a reception gumi na tsatstsa mata. Amani na ganin ta, ta rugo da gudu ta riƙe hannunta, "Jannah! Me suka ce miki?! Lafiya dai ko?"
Jannah ba ta ce komai ba, sai kawai ta gyada mata kai alamar su fita. Suka jera cikin sanyin jiki suka nufi elevator don barin babban ginin hukumar DSS
To my lovely fans Allahuma bareek for all the love jannah yar gidan Anderson is getting the love is massive thank you guys 🥰
Another free page for appreciation